Author : Queenmerh Category : Complete Novels
ban sameka ba zan iya rasa raina, ina kishinka, banason kowacce mace ta rabeka, banason kowa ya rabeke,”
Shi courage dinta ne ma da futsararta yafi bashi mamaki, tashigo har cikin dakinta ta kalli cikin idanunsa sannan tace wai tana sonshi? Unbelievable to him.
“Ya kamata ace ka gane hakan,tunda na sanya idanunka akanka ka shiga zuciyata, ive been longing for you, i hate seeing you smiling to someone else shiyasa na tsani wannan shegiyar yar aikin, banason ta rabeka, banasonta kusa dakai don kafi karfin hada nunfashi da inuwa daya da ita,“
Ay tunda ta fara magana ranshi bai gama ba ci sai yanxu data ambato sabeeha, saiya tuna da abunda ta masu dazu kan dining, wanda hakan ya bata mashi rai sosai ba kadan ba.
Tana kokarin yin magana ya daga mata hannu daya, sannan ya mata nuni da kofa,ko matsayin ya amsata bata samu ba, maganganunta a banza, take taji wani abu ya chaketa a zuciyarta kamar zata hadiye zuciya don bakin ciki, “meysa kake sakema wacchar yar iskar yarinya fuska? Menene tsakaninka da ita???”
Sai a lokacin ya iya bude bakinshi don da farko baiga yanada time din bata amsa ba sai yanxu.
Calmly yake magana don bayason loosing steezs dinshi yace “this should be the last time zakiyi questioning dina, ni sa’anki ne? Are you insane?????and the next time naji kin kirata da yar iska..” ya wani cije lebe kafin ya mata nuni da kofa “outtt!!!”
Wannan magana dayayi ba karamin hargitsata yayi ba, ta kara tabbatar da dakyar ne idan bason yarinyar nan yake ba abunda take gudu kenan, inva haka ba me zaisa ta ga kafafunshi kan na sabeeha don wallahi kiri kiri taga kafafunshi kan na yarinyar yana yawo dashi, dazun ta rasa yanda zatayi ne yasa ta juya maganar kan cewa ay sabeehar ce ke flirting dashi, saita tuna sanda ranar nan da sabeehar ta futo daga part dinshi a firgice har sukayi fada a compoud ita da sabeehar, wannan yarinya ta tsaneta kamar ranta,tsana mafi tsanani kuma wallahi bazat ataba bari tayi loosing Dinshi to her ba, yar aiki, yar shege, yarda bata da uba, mara gata…inaa bazai yuwu ba.
A kausashe ya sake daka mata tsawa dis time around da dan karfi yayi “i said out!!!!!”
Kukan datake kokarin matsewa ta kasa, tafarfasa kawai takeyi, tana jiyoshi yace “what sort of rubbish” kafin ta fuce, ay idan bata fitar da yarinyar nan daga gidan nan ba a gobe toh ba a haifeta da cibiya ba, saita wulaqantata.
A harzuke ta wuce part dinsu, tana shiga bangarenta ta rufo kofar gam sannan ta bude handbag dinta, ta zaro wasu kwayoyi, batama tsaya duba ko nawa bane kawai ta watsa bakinta, gaba daya sannan ta nufi wajen dressers dinta ta wawatsa kayaj wajen gaba daya suka fashe a kasa ta soka ihu…..”
8pm
Misalin karfe takwas bahijj ta shigo gida, gaba daya jikinta a mace yake, idanunta yayi jaa sosai, ga wani matsanancin ciwon kai datake ji kamar kanta zai rabu gida biyu.
Basira na bude mata kofa ta mata sannu da zuwa ta amsa sannan ta tambayi maya, nan basira ta shida mata tana sama dakinta.
Ko ta kan abuncin da basira ta sauke batabi ba ta nufi sama, zuwa ga dakin maya, tana isowa ta murda kofar taji a rufe tayi knocking “baby!!!”
Shuru babu reponse tana kokarin sake knocking call ya shigo mata tana ganin sunan majeed ta daga wayar sannan tabar bakin kofar zuwaga bedroom dinsu.
Tana shiga ya shaida mata zai danyi dare saboda ya shiga kaduna, batasan maiya kaishi ba amma dai bata kawo komai aranta ba wannan yasa tace “allah ya kiyaye” sannan ta kashe wayar, tana kokarin aje wayar gefen bedside idanunta ya sauka kan hannunta inda aka deba jininta daxu a asibiti.
Maya fa na chan kwance an shawu, gaba daya ta gama zama high don tayi over over dosing kanta just to relieve abunda ke ranta, ko lokacin da bahijja tayi knocking kofar already tayi knocking out batasan inda kanta yake ba.
Bangaren taj futa yayi daga gidan yaje asibiti bai dawo ba sai dare, sabeeha ko kwana tayi gabanta na faduwa, haka kawai ta rasa natsuwarta gaba daya.
***
Ana idar da sallar isha’i jamila ta shugo gidan a gajiye, da jamilu taci karo dayayi bake bake a tsakar gida, jiranta dawowarta kawai yake, don ya kasa gane mata cikin kwana biyu, wani irin zubabban wulaqancin take shirgawa, zata futa sanda taga dama ba tare da ta nemi izininsa ba da zarar yasa kafa ya futa sannan kuma ta dawo a lokacin dataga dama.
Kallo daya ta mashi ta kauda idanunta zata nufi uwar daka ya dakatar da ita.
“Daga gidan ubanwa kike??? Wato yawon ta zubar din naki kika koma?? Ehhh””
Wani irin izgilallan kallo ta mashi ko kunyar yayansu da sukayi zuru zuru suna jiran dawowarta bai jiba,
Tsakin nan datayi ne ya kara harzuka shi yace “kutmar ubanchan, ina maki magana kina min kallon dan iska??? Toh na rantse da allah inda kika futo zaki koma, kai nima dai lusari ne wallahi, daman ya za ayi nayi tunanin bazaki koma rayiwarki ta da ba??? Waye baisan sheqe ayar da baki ba a baya, wato yanxu nayi sanyi shine bari ki fara satar hanya ko??? Toh billahillzi…”
“Dallah rufe min baki munafiki annamimi, matsiyaci, har kanada bakin magana? Har kanada bakin magana jamilu??? Toh bari kaji wallahil azeem ka bini a hankali don wallahi azeem kasan niba kanwar lasa bace, kabarni kawai yanda ka ganni,mtewwww”
Ta doka tsaki tana mashi wani irin kallon tsana,
Tana fadin haka ta shige daki, a harzuke ya bita dakin kamar zasuyi dambe yace “ni kike kira da munafuki matsiyaci???”
“Kwarai kuwa, na hada da tsinanne ma duka”
Tass taji saukar hannunshi kan fuskarta batayi wata wata ba tana dagowa ta wankeshi shima da mari hau sau biyu,tuni yasha jinin jikinshi idanunta sunyi jaa sosai, “fita na sake ki”
Yana fadin haka ta kyakyace da dariya tana kallonshi tace “saki na shida kenan, ay bari kaji ni jamila bazan taba sakuwa ba, saidai idan da kafata nace banayi, kuma inka kwantar da hankali lokaci na zuwa da zan tattara yayana na kara gaba amma kafin nan saina tabbatar na wulantaka da wacchar tsinanniyar tunda har kukaci amanata kaida ita”
Tana kaiwa nan ta wani jawo colar rigarsa yayo gaba yuu, gashi daman a bushe, wallahi jan ido yake mata amma yasan tsaf zata iya masa shegen duka don jamila badai karfi fa, gata yar bala’i, shima kanshi baisan yanda akayi duk abubuwan da yake mata take chanyewa ba ashe ashe, “wallahi wallahi in kaga na hkura da cin amanata da kukayi saidai idan bana nunfashi, kai kasan wacece jamila basai an fada maka ba, ni jamila da bala’i ma an ganni an barni, daman na fada maka duk abunda zakayi karka sake ka kaini bango, albarkacin yayan ka kawai kakeci nake daga maka kafa amma wallahi wallahi….” Hmmm ta cije lebe har zuwa lokacin hannunta na chakume da corlar shi, wallahi gaba daya ya gama tsorata, gabansa ko faduwan da yake allah kadai ya san yanda yake bugawa, ta wani bangajeshi ta wuce uwar daka tana huci.
Ayfa jamilu tunda ya fita daga gida bai iya dawo wa ba sai wajen karfe sha biyu, gaba daya ya tsorata da jamila, daga cikin maganganunta ya gane ashe ta gano cin amanarta da sukeyi da hadiza, amma shine tayi shuru bata nuna ba? Chap akwai kura, yanda tayi rantsuwar nan yasan wallahi bazata barsu ba, shiko yasan hatsabibbancin jamila, zata iya komai wallahi.
Da kyar dai ya dawo gida don bashida wajen kwana ya kwana dakin yayansa su kuma ya turosu parlor, duk zarnin dakin nan haka ya kwanta a ciki don taoron da yakeji kar saiya rufe ido ta luma mashi wuka don kamar yanda tace zata iya komai gwara ya lallabata da safe ya bata hkuri ya nuna mata ay hadizar ce ke bibiyarsa, bada son ranshi ba.
Idan ya rabu da jamila ay ya shiga uku, ay gaba daya yama manta cewa gidan da suke ciki ma nata ne, har yana wani ihun ta futa ya saketa bayan wannan ma mutanen da ya zalumta a anguwar nan ay bazasu barshi ba, ga yaran dayayi ma ciki saboda jamilar tayi rufa rufa an danne komai idan ta tabe masu ay ya shiga uku, ay dole ya lallabata ya mata dadin baki.
Washe gari da asubar fari sai gashi ya tashi, ya share tsakar gida harda dora ruwan wanka, itako barcinta tayi cikin kwanciyar hankali.
Sai wajen goma ta tashi, lokacin yaran duk sun tafi makaranta, yawanci daman suke tashinta neman abun karo, yauko babu wanda ya shugo dakin saboda ya basu dari biyu sun sayo koko da kosai sun karya dashi.
Tana tashi ta fito tsakar gida, ta deba ruwa tayi lafiyayyan wankanta kota kanshi batabi ba, ta hada tea mai kauri da bredi taci harda soyayyan kwai.
Tana gamawa ta shirya cikin wata farin lace, kwalliya fa taci abunta fess fess ta dambara jan baki sannan taci daurin ture kaga tsiya, tana gamawa ta futo da jakarta a kafada, kai kaga jamila kace gasar kyau zata tafi, tayi kyau abunta.
A tsakar gida ta taddashi yana shara, abunda zatace bai tabayi ba tunda sukayi aure, aurenda tun shekaru hudu da suka wuce igiyoyin suka tsinke gaba daya amma ake zaune kamar jahilai.
Jakarta ta bude ta dauko chewing gum har biyu ta bare ledar ta watsa baki sannan ta tauna sautin ya bada qass, kota kanshi bata bi ba ta nufi kofa yayi saurin dakatar da ita.
“Jamila…”
Chak ta tsaya tana mashi wani wulaqantaccen kallo, “jamu dan darajar allah kiyi hakuri, ki yafe min , wallahi ba laifina bane, laifin wannan tainanniyar ce,na rantse da allah bana cikin hayyacina ba ason raina bane sharrin shaidan ne, daman saida na fada mata ni bazan iya cin amanarki ba jamu…”
“Kaga dama ka daina bata bakinga da yafi maka, dan wannan a banza, ni ganau ce ba jiyau ba, munafuki, da idanuna na kamaku turmi da tabarya kuna iskanci, a gidana a dakina, wato gani wawiya ko? Kum shafe shekaru kuna cin amanata,toh wallahi ka sani, na rantse da allah saina dau fansa, yanxu zanje na fara da ita, ka jira naka hukuncin, ka gama yawo jamilu wallahi, karkayi tunanin wai zaka iya guduwa, duk inda kaje saika dawo da kafarka wallahi, don kana tafun hannuna jamilu, yauwaaa”
Tana fadin haka ta tofar da miyau taja mayafinta dake yawo a kasa, “jamila…jamilaaa..!!”
Ya soma kiranta hankali tashe, innalillahi shikenan zata tona mashi asiri, gaba daya ya gama rikicewa.
The santuraki’s…
Monday morning.
Bayan sallar subh bahijja ta futo daga bedroom, babu inda ta nufa sai dakin maya jiki a mace, jiya sai wajen karfe sha daya dady ya dawo, so basu samu damar yin maganar datakeson yi mashi ba sai bayan sallar asuba, koda ta tunkareshi da maganar, saiya nuna kamar baiyi naam da maganar ba, musamman data shaida mashi anne bata bada amincewarta ba, shima dai akwai abubuwan daya hango, wanda yake ganin zai iya zamo matsala musamman tsakaninta da anne, tunda daman har zuwa yanxu bata gama gyaran muamalarta da mahaifiyar tata ba.
Ita bahijja gani take duk sun kasa fuskantarta, don ita datasan halin da mayan ke ciki da yanda ta nuna tana son taj idan har ba’a hadasu ba akwai matsala, tunda har ta nuna tana son auren gwara kawai a mata, don shine kawai solution.
Shi ta bangaren shi yana nusar da ita rashin amincewar anne babbar matsala ce, idan har ta qi to dole tana da kwakwaran dalili, sannan secondly idan maya na sonshi shi yana sonta ne?,
Rasa answer da zata bashi tayi, don tabbas ita tafi kowa going against auren hadi, amma gashi yanxu ita ke son ta hada, duk kawai saboda farin cikin mayan, tabbas tasan abun da son kai amma dai gani take batada solution daya wuce ta hada mayan da taj din, tunda dan uwanta ne, jininta ne.
Haka dai suka rabu suna jayayya akan maganar, ta futo daga bedroom din cikin bacin rai.
Koda tazo part din mayar taji kofar a rufe again sai hankalinta ya tashi ta soma knocking, shuru babu response, tuni gabanta ya soma faduwa, ta sauko kasan wajen basira data futo gyaran part din.
Bayan ta gaisheta ta tambayeta kamar haka “tun yaushe rabonki da maya?”
“Bayan kin fita naga ta futa zuwa cikin gida sai kuma ta dawo ta wuce sama, tun daga lokacin dai bata sauko ba”
Bahijja najin haka ta koma sama, nan ta shiga knocking a hankali gudun kar dady yaji, “maya!! Maya!!!”
Ta soma kiranta, jin shuru yasa ta soma dialing number ta, ga ringing dai tana ji amma shuru daga dakin, tuni hankalinta ya tashi, gashi extra keys na bedroom dinsu, batason komawa kar dady yayi suspecting wani abun, dole haka ta cigaba da knocking.
Ahankali ta soma bude idanunta, ba itace ta farka ba sai wajen takwas ta gifta, ba sallah ba salati, knocking din dakinta ne yasa ta farka, tuni ta miqe da sauri gabanta na faduwa, idanunta yayi jaa sosai kana ganinta kaga wadda ta jima tana barci, motsin budewar dataji ne yasa ta fara tattara nastuwarta, hade jikinta waje guda daman a kasa ta mangare, ana bude kofar kawai ta fara kukan munafurci kasa kasa, cikin sauri bahijja ta shigo dakin gaba daya hankalinta a tashe yake, bata samu daukan keys din dakin ba saida ta sallami daddy ya fita, tabbas a lokacin data dunga knocking babu response jikinta ya bata maya tasha wani abun, don babu yanda za ayi ayita bugun kofa kamar haka bataji ba, kuma tana cikin dakin.
Tana ganinta zaune ta hade jiki kuwa tayi saurin rufe kofar dakin ta shugo zuwa inda take, duk abunda maya keyi da bai dace ba duk yanda bahijja taso ta mata fada kasawa takeyi, ayau kam data tabbatar ta sake shan wani abun ranta ya baci sosai ba kadan ba don ta mata alkawarin bazata sake ba.
“Maya!!!!!, Bahijja ta kira rai a bace, ahankali maya ta dago da fuskartar datayi jaga jaga da hawaye harda majina, ga idanun nan yayi luhu luhu kamar wadda ta kwana tana kuka, tuni gaban bahijja ya fadi damm!!!
A shagwabe maya tace “mummy…mummy” sai tayi luu kamar zata fadi bahijja ta taimaka mata ta tashi zuwa kan gado, “mummy uncle taj…”
Ta dan dakata tare da fashewa da kuka sosai,
“Menene?? Meya faru? Have you been crying all night? Meysa?”
Girgiza mata kai maya tayi kamar munafuka ita bahijj sai tayi tunanin ko tun maganar jiya ne yake damun mayar, wannan wani irin so maya ke ma wannan bawan allah? Bahijja ta fada a zuciyarta.
“Mummy wallahi banason uncle taj yaso kowacce a duniyar nan bayan ni, zuciyana yana min zafi yana min ciwo, wallahi ina sonshi, banason na rasashi”
Ko irin kunyar nan wallahi maya bataji ba, ita gani ma take komai normal ne, kuma idan tayi pressuring mummyn nata dole ace ya aureta dole ta sameshi.
“Ya isa maya, wayace zaki rasashi? Insha allah shine mijinki na sunna, indai ina raye taj mijinki ne da yardar Allah, ki kwantar da hankalinki, kinji ko” tana karashe tana jin tausayin diyar tata
Kauda fuska maya tayi ta wani sauke wani makirin murmushi, kafin ta juyo ta sauya fuska ta dubi mummy nata sannan ta rungumeta “thank you mummy, thank you for supporting my choice, insha allah bazan baki kunya ba”
“Meysa kikaqi bude min kofa? Did you take something??”
“No mummy,ay na maki alkawari bazan sake ba, na kasa barci ne da daddare sai wajen subh na iya barci banma san nayi ba, mummy zanci special pancake dinki please”
Badan ta yarda ba kawai tace mata “okay tohm freshen up saiki sauko kici”
Tana ganin futar mummyn nata ta tashi tsaye, gaba daya abunda ya faru jiya ya dawo mata sabo fil, a yau yau dinnan yanda ta rantse saita futar da sabeeha daga gidan nan saita koreta.
Acahn main house ko yau an tashi da murnar dawowar anne gidan bayan wata uku da suka shafe a asibiti tana jinya, su rabi sai faman hada hada akeyi, kusan ma tare suke komai ita da sabeeha wadda gaba daya tsakanin jiya da yau ta rasa sukuni,gabanta sai faduwa yake.
Hadiza dake zaune daki batasan meke faruwa ba a cikin gida, tunda ta tashi sukayi waya da jamila ta shaida mata ay tana nan zuwa ta kasa sukuni, allah allah kawai take tazo ta mata bayanin yanda sukayi da malamin, don itama ta matsu kawai taga yarinyar nan bata gabanta.
Tana cikin safa da marwa a daki Misalin wajen karfe sha daya kuwa saiga wayar jamilar ta shugo, cikin sauri ta dauka tare dakaiwa kunne, “kin qaraso ne?”
Daga chan jamila ta amsa “eh ina bakin gate, waennan mutanen naku ba barina zasuyi na shigo ba kizo ki shiga dani”
Batama tsaya bata amsa ba ta jawo mayafinta ta aza aka sannan ta futo da wayar a hannunta, ta kofar baya ta bi, sabeeha da rabi dake kitchen suka bita da kallo sabeeha ta dan duqa zata gaisheta ko kallon inda take batayi ba ta fuce, rabi ta kalli sabeehar, sai kawai ta girgiza kai, har zuwa yanxu mamaki take game da maganar da jamila ta fada mata jiya.
Yanxu daman wannan ba yar hadiza bace???” Ta fada aranta, “no wonder shiyasa take yi mata abubuwa, babu kusanci batama damu da ita ba kwata kwata, amma…
“Anty rabi!!!”
Sabeeha ta katse mata tunaninta tana kallon yarinyar tausayinta na ratsata, “yana zubewa” sabeeha ta mata nuni da ruden tuwon da rabi keyi. Rabi tayi saurin rage wutar, suna cikin aiki kawai sukaji sallama, rabi ta juyo da mamaki tana kallon jamila, itaka jamilar kallonta take sai kawai ta waske tana dariyar yaqe, “sannunku da aiki”
Sabeeha ta dan duka tace “ina wuni”
Ganin hadiza na kallonta yasa jamila yatsine fuska kamar batason amsawa tace “lafiya”
“Muje ciki” hadizq ta fada tana yin gaba, mamaki ya cika rabi, lallai wannan katuwar munafuka ce, kamar ba jiya tazo ba tana neman Alfarma ta kaita wajen anne, koda ta tambayeta meysa saita fada mata cewa rayuwar sabeeha na cikin hadari, kuma yarinyar ba yar hadiza bace, sannan akwai wani boyayyan al’amari game da yarinyar wanda take ganin zasu iya taimakawa su kubutar da yarinyar daga cikin makircin hadiza, don hadiza fuska biyu ce, ayanda ta fada mata wai kamar wani dan iska take son ta aura mata dan shaye shaye, babu irin maganganun da bata fada ba kan