Author : Queenmerh Category : Complete Novels
komai tass ya rage ko katifa babu sannan hadiza ta fidda gana masgo dinta waje sannan ta wula ma sabeeha leda tace “tattara kayanki ki fito”
Tana hadasu cikin ledar ta futo hadiza ta kulle kofar sannan tayi gaba sabeeha taja buhun suka kara gaba ko sallama.
Anan bakin kofa ta bawa gwari mukulli tace abawa landlord idan yazo don ko haduwa dashi bazatayi ba sabda akwai dubu goma da zata biyasa amma taci banza.
Gidan jamila suka karasa sabeeha ta tsaya bakin kofa ita kuma ta shiga daga ciki saida ta shafe wajen 30mins sannan ta fito.
Sunyi tafiya mai tsayi har bakin titi kafin su samu drop, nanda maitama saida suka bada wajen dubu biyar hadiza sai faman masifa take, tafiya suke mai dan tsayi har suka iso area din, kamar kullum ko’ina a a gyare fess fess babu qazanta babu hayaniya, har suka karaso estate din, nanfa ake daru drop yace bazai kara koda second daya ne a wajen ba nan yayi dropping dinsu suka karasa bakin entrance sojojin wajen suka taresu, duk bayanin da hadiza ta masu baisa sun barsu ba don ance ta kira daga chan a kira batada number kowa haka suka zauna gefe jugum sabeeha ga uban buhu aka kamar wadda tayi hijira.
Sunfi kusan 30mins suna kallo motoci na shigewa babu dauki, cikin ikon allah saiga motar hamad, kallo daya yayi ma sabeeha ya ganeta dan bayajin zai iya mance fuskarta, fuskar look so familiar.
Nan ya tambayi security meysa suke zaune suka shaida mashi ay gidan santuraki suke son zuwa and they couldn’t contact anyone from inside, nan ya bada umarnin abarsu su shiga dayake sun sanshi basu musa ba yayi gaba da motarshi su kuma aka shaida masu zasu iya shiga aka bude musu kofa, tafiya sukayi mai shegen tsayi kafin su karaso main gate entrance din mansion din santuraki’s, suna karasowa nan ma ba a tambayesu ba aka barsu suka shiga, sabeeha sai mamakin gidan take, tabbas nan suka zo kwanaki.
Direct babban part din hadiza ta nufa kai tsaye, da sallama suka danna bell aka bude kofa, kamshin tiraren wuta da sanyin ac ya masu sallama, dqman sai zafin rana suke saboda dadewa da sukayi, idanun sabeeha har wani jaja suke, tayi laushi sosai fuskanta harta soma duhu.
Yar aikin ce ta jagorancesu parlorn farko suka zauna a kasa, sannan ta wuce ciki donta sanar da masu gidan.
Suna nan zaune maid din ta sake futowa ta bude kofar nanna ta shigo da sallama, tana sanye da lafiyayyan lace ga kamshin dadi da take Masha allah, matar nan bata tsufa kwata kwata, zaka rantse bata haura 50 fa, skin dinta sai glowing yake.
Harzata wuce walkway ta hango su zaune, har wata ajiyar zuciya hadiza ta sauke data ganta, “ah ah hadiza kune”
“Eh hajiya mune, ina wuni”
“Lafiya lau hadiza ya gida”
“Lpy lau,”
Sabeeha ma ta dan dago ta kalleta cikin sanyi tace “ina wuni”
“Lafiya lau, ya sunanki”
“Fatima”
“Masha Allah sannu fatima”
Daidai nan anne ta sauko daga sama, tana sanye da glass fari akan fuskanta.
Main sitting room ta wuce nan, yar aikin ta karaso first parlor ta shiada masu cewa hajiya ta sauko.
Nanna tayi gaba hadiza na biye da ita a baya har sabeeha ta miqa hadiza ta dakatar da uta ta koma ta zauna.
Suna shigowa hadizq tayi saurin zama kasa ta gaisheda anne cikin aminci, nanna na daga gefen anne hadiza ta soma magana harda yan hawayenta. “Hajiya daman ina neman taimako ne, gidan da muke zaune ne akayi rusau, gashi bamuda wajen zuwa gashi inda nake aiki ma madam din ta sallamemu gaba daya saboda zata koma kasar waje da iyalanta, shine nace ko bari nazo neman taimako, ko aikatau ne zanyi”
Shuru anne tayi tana sauraronta har takai aya, kallon anne nanna tayi jin tayi shuru tana kallon hadizar, tasan dakyar ne idan anne zata barta tayi aikatau a cikin gidan saboda ba ayi rabuwar mutunci ba kwata kwata lokacin da ita da babarta sukabar aiki a gidan, saidai kuma komai ya wuce ana maganar abunda ya faru shekara da shekaru kennan fa.
Da mamaki gaba daya daga nanna har hadizar suka dago jin abunda anne ta fada “ba damuwa, albarkacin diyarki ku zauna, duk wani hidimarku ci da sha da sutura na dauka, saidai kuma zaku dunga aikin, sannan duk wata za a biyaki”
“Kai nagode Hajiya, kin gama mana komai, ni basai kin biyani bama, allah ya saka da alkahiri”
Nanna taji dadi sosai doj batayi tsammanin anne zata yarda ba kwata kwata, saboda anne bata mantuwa kwata kwata, idan ta baka chance ta yarda dakai kayi betraying dinta ko kaci amanarta bata sake yarda da mutun.
Nan indo ta shigo ta wuce da hadizar donta nuna mata masaukinsu, nan guest room dake kasa kusa da dakin ma’aikatan gidan saidai ba irin dakunan su bane wannan ya danfi kyau tunda akwai gado akwai wardrop dresser harda ac ma da dan carpet.
Bathroom dinma ba laifi akwai komai shower ne da komai.
Sake shugowa indo tayi ta aje masu ruwa da lemo, nan hadiza ta roketa data kira mata sabeeha, suna gab da wucewa anne ta kira indo, har sabeeha ta tsaya anne tace ta karaso itama, tana zuwa ta dan duqa har kasa ta gaishe da anne, kallonta sosai anne keyi babu kiftawa sai kuma chan tace “ya sunan ko?”
Tace “fatima”
“Kinyi karatun boko?”
Shuru sabeeha tayi tama rasa mw zata ce mata, kawai saita tsinci kanta da kasa yi mata karya tace “eh, inda nayi aiki sun sani makaranta, ina gabda gama course din da suka bani na dawo”
“Me kika karanta?” Anne ta sake jefo mata tambaya
“Business ad”
“Shekarunki nawa?”
“Ashirin da biyu..da uku”
Murmushi nanna tayi tana hango ladabi da hankali a tattare da yarinyar, babu alamun rawar kai kwata kwata a tattare da ita.
“Jeki” anne ta dauke idanunta daga kan yarinyar sannan ta maida ga news din data dauka dake kan table.
Suna bari wajen nanna tace, “oh wani ikon Allah, yanxu wannan yar hadiza ce babu gigiwa babu hayaniya,lokacin da uwarta ke kamarta akwai hayaniya, larai taita fama da ita, ga neman fada, amma wani ikon allah kwata kwata bata kama da hadiza, yanxu haka kamannin nata ta wajen ubanta ne, allah dai ya jiqan musulmai baki daya ameen”
Anne ta ce “ ameen”
Sallamar anty fadila tasa suka dago gaba dayansu, gefenta hamad ne hannunshi da tray na snacks.
“Anne kuna kasa ashe”
Nanna tace “wallahi fadila yanxun nan na shigo nima”
“Ya office nanna?”
“Alhamdulillah dear ina kishiyar tawa”
“Basu dawo daga school ba ita da abokiyar fadan tata”
Dariya akayi nanna tace “yanxun nan su hadiza sukazo kuwa”
“Hadizq dai?”
“Eh wallahi ashe rusau akayi a anguwarsu, abun tausayi wallahi ko wurin zuwa basu dashi”
“Wayyo allah ya rufa asiri, yanxu anan zasu zauna,”
“Eh ta nemi alfarmar a barta tayi aiki sai a biyata”
Jinjina kai fadila tayi tana tuna rayuwar da sukayi a baya, kai hadiza yar rigima ce ta karshe, dama itace abokiyar fadanta a koda yaushe, basa jituwa kwata kwata har gwanda bahijja, ita dake tanada sanyi sanyi tana daukan rashin mutuncinta, dake tare duk suka taso, idan suka fita kuwa saika rantse hadiza ce yar gida, komai itace a gaba gaba, babu mutunci lol.
Anne dake jinsu batace komai ba ta dubu fadila tace, “cikin kayan laila ki duba ma diyarta kayan da bata so, naga yarinyar kamar batada suturar arziki”
Nanna tace “daman anne dole ay, baki gansu bama gaba daya babu kwanciyar hankali, babu jimar arziki, kai ana wahala a kasar nan, allah ya rufa asiri”
“Ameen” duk suka amsa a tare.
Daga nan suka dan taba hira kadan kadan.
Sabeeha na shugowa hadiza tace “me kika tsaya yi?”
Tsoron kartayi fada yasa tace “ban tsaya ko’ina ba,“
“Zquna” zama sabeeha tayi hadiza na fuskantarta tace “inason na maki kashedi ki bude kunnuwanki karki jawo min masifa, babu ruwanki da harkar kowa mu ba kowa bane face yan aikin gidan, babu ruwan da sha’anin yan gidan indai ba aiki muka fita yiba karna sake na ganki da kowa, ban amince ba kuma ban lamunta ba. Abunda ya shafi rayuwar mu a baya bakida hurumin fada ma kowa, dan wallahi kikayi sanadiyar barinmu gidan nan ko aka koremu hmmm, banida zabin daya wuce na aurar dake ga duk wanda na samu”
Maganar aure data kawo saida yasa gaban sabeeha faduwa, saita nemi jin hawaye na neman sauko mata tayi saurin hana kanta yi.
“Dauka kisha”
Daukan ruwan sabeeha tayi ta dan sha kadan, lokacin sallah nayi hadiza ta miqe ta dauro alwala lokacin har indo ta kawo masu abunci, sabeeha da tun ruwan bunun da tasha da safe bata ci komai ba, tana kallo aka kawo abunci a tray kamshi ya gama bugun hancinta, batayi gigin tabawa ba har saida hadizar ta fito daga bayi itama ta shiga bayin, toilet din yayi kyau kuka a taaftace ba kamar gidan hayan da suke ba, duk sanda ta shiga ta futo saitayi amai sosai, jikinta kuwa sai yayi wani jajaja tsabar jininta baya son qazanta, dauro alwala tayi ta fito, ta koma gefe tayi sallah harta idar, har hadiza ta zauna ta fara ci, saida ta koshi sosai ta kara daga platw din sabeeha kafin tayi gatsa ta tashi tabi lafiyar gado.
Saida tayi nisa sosai cikin barci sannan sabeeha ta janyo plate din taci sauran ta koshi dam ta kora da ruwa, harda juice.
Ya allahu its been long rabonda taci proper abunci wallahi, nama zuqu zuqu har ya soma hawa kanta, allah karka barbu da wahalar abunda zamuci a cikin mu Ameen.
Saudi…
After 2days…
Futarshi yake son ranshi, kuma hidaya na ankare dashi, da inda yake zuwa, da wanda yake haduwa da,wani ikon Allah, allah baibata ikon shaida mutallib ba saboda duk hoton da za a dauko mata dake nuna tare da mutallib yake ba a ganin fuskarshi saidai tasa a bincika mata waye shi, ina suka fara haduwa kuma ina taj din ya sanshi.
Mutallib yasha wahala sosai wajen neman detective dinnan kuma allah ya bashi nasara, yabar kasar ma gaba daya amma haka mutallib ya nemoshi sannan ya mashi bayanin komai ya roki alfarma a wajenshi, da farko detwctive din ya nuna baisan komai ba kuma bazai iya taimakonshi ba dalili kuwa wannan case din daya taimaka wa jamid suka bude na khaal yayi sanadiyar aikinsa, daga manyanshi, ya rasa komai ta sanadiyar hakan,gashi ya nemi jamid sama da kasa ya rasa baisan cewa ya samu paralyse ba kwata kwata, sai a yanxu mutallib ke fada mashi, bayan ya bama jamid information dinnan ya hadu dashi a ranar washe gari kuma aka samu labarin ya samu paralysis, abun ya bama detective mamaki wannan yasa shi tunanin sosai sannan yace zai nemi mutallib din if hes ready to open up, mutallib yayi understanding detective din is being cautious,wannan yasa bai matsa mashi dole saiya taimakeshi ba.
Cikin ikon allah a daren ranar wallahi detective din ya kirashi ya zayyane mashi komai da binciken da sukayi shida jamid, da wanda suke suspecting don anyi fabricating results din gawar khaal.
Mutallib baiyi mamakin jin wannan zancen ba, saidai kuma ba kowa ne ya dace yaji wannan ba sai taj, wata qila wannan zai zame mashi eye opener ya kara tabbatar da akwai kullaiyar da akayi akan batun accident dinshi, sannan wannan zai kara tabbatar mashi da khaal has always been there for him.
Rokonshi mutallib yayi akan yanaso su hadu idan babu damuwa, da farko detective din yaso qin amincewa saida mutallib ya mashi bayani qalilan daga cikin abunda ya sani gameda taj, daga baya da detective ya gamsu ya amince da zasu hadu washe gari.
Yana kashe wayar ya kira taj, yana dagawa ya sanar mashi akwai wani abu dayayi bincike akai, damasaidai kuma ya wayance da detective din abokinshi ne tun yarinta, kuma akwai wani abu daya sani game da abubuwan da suka faru a baya don yayi handling file din khaal lokacin da akace ya mutu.
Taj yayi mamaki kuma yaji dadin wannan zancen wannan yasa sukayi planning haduwa da mutallib din gobe.
Yana kashe wayar ya sake duban hannunshi, yanxun nan yazo daukan abu a drawer din gefen bedside dinshi yana budewa yaci karo da black box din da sabeeha ta taba tsintowa a cikin bathroom, jujuya black box din yayi da kyau yana nazarin abubuwan da dama, instint dinshi na bashi dis is suspiciou, wannan yasa ya fara duben duk wani lungu da sako na cikin dakinsa, haba waa, he was double shocked, no triple shocked, ya tsinci wajen guda uku a cikin bedroom dinshii da closet dinshi,no one can tell him koma menene don yana gani ya gane its a spy recorder, waye ya saka? Yaushe aka saka? Meysa aka saka? Duk wannan tambayoyin nashi babu mai bashi amsa saidai kuma yanxu ya kara tabbatar da something is terribly wrong.
Washe gari da safe fadwa na tashi first thing first recorder bedroom dinshi ta saka, daman duk safiya da voice dinshi take tashi, inda yake kiran sunan allah kafin ya miqe ya wuce bathroom, koda ta saka na bathroom dinshi is meant for sound din tafiyarshi,da wankanshi, that keeps her wanting him more and more taita imagining gata nan ita dashi a bathroom kai thats so creepy..🤮
Yau to her surprise taji blank, anyi disabling recorders din, tsabar bacin rai batasan sanda ta buga wayar ba a kasa duk tsadarta ta tarwatse kasa ta fara ihu kamar mahaukaciya.
Bangaren taj yana tashi da safe as’usual ya gama shirinsa yayi ficewarsa.
Yana cikin tafiya yayi noticing kamar ana binshi a baya, batun yanxu ya lura da ana binshi ba kuka bai damu ba but this time around dole yayi stepping up.
Haka yayi motar wani mugun speed take ya bacema motar dake binshi a baya.
Bai tsaya ko’ina ba sai cafe din da sukayi zasu hadu da mutallib, coffee yasa aka bashi da croisaant yayi breakfast fast dashi yana gamawa saiga mutallib ya iso, shima dai baiyi breakfast dinma so anan yayi order sukaci suka koshi sannan suka fita a tare, motar taj na gaba mutallib na biye dashi har suka iso inda zasu hadu kusa da wani beach haka.
Sun dan jira for about 30mins detective ya iso, yana sanye da normal kaya ya saka facing cap, chan wajen wani open place suka zauna detwctive din ya dubi taj, kamar dai shi ya gani a news da ita hidayar kwanaki, wanda akace bashi da lafiya,
“This is tajudeen, nasan kasan koshi waye basai na maka bayani ba, inason musan komai please karka boye mana”
Jinjina kai detective din yayi sai kuma ya danyi dariya yace “banyi mamaki da akace bakada lafiya ba yanxu kuma naga akasin haka,”
Da mamaki taj ke kallonshi don son jin karin bayani, “on the 20th oct of last year, jamid yazo ya sameni da batun case din murder daya faru on the 10th of july, because he couldn’t believe if the death of the person was actaully a murder or a planned murder after the accusation and cases that followed next, on the 9th of july you were kidnapped kaida matarka, and the next day an tsinci gawar uncle dinka, that same day an samu hoton motar da akayi kidnapping dinka dashi wanted kidnapper din tare da uncle dinka, everything seems planned cause it doesn’t add up, aranar da akayi hoton aranar ya mutu, jamid convinced me sannan yayi min pointing out kan cewa this doesn’t add up and i believe that, first of all abunda muka fara questioning shine, what if he was framed? Yes it can be possible but how can we be sure if that? And we got an answer, nida jamid we checked on the forensic results which shows that he was dead, anan mukayi noticing wani abu, saidai the next day daya kamata mu hadu da jamid bamu samu mun hadu ba, i lost his contact and i was questioned for opening the case which leads to my dismissal,na nemi jamid na rasa, I couldn’t contact him, sai yanxu danake jin labarin he had a paralyze, i was shocked, and i definitely suspect ana kokarin ganin an toshe duk wata hanya da zai bayyana gaskia.
Shuru ya danyi chan kuma ya dan nunfasa ya dubi taj cikin ido yace “the first person jamid yayi suspecting yanada hannu cikin wannan ba kowa bane face mayarshi, the ceo of taheel and i can say she’s the primary suspect”
Take idanun taj sukayi jaa sukayi rudu rudu, jijiyoyin kanshi suka fito sosai ba kadan ba, ganin yanayinshi yasa mutallib kama hannunshi ya rike alamun ya saita kanshi.
“Akwai abu daya dazan fada maku, da farko gaskia banyi niyar fada maku ba amma ina ganin you need to know, koda akayi dismissing dina banbar bincike ba, anan ne ma na gano zoben dake hannun gawar da akayi declaring ta shi deceit din da aka tsinceshi dashi wanda ya kasance nashi, akwai traces din prints guda biyu da suka banbanta a jiki, we found of someone else’s on the picture, i couldn’t tell jamid results, but wannan gawar ba gawar khaal bace”
Gaba daya zuba mashi idanu taj da mutallib sukayi in full if shock and surprises, abun yafi tada ma da taj hankali,
“Kana nufin kace akwai possibility din khaal
Bai mutu ba?”
“Yes wannan gawar ba tashi ba”
“Innalillahi wa inna ialaihi rajiun” hankalin mutallib fa ya tashi sosai ba kadan ba har yaso yafi taj dinma.
Shifa taj is lost tunda aka ambaci hidaya as a primary suspect, saiyafara reviewing kanshi? What is he digging? Gabanshi na mugun faduwa yake wannan nazarin.
Karya ta mashi kenan? Its all a lie? Duk abunda ta fada game da khaal duk karya ne? Tace khaal ne ke kokarin ganin ya kasheshi saboda yaci gadonshi? Yanxu dukka karya ne? Innalillahi wa jnna ilaiahi rajiun
Wallahi taj baima san sanda detective dinnan ya kara gaba ba, he’s so lost in his thoughts, mutallib ko ya rasa tunanin mai yake, yanxu akwai possibility din khaal
Na raye? Innalillahi wa inna ilaihi rajiun, wannan wani irin baqin zalinci ne? Saiyakejin gwara kawai ya fito fili ya fada ma taj gaskia kawai.
“Tajudeen..akwai wani abu danake so na fada maka, but ina fatan zaka saurareni, duk wani abu dakaga ya faru yana da dalili”
Miqewa taj yayi tsaye a fusace, bayajin zai iya tsayawa yana sauraron wasu magnganun kuma, wace iriyar dark rayuwa yake living bai sani ba? Is he blind or what,
“Dan allah ka saurareni kaji abunda zan fada maka, tabbas ni