Advertisements
Chapter 45 Reading Matar Taj Book 2 Complete Hausa Novel Hausa Novels
Advertisements

Matar Taj Book 2 Complete Hausa Novel

Author :  Queenmerh Category :  Complete Novels

Chapter   45 / 107

132K to 135K   out of 320.4K words

time ya kure, wayanshi ta soma kira baya dauka.

Chan taj baibar wajensu khaal ba saida yayi wata doguwar magana da mutallib, sannan ya roki karya bari khaal yasan da zancen don bayason hankalinshi ya tashi kwata kwata.


Bai kwana gidan ba don yasan fadwa zata iya takurashi kuma yanxu babu wani amfani da zatayi mashi, she’s useless to him don ya samu abunda yake nema.

Wasu yan ayyuka yayi qalilan a laptop dinshi kafin ya kwanta wajen karfe uku, lokacin sallar subh ya tashi yayi sallah ya koma bashine ya farka ba sai wajen karfe goma,baiyi tunanin zaikai har zuwa lokacin ba, yana duba wayanshi yaga missed rututu kamar yaqi.

Number mutallib yafi yawa wannan yasa ya soma
Kiranshi don duk a tunaninshi ko wani abu ne ya faru, yana dagawa ko gaisawa basuyi ba mutallib yace “kaga news?”
“Meya faru?”
Shuru mutallib yayi chan yace “ka duba wayanka, gaba daya news…”
Bai jira sauraronsa ba ya bude wayar ya duba, yayi mamaki matuqa sosai don baiyi tunanin hidaya can go to this extent ba, rubutu ne akayi kan cewa shi ba dan halas bane, kuma ba a taba ganin mahaifiyarshi ba, an kawoshi gidan ne, so akwai possibility din shiba jinin taheels bane.
Jefar da wayar kawai yayi ya shiga bathroom ya watsa ruwa ya shirya sannan ya futo.
Bai tsaya ko’ina ba sai taheels, tunda ya fito aketa binshi, ra’ayoyin mutane baka iya masu jiya sunata tausaya mashi halin daya shiga, yau kuka kallon wani abun kyama suke mashi,koda ya wuce sama ya tafda merk harya iso yana jiranshi ya shaida mashi ana board meeting.
Yana shiga duk suka dago suka kalleshi, yana kallonsu ga hidaya zaune taci wani jan jambaki tana kallonshi.
Kujera ya samu ya zauna yana kallonsu suma kafin daya daga cikinsu ya soma magana , “with the news da mukayi receiving, zamu dakatar da sauyin chair leader, untill further notice”
Suna gama jawabi suka fita bai dakatar dasu ba saiya rage dagashi sai ita, “that’s a fantastic move mrs hidaya”
Miqewa tayi ta fuce “this is just the beginning taj”

Bugun table din gabanshi yayi ya miqe tsaye ya fuce daga office din, daidai nan call din fadwa ya shugo yayi ignoring ya wuce office yana shiga ya ganta zaune, tayi saurin karasowa inda yake tace “you most be upset ko,”
Bai kulata ba ya zauna mazauninshi ta dubeshi tace “i have something for you,”
Dagowa yayi ya kaleta ta zagayo inda yake tace “ ta hanyar nan ne kadai zaka samu avunda kake so…,
“Just go straight to the point”
“Khaal…khaal bai sa anyi kidnapping dinka ba sannan duk slush funds din da akace yanayi ta karkashin kamfani an juya komai ne don hidaya ce keyi, ita ta juya komai saboda khaal ya gano duk sirrikanta, wannan yasa ta fiddashi daga cikin lissafi don yana neman kawo mata matsala”

“Ya akayi kika san da haka?”
Takardun ta aje mashi gabanshi tace “saboda dani akayi plans din komai,”
Haba wa she messed up big time bata sani ba,
“Tare kukayi plans din kenan?”
Sai a lokacin ta lura da abunda ta fada, “at the end of the day kuma kukayi kidnapping dinshi kukayi fabricating mutuwarshi, kuka wulaqantashi, kuka maidashi prisoner ku dukda saboda karya kawo maku matsala?”
Wallahi batayi tunanin ta kwafsa ba sai yanxu, gaba daya saitaga taj din ya sauya an koma gidan jiya, ya akayi ya san khaal bai mutu ba? Ya akayi yasan komai how? Khaal, Na hannunshi kenan? He hid him kenan?”
Tana tunanin zata iya manipulating dinshi ta matso kusa dashi har tana kokarin rungumeshi ya wani irin bangajeta ta fadi kasa “ke atunaninki zan taba yarda dake ko? Toh kinyi kuskure, kece mace ta farko dana tsana kaf rayuwata, ina maki tsana mafi kyama tun daga ranar da kika bayyna dirty mind dinki, and you expect me to trust you bayan kinci amanar yar uwarki? What makes you think bazan yarda zaki cuceni ba nima, kina tunanin you can play with me? You’re not that smart fadwaaaaaa”
“So you used me don ka samu abunda kake nema?”
“Yes and dayake you’re the dumbest person you fell for it,“
“Kayi kuskure taj, kayi kuskure, you’re playing with fire, da bakayi kuskuren using dina ba,”
“Get your stinky body out of my office”
Juyawa tayi idanunta yayi jaa sosai tace “you’ll regret this”
Ta fuce afusace.
Tana futa office din hidaya ta wuce, tun kafin ta shiga ta bada umarnin kar wanda ya shugo.

Merk ya kwankwasa mashi kofa tare da waya a hannunshi ya kalli taj yace “ she fell for it sir”
Murmushi taj yayi yace record everything karka bar komai.
“Yes sir ya amsa shi sannan ya futa.
Shi kuma ya fiddo da wayarshi daya saka record tunda ta ce mashi she has something for him, duk conversation din saida ya nada gaba daya, chan office din hidaya ma basu san cewa secretary dinta yayi planting wani device ba a office din duk conversation dinsu anaji.

Yanda ta shugo saida yasa hidaya kallonta da kyau don kamar ta zauce, “let’s finish him, its high time, ya zame mana babbar barazana, you can have the company all to your self, i don’t need anything I just want him to be miserable”
Sun dade suna tattaunawan su ta futo ta shiga motarta tana shiga ta soma dialing number datayi saving da papii ana dagawa ta soma magana “papiiiiii” sai hawaye
Daga chan aka soma Magana “who ever is the reason behind your tears bazai taba samun kwanciyar hankali ba now tell me me kikeso my princess”
Share hawayenta tayi tace “khaal Na hannunshi, i want both of them dead, banason na kara ganinsu suna nunfashi” saita kyakyale da dariya, “consider it done”
“But papi hold on, lets use our methods okay, hitting 2 bird with one stone i love it that way”
“Sure darling”
Murmushi tayi tare da kashe wayar ita kadai tasan abunda takeji aranta, dole ta watsar da matsalolinta biyu a rayuwa, which are Tajudeen and khaal, for hidaya kuma she will Come for her don tana tafin hannunta already sai yanda tayi da ita, gaba daya sirrikanta ta gama saninsu, at anytime zata iya cireta daga lissafi.

She regret yanda akayi stupid zuciyanta ya kusa cutar da ita, she will be satisfied only if baya nunfashi, she can’t have him right? Okay then menen amfaninshi a doran kasa kenan? Babu!! Kai kota sameshi dole saitaga bayanshi, don kiyayyar da hidaya ke mashi wasa ne, yayi sanadiyar mahaifiyarta mafi soyuwar mahaifintaaaaaa Abdul-basit


Wai chakwakiya…the most awaited reveal of fadwa’a real identity……


✊💋BOSS LADIES WRITERS💋✊

MATAR TAJ (destined with you🩵🤍)
Written by
Queenmarh✍️
Book2
PAID
Chapter 87
Fadwaaa….fadwa yace ga abdulbasit, mafi soyuwa a gareshi, his only happiness, babu abunda zata nema a duniyar nan bazai bata ba, he gave her the whole world and power.
She is the result of the affair daya shiga tsakaninshi da mahaifiyarta, mahaifiyarsu bata taba son taheel ba, she experienced obsessive love with abdul basir taci amanar taheel kuma da auranta akanshi ba tare da sanin kowa ba, its a bloody affairs daya shiga tsakaninshi da ita,she fell for him harder to the point that she gave him everything, itace silar arzikinsa dukda taheel ne ya kawoshi kamfanin.
Haramtacciyar soyayya mai tsanin sukayi na tsawon shekaru da dama, and she made sure that asirinsu bai tonu ba, babu wanda yasan da mu’amalar su, duk wani arzikinta data mallaka a boye ta sakashi karkashin sunan abdul basit, har takaiga aikinshi karkashinta ta maidoshi, very close to her in her obsession.
Lokacin data gane tana da cikin fadwa, dagashi har ita sunyi farin ciki sosai ba kadan ba, don tasan tabbas cikin nashi ne, she was hoping ta haifa da namijin da zai gaji kamfanin,kuma da wanda takeso wato shi basit din, shidai the fact that tana dauke da cikinshi he have already achieved what he wants, and he was so happy yaga jininshi.

Bayan ta haifu da wannan burin taga akasin haka, she was so disappointed, basit never cared don shi diyarshi kawai yakeso, a wannan lokacin ne suka samu babban misunderstanding donta nuna bata wani damu da haifuwar datayi ba don namiji taso, shi kuma a lokacin yakeson karbar diyarshi, which can result to tonan asirin su, it was a tough moment for them har suka dawo in conclusion of idan har ya karbi fadwa aisirinau zai tonu and she wants what is best for her children, bazai taba yuwu wa bq asan fadwa ba jinin taheel bace,
Saida ya zauna yayi nazari ya gane duk abunda take hango masu harma wanda bata gano ba, ya dauka babban buri akan yarshi, he wants her to have everything, da kamfanin taheel din gaba daya ma.
Wannan yasa ya barta watching her from far, amma ya buqaci kusanci da diyarshi.
Bata hanashi ba don duk sati haka zata dauka fadwa tun tana karama ta fita da ita zuwa office ya samu quality time da diyarshi, tun yarinyar bata mallaki hankalinta ba, kuma sabo ya shiga tsakanin su sosai, lokacin data lura fadwa na girma sosai kuma zata iya fuskantar wani abu nan ta dakatar da kusancin, nan ma sun samu misunderstanding sosai shida ita, it was very hard for him to accept it, kuma he made sure that yarinyar ta shaku dashi sosai.
Second encounter dinshi da ita baima bari fattu ta sani ba, kuma yayi nasara sosai don bata mance dashi ba, he gave her everything, he makes her happy sosai lokacin teenage age dinta da adult age dinta.
Duk wata damuwarta shine a farko, fattu bata san da wannan ba sai daga baya, kuma ranta ya baci sosai don taso ta rabasu ta karfi da yaji gudun kar asirinta ya tonu, dake babu wani kusanci sosai tsakaninta da fadwa wannan yasa fadwar taji zafin abunda maman nata ke shirin yi, daman gashi ta taso da ganin yanda take bala’in son hidaya fiye dasu, wannan Yasa ta soma questioning dinta.
Fattu wants wat is best for her children kuma burinta na kan taheel company, bata bari soyayya ta rufe mata ido ba, don son abun duniya ya wuce soyayyar da takema basit, kuma bazata so wani abu ya ruguza mata dogon burinta ba wannan yasa ta karfi da yaji ta raba shi da fadwa dukda alokacin ma fadwa batasan aina’hin mahaifinta bane, wannan ya jawo babban misunderstanding tsakaninsu shida ita wanda hakan yasa dole yabar kasar gaba dayanta.
Abunda bai saniba shine, koranshi da akayi daga kamfanin da akayi ba kowa bace fattu ce tayi hakan saboda akwai mutun daya daya san abundake tsakaninsu, kuma zai iya zame mata barazana a gaba wannan yasa ta san yanda tayi korar ta fito daga shi kanshi abdullah taheel.

an sami basit da laifin daukar sirrin babban project din kamfanin ya saida ma wasu a market, kuma hannunshi ya futo dumu dumu a ciki, kora an mashi kora ta wulaqanci don babban laifi ne har hukuma tazo tafiya dashi fattu ta hana aka barshi ya tafi, agabanshi ta nuna batada yanda ta iya, and he understands her amma tayi alkawarin she will continue to love and support him kuma zata bashi duk abunda yakeso, nan ne mafarin qiyayyar taheel da basit.Kuma duk arzikin dayake dashi ta karkashin taheels company ya samu da taimakon fattu.

Bayan wasu yan shekaru mutuwar fattu ta riskeshi, Mutuwar tazo mashi a bazata ya shiga yanayi mai tsanani, yasota kamar hauka, don ta kasance mace ta farko data bashi farin ciki ta haifa mashi jininshi, saidai bashida damar zuwa yi mata ganin karshe, kuma bashida damar karbar yarshi.

Bai sake dawowa kasar ba sai bayan shekaru goma sha, yayi arziki sosai kuma ya shiga irin business field din taheels, ya zame masu babban competitor duk da a lokacin yayi hidden identity dinshi baibar kowa ya sani ba.
Dawowarshi ya bashi damar bin didigi cikin ahalin, duk wani motsinsu da yanda suke tafiyar da alamarin business dinsu na hannunshi don ya zuba mutanenshi sosai a kamfanin, harma da cikin gidan, ta nan ne ya fara sanin abubuwa da dama ciki harda dalilin mutuwar fattu, a lokacin fadwa ta mallaki hankalinta sosai, din harta gama makaranta ma.
Saida ya fara karantarta sosai da halayenta gaba daya kafin ya tunkareta,duk wani motsinta yana ankare dashi, ya saka yaranshi na binta duk inda zataje, suna protecting dinta.
Ranar da suka sake haduwa a karo na uku shine lokacin dataje shopping, ta gama siyayya gaba daya ta bada card dinta donyin payment akayi denying biyan, kuma tasan hidaya ce tayi hakan, don sun samu misunderstanding a lokacin, fadwa ta nuna mata tanason shiga family business dinsu hidaya ta hanata, kuma bawai tace bazatayi aiki a kamfanin bane, ah ah kawai dai ta hanata title din data nema, abin yayi ma fadwa ciwo sosai, don itama tana som ta shiga business din a dama da ita, kuma abun saiyazo da idonta ya rufe itama, she wants the business, she wants to have the power yanda hidayar keyi, she wants to have it all itama tunda duk gadonsu ne kowa yana da right a kamfanin saidai hidayar tayi bake bake ta hana kowa ya samu saidai ita kanta daya.

Tana tsaye she feels so embarrassed, a matsayinta na ya ga taheel, kuma cikin babban building din shopping center dinsu amma ta kasa nuna isa.
Harta juya zata bar wajen basit yayi appearing a gabanta, kwata kwata da farko bata ganeshi ba harya gama mata payment din sannan yasa aka fitar mata da kayan zuwa motanta, ya dube ta yace ta zabi duk abunda takeso a wajen, idan akwai wanda takeso da baya nan dinka ta fada za a kawo mata a take.
Da farko ta nuna rashin jin dadin abunda yayi don ta dauka irin manyan nan ne masu kudin kasar yawanci zaka gansu matansu uku suna son yammata.
She totally misunderstood him wanda hakan ya sa dole ya mata bayanin koshi waye, ta hanyar nuna mata hotunansu shida ita a wanchan lokacin, tayi mamaki sosai kuma taji dadin ganinsa, don jefi jefi sometimes tana tunawa dashi don fattu ta shaida mata kamar dan uwanta yake, don har uncle fadwa ke ce mashi.
Yaji dadi yanda taji dadin ganinshi sosai, don yayi tunani Ta manta dashi ma gaba daya ashe abun zaizo mashi ta sauqi.
Tun daga ranar wani kusanci shakuwa ya sake shiga taakaninsu, babu abunda zata nema ta rasa a wajenshi, wallahi duk abunda take buqata da wanda bata buqata yake bata, gata fa sosai yake nuna mata harya fara tunanin meysa yake mata gatan, koda ta tambayeshi ya shaida mata saboda mahaifiyarta da yanda tayi mashi halarci wannan yasa duk abunda zaiyi mata bazai iya biyan abunda fattu ta mashi ba.

Akwai ranar da fadwa ta shiga damuwa sosai, daya lura da hakan hankalinshi ya tashi sosai ya tambayeta ta fada mashi koma menene, nan ta shaida mashi komai, yanda hidaya tafi tsayawa kan taj, ta fifitashi akansu, komai shi, ta turashi kasar waje, sai take ganin kamar ma arzikinsu shi takeson bama,ita kuma ta dau alkawarin bazata taba barin hakan ta faru ba, saboda ta dalilinshi mahaifiyarsu ta rasu, tana mashi tsana mafi tsanani.
A take a lokacin basit ya tambayeta me takeso? Word daya kawai zata fada kuma zaiyi mata providing, kuma zai iyayin komai akanta.
Anan ne tayi questioning dinshi, meysa yake mata komai? Meysa yake bata duk abunda takeso?.
A lokacin ne yaga that’s the perfect time da zai shaida mata koshi waye a wajenta.
Fadwa felt so terrible, hankalinta ya tashi, she couldn’t believe him, ya za ayi ya zama mahaifinta? That’s impossible.
Duk yanda yaso yayi mata explaining komai taqi saurara, wannan yasa ya bata dan lokaci.
Daga baya ta zauna tayi dogon nazari tare da tunanin abubuwan da suka wuce a baya, akwai lokacin dataji suna magana a office ita da mahaifiyarta, a ranar ne ma bata sake barinta ta hadu dashi ba, bayan nan ma akwai ranar data taba kamasu a office din, kusancin dataga a tattare dasu baiyi kama da wanda za ayi ma fasaara mai kyau ba saidai kuma rashin hankali yasa bata gane komai ba, nan ta fara questionining kanta what if da gaske yake? What if ita ba jinin. Taheel bane? Shikenan batada gadonsu? Ina bazata taba barin wannan sirrin ya bayyana ba inka da gaske ne wannan yasa ta nemi basit sukayi DNA test result ya fito 99% yarshi ce, she can’t change it dole tayi accepting shi din mahaifinta ne,kuma yana nuna mata so ba kadan ba, son da bata samu ba wajen iyayenta.
Daga nan ne suka fara plans ita da mahaifinta, kuma yayi alkawarin supporting dinta kuma bazai taba bari a gano gaskiar alamari ba.


Cigaban labari..
Zaman da yayi bayan futar fadwa babu abunda yake sai Kallon wayanshi, he’s trying so hard kar maganganun daketa trending akanshi karsu dameshi amma ina ya kasa, maganganu iri iri wasu ma na yaqinin ay shi din kamarma bakinsa daya da khaal, ba a san asalinshi ba, don bashida mahaifiya, yanxu haka ma tsintoshi akayi blaa blaa, maganganu dai kasu suka sosai babu dadin ji.
Hidaya makesure that blogs an yada wannan labari mara dadi jin, da suka sosai, wasu abubuwan ma da bai kamata ba.
Rufe wayar yayi ya aje tare da dafe kanshi, he has all the evidence akanta and he’s digging more,yanxu idan ya fiddasu to wallahi ta gama yawo gaba daya, dalili daya ne ke dakatar dashi, which is ahalin gidan, da company, yasan da zarar ya fallasa sirrikanta da Abubuwan datayi mashi harma da khaal reputation dinsu zai zube, za a zagesu, zq a zagi iyayensu, kuma kamfanin zaiyi kasa gaba daya wata qila ma a rufe shi, and he wouldn’t want that for the family name, wannan hardwork din mahaifinsu ne, kuma yasan khaal bazqi taba jin dadi ba, don these family has been there for decades, title dinsu ne, darajarsu ce sannan qimar ahalin gidan ne.
tsabar ciwo da kanshi ke mashi yasa ya dafe kan, shi kadai yasan abunda yakeji a cikin zuciyarshi, abunda bayason tunani akai don shine weakness dinshi wato zancen bashida mahaifiya.
Yana cikin wannan yanayin saiga call ya shugo wayarshi, harya tsinke wani call din ya sake shugowa ya dago da kanshi tare da aza rinannun idannshi kan wayar ya dauka, ganin mutallib ke kira yasashi daukan wayar tare da kaiwa kunenshi baice komai ba.
“Tajudeen!” Yaji muryar khaal ya kira sunanshi
“Na’am” ya amsa shi jiki a mace.
“Kazo yanxu ka

45 / 107