Advertisements
Chapter 89 Reading Matar Taj Book 2 Complete Hausa Novel Hausa Novels
Advertisements

Matar Taj Book 2 Complete Hausa Novel

Author :  Queenmerh Category :  Complete Novels

Chapter   89 / 107

264K to 267K   out of 320.4K words

su.
Duk wata hanyar lalacewa bahijja ta raba hanya dashi, inbanda neman ilimi dake gabanta babu abunda takeyi, bahijja ta kasance mai hakuri fadila cema mai zafi sosai don bata daukan nonesence kwata kwata,dake gidan nasu akwai ka’idoji sosai musamman abunda ya danganci alakarsu da mutane da kawaye na waje yasa bahijja bata da abokiyar hira kamar hadiza, koda yaushe zaka gansu tare, kodai hadizar na dakinta ko kuma kaga bahijjar a dakin inna suna hira da hadiza, karshe ma dai bahijja ce tasa aka maido da hadiza makarantar da take don suna zuwa tare, duk zaman da suke da hadiza da yardar data bama hadiza bata taba kawo kishi take da ita ba ko kuma fuska biyu take mata don bata taba nunawa ta gani ba a bayyane saidai a zuciyarta. 
Lokacin da hadiza ta nuna tana son sameer wato yayan su babu wanda yasan da zanjen in ba bahijja ba, itama bawai ta fada mata bane kawai ta fuskanshi yanda take yi da zarar yana kasar don ya kasance matafiyi lokacin anty laila kawai ya aura, wadda ta kasance agola a gidan, itama dai aurwnta dashi bawai a son ran anne bane kawai dai dan babu yanda ta iya ne, hadiza dama chan tayi alakwarin duk yanda za ayi saita aureshi, burinsu kenan ita da inna wadda tabi bayanta, don itama dai kwadayi ne da ita, ga rashin godiyar Allah.
Ganin batada chance don kwata kwata hankalin sameer baya kan hadizar yasa ta fadama bahijja in a manipulative way, ganin yanda sukeda kusanci,daga reaction din bahijjar hadiza tayi misunderstanding dinta, a tunaninta ba son ta take da dan uwanta ba kasancewarta yar masu aiki, itako bahijja ba wannan ne ba, tasan ba abu ne mai yiwu wa ba don ko ya nuna yanason hadizar anne ba lallai ta yarda ba, bazata taba yarda bama, don maganar aure ko hadakar aure anne is very strict when it comes to that, akullum batada burin daya wuce iyalanta su kasance waje daya, kuma hadakar kusa kusa bawai ta bare ba, hakan kuwa ta kasance, don kai tsaye bahijja ta fada mata tayi hkuri bazai yuwu ba, bazata iya taimaka mata ba,hadiza dai ganin bata da chance yasa ta hakura, amma fa ta kullaci bahijja don a ganinta basusan kowa yaci arzikinsu ta hanyar shugowa cikinsu tunda gashi akan idanunsu akayi rigimar aurenshi da na anty laila, daman gashi ta tsaneta bama ita kadaiba har uwar tasu wato anne.

a kwana a tashi haka shekaru suka ja, bayan fadila tayi aure harta haifi hamad da wasu yan shekaru, bahijja ta hadu da majeed, daga nan fa wata sabuwa ta bullo don hadiza na sanya idanunta akan majeed taji duk duniya shi takeso, itama, itafa duk abunda bahijja takeso ko kuma ya kasance nata ne haushi takeji, kuma ta dauki alkawarin saiya zama nata ita, kodai ta lalata shi ko kuma ya zamo nata, haka ta kudirci duk yanda zatayi saita rabashi da bahijja don ta sameshi. 
Data fuskanshi ba a san bahijja na tare da majeed ba kuma tana kokarin boye relationship dinsu don anne bazata taba amincewa ba kasancewar shi dan wata kasa daban irin yan Lebanese dinnan ne da iyayen su kasuwanci ya kawosu kasar na dan wani lokacin kafin su koma kasarsu yasa saitayi amfani da wannan damar don cinma burinta, koda ace ma annen zata yarda bazata taba barin bahijja tayi aure ba ita kuma tana zaune babu mabiya, gashi daga ganinshi yana da zababben kudi sosai ga kyau.

matakin farko databi shine shiga tsakanin bahijja datayi da anne, ta hanyar yi mata sharri mafi muni, wanda yasa anne tayi prohibiting bahijja da haduwa da majeed, ta kuma rantse akan cewa bazata taba aurenshi ba.

wannan abu yayi ma hadiza dadi ba kadan ba,don tayi nasarar rabasu saidai kuma duk yanda taso ta sami majeed batayi nasara ba, don tabbas tasan yafi karfinta, ammafa ta gwammaci bahijja ta rasashi koda kuwa ita baza ta sameshi ba.

Kiyayyace takeyima bahijja ba kankanuwa ba as time past, kuma haka kawai batayi mata komai ba.
Da yake komai na allah ne, kuma idan ya kaddara abu babu wanda ya isa ya hana, allah ya kaddara majeed ne zai kasance mijin bahijja dukda obstabcle din da suka shiga, na rashin amincewa da anne tayi, daya daga cikin dalilin dayasa anne taki amincewa shine, ta taso da akidar duka iyalanta zasu zauna waje guda, shiyasa ma sukeda babban estate, don karfafa zumuncinsu, wannan akidar tun mahaifinsu, shiyasa daya basu zabi sukebi, haka itama taso yima yayanta sai ya kasance bahijja ce ta bujire mata, mahaifinsu bahijja kuma ya tsaya mata.

lokacin da hadiza ta lura da sharrinta bai cimma ruwa ba ta shiga tashin hankali, don bazata taba zama tana gani bahijja tayi aure ba kuma ta fita, wanna yasa ta shiga tashin hankali.
Sai a lokacin ne kuma allah ya budema bahijja idanunta ta gane hadiza munafuka ce, annamimiya ce, kuma itace sanadiyar shiga tsakaninta da anne data rabata da majeed ta hanyar yi mata kazafi mai muni, ta danganta hakan da majeed dake nemanta, ganin sunan ahalin na neman baci yasa anne ta rabata da majeed din, don hadiza kiri kiri ta munafunci bahijja ta nunma anne cewa ita da majeed bayan soyayyarsu akwai haramtacciyar alaqa dake tsakaninsu shiyasa take boye babu wanda yasan dashi, don cewar kissarta da munafuncin datayi wai harda zubda ciki sunyi kuma babu wanda ya sani sai ita, kasancewar kowa yana ganin bahijjar da hadizar yasa anne ta yarda da zancen,wannan yasa da farko tayi alkawarin bazata taba bari bahijja ta auresa ba don kallon irin mutumin banza anne ke mashi.

jamila data kasance aminiyarta tun suna kananu, daga gari daya ma suka fito kuma sai ya kasance zamansu ma a anguwa daya sukayi, har suka girma suna tare, lokacin da suka bar anguwarsu ita da inna a lokacin ne jamila tayi aurenta na fari ta auri wani babban mutumi daga zuwa aikatau gidan, ko shekara biyu bata hada ba mijin ya mutu sanadiyar kasheshi datayi dake irin tsoffin nan ne masu budurwar zuciya baisan hadarin daya jajibo ma kanshi ba da iyalansa, a tunaninta tayi auren don ta samu kadara da wasu abubuwan daga karshe dai ta fito babu komai saboda bashishikan dayake dasu, saida fili daya ta tsira wanda suka sha gwagwarmaya da yayansa kafin tayi nasarar kwacewa taci banza shima saida ta hada da aikin malami, jamila dai tun tale tale takaddararriya ce, duk wani kissa da mugunta ta san yanda akeyi, kuma ta iya, kuma duk ba komai ne ya rufe mata ido ba sai kwadayin abun duniya, wannan futowar tata yasa suka sake hadewa da abokiyar shu’umancinta wato hadiza, don sunyi yanmatancin gagari da bariki a tsohuwar anguwarsu nan cikin gwagwalada a wata anguwa babu wanda baisan hadiza da jamila ba ta wannan fannin.

Bayan auren bahijja da majeed hadiza bata kara samun natsuwarta ba, don a lokacin ne bahijja ta fayyace komai akan abunda hadiza tayi mata a baya da yanda ta gano irin munafurcin data mata da hadata datayi da mahaifiyarta, da irin zaman da take da su, da baqin cikin da take mata ba tare da ta mata komai ba, zama dai ya gagari hadiza bayan an gano halinta, karshe ma dai tattarawa tayi tace ma inna bazata kara zama ba a gidan, don data zauna tana ganin bahijja da mijinta gwara tabar gidan ta koma inda suka fito, kuma bawai ta ajiye makamanta bane ko kiyayyar datake ma bahijja ah ah saima abun kara gaba dayayi ta fuskanci rabata da majeed bashine zaisa taji ta fi bahijjar ba ko taci galaba akanta, so take kawai taga ta wulaqanta, so take ta mata abunda har ta mutu bazata daina jin zafin itadai kamar tazo duniya ne kawai dan qiyayyar bahijja, kuma badan komai ba kawai don ta fita da komai kuma tana baqin ciki da ita.

idan an tanbayi inna hadiza a gidan ko kullum saidai l tace taje wajen dangin ubanta,don har zuwa lokacin inna na boye irin tabararriyar rayuwar da suke da yarta take.

yau sune bin malamai ita da jamila, gobe sune yawon titi, ta koma bin maza manyan maza waenda jamila ta samu hanyar hadaka dasu, har wani mutumi suka samu dayake basu maqudan kudade suna bashi jinin da babu wanda yasan daga inda suke samoshi, babu abunda bazasuyi ba indai zasu samu kudi ta kowacce hanya zasu iya komai,tare dai suke duk wani shiadancin su, a haka hadiza ta samu ciki a titi, koda ta gano hakan ta shiga tashin hnakli, jamila ta bata shawarar zubarwa daman ay dole su zubdashi, sukaje asibitin nan hankalin hadiza ya tashi da aka shaida mata mahaifarta batada kwari kuma idan har aka zubda cikin ba lallai ta sake samun wani ba, hankalinta ya tashi sosai don da farko ta gwammaci data haife shegenda koda yazo duniya batayi mashi tanadi ba gwara ta barar, sai kuma gashi allah daya tashi kamata sai yasa mahaifarta ta kasance batada kwari, shi kanshi cikin ma ba lallai yasha ba, karshe dai haka suka hakura da zubda cikin, suka shiga tunanin yanda zasuyi kan cikinn.

ana cikin haka inna ta gano cikin da hadiza ke boye da shi, ranar sun shiga tashin hankali daga ita har hadizar, dake inna na son hadizar kuma bata son asan cewa cikin shege tayi yasa suka hada plan, inna ta shaidama anne batun hadiza ta samu muji achan kauyensu zasu aurar da ita.

anne tayi murna sosai kuma yanda tayi alkawari idan auren hadiza ya taso ita zatayi mata komai hakan kuwa akayi, anne ta masu tara ta arziki suka tarkata suka tafi da sunan zuwa kauye.

bayan yan wasu kwanaki da komowarsu hadiza ta zauna tayi wani nazari, ta shiadama inna akwai wanda zata aura, dahiru kenan shima dan lafia ne, kuma gwari, ya dade yana son hadizar saidai kuma sun raba hanya, don gani take tafi karfin matsayinsa na talaka wanda bashida komai, tunfa suna anguwa daya kenan, yanxu kuwa dataga haza gashi bata da wani option yasa ta amince saboda cikin dake jikinta, ko dan ta rufama kanta asiri ma, kar abunda ke cikinta yazo duniya matsayin shege, zata iya yin komai akan abunda ke cikin nan nata, gaba daya duk wannan abun bai wuce cikin wata guda ba, jamila ma ta bata karfin gwiwa ta aureshi dukda talaka ne sosai, don su laqaba mashi cikin karta haifi shege, koba komai idan an ganta da ciki za asan tayi aure, don tun bayan dawowarsu hadiza taji duk duniya babu abunda takeso kamar cikin nan.
Shi dahiru irin aikin kano to abuja line dinan yakeyi wato driver mota, inna dai batada zabi ta amince don a rufama juna asiri, akayi aurensu kafin ta koma chan wajen aikinta.

Bayan watanni sun wuce hadiza na dauke da cikin jikinta haryakai wata takwas lokacin auren nasu bai wuce wata shida ba yan anguwa da yan uwan mijin harma dashi dahirun babu wanda yace tak akan cikin kamar waenda aka rufewa baki, kuma hakan ce ta kasance don saida jamila ta shiga ta futa lokacin ta samu wani matsubaccin malami ya masu aiki, babu wanda yayi magana akai.
A cikin watanne dahiru ya samu accident akan hanyarshi ta dawowa, tun achan ya mutu don gawarshi aka kawo.
Hadiza ta shiga tashin hankali soaai bawai don jimamin mutuwarshi ba sai dan yanda zatayi da wannan tsohon ciki, don ba karamin rufin asiri ya mata ba, dukda kasancewarshi kamar fanko a wajenta, amfanuwa kawai take dashi ba dan komai ba, cinta da shanta da komai ma dukda bashi da karfi, gashi komai yayi mata kasa, ita ba sana’a ba saima dai idan inna ta tura mata dan wani abu cikin albashin aikin datake achan gidan santurakin, ga jamila ma kasuwa tayi kasa yanxu abubuwan basa gaba, wani dan aiki data samu as cleaner, wani company masu daukar yan aiki suka dauketa ta kama takeyinshi anan cikin gari ana bata albashi shiyasa haduwarsu ma ke wahala sai jefi jefi.
Ko sadakar arba’in batayi ba babu kunya ta tarkata tabiyo inna, sanin cewa mijin nata ya rasu gata da tsohon ciki yasa inna ta roki alfarmar zamanta wajen anne, sanin yanda aka taso yasa duk kowa yaji tausayinta ta dawo gidan banda bahijja data san ko ita wacecece.
Lokacin itama bahijja cikinta ya tsufa don ta kai wata tara cif cif.
For the mean time hadiza ta sauke kanta sosai, kullum tana daki, bata yarda ma ta fito ba, don kamar bata existing a gidan kamar dai ba hadiza ba ta suake kanta.

Akwai wata ranar juma’a, bahijja ta tashi ta ciwon baya irin mai rikewar nan kan kace kwabo naquda tazo mata gadan gadan, daman tunda cikinta ya tsufa ta dawo gidan itama da zama bayan ta haihu saita koma.
Hankali tashe anne da fadila suka fito da ita, suna gab da sakata a mota saiga inna ta futo itama hankali a tashe, ta shaida ma anne a taimaka mata hadiza ma na nakuda, gaba daya daga fadila har anne mamaki sukayi jin hakan, ganin hankalin innar a tashe yasa anne ta karbi bahijja sannan ta shiadma fadila tabi inna su fito da hadizar, hakan kuwa akayi fadila na shiga dakin su ta tadda hadizar da wata a gefenta jamila kenan, zuwanta kenan rabonta da hadizar sun dade sosai sai yau kawai allah ya jefota zuwa gidan, suka taimakawa hadizar suka fito da ita, daidai nan majeed ya karaso gidan hankali a tashe.

Suna fitowa suka taddashi rike da bahijja, tsabar rudewar dayayi daukanta ma yayi gaba daya yana kokarin sakata cikin mota, anne kuma na daga gefe, tunda yazo yanayinta ya sauya gaba daya, da kamarma bazata asibitin ba ganin ya iso sai kuma daga baya tasa fadila ta bisu shida bahijjar ita kuma suka shiga motar driver da hadiza da inna.
Tunda suka fito hadiza na cikin naquda ihu takeyi harma yafi na bahijjar amma tana daura idanunta akan bahijja da majeed lokaci guda kamar an tsuke mata bakinta, ta kafesu da idanu kamar idanun nata zasu zazzago sukayi jajawur,take taji tsanar da takema bahijja ta dawo sabuwa fill, ganin yanda majeed din ke mata da saitaji dama bata futo ba, jamila na ankare da komai ita da inna suka taimaka mata suka shiga mota.
Tunda suka shiga motar kwata kwata hawayen dake fuskar hadiza ya kafe kaff, naquda takeji soaai amma kiyayyar dake cinta batasa ta cigaba da kukan ba, tunani kawai take yanda zatayi ta dau fansar qiyayyar datake ma bahijja da majeed.

Suna shiga driver yaja motar sukabi bayan motar majeed, basu tsaya a ko’ina ba sai a wani sabon asibiti da aka bude na yan Lebanese, anne dai bata ce komai ba amma bata da ikon yin magana, kuma hakan bawai dadi ya mata ba.

Suna isowa jamila ta dubi hadiza ganin tana cikin naquda kuma yasa tayi shuru,suna fitowa aka turo da gadon marasa lafiya, lokacin har an shigar da bahijja aka sakasu akai zuwa labour room.
A daidai lokacin da duk suka shigo emergency wajen first ward nurses suka dakatar da su, fadila ma na taaye don majeed ya shiga da bahijja, daman ba a yarda a shiga gaba daya saidai mutun daya, nan suma suka buqaci mutun daya da zata shiga da mai naqudar, inna na kokarin shiga hadiza tace da jamila take son shiga, basu kawo komai aransu ba aka shiga da hadiza labour room jamila na rike da hannunta.
Suna shiga second ward kafin labour room a gaggauce nurse ta soma shirya hadiza cikin kayan delivery, tana gamawa ta dan fita wannan ya bama hadizar damar magana, jamila ta matso da kunenta yanda daga ita sai hadizar ne zasuji abunda zata fada nata. “inason ki sauya duk abunda na haifa da abunda bahijja ta haifa”…..


Take gaban jamila ya fadi ta dubi hadiza
Cikin sauri tace “ta ina kike tunanin hakan zai yuwu hadiza? Ina zan iya yin haka? Asibiti ne nan fa? Kuma goge goge kawai nakeyi anan”

“Jamila ki taimaka min ta hanyar nan ne kawai zansan cewa nayi masu abunda bazasu taba mancewa ba, kuma koba komai abunda na haifa bazaizo duniya ba ya taso cikin rayuwar dana taso na girma a ciki ba”
Jamila hankali a tashe tace “idan aka gano fa”
“Jamila ke kadai zaki iya kin haka” hadiza ta fada tana cije lebe, jamia tayi shuru tana nazari kafin ta dubi hadizar tace “shikenan, daman ban fada maki ba anan nake aiki, zansan duk yanda zanyi na sauya su”
Tana fadin haka daidai nan nurse ta shigo, ta shiga da hadiza labour room ita kuma jamila tayi gaggawar zuwa dakin su na cleaners ta sauya kaya zuwa na masu goge goge ta futo.
Tana futowa daidai nan tayi kicibus da dahiru da shine ya mata hanyar aikin don tare aka kawosu shida ita ma, su kadaine hausawan da aka dauka anan.
Yana ganinta kuwa ya tambayi zuwanta don yau ba shift dinta bane, ba tare da wani tunani ba ta shiada mashi wani abun ya kawota daban, harzai sake mata wata tambayar ta dakatar don daman shishige mata yakeyi, ganin yar hannu ce .
Tana futa ta nufi emergency ward, harta wuce su fadila da inna babu wanda ya lura da ita saboda mask data saka sannan ta shige ciki, tana shiga second ward daidai wajen room din da aka saka hadizar da bahijjar ta tsaya kamar wadda ke aikinta na goge goge saiga nurses sun fito da jarirai, lokaci guda coincidentally, akan idanunta aka wuce dasu dakin da za gyara su sannan a bunciki lafiyarsu, suna shigewa dasu ta nufi wajen ta saka dan card din dake bude kofar duk wani authorize ward da ake basu idan zasuyi gyara, tana sakawa yaqi buduwa, duk yanda taso ya bude yaqi budewa, take hankalin ta ya tashi ta koma da sauri ta tsaya bakin kofar tana gogewa daidai nan daya daga cikin nurse din data shiga ta futo da sauri, sukayi kicibus da dayar nurse din ta taho hannunta rike da baby bag dake dauke da abubuwan da za a gyara jarirai dashi, dayar na ganinta tayi gaggawar cewa “we need pediatric immediately” tana fadin haka dayar tayi saurin karbar abubuwan ta wuce ciki tana shiga bata jima ba tayi saurin futowa itama cikin gaggawa ba tare da ta rufo kofar ba daman

89 / 107