Advertisements
Chapter 47 Reading Matar Taj Book 2 Complete Hausa Novel BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Matar Taj Book 2 Complete Hausa Novel

Author :  Queenmerh Category :  Complete Novels

Chapter   47 / 107

138K to 141K   out of 320.4K words

pdf ne.
Image din ya fara shiga take wata fuska ta bayyana, lokaci guda ya kurama screen din idanu sosai kamar zasu zazzago, nidai na kasa ganin hoton saboda expression dinshi nake kallo kawai yanda gaba daya ya sauya ya chanza lokaci guda.
Saurin fita yayi daga imagine din ya shiga other files din, take yaci karo da abubuwan daya shafi kamfani, da yarjejeniyar da khaal yayi da hidaya, da takardun inheritance din taj, da shaidar kasancewarshi the only heir, dukdai wani abu daya danganceshi yana ciki, fita yayi ya shiga dayan take yaci karo da bayanan slush funds da hidaya keyi, da wasu abubuwa daya shafi kamfani da illegal abubuwan da takeyi babu avunda babu a ciki,
Taj was so shocked and surprised at the same time, me wannan keyi a laptop din yarinyar nan? How did she come across this?
Take kuma ya tuna da magnganun khaal, “fatima itace answers din komai, fatima ce komai naka taj, itace ke protecting dinka all these while”
Sake kallon files din yayi, tabbas wannan shine abunda zai wanke khaal Gaba daya and its a concreate evidence, now he’s left with 2 option, to save khaal or to save the company, dole yayi tunani akai dole yasan yanda zaiyi, he needs to do something.

Zama yayi yana nazari sosai, maganganun da sukayi da khaal dazu na zuwan mashi.
Gefen bedside dinshi ya jawo ya zaro envelope dinnan da matar khaal ta bashi, tunda ya dawo bai bude ba kwata kwata ya aje a wajen sai yanxu.
Nannadewa ya somayi a hankali yana budewa……….

Cikin hanzari mutallib ya bude idanunshi jin nunfashi na tashi kadan kadan, daman akan couch yake kwanciya saboda khaal, miqewa yayi zaune jin nunfashin na hauhawa sosai,

Yar karar kofar daya danji ne yasashi miqewa ya kunna fitila, take haske ya bade ko’ina ya dubi kofar, ganin kamar an budeta an fita, gabanshi ne ya dan fadi jin kara timm kamar abu ya fadi daga ciki.
Cikin sauri ya nufi dakin khaal hankali tashe, yana bude kofar yayi turus ya tsaya, gabanshi na faduwa dam dam dam ganin khaal a kasa yana shure shure, idanunshi sun fito kwala kwala jikinshi ya karade ya koma green, ga jini na neman fita ta bakinshi,
Aguje mutab ya doka uwar kara, ya nufi khaal din, “innalillahi wa inna ilaiahi rajiu, khaal khaal khaal ya soma jijiga shi hankali tashe, karar dayayi yasa gangs dinnan suka tifito da bundigu da wukake, suna zuwa dakin sukaga khaal kwance ogansu ya dora hannu aka.
“Meya faru? Meya faru oga”
“Ban sani baaaa, ku taimaka min karya mutu innalillahi wa inna ilaihi rajiun”
Jini na ambaliya ta baki ta hanci, yayi wata iriyar miqa kyaf kyaf kyaf ya sandare, ogan nan ya kura mashi idanu sosai, kafin ya duqa ya bangaje mutab ya janyo hannun khaal nan yaga alamun allura, kuma ko ba a fada mashi ba yaga sign and symptoms don suna yawan yiwa mutane haka idan zasu kashe ko in an sasu suyi threatening mutun, deadly injection ce “ anyi poioning blood dinshi”
A fusace mutab ya dubeshi, tare da shaqoshi, “waye zaiyi haka? Kune ko? Cin amanar mu kukayi? Eh menene amfaninku?, waye zaiyi?????????? Idan ya mutu bazan kyale ku ba dukanku”
Kama habanshi ogan yayi kamar zai balla hannun mutallib yace “we have no time for this, he’s going to die any minute”
“Innalillahi wa inna ilaihi rajiun”



✊💋BOSS LADIES WRITERS💋✊

MATAR TAJ (destined with you🩵🤍)
Written by
Queenmarh✍️
Book2
PAID
Chapter 88
Miqewa ogan yayi ya futa cikin gaggawa, ko second goma baiyi ba ya dawo dakin hannunshi riqe da wata allura, yana kokarin fasawa zai saka a syringe, mutallib ya kalleshi idanunshi sunyi jaa sosai ya kama hannun ogan kamar zasuyi dambe fa, don harga allah yana zargin sune, ko cikin yaranshi ne.
“Menene wannan din? Kamin bayanin meke faruwa dashi”
“Ka sakeni indai ba so kake ya mutu ba yanxun nan…nunfashinsa ya dauke”
Dole mutab ya sakeshi ganin khaal din baya ninfashi gaba daya.
Duqawa gang leader yayi gaban khaal cikin gaggawa ya jawo hannunshi ya tsira mashi allurar, yana gamawa ya soma dukan kirjinshi da karfin gaske wajen zuciyarsa, don idan zuciyarshi ta tsaya toh mutuwa kawai zaiyi saboda allurar nantake take damaging jijiyoyin dake connecting to heart dinshi shiyasa ake kiranta da deadly poison.
Bugun shi yake iya karfinshi sosai, mutabb ya kasa kallon khaal din, zuciyarshi gaba daya ta tsinke ya tunkari gang leader zai ture shi yaranshi suka kama mutab din suka ririkeshi don su kansu sunsan wannan ce hanya kadai da zasu samu suyi mashi taimakon gaggawa don ko minti daya ya kara zqi mutu.
Haka ya dunga bugun wajen zuciyarshi iya karfinshi babu response, mutab kuka shabe shabe, sai faman runtse idanunshi yake yana kokarin dambe da yaran gang leader din.

Juyowa gang leader yayi ya kallesu hankali tashe yace “I can’t feel his pulse, zuciyarshi zata bugawa anytime”

Wani daga cikin yaran gang dinne ya shugo dakinsu yana haki don fitar da yayi ogan nasu ya sashi duba cctv camera da sukayi installing privately.

“Sir It’s the doctor, shine yayi snicking cikin dakin 10mins ago !!!” Shine abunda ya fara furtawa.
Mutabb ya kama kanshi kamar zaiyi hauka, “mu kaishi asibiti”
“We can’t sir, babu wani amfani don bazai….”

“Innalillahi wa inna ialaihi rajiun”


Dukda wayanshi na silence, vibration din dayaji yasashi bude idanunshi, don wayar ta dade tana vibrating babu qaqautawa,yana jingine jikin gadonshi ya rungume wani dan hoto da takarda a kirjinshi, jawo wayar yayi don tana hannunshi baima san sanda barci ya jashi ba.
Time ya fara duba ba its past 3am, wani call din ne ya sake shugowa saida gabanshi ya fadi sosai ya bude idanun nashi tarrr tare da hanzarin picking call din.
“Tajjj tajj…sun kasheshi, sun kasheshi, sun mashi poisonous injection taj…..”
Dammmm gaban taj ya bada a razane ya miqe tsaye har zuwa lokacin hoton nan da takardar na hannunshi.
“Innalillahi wa inna ialaihi rajiun”
Juyawa kawai yayi ya zari key din motar shi ya futa, da laptop din da wayar sabeeha na ajiye gefen gadon.
Sound din tafiyarshi kamar zai fasa ginin dip dip dip, ko ganin gabanshi wallahi bayayi kwata kwata tsabar rudu.
Yana sanye da wata long sleeve white top da farin wando sai bathroom shoes, ko buttoning rigar baiyi ba.
Yana shiga mota ya figi motar aguje, gudu yake sosai na kadan ba kamar zai tashi sama.
Kokarin dialing number mutab ya sakeyi ya daga “please don’t let him die please please ku ceceshi, i need him in my life, ban cika allawarin danayi mashi ba, baiga iyalanshi ba, we need him d most, please karkacemin ya mutu, innalillahi wa inna ialaihi rajiun, wallahi bazan yafe masu ba idan har wani abu ya samu khaal, i will destroy them wallahil azeem,”
Kamar zaiyi hawaye haka ya ke magana da karfin gaske ga gudu da yake kamar zai tashi sama.
Mutabb dayaji kamar taj din na neman zaucewa yayi saurin cewa “taj… calm your self,”
“I will fuckingggg make demm pay for this… wallahi bazan barsu ba…”
Yana cikin magana kawai yaga haskee bauu bai ganin gabanshi…….
Gabannnnnnnnn wata katuwar truck ta taho from nowhere tayi gaba dashi ta hanyar turashi chan irin dajin gefen highway don ba cikin gari hideout din nasu yake ba.
Ko tsawa truck din batayi ba ta kara gaba,hayaqi ya zagaye motar, gaba daya outer part din motar yayi damage ba kadan ba, tik tik tik tik haka wani sound ya soma fita daga motar, cikin abunda baifi minti biyu da yan seconds ba motar ta tashi da wuta bal bal bal bal,innalillahi wa inna ilaihi rajiun, masifa iri iri…kai my heart is so heavy, akwai marasa imani a duniya wallahi…


Tashin hankalin da mutallib ya shiga yafi wanda ke gabanshi, cha yake “hello hello tajjjjj tajj..” amma shuru babu response karshe ma wayar disconnecting tayi.
“Na samu ninfashinsa….na samu ninfashinsa, yana rayeeee”
Sauke wayar mutab yayi ya tunkari inda khaal yake cikin sauri.

3:30am dot na clicking wayarta tayi ringing,tana zaune cikin daki babu wani haske sai irin inner red light dinnan, don ko fuskarta bana gani, gabanta red strong wine ne datasha wajen half, a gefe kuka wani dan tray ne na different substances akai.
Wine glass din dake hannunta ta ajiye sannan ta daga wayar takai kunnenta, banji me akace daga chan ba kawai saita dan murmusa ta aje wayar ta cigaba da shan wine dinta tana layi.

Motar nan saida taci taci taci sosai, babu abunda yayi saura ko kadan tun kafin fire service su karaso, koda suka karaso kokarin tracking ko akwai mutane a ciki suka farayi cikin gaggawa, abunda suka gani ya tayar masu da hankali sosai yan forensic research suka karaso da police gaba daya aka zagaye motar.
Yanda motar ta cinye tass harda dalma yasa sukayi using special forces don binciken gaggawa, abu na farko daa akayi tracking shine bomb din daya tashi da motar, don shi yayi causing wannan explosion din, sai traces din jini da forensic researchers suka samu wanda hakan ya tabbatarda akwai mutun cikin motar tayi exploding, gaba daya basu var wajen nan ba har saida gari ya soma wayewa, akayi gathering duk wani abunda za a buqata don yin bincike.

Bincike police suma suka soma nasu, aka duba plate number motar akaga its fake plate number, gashi motar ta kone balle a gano series dinta da inda aka sayo ta.
Bangaren forensic researchers suma haka suka fara nasu observations din, dan jinin da sukayi tracking jikin wani fabric da suke tunanin kayan wanda ke cikin motar ne, su daman duty dinsu don su samu identity dinshi ne nanma dai babu abunda ya bullo.

A safiyar ranar kawai akayi wrapping case din as unknown disclosed scene don hatta the type of the bomb sun kasa ganowa.
Abunda yasa sukayi wrapping case din shine saboda reporters har sun samu labarin acceident din, avunda sukeson tabbatarwa shine ko bomb dinne ya tashi da gaske? Kunsan yanda police suke, basa kaunar ayi questioning aikin su, don tabbas idan ya tabbata bomb ne ya tashi za a tambayesu how? Kuma meysa suka kasa gano komai gameda bomb din, what if anso attacking kasar ne, abunda zai zamo complicated wannan yasa sukayi wrapping case din kawai aka miqashi ga SSS secret service.

Masu yada labarai da safiyar ranar suka fara yada labarin accident din inda suka shaida accident din ya faru cikin dare misalin karfe 3:25 daidai sannan anyi tracking mutun daya cikin motar wanda ake kokarin bincike kan identity dinshi.

Chan wajensu mutallib gaba daya ya kasa natsuwa kwata kwata, matsalar dake gabanshi ma batasashi tsayawa kallon wani news ba balle yasan meke faruwa.
Babu taj babu labarin taj, ya sake kiran wayar yafi sau dari a kashe, jikinshi na bashi wani abu ya faru da taj din,hankalinshi ba a karamin tashe yake ba, sai faman sintiri yake, khaal ko cikin ikon allah he’s safe amma ya shiga semicoma.
Abunda ya faru jiyan bayan wayar da sukayi da taj wayar na katsewa gang leader nan ya tashi zaune yana haki, ya dubi mutab yace “nunfashinsa ya dawo amma dole yana buqatar medical attention”
Cikin murna da jin dadi mutallib ya tunkari khaal din dake kwance kamar matacce yana fidda nunfashin wahala, sai a lokacin ya tuna da akwai mutun daya da zai iya trusting ayanxu, shine babban likitan khaal wanda ke kula da iyalanshi.
Cikin gaggawa suka sashi cikin mota suka fita dashi, mota biyu sukayi daya tayi gaba gudun karya zamana ana tailing dinsu.
Cikin ikon allah suka kawoshi asibitin, mutab ya nemi ganin doc din kuma ya sameshi, suka bashi irin private dakin nan irin wanda manyan kasar ake kawosu idan ba a son sanin rashin lafiyar da suke.
Saida yaga khaal yyi stabilizing tukunna gang leader dinnan ya nuna mashi cctv cam din dayayi capturing doctor din, da yanda ya shiga yayi injecting khaal ya fita, allah yaso ko sakan goma baiba da futar shi mutab ya farka badan haka ba daya wuce haka saidai su tashi suga ya mutu, minimum time din dake shiga jinin mutun gaba daya baya wuce minti goma sha biyar.
Abu na biyu da gang leader ya fada ma mutab yasashi shiga wani yanayi mara dadi, mutane babu amana kwata kwata, cikin yaranshi akwai mutun daya da suka hada baki da doctor din, kamarma shine yake yima doc din jagora, shi doc din ya tsere don badda kama yayi shi kuma yaron ya nemi ya gudu suka kamashi, suka mashi jina jina ya fada masu komai, and he keep insisting doctor ne ya nemi su hada kai, zai bashi kudi sosai don haka baisan komai gameda waenda suka turo doc dinba.

Yanxu duk wannan mai sauqi ne damuwar mutab yanxu ta koma ga taj, rabanshi dashi tun wajen karfe uku da rabi na dare, da sukayi waya, tabbas yaji alamun taj ya futo a wannan daren hankali a tashe, kuma yana tsammanin wajensu zaizo dubaga yanda hankalinshi ya tashi da jin batun khaal, toh yanxu tashin hankalin mutallib bai wuce babu taj ba babu labarinshi, wayarshi a kashe, abu fa kamar wasa hankalin mutallib ya tashi ba kadan ba har wuraren yamma gashi khaal bai tashi ba.

Yasan yabar khaal karkashin kulawar liktan khaal din dayayi mugun mamakin ganin khaal din bai mutu ba shima koda yaga labarin mutuwarsa da scandal dinshi watannin bayan yayi mamaki sosai kuma zuciyarshi taqi yarda da hakan.
Dole mutab ya futa daga asibitin ya wuce company, koda yaje ma ya rasa ta yanda zai nemi taj din, at that point tsoro ya gama cikashi, ya fara tunin last conversation dinsu dashi, ko abunda yake nufi da last comment din da yayi kenan? “at anytime komai zai iya faruwa dashi”

Tunda ya tuna da haka ya tabbatar da suna da hannu cikin bacewar taj din.
Don tabbas jiya daya kirashi around 3am dinnan wayarshi ta mutu bai sake samunshi ba.
Yanda taj din ya tada hankalinshi jiyan yasa mutab tunanin kodai wani mugun abu ya sameshi ne? Baya fatan haka amma ina taj????
akwai matsala babba, ina taj ya shige? Daga daren jiya zuwa yanxu? Fatanshi daya allah yasa ba wani mugun abu sukayi mashi ba gashi bazai iya zuwa gidanba.

Island…
Anatse ta futo daga cikin yatch dinta ta nufi inda motarta take, da mamaki take kallon sabon driver da aka kawo, kallon black dake taaye da driver tayi yayi saurin tarar nunfashinta “welcome madam”
“Wannan fa? Ina tsohon driver yake?”
Shuru black yayi chan kuma yace “ he’s gone”
Batayi questioning dinshi ba don ya rigada yasan komai wannan Yasa ta shiga motar shi kuma ya bita a baya.
Suna karasowa yayi hanzarin bude mata kofa ta futo suka nufi cikin uncompleted building din.
As usual shigewa kawai tayi cikin dakin black ya tsaya daga waje, dakin duhu dum yauma saida ta kunna hasken wayarta sannan ta kutsa kai dan nesa da mutumin dake zaune.
Farar kujerar dake wajen taja ta zauna tana fuskantarshi ya juya mata baya amma yasan itace ta shugo.
“Abdallah!!!”
Bai juyo ba haka zalika bai amsata ba.
“Taurin kanka babu inda zai kaika, koka fada min sirrin dakake magana akai ko kuma ka kare rayuwarka anan”
“Babu abunda zan sauya daga maganata,”
Ya juyo a fusace kai saida ya bani tsoro wallahi, fuskanshi abun tsoro, he looks so familiar don’t kamar na taba ganinshi.
“Abunda bokyason ji kuma kika kasa yarda dashi,”
“Babu yanda za ayi na yarda da maganrka, karyane karyane karyana”
“Kina kan bakarki ta cewa shi mahaifinki shine yaci amanar mahaifiyarki kenan?”
A fusace ta miqe tsaye idanunta yayi jaa sosai kamar ta shaqeshi, itafa duk maganar da za ayi kan mahaifiyarta sai inda karfinta ya kare

“Saina wulaqanta rayuwarka,akan mahaifiyata zan iya komai”
…”zakiyi dana sani a lokacin da lokaci ya kure maki”

Juyawa tayi a fusace ta futa daga wajen, taci karo da black dake tsaye yabi bayanta.
Tunda ta fito ta cire wayanta daga plane mood calls ke shugowa daga us, tasan abunda ya danganci jamid ne and yanxu bata da time din wannan.
Abubuwan dake gabanta sun isheta,ganin call din yaqi karewa ta daga, wata baturiya ta amsa ta “good morning mrs hidaya, were happy to inform you..”
“Please i’m busy right now,“
Tana fadin hola ta kashe wayar ta jefa kala, tasan maganar da zasuyi mata bazai wuce an samu wani method din za ayi mashi operation bane ko kuma yanda zai samu sauqi.
Ana kashe wayar nurse din ta dubi jamid daya farka, ya tashi zaune da kanshi abun al’ajabi, bakinshi daya karkarce ya soma komawa daidai,
“Do you need anything sir”
Nurse din ta taimaka mashi zaune, “are you?”
Ya nuna mata wayar datake kira dashi, “yes sir, i contacted your wife, but its seems she’s busy”
Ajiyar zuciya ya sauke yace “please don’t contact her anymore, I don’t want to bother her”
Ya fadi haka ne only to stop them from contacting hidayar, yanasonsaiya samu lafiya completely kafin ta sani don yasan zata iya yin komai don ganin bai samu lafiya ba.


Mutab zauncewa ne kawai baiba, duk yanda zaiyi ya nemi taj yayi amma babu labari, ka allah bai bashi ikon kallon news ba kwat kwata, haka ya baza duk wani connection dinshi da yaran gang leaders dinnan aka soma neman taj, kwana sukayi ido bude, mutab ya rasa sukuni abun ya hade mashi ga khaal a kwance a boye, gashi ba y taj ba labarinshi, wani hali yake ciki, meke faruwa dashi? Yana ina? Allah kadai ne masani.
Amma yasan tabbas idan wani abu ya samu taj to wallahi suna da sa hannu.


The next very morning, ranar ne daman aka shirya board meeting inda aka buqaci taj din yayi presenting shaidar dake nuni da akasin allegations din da akeyi na cewa shi din ba asalin jinin gidan bane “the heir to the company”
Ana zaune for about 20mins babu taj babu alamun zuwanshi board meeting, hidaya na zaune ta daura kafa daya kan daya tana kallon munafukan dasukabi bayan taj daya dawo kamfanin, masu daga wuya kan dole sai an sauya leadership an bashi don shine heir.

Kallon juna kawai sukeyi gaba dayansu don kowa ya san qin zuwanshi abunda zai haifar, yana nufin bashida shaidar da zaiyi protecting kuma kamfanin bazaibar hannun hidaya ba har abada.
Gyaran murya tayi tana dubansu tace “are you still going to risk our comapny? What we build for over the years? Kunsan cikin kwana biyu yanda stock dinmu ya sauka kasa? Is that not enough reason for all of us to make reasonable decisions?”
Ta karashe tana bugun table din gabanta
“But ma’am…”
Wani

47 / 107