Advertisements
Chapter 88 Reading Matar Taj Book 2 Complete Hausa Novel BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Matar Taj Book 2 Complete Hausa Novel

Author :  Queenmerh Category :  Complete Novels

Chapter   88 / 107

261K to 264K   out of 320.4K words

hakan yasa ta yi shuru.

Daidai nan taj ya shugo gidan da sallama, da kyar sameer ya iya amsa mashi, ganin yanayin kowa yasa shi tambayar ko lafiya?
nanna ce kawai ta iya cewa ya samu waje ya zauna.
Ganin anne ma ta kasa cewa komai yasa nanna cewa ''yaya…ki mana bayanin abunda ke faruwa?''

Dakyar anne ta samu ta danne zafi da dacin da takeji aranta ta kalli rabi, wanda hakan yasa rabi ta soma magana kamar haka, ''jiya misalin wajen karfe sha biyu aka kirani daga security post kan cewa wata bakuwa tazo tana nema, ina futa sai naga wannan''
tayi nuni da jamila, ''kawar hadiza ce, don ta taba zuwa sau daya gidan nan, saina tambayeta dalilin nemana da take sai tace wai tanason na kaita wajen anne, ni kuma nace indai bata bani kwakwaran dalili ba babu abunda zaisa na kaita, nan ne take shaida min rayuwar yar hadiza wato sabeeha na cikin hadari, kuma ba kowa ne ke kokarin sata cikin hadari ba sai hadizar, wadda ta kasance ba mahaifiyarta ta asali ba a cewar jamilar, jin wannan yasa na amince muka dauki drop zuwa ga asibiti wajen hajiya, muna zuwa na kaita har wajen hajiya''
tana fadin haka ta dakata, fadila ta dubi jamila sai a lokacin ta tuna da, ta ganta asibiti kuwa tabbas lokacin ta futo daga dakin anne ita kuma a lokacin taje ganin doctor kan prescription din anne…

A day before (Abunda ya faru a jiya).
rabi da jamila na isowa asibiti da sallama rabi ta bude kofar bedroom din anne jamila na biye da ita, lokacin kuwa anne ce kawai a dakin, cikin sauri rabi ta karaso cikin ladabi ta gaishe da anne, jamila ko tana daga tsaye, saida rabin ta gama gaisheta kafin ta gaishe da annen itama cikin mutunci baza kace tazo da wani abu aranta ba.
jamila bata bama rabi damar yima anne bayanin ko ita wace ba da dalilin zuwanta kai tsaye ta fada mata yanda take da hadiza sannan tace mata tazo ne wajenta da magana mai nauyi kuma mahimmiya wadda ta shafi ahalinta, anne najin haka da mamaki ta buqaci rabi ta futa ta basu waje, rabi na futa jamila ta dubi anne sannan tace.
''ba komai ne ya kawo ni ba sai dan na fada maki wani sirrin da ba kowa ya sani ba dagani sai hadiza.''
Jamila ta danyi shuru kafin ta cigaba, ''dalilin dayasa nace ya shafi ahalinki kuwa shine, fatima wato yar hadiza ba yarta bace ta asali yar bahijja ce''
confusely anne ta kalleta, jamila na ganin haka tace ''nasan bazaki manta da ranar da hadiza da bahijja suka haihu ba, tabbas a wannan ranar muka sauya yaran ba tare da sanin kowa ba… idan baki yarda ba zaki iya yin bincike akai saiki nemeni don ni banida da asara''
jamila na kaiwa nan ta tashi sannan ta mata sallama ta futa, ko tsayawa taji me anne zatace batayi ba, zabi ne tabarta dashi kota yarda ko kar ta yarda.
fadin irin tashin hankalin da anne ta shiga bata lokaci ne,sai kawai ta tuna ranar da aka haifesu.
jamila na futowa ko jiran rabi batayi ba ta kama hanyarta, rabi ta koma dakin anne ta mata sallam lokacin fadila ta dawo daga wajen doc so batasan meya faru ba, rabi na komawa gida anne ta kirata a waya, tana dagawa ta umarceta data nemo mata gashin sabeeha ko kuma brush na wanke baki, rabi batayi qestioning dinta ba tayi abunda tace, tana daukan brush din sabeehar ta taho asibitin,yanda anne ta umarceta kan cewa karta bari kowa ya sani hakan tayi kuwa.
bayan barin asibiti da rabi tayi a daidai lokacin ne kuma bahijja ta iso, saboda kiran gaggawa da anne tayi mata, itama dai tana zuwa anne tasa doctor ya deba jininta, bahijja was so confuse bama ita kadai ba hatta fadila, saidai ganin yanayin annen yasa basuyi questioning dinta ba.
A ranar anne tasa ayi maternity DNA test, test din dake daukan kwana biyu kafin result ya futo a ranar anne tasa ayi cikin gaggawa, misalin wajen karfe sha biyun dare kuwa dr barau yayi mata presenting result, gabanta na faduwa ta bude result din, tabbas sabeeha yar bahijja ce ta asali, a daren dai anne kasa barci tayi tana hawaye, tashin hankalin data shiga yasa jininta hawa sosai, dakyar aka samu yayi regulating, washe gari kuwa tayi insisting dole a sallameta daman a ranar ya kamata a sallamota.
''hadiza ta cucesu ta cucesu cutar da har abada batajin bahijja zata iya yafema kanta, tana rike da yarda ba tata ba while tata na rayuwar wulaqanci, don ba tun yanxu anne ta lura da yanda hadiza ke treating yarinyar ba, ta rabata da iyayenta tun daga haihuwarta innalillahi wa inna ialihi rajiun, hadiza ta cucesu ta cucesu, gaba daya ahalin gidan, har zuwa lokacin anne ta kasa gane wani dalili ne zaisa hadiza ta chanza yar bahijja da tata,''


cigaban labari….
anne na hawaye ta soma magana ''tabbas fatima yar bahijja ce wadda suka sauya ta da maya lokacin da aka haifesu''
take kowa ya zaro ido in so much shock, tuni maya ta nemi natsuwarta ta rasa, tama kasa gane inda gabar maganr take, wannan wani irin magan banza sukeyi? ta tambayi kanta.
hamad ko da sameer babu abunda suke sai kallon anne baki a bude, jamila ko babu abunda take sai murmushi.

Hankali a tashe fadila ta soma magana ''ya zaayi ta zama yar bahijja anne?'' bata kaiga karasawa ba ta dakata tunawa da ranar da aka haifi maya, tabbas in bata manta ba tare suka kai bahijja da hadiza asibiti, don ranar a tare suka fara naquda.


Jikin bahijja na tsuma ta miqe tsaye, ta tunkari inda anne ke zaune ga envelop a hannunta, tayi saurin karba jikinta na rawa, tundaga lokacin da anne ta soma magana ta shiga tashin hankalinda gaba daya ji take dama nunfashinta yabar jikinta.
idanunta na cike da kwalla hannunta na rawa ta bude papers din, bata gama bude takardar ba duka idanunta ya sauka kan sunanta, ''DNA maternity test result, Name; Hajiya bahijja santuraki, and ''Fatima,''
tana kai idanunta kasan paper din inda aka rubuta result taga an rubuta probability of maternity test 99.9%''
tana ganin haka ta soma jin wani juyayi kunenta ya toshe gaba daya kanta yayi dummm, a take paper ta sulale, majeed dake zaune gefenta yayi saurin mikewa ya dauki papers din ya bude shima yana karanta bai kaiga dagowa ba sai jin bahijja yayi ta soma cewa ''innalillahi wa inna ilihi rajiun….innalillahi wa inna ilaihi rajiun, na shiga uku, innalillahi wa inna iliahi rajiun, majeed yatace da gaske, yatace…what have i done???? tana fadin haka ta sulale kasa.
shima dai takardar faduwa tayi daga hannunshi, gaba daya hannunshi sai faman karkarwa yake yana kallon sabeeha, tabbas tundaga ranar daya sanyata a idanunsa yaji wani abu game da ita.
Tuni nanna ta runtse idanunta sai hawaye, hadiza ko dora hannu kawai tayi aka tana kukan munafurci.

Tuni hankalin maya ya tashi tana daga zaune tana kallon mummynta dake hawaye tana kuka, me mummy ke magana akai?, wacece yar hadiza? wai meke faruwa ne?'' haka ta dunga tambayar kanta.

fadila da taga yanayin da suka shiga itama miqewar tayi ta dauka takardar ta soma karantowa, tuni hawaye ya soma sulalo mata ta miqawa sameer dake gefenta takardar, tayo kan hadiza a guje, ta soma bugunta kamar an aikota, nanna na hawaye ta soma kiran fadila, ''fadila fadila '' amma ina bataji bataji bata gani,

taj da tun shugowarshi idanunshi ya kaiga sabeeha ganin yanayin daya ganta yasa ya kasa natsuwa, controlling kanshi kawai yake saboda ita, saboda bayanson ya nuna akwai wani abu tsakaninsu badan haka ba, bayajin zai iya zama yana ganinta tana hawaye gashi baisan dalili ba, gashi babu wanda ya bashi damar sanin abunda ke faruwa sai binsu kawai yake da ido.
karban takardar dake hannun sameer yayi shima ya soma karantawa, yana gama karantawa ya dago da kanshi ya kalli sabeeha, sannan ya maida dubanshi ga bahijja in so much shock, gaba daya yafi shiga confusion don baisan meke faruwa ba.

''me muka maki?me muka maki?, duk abunda muka maki ta hanyar nan zaki saka mana?'' fadila ta fada tana ihu tana dukan hadiza.

hadiza fa saida ta rasa natsuwarta saboda irin dukan da fadila ke mata jamila na daga gefe sai faman taunar gums dinta take hankali kwance, kwata kwata bata ma tunanin ko zasu sa a kamata ita da hadizar kai ko an kamata wallahi tasha don burinta ya cika,

''ya isa fadilaaa ya isa'' nanna tayi magana dakyar tana kukan tausayin bahijja da sabeeha data fashe da sabon kuka dukda tana cikin rudu da tashin hankali magnagnunsu na zuwa kunenta, kuma ta kasa yarda da hakan.

''ki barni nanna, ki barni na kashe tsinanniyar nan, kin cucemu kin cucemu,yau shekaru ashirin da biyu kenan, muna barci cikin kwanciyar hankali ba tare da sanin yarmu na chan wata duniyar ba? a wulaqance?, ke kuma taki tana nan cikin jin dadin rayuwa? ba a rageta da komai ba? wannan wani irin baqin zalinci ne, wallahi bazaki taba samun rahamar allah ba hadiza wallahi saikin gwammaci baki taba sanin ahalinnan ba''

anne dai na daga zaune ta kasa cewa komai sai hawayen da takeyi,tanajin guilt din komai, tabbas a lokacin da aka sauyasu allah ya nuna mata ta wata sigarda dan abu kadan zatayi da zaiyi preventing sauyasun da sukayi, saidai kuma saboda yanda bason auran majeed din da bahijjan take ba yasa kwata kwata bata maida hankali ba musamman akan abunda ya shafesu, ko haihuwar ma bawai nuna jin dadinta tayi ba lokacin da bahijjar ta haihu, amma tabbas a lokacin da aka sauyasu allah ya nuna mata amma taqi yin komai akai, she choose to turn a blind eye on it.

fadila na tsaka da jibgarta suka soma jin jiniyar motocin DSS,
Jikin maya na rawa ta miqe hankali a tashe sai yanxu kwakwalwarta ta fayyace mata komai, suna nufin an sauyata da sabeeha? sabeeha ce yar asalin daddy da mummy ita kuma itace yar mai aikin nan hadiza?'' bakinta na karkarwa ta dubi hadizar sannan ta dubi sabeehar ta dubi daddy da mummy, ta fashe da kuka tana juya kanta, ina bazai yuwu ba bazai yuwu ba, bazai taba yuwuwa ba ta kasance yar mai aiki,

bakinta ra rawa ta soma magana ''wallahi karya ne, ni ce yar mummy, ni ba yar mai aiki bace, karya ne wallahi, ni kadai ce yar mummy naa'' tuni ta furgice hawaye na sauka kan fuskarta harda majina, duk suka bita da ido, bahijja ko kasa kallon kowa tayi musamman sabeeha, ya zata kalli yarta? da wani irin ido zata kalli yarta ta asali?, innalillahi wa inna ilaihi rajiun, da kanta ta so illata yarta,da kanta ta nuna tsana mafi muni gareta, ?? take ta tuna yanda ta dunga treating sabeeha tunda ta fara ganinta, da yanda ta dunga dukanta dazu, inama ace zata iya maida hannun agogo baya?, inama ace zata bude idanunta taga mafarki takeyi, Ya allah, this is so unbearable to her, yarta tayi treating hka ba tare da saninta ba, maya kuma ba yarta bace?, ba asalin yarta bace yar hadiza ce, yarta ta asali takema kallon yar iska kuma barauniya? duk dan saboda zalincin hadiza???

Bahijja na kuka tana kankame da majeed tana hawaye shima sai girgiza kanshi kawai yake, idanunshi sunyi jaa sosai, hadiza ta cucesu ta cucesu, cutarda har abada bazasu taba mancewa ba, ta rabasu da yarsu, yarinyar da bataji ba bata gani ba, saboda wani dalili nata daban da basu san ko menene ba? shima kanshi kasa kallon sabeehar yayi, he raised yarinyar da ba tashi ba all those years, tashi kuma tana chan uwa duniya.

Babu wanda ya lura da sumewar da maya tayi sai nanna'tayi saurin miqewa ta tunkari inda take a kwance ta tallabo kanta tausayin yarinyar ya cikata, dole zata shiga shock itama.

dakyar hadiza ta kwace daga hannun fadila bakinta duk a faffashe ta miqe tsaye tana zare zaren ido ta fashe dariya ''kona mutu yanxu naci galaba akanki bahijja kodan saboda yarki dana juyawa rayuwa kuma na tabbatar rayuwarta ta wulaqanta tun haihuwarta,kin ganta nan saida na tabbatar batasan wani abu waishi gata ba balle jin dadin rayuwa,kima godewa allah ban watsa ta duniya ba ta zama kwantacciyar karuwa mai lasisi koba komai na dandana maki zafin cin amanata da kikayi, ay wallahi duk abunda na maki baikai kwatankwacin abunda kikayi min ba, wallahi wallahi bahijja indai ina nunfashi bazan taba bari ki samu farin ciki ba ke bake kadai ba duka ahalin nan''
tana cikin magana batayi auni ba saiji tayi an kwasheta da mari, dagowan dazatayi sameer ya sake sauke mata wani marin, a daidai lokacin kuma wasu samudawan DSS officers suka shugo, su kusan biyar rida rida dasu, baqaqe suna sanye da baqaqen kaya da bindigu abun tsoro.

daman musamman anne ta kira general director dinsu tun kafin su dawo gida, ta shiada mashi crime din hadizar da jamilar, daman kwana tayi da tunanin wani hukunci ne ya dace dasu,don duk abunda zatasa ayi masu batajin zai wanke laifukan abunda hadiza tayi.
Anne na daga zaune tayi instructing a fita dasu, take hankalin jamila ya tashi don batayi tsammanin harda ita za a hada ba amma ta dake don koba komai dai ta tona asirin hadiza hankalinta ya kwanta.
kafin a futa dasu hadiza tace ''banyi asara ba kona mutu na aje maku tabon da har ku mutu bazaku manta dashi ba,''ta karaashe tana kallon gaba dayansu ,yanda fa hadiza ke maganganu kwata kwata babu any remorse ko regret
jamila dataga da gaske harda ita za a hada a tafi, tuni yayanta suka zo ranta, tace
''hajiya hardani za a hada? nifa yar rakiyace? itace ta shirya kuma ta gudanar da komai''
hadiza ta dubeta da fashesehn lebe tace ''au bakisan da haka ba sai yanxu? ay tunda kika tonan asiri nima saina tona naki wallahi, sai duniya tasan da hannunki kika kashe tsohon mijinki tsinanniya''
''akwai tsinanniya data wuce ke? shi uban wacchar yarinyar da kike ikirarin kunyi aure kema ay kasheshi kikayi, au nama tuna ashefa bata da uba ko yar taki?'' jamila ta bata amsa, filin saiya zama kamar na bankade bankade.

suna kallo aka fita da ita da hadiza, yanda ma dss dinnan ke jansu kamar dabbobi.




MATAR TAJ (destined with you)
   Written by 
          Queenmarh

Book2 
PAID
Chapter 108

TAKAITACCEN LABARI
SHEKARUN BAYA DA SUKA WUCE
Gidan Alhaji santuraki, gida ne mai jama'a ta kowanne fanni tun shi kanshi alhaji santurakin na raye, harya rasu ya samu shaidar taimako musamman ga waenda basuda karfi, hajiya anne ta kasance mace jajirtacciya kuma tsayayyiya mai zafin nema kamar yanda taga mahaifinta nayi, sannan ta bangaren taimako kuwa harma ta wuce mahaifinta wajen kyautatawa mutane musamman marasa karfi harma da waenda ke karkashinta, musamman ma'aiktanta, hadiza da inna wato mahaifiyar hadiza sun kasance ma'aikatan cikin gida tun mijin anne na raye, lokacin hadiza na budurwa inna tazo da ita gidan,anyi zama na amana da mutuntawa shekara da shekaru daya sanya anne daukar nauyin hadiza tayi sponsoring iliminta na boko, babu abunda ta nema ta rasa kama daga sutura mai kyau da cima mai kyau, da abubuwan da baza a rasa ba daya danganci buqatun budurwa, cikin yayan anne bahijja ce kawai tazo sa'a daya da hadiza kuma suka shaku sosai, don bahijja tana da hakuri da son mutane, abun duniya bai rufe mata ido ba kuma kwata kwata bata taba considering hadiza yar mai aikinsu ba, wannan yasa hadiza da bahijja suka taso a tare don fadila ta girmesu, ita harta gama karatu, idan kaga hadiza bazaka taba cewa ba yar gidan bace yar mai aiki ce, don an dauke mata komai kamar yanda aka dauke ma yaran gidan,daga kan sutura har abunda baza a rasa ba, sai abun ya zo da suma yayan gidan basu da kyamar talaka don tarbiyyar da aka masu kenan dukda sun kasance yayan masu arziki sosai.
Yanda za a fita dasu a mota a duk lokacin da suka buqata haka hadiza ma ke fita itama, don driver daban aka fidda masu, duk wata kuwa yanda za a bawa babarta albashi haka anne zata bata allowance na kashewa kuma bawai don tana yin komai ba sai dan kawai ta kashema kanta.

Ta samu gatan da gaba daya rayuwar ta bata taba tsammanin zata samu ba saboda irin rayuwar da sukayi tun a lafia kafin su shugo abuja ita da babarta neman na kashewa don su rufama kansu asiri tun bayan mutuwar babanta.

Sakewar da hadiza ta samu har ta kaiga zakace itace yar masu gidan, harma taso ta fisu wajen jiji dakai da dagawa, daman hausawa nace wa dan talaka bai iya samun waje ba,jin kanta take tafi kowa. 
Yau itace fada da masu gadi, jibi itace da driver, don su kadaine sukasan halinta.

inna ko ba karamin dadi taji ba da wannan karramawar da aka mata da yarta,dukda sun kasance yan aiki kawai a gidan, basu hada dangi dasu ba kwata kwata,don saboda talaucin da suke ciki ne ma yasa ta futo aikatau da yar tata, don tunda ubanta ya rasu suke rayuwar wahala, cimar da zasu kaima cikin su ma wahala take balle akaiga karatu,gashi innar na bala’in son hadizar, don ta dauki alkawarin bazata taba barinta tayi rayuwar wahala ba tunda suka shigo abuja, toh itama dai innar da nata kudirin, saidataga yandq aka rike hadizar ne yasa ta aje duk wani kudirin data taho dashi garin, daman burinta bai wuce hadizar ta samu ilimi ba tayi aure cikin arziki don su kaucewa talaucin da suka baro a gida.

Tasowarsu bahijja da hadiza ta kunshi abubuwa da dama, ciki kuwa shine baqin ciki da hassada tsantsa da hadiza keyi da ita,musamman data kasance sa'arta, ta tsani bahijja batare da tayi mata komai ba saboda kawai ta fita komai, daga kan ilimi har kyawu na halitta,  batada abokiyar hamayya kamar bahijja, kuka bawai nunawa take ba, a ciki take dauke da wannan qiyayyar da baqin ciki, inda da akwai yanda zatayi tayi replacing bahijja da kanta datayi, bakin cikin da take da ita har takaiga ko kaya bahijja ta saka irin wanda bata dashi tana bakin cikin shi, kuma duk yanda za'ayi saitayi irin kayan ko kuma ta raba bahijjar da kayan, ta hanyar lalata

88 / 107