Author : Queenmerh Category : Complete Novels
take magana zaka dauka kamar da danta take sannan zakayi tunanin she's worried of him, nan ko allah kadai yasan meke cikin ranta, shiko ya dauka she's worried ne kuma ta damu ne shiyasa take tambayar hakan ya sashi soma magana cikin ladabi, ''naje gym ne, didnt know you called ,''
shuru kawai tayi tana kallonshi don tabbatarda gaske yake maganar, ganin irin kallon da take mashi ya sashi kama hannunta yace ''i'm sorry for worrying you first love''
kauda idanunta tayi daga kanshi
''karka sake futa ba tare da sanina ba sannan duk abunda zakayi ka fadamin''
abunda taso fada mashi kenan saidai tsoron karya zargi wani abun ko yayi sensing wani abun yasa ta basar da zancen daidai nan wayarta ta soma ringing tabar inda yake, shiko ya bita da idanu harta wuce sama,sauke ajiyar zuciya yayi jin yanda zuciyarshi ta mashi wani irin nauyi sosai,sabeeha dake tsaye daga wajen dining area gaba daya maganganun da sukayi taji, daman fitowarta kenan daga daki zata nemi abunda zataci, har hidayar ta wuce sama, tunda ya tsaya sabeeha ke kallonshi, ya sauya gaba dayanshi kamar bashiba, badan ta san muryarshi ba zata rantse bashi bane, personality dinshi ya sauya haka zalika facial and physical appearance dinshi, saida ya soma takowa daidai wajen stairs tayi saurin komawa sako yanda bazai ganta ba tana dafe da kirjinta, sautin takun tafiyarshi har cikin zuciyarta takejin shi, yau tunda ta tashi da fargaba ta tashi, daman idan har wani abu yana shirin faruwa wadda tasan outcome dinshi ba mai kyau bane haka takeji, yanxu data ganshi da hidaya kuwa sai fargabar nata ya tsananta, yanda takeji kamar ana ingizata, so take ta fayyace mashi komai saidai babu halin yin haka, tasan tabbas hidaya bazata fasa kokarin cutar dashi ba koda kuwa batayi yanxu ba tasan nan gaba zatayi, kuma alamu ya nuna tana son manipulating dinshi, tana hango fargabar da take ciki na tsoron karya gano komai, yanxu hakan ma tasan tayi sanyi saboda tana tsoron karya tuna, dole tasan yanda zatayi ta kusanceshi, to amma ta yaya?, how can she be close to him again?,how can she make him trst her kamar yanda yayi a baya?, bayan hidaya ita kadaice ya yarda da, yanxu kuwa baisanta ba bai ganeta ba babu yanda za ayi yayi trsuting dinta,hannunta na kan kirjinta dake mata nauyi siririn hawaye na sauka akan fuskanta.
kwata kwata bai lura da sabeeha ba dake labe harya haura sama, ya shige bedroom dinshi, jakarshi ya ajiye gefen gadon sannan ya zauna ya dafe kanshi,har yanxu kanshi ciwo yakeyi da zarar ya fara kokarin tuna abu.
hidaya ma bayan ta haura sama ta amsa wayar, idanunta yayi jaa sosai fargabar da takeyi kenan ta tabbata, tana sauke wayar daga kunenta ta damke wayar kamar zata fasa ''meysa zaije gidan khaal?, ko ya gane ya mutu ne?'' she cant predict komai, d more ta tuna wani abu saitaji gaba daya ta sukurkuce.
knocking din dakinta da akayi yasa ta dan jinkirta, fadwa ce ta shugo tana mai kallon hidayar bayan ta rufo kofar.
''ukty !!''
''fadwa please not now, i dont have time for arguement''
''niba arguement nazo muyi dake ba, we have to be on the same table ukty don mu kawo karshen matsalarmu, yanxu ya zamuyi?,''
zarya hidaya ta soma yi a cikin dakin fadwa na kallonta ''i don't know fadwa, i dont know….ganinshi kadai da nakeyi a yanxu i can't stand him, ina danasanin qin kawo karshen shi, i never knew i will be screwed up in between''
''shiyasa na fada maki mu kawo karshenshi tun kafin ya dawo hayyacinshi cikin ruwan sanyi, that was the only chance we had yanxu gashi nan ya dawo hayyacinshi, a lokacin da we never expect that, we all know what dawowar memories means, yasan koshi waye, and we cant do anything, fargaba mu yanxu what if ya tuna komai?, what if ya tuna message din da aka tura mashi kafin accident din,kindai san dukda kin goge komai daga cloud dinshi bazai hanashi iya tunawa ba ko?,''
hidaya najin haka tayi saurin runtse idanu kafin ta bude su akan fadwa ''yanxu ya zamuyi''
da mamaki fadwa ke kallon hidayar, yau ita da kanta ke neman mafita wajen wani?, tab she never expect that so soon, bata taba tunani she will be clueless, and indecisive ba very soon, the mighty hidaya her self, daman abunda take nema kenan kuma wannan dama ce a agareta, haka ta gyara tsayuwarta in a manipulative way ta soma mata magana ''yanxu kika fara magana ukty.. dole yanxu duk yanda zamuyi mu hanashi sanin duk abunda ya faru dashi,…..
jiki a mace ammu ta saki handle din dakin hidayar gaba daya jikinta ya mutu murus, jikinta har rawa yakeyi jin abunda suka fada,daman ta shigo part dinne donta duba jamid, koda ta shiga bataga hidayar ba ta tambayi nurse din dake kula shi nan ta shaida mata ay tana dayan dakin shine fa ta fito ta nufi chan din, batama kaiga bude kofarba hannunta na kan handle din ta soma jin maganganun su, tundaga farko har karshe, take gabanta ya fadi sai innalillahi a cikin zuciyarta, dakyar ta iya daga kafarta tabar part din ta nufi dakin sabeeha.
da sallama ta shugo dakin, daidai lokacin sabeeha ta futo daga bathroom ammu na ganinta tayi hanzarin kamo hannayenta ta jata har bakin gado ta zaunar da ita,kallon hannunta dake karkarwa sabeeha tayi kafin ta dago tana kallonta, tana hango tsansatr fargaba akan fuskanta da tashin hankali,''fatima!!! don allah ina rokonki ki fada min duk abunda kika sani a cikin gidan, karki boye min komai na rokeki, nasan kinsan komai kuma''
ganin hankalinta a mugun tashe yake hakan ya tabbatar ma da sabeeha taji wani abunne ko ta gano wani abun da suke shiryawa, take hankalin sabeeha ya tashi sosai, harga allah batason tace komai saidai ganin yanayin ammu yasa taji gwara ta fada mata komai at least koba komai yanxu ta fuskanci matar tana bayan taj din, ''ya akayi ya samu accident?, shin yan uwansa sunada sa hannu a cikin…''
tun kafin ma ta karasa sabeeha ta tari nunfashinta ''eh……..''
nan ta kwashe komai daga farko har karshe ta bayyana mata bata boye mata komai ba, da yanda tazo gidan,da yanda khaal ya daura aurensu da yanda taj din yasha wahala wajen yan uwansa har zuwa lokacin da sukayi poisining dinshi da labarin da mutabblib ya bata har zuwa accident din da sukayi bata boye mata komai, tana magana tana hawaye, itama ammun hawayen ta dunga yi, tana fadin ya rabbi, ya rabbi tana runtse idanunta jin wannan rashin imanin da sukayi 'sai ya zamana gaba dayansu aka rasa wa zai rarrashi wani, dakyar sabeeha ta tsagaita ta kalli ammu atace ''wallahi basa sonshi, babu rana daya da yake yinta cikin kwanciyar hankali,akullum khaal fargaba yakeyi yana tsoron abunda zasuyi nan gaba,har ya mutu yana protecting din taj daga abubuwan da takeyi, kafin ya dawo hayyacinshi ma wata kwaya take bashi wadda ake bama mahaukata,''
''ya rabbiii…wannan wani irin rashin imani ne da qiyayya, koda yake banga laifinsu ba, a nonon uwarsu suka sha, duk wannan abun da sukeyi saboda mahaifiyarsu ne''
da mamaki sabeeha ta dago ta kalleta, wanda hakan yasa ammu cewa ''nasan zakiyi mamakin abunda na fada, tabbas saboda mahaifiyarsu sukeyin komai,ban taba tunanin zasu iya illata jininsu ba dukda ba ciki daya suka fito ba amma babu komi, insha allahu, allah bazai basu iko ba, inason kiyi min taimako daya,''
cikin natsuwa sabeeha ta girgiza mata kai tace ''ki fada min koma menene ma'am, insha ALLAH daidai gwargwadon iyawata zan yi duk abunda kikace, zanyi komai don nayi protecting dinshi, i dont want him to suffer''
share hawayen fuskanta ammu tayi,she can see how young and beautiful she is, yarinyar tanada shiga rai saima an zauna da ita ake fuskantar haka,da farko tayi judging dinta sai yanxu taga how sincere yarinyar take and how honest she is, bata da wani aibu kwata kwata saidai kawai yanayin halittar bakinta, inka ganta ma bazaka dauka african bace sai tayi magana, don yanayin irin halfcast dinnan ne, she's so innocent on the outside yet strong lady on the inside, tana yaba courage din yarinyar da yanda ta tsaya tsayin daka akan taj din, tayi bearing duk abubuwan da suka dungayi that are so traumatic, idan wata ce da tuni ta gudu don zama da irin waennan babban hadari ne, babu abunda bazasu iyayi ba, zuciyarsu ta dishashe ta mutu, babu komai aransu sai hatred da fansa, ga rudun duniya take ta kara tabbatar da maganar khaal dayace mata wannan yarinyar haske ce a cikin rayuwar taj sai ayanxu ta tabbatar da hakan.
''Thank you, thank you so much, ALLAH ya biyaki da gidan aljanna, yanda kika tsaya mashi allah ya tsayar maki, you're a truly blessing in his life, khaal yayi gaskia,ke haske ce a cikin rayuwar taj, insha allah i will stand by you, zamuyi protecting dinshi kinji, komai yazo karshe bi'izinillah, yanxu duty dinmu ne mu fayyace mashi gaskia,yanxu kokarin da sukeyi na ganin sun hanashi sanin komai ne, suna tunanin zasuci galaba akanshi saboda ya mance da komai, amma ba komai allah yana tare da mai gaskia, no condition is permanent''
ba karamin dadi sabeeha taji ba aranta, kalaman ammu are soothing, saitaji nauyin dake danqare a zuciyarta ya ragu saboda sharing burden dinta da tayi da ita.
sun dade sosai suna tattaunawa akan maganganun da yanda zasu shawo kan komai.
✊💋BOSS LADIES WRITERS💋✊
MATAR TAJ (destined with you🩵🤍)
Written by
Queenmarh✍️
Book2
PAID
Chapter 63
UPDATE!!!
Monday morning…
yauma da sassafe ya sake futa kamar jiya, wajen karfe shida,sabeeha ma a daidai lokacin ta futo, ita ta ganshi saidai shi bai ganta ba, samun kanta tayi da son hawa saman nashi, tunawa da maganar da sukayi da ammu yasa ta samu courage din hawa.
ahankali ta soma bude kofar dakin, yau kwana biyar kenan rabonta da shigowa part din, bin ko''ina ta soma yi da kallo kamar yau ta fara shugowa memory din rayuwar da sukayi a cikin gidan nayi mata yawo akai, ajiytar zuciya ta sauke sai dan murmushi daya buyo baya, ta nufi bedroom din tana tafiya ahankali ahankali harta tura kofar bedroom din nashi.
wani irin daddan kamshi ne ya bugi hancinta cikin sauri ta runtse idanunta kafin ta bude, ko'ina is tidy as always babu datti ko digo saima kamshinsa mai tsadan gaske daya bade dakin daya hade dana sanyin ac, dakin kamar an saka freezer tsabar sanyi.
samun kanta tayi da kunna gaba daya light din dakin tabi ko'ina da kallo tana tuna lokacin da suke rayuwa a ciki, kamar ba ayi ba.
ganin beddings dinshi a hargitse yasa ta soma cire wanda ke kan gado ta wuce dashi bathroom ta saka shi cikin washer sannan ta fito ta wuce closet ta dauka sabon beddings ta shimfida mashi yanda takeyi lokacin da suke kwana tare.daga nan ta wuce bathroom ta gyara shi tsaf, dukda bai wani baci ba, ya sauya komai na wankanshi,sai a lokacin ta tuna da panties dinta da towel dinta dake toilet din, gaba daya bata tadda ko daya ba a cikin bathroom din, qila ma ya zubar tunda baisan kona waye ba, kwata kwata bataji rashin dadi ba don haka ta futo ta wuce closet room dinshi, tana shiga ta tadda kayayyaki sabbi a kasa, gaba daya ya fiddasu dagaqa leda harda kwalayen takalma wajenma ya zama disorganize gqba daya kamar yana kokarin shirya kayan nashi ne ya futa, samun kanta tayi da tattara kayan ta ninkesu tass ta bude wardrops dinshi, unlike yanda yakeyi ada idan zai dauka kayan da zaisa ya hargitsa su yanxu komai neat neat a jere, murmushi kawai tayi sannan ta ajiye jera sabbin data ninke ta saka mashi a ciki, wajen takalma ma haka ta tattara su ta jera mashi inda yake ajiyewa da turarrukansa kafin ta futo.tunawa da kayanta yasa ta koma closet room din ta bude wardrop gefen wajenda kayanta suke ta deba wanda zata iya kwasa ta dauka laptop dinta da khaal ya bata sannan ta rufe closet din ta fito ta wuce kasa zuwa dakinta, bata bari kowa ya ganta ba.
bangaren taj ya dade sosai yauma wajen gym yana gamawa da nan ya dawo gida, lokacin duk suna breakfast don haka yayi joining dinsu a tare, hidaya dake zaune tunda ya zauna take kallonshi ta gefen ido.
da yake baya wani cin abunci sosai sai ya riga kowa gama wa amma yaqi tashi saida hidaya ta tashi tabar wajen tukunna kafin ya tashi shima ya wuce bedroom dinshi, yana shiga yabi ko'ina da kallo ganin bai tadda yanda ya futa ya barshi ba, bai kawo komai ranshi ba don atunaninshi ko hidaya ce tasa maid ta shugo ta gyaara mashi, daman ita kadaice keda damar saka hakan don shi duk abunda ya shafesa bai fiye son maid suna mashi ba saboda yana da saurin tsantsanin abu, shiyasa ko gyara za a mashi ba kowa yake yarda ya mashi ba, particularly akwai yanda yakeson a mashi gyara komai ya zamana a daidai babu mistake.
closet room ya shiga don ya ajiye jakarshi, yana rufo kofar yabi closet din da kallo mamaki kwance akan fuskanshi, kayan daya bari akan console din walk in closet table din gaba daya babu, hatta packaging dinma an tattare gaba daya, yayi mamaki sosai wakeda audacity din taba mashi abu a cikin ma'aikatan gidan?, don bai buqaci ayi mashi hakan, ranshi harya soma baci saidai tunawa da qila hidaya ce tasa ayi mashi hakan yasa ya kauda kai kawai ya bude wajen closet wardop dinshi, kayan ya gani a jere, komai an saka shi inda ya kamata,hatta perfumes dinshi ma an jerasu yanda ya kamata…
misalin karfe daya da rabi ya farka daga barcin daya daukeshi, wani irin mafarki yayi mai dadin gaske, he can cleary see how happy he was a cikin mafarkin, wai yana daga tsaye ya rike hannayen mutane biyu wanda ya kasa ganin fuskokinsu su duka, daya na daga gefen hagunsa daya kuma na daga gefen.
mikewa yayi ya wuce bathroom yayi wanka ya dauro alwala sannan ya futo ya sauya kaya marasa nauyi.
sallah ya farayi ya dade sosai a zaune kafin ya miqe ya wuce inda ya jiye wayoyin daya sayo ya fito sitting room ya zauna.
remote din dake kan center table din parlor ya dauka ya kunna tv, tunda ya zauna wani memory din ya sake zuwan mashi, abun fa yanxu ya fara damunsa sosai, wasu abubuwa yake gani da suke bashi mamakin,he's so confuse with the situation daga remote din ma da yayi saida wani memory ya sake zuwan mashi, ganin kanshi na neman fara ciwo yasa yayi saurin kauda tunanin a ranshi, karshe ma dai ajiye remote din yayi bai chanza channel dinba ya maida hankalinshi ga wayoyin daya fito dasu, setting daya daga cikin wayoyin ya somayi ya shigarda dayan icloud dinshi a wayar sannan ya fara dannawa, emails da yawa ya tadda ritutu daya danganci kamfaninsa, duk wani abu dake faruwa a kamfanin kusan kullum sai anyi updating dinshi,dukda baiyi responding ba over a year ba a fasa tura mashi ba, tun kafin ya dawo daga london daman yabar kamfanin nashi a hannun professional business managers waenda ke mashi managing, tunda ya zauna yake bin gaba daya emails dinshi yana karantawa ya dade sosai yana bin didigin duk wasu abubuwan da ya kamata ya duba wasu daya kamata yayi responding kuma ya amsa su,har aka kira sallar la'asar don haka ya tashi ya koma bedroom yayi sallah, yana idarwa yaji cikinsa nayin kugi sosai don haka ya futo daga bedroom din ya, sabeeha najin karar kofar bedroom din tayi hanzarin fucewa jikinta har bari yake, daman suna ankare da dawowarshi ita da ammu, ganin bai sauko kasa ya nemi abunci ba yasa ammu ta turota ta kawo mashi abunci, sune ma sukayi abuncin don yanxu ammu tace akan idanunta za a dunga komai, shi daya futo sitting room tabbas yaji alamun rufe kofa baima lura da abuncin da aka ajiye mashi ba a dining din sitting room ya fuce daidai hanyar stairs yaci karo da ammu ta hawo saman, daman tun dawowarshi suna ankare dashi ita da sabeeha, yana ganinta ya tunkaro inda take cikin natsuwa da kamala yace ''masa'alkhair ammu''
''masal-ward taj, zaka futa ne?''
''yes ''
''kayi lunch kuwa?,''
''i will later '' ya amsa ta da american accent dinshi, don larabcin nashi ba wani sosai yake fita ba,
tasan daga tambayr nan datayi mashi bazai sake cewa uppan ba don haka har yayi saurin juyawa ta dakatar dashi, ''kaje ka duba jamid kuwa?''
chak ya tsaya bai daga kafarshi ba haka zalika bai juyo ba saida ta sake cewa, ''nasan bakasan bashida lafiya ba ko?,'
sai a lokacin ya juyo ya kalleta, ''me..ya sameshi''
kai tsaye ta amsa shi, ''ya samu ciwon barin jiki, he's paralysed''
take gabanshi ya fadi yayi wani irin dammm, tunda tayi magana bai sake cewa uppan ba, amma tana hango tashin hankali akan fuskanshi da rudani, tasan he will never ask hidaya abunda ya faru dashi da abubuwan daya faru a cikin gidan,don saiya jira ta fada mashi da kanta tunda ya taso he never questioned her, duk abunda tace shi daidai ne a wajenshi,
haka zalika hidayar ma tasan bazata taba fada mashi komai ba kuma tasan kudirinta nayin haka, so suke su barshi cikin duhu duk don su samu abunda suke neme kuma su toshe hanyar da zaisa ya gano gaskiya, wanda ta yanke bazata taba barin hakan ta faru ba,koda kuwa bazai yarda da maganar ta ba.
kallonshi kawai tayi saita girgiza kai ta tako inda yake ta kama tace '' zo'' ta kama hannunshi suka nufi part din hidaya, tunda suka tunkari bangaren nata gabanshi ya soma faduwa, take jijiyoyin kanshi sukayi jaa sosai kamar wani wanda keda trauma haka ya koma lokaci guda, tsabar tashin hankali, janshi kawai ammu keyi don gaba daya hankalinshi ya tafi wani wajen yayi zurfi a tunani, bude kofar ammu tayi suka shige daga ciki, jamid na daga kwance an bashi magani yasha, nurse dake kula dashi tana ganin shugowarsu tayi saurin miqewa ''ma'am madam tace kar abar kowa ya shugo''
wani irin kallo ammu ta mata kafin tace ''idan tazo kice mata ni ce nan na