Author : Queenmerh Category : Complete Novels
jiji da kanshi da nuna isa da izza da girman kanshi yana bata haushi sosai, kamarma jira yake ita ta gaisheshi kenan yake nufi koko yaya?,
sai bayan ya zauna ne ammu tace ''bismillah!!'' kowa ya fara ci, maid ta danyi serving dinshi few abubuwan da yakeci, normally da safe saiyasha hot espresso coffee tukunna kafin ya sama cin abunci, sannan daman shi ba komai yakeci ba.
kallon maid din dake wajen hidaya tayi kafin tace ''make hot espresso with low calories milk''
'yess ma'am''
futa maid din tayi donta hado coffee din, cikin mintuna qalilan saiga maid din ta dawo da coffee din, tana ajiyewa ya dago da kanshi, ba zato ba tsammani hidaya taji tambayarsa ''banga akhi jamid, ko yayi tafiya''?
shuru kowa yayi aka rasa wanda zai amsa shi, daidai nan barad ya dago ya kalli mamanshi, allah yaso ta kalleshi cikin ido ta gwabeshi don haka yayi shuru, yana mamakin uncle taj, ya sauya ba kamar uncle din daya sani ba wanda suke wasa da aunt sabeeha.
Ganin kowa yayi shuru yasa shima bai sake cewa komai ba, har sukayi nisa wajen cin abunci, ''ahh ina matar tashi ban ganta ba?….''
nanma dai shuru akayi babu wanda yace qala, shi taj baima san shi take nufi ba, yawanci daman shi magana bata dameshi sosai ba,
''nayi waya da afiya, tana nan dawowa yau ko gobe'' fadwa tayi saurin kauda tambayar da ammu tayi, hidaya ko miqewa tayi ta fuce daga dining area din, ammu na ankare da su, saidai batace komai ba ta basar da zancen.
bai wani ci sosai ba ya tashi shima ya fuce daga dining area din, ya wuce sama.
saida kowa ya watse ammu ta miqe ta wuce bedroom din datake tunanin sabeeha na ciki.
bakinta dauke da sallama ta shugo, a zaune ta tadda sabeehar jingine da gefen gado, hijab din jiya ne a jikinta ta raqube gefe guda.
tana ganin ammu tayi saurin miqewa kanta a kasa har ammu ta karaso inda take, sabeeha na ganin fuskarta ta ganeta, don haka tayi saurin duqawa ta gaisheta cikin kamala,
zama ammu tayi gefen gado ta fuskanceta kafin ta soma magana ''zauna!!!''
zama sabeeha tayi chan gefe ta maida hankalita ga ammu,
''dago ki kalleni'' ammu ta umarceta dagowa sabeeha tayi saita kasa kallon cikin idanunta saboda nauyinta datake ji kawai
''inason ki fada min abunda ke faruwa a cikin gidan, karki boye min komai ki fada min duk abunda kika sani na cikin gidan nan''
shuru sabeeha tayi ta rasa ta ina zata fara, tama rasa amsar da zata bata kawai sai taji hawaye na saukowa daga kan fuskarta, ganin hawayen dake sauka kan fuskanta yasa ammu cewa, ''karki damu you can trust me kinji,naji magamganun da kukayi keda hidaya ranar da kuka dawo daga asibiti, ina neman karin bayani inason nasan komai saboda haka karki boye min komai''
ganin ta kasa cewa komai yasa ammu ta dafa kafadunta muryarta a karye tace ''dont worry take your time, i will be waiting for you, if you feel like you can open up to me kinji, naga bakiyi breakfast fa why''
''zanyi anjima''
''no get up, kije kiyi breakfast okay?''
girgiza mata kai sabeeha tayi tana mai jin wani irin sanyi aranta magana kawai datayi da ammu.
bayan futar ammu daga dakin ta kudirci duk yanda zatayi ta jawo sabeehar a jiki don taga alamun ta wajenta ne kawai zata samu amsoshin da take nema at the same time batabar observing dinta ba.
yau kwanan su uku da dawowa daga asibiti, har yau babu wanda yace mashi komai, shima kuma bai sake maganar ba saidai abun na cinshi sosai aranshi, duk dare kuwa haka yake kwana feeling so lonely ya rasa dalili, dakin ya mashi fadi sosai.
tun kafin ya buqaci keys din mota da waya hidaya tayi mashi providing sabbi gudun karya tambayi tsohuwan wayarshi da motanshi, da cards dinshi, daman tasan he will never question her don haka hankalinta ya dan kwanta, neman mutalib kuwa bata fasa yinsi ba, kamfanin taheel kuwa yanxu data san kamfanin ya dawo hannunta gaba daya hankalinta a kwance yake saidai tsoronta daya kar zancen samun lafiyarshi ya futa don wannan zai iya jawo mata matsala, bayan wannan ma yanxu data tabbatar da shine babban investor din kamfanin komai zai iya lalacewa,risk din lossing kamfanin ba karami bane, gashi bazata iya tunkararsa da maganar sponsorship din da yake bayarwa kamfanin ba da identity dinshi saboda tana tsoron kar wani abun ya buyo baya ko ya tuna wani abun wannan yasa ta danyi sanyi.
misalin karfe 4 na yamma ya sauko,sanye da wannan fararen kayan sun amsheshi sosai ya fuce daga gidan.
daidai nan sabeeha ta fito daga bangarensu daya zagaye walkway din hawa stairs, haka kawai taji yanayin bugun zuciyarta ya sauya kuma a daidai lokacin ya fado mata arai, yau kwana uku kenan rabon data sanya shi a idanunta, idan tace kwanakin nan tayishi cikin sauqi tayi karya, he has become part of her, data tunashi sai ta dunga jin kamar wani bangare daga jikinta is not part of her, yayi mata nisa, baima san ko ita wacece ba, a wajenshi she doesnt even exit,jikinta gaba daya yayi sanyi, taanason ta ganshi, she miss yanda suke hira, da yanda yake mata shagwaba and all, harga allah tanajin inama zata iya zuwa ta ganshi saidai tsoron yanda yayi acting ranar take, kayanta ma dake part dinshi haka ta hakura dasu, allah yaso tana da few kaya anan part din kasa, sauke nauyayyiyar ajiyar zuciya tayi ta wuce kitcehn wajen ammu data zo ta kirata don suyi girki tare.
gaba daya maids din gidan ammu ta kora suka tafi bangarensu sai few da suke harkar abinci ta tsaida don su taimaka mata da sabeeha wajen girki, ahankali ahanakli ammu take janta a jiki harta fara sakin jikinta, haka suka dauka wajen awa biyu suna girke gieken larabwa sabeeha na kallo tana koya abun gwanin ban sha'awa.
bangaren taj bayan futarshi bai tsaya ko'ina ba sai one of the popular gym waenda sukeda kayan activities sosai, baya wasa da wannan harkar, saida yayi renewing membership a wajen kafin ya wuce wani hadadden barb shop, tunda ya shugo gaba daya ya cikama mutanen wajen idanu, ba tare da wani bata lokaci ba ya buqaci abunda yakeso a mashi, aka mashi gyaran fuska dan cute sajenshi daya zagaye fuskan nashi aka gyara mashi sannan aka mashi aski na zamani, take ya fito kamar bashiba, masha allah, waiii, sai yayi kyau sosai kwarjininsa ya kara bayyana, shidai a jininshi yake, ya dan dade anan kafin ya fito ya wuce apple shop ya saya brand new phones har guda biyu, daga nan ya sake wucewa babban mall din dake jedda ya saya kaya masu kyau da gym outfit dinshi, kusanma yafi jidosu da yawa da pjs, harda mayukansa dadai sauransu,turaruka ma haka ya kwasosu daga gani ma'abocin son kamshi ne, bashi ya fito daga mall ba sai wajen nine, saida ya tsaya ya kwaso chocolate masu yawan gaske a wani choco bar kafin ya nufi hanyar dawowa gida.
calmly yake driving din motar hankali kwance , sanyin ac na bugun shi, he's so calm and hard at the same time,bakinshi yake motsawa ahankali yana taunar chocolate din, yanda yakeci ma abun kallo ne, fuskanshi tayi kyau sosai hancin nan ya fito zuwait, gashi da cikar gira, lips dinshi daidai bakinshi, gaskia yana da kyau masha allah, sai ayanxu ne ma nake ganin kyawunshi na dabanne irin wanda ba a resisting kallo, komai cikin natsuwa yakeyi,yana karasowa gida yayi parking, bai kashe motar ba ya dan dade sosai a zaune cikin motar, take tunanin memory din daya zo mashi ya fado mashi arai, bayan futarshi daga gidan yana hawa babban titi kawai memory din yayi flashing akanshi.
wai ya futo daga gida, yana cikin driving wayanshi ya dunga ringing daga annonymous caller, bai akwo komai aranshi ba don haka yaqi piking call din ganin call din yaqi karewa yasa ya daga wayar, he cant recall abunda yaji a cikin motar sai kawai ajiye wayar da yayi daga nan kuma yana cikin driving din ya soma danna wayar har idanunshi ay sauka kan messages din da aka tura mashi harda audio recording, daga nan ne kuma ya kasa tuna komai, take yaji kanshi ya sara mashi yayi saurin dafe steering shi, saida kan nashi ya lafa ya bude idanunshi ya suake su akan yatsun hannayenshi, take wani memory din ya sake zo mashi gashi yana daga zaune yana dariya ga wata (sabeeha) tana yanke mashi farce, lokaci guda ya zama very confuse, wacece ke yanke mashi farce?, and why is he happy?, ''what's this memory?, god'' ya daki steering din motar yana mai cije lower lips dinshi, forcefully yakeson ya tuna komai ya kasa, rai a bace ya futo daga motar, yana shgowa cikin gida ya tadda kowa a zaune banda hidaya, kota kansu baibi ba ya wuce sama….
***
yan dubai…
yau kusan kwana uku kenan suna neman flight from dubai to saudia basu samu ba, su sonata hankali ya tashi, dakyar suka samu flight in 2days, bataso haka ba duk wannan tashin hankalin don ta ga zaddy take yinshi, afiya kuwa so take taje gidan ta tabbatar da gaske ya dawo hayyacinshi ko kuwa….
Mu hadu gobe insha Allah,…
Please karki karanta in kinsan baki biya ba.
You can pay into 8032542629
Opay
Rukayya umar…
Mu hadu gobe don jin yanda zata kasance…💃🏻💃🏻
Sighned queenmarh…
✊💋BOSS LADIES WRITERS💋✊
MATAR TAJ (destined with you🩵🤍)
Written by
Queenmarh✍️
Book2
PAID
Chapter 62
Update!!!
washe gari tun wajen karfe shida ya futo daga part dinshi, yana sanye da fitting sleeveless hoodie blue da cross trainer shorts, sai wani footwear jordan a kafarshi, a banyanshi kuma ya rataya gym duffel bag sai katon water bottle a hannunshi, lokacin ma'aikatn gidan kowa ya futo ya fara hidimar aikin gabansa, basu lura dashi ba saida sukaji takun tafiyarsa da kamshinsa da yayi masu maraba, gaba daya binshi suka dunga yi da idanu, da yake zancen samun lafiyarshi ya zagaye gaba daya kunnuwan ma'aikatan gidan kowa mamakin ganinsa ya dunga yi waenda basu san da warkewar tasa ba kuwa tambayr koshi waye suka dunga yima kansu, don gaba daya ya sauya, gyaran fuskan da yayi da askin da yayi ya sanya asalinshi ya futo, wasu da suka gane koshi waye kuwa mamaki suka dunga yi, gaishesa suka dunga yi, ba tare da ya kallesu ba yayi responding dinsu da kanshi,cleaners din parlor har ya fice binsa suke da kallo suna admiring dinshi, parking ya nufa ya ajiye jakarshi a booth din motar kafin ya shige daga ciki,
bai tsaya ko'ina ba sai wajen gym&fit, lokacin daya shugo babu mutane sai couches din dake kwana anan, daman yafi prefering haka, shiba ma'abocin hayaniya bane da mutane,abunda ya kaishi shi ya farayi ba tareda ya kalli ko daya daga cikin su bayan sallamar da yayi masu.
jakarshi ya fara ajiyewa a drawer kafin ya rufe ya futo activity room, daya daga cikin couches dinne ya tunkaro inda yake friendly ya soma magana ''good morning sir''
a daidai lokacin taj ke kokarin daga wani huge 50kg dumbell, kamar bazaiyi magana ba chan kuma ya amsa shi da ''morning''
''sir are you a beginner?''
shuru taj ya mashi baice komai ba saida mutumin ya sake cewa ''may i assist you'' ya karashe yana mai kokarin taimaka mashi da dumbells din don duk a tunanin ko first timer ne, kuma yaga ya dauka 50kg,
saurin dakatar dashi taj din yayi yace ''no need''
yana kaiwa nan ya daga 50kg dumbells dinnan gaba daya da both hannayenshi, matsawa coach din yayi yana kallonshi da mamaki, bai taba tsammanin professional bane trainer bane, take musles dinshi suka fashe suka fito rudu rudu a cikin hoodie din jikinsa, salam salam coach dinnan ya bashi waje ya koma wajen mutanen trainers din da suka shigo yana mamaki.
ya dauka wajen awa biyu a cikin gym din, gaba daya ya gama zufa sosai ya jike, he looks steamy jikinshi ya murde damm, tunda ya fara workout few mutanen da suka shugo suke kallonshi, profesionally yake komai kamar wani weightlifter, bottle water dinshi ya dauka ya kafa a bakinsa, saida ya shanye ruwan protein powder din dake cikin bottle din tass kafin ya fice ya wuce bathroom din wajen don yayi wanka,
Taheel residence..
misalin karfe takwas daidai kowa ya hallara a dining, hidaya ce last din saukowa, saida tazo maids suka fara serving, ammu dai batace komai ba ta bisu d idanu, sai a lokacin hidaya ta dago ganin babu taj yasa ta aika maid ta duboshi, tareeq ne yayi saurin dakatar da ita yace ''its seems like ya futa da safe ''
hidaya najin haka ta dakata da cin abuncin, batama san lokacin datace ''ina zaije? yaushe ya fita?, maysa ya fita ba tare da sanina ba?,''
dagowa sukayi gaba daya suna kallonta,gaba daya sai sukaga kamar hankalinta ya tashi, abuncin da bataci ba kenan cikin natsuwa ta miqe tabar wajen.
binta da ido ammu tayi tana mamaki, meysa zata damu da futarshi?, shi ba yaro bane balle ace ko zai bata, idan zai fita saiya fada mata ne?tunawa da yanda tabar wajen yasa ammu ta jinjina kai.
tunda hidaya ta hauro sama ta wuce bedroom dinta don ta raba masu daki ita da jamid haka ta dunga zuba idanu ko zata ga dawowar taj shuru har wajen 9 gaba daya hankalinta ya gama tashi, gashi ta kira wayanshi babu response, ayanxu batada tashin hankalin daya wuce motsinsa, duk movement dinshi tashin hankali ne a wajenta.
wayarta ta dauka ta shigar da kira, ana dagawa takai kunenta, ''good morning madam''
bata ma tsaya amsashi ba tace ''inason ka fara tailing dinshi i want to know duk wani movement dinshi da abubuwan dayakeyi karka bar komai inason ka buncika min i need everything he has been up to''
''yes ma'am''
tana kaiwa nan ta kashe wayar, tana zarya a tsakanin dakin.
ya dade sosai a tsakiyan shower ruwa na dukanshi, he feels so lightweight muscles dinshi sun amsa sosai, idan bai motsa jikinshi ba yanajin kamar wanda bashida lafiya shiyasa ya zame mashi kamar hubby, kuma saiya zamana abun ya zama part of lifestyle dinshi tun yana london, tunda ruwan nan ya soma sauka akanshi yayi shuru ya yana nazari, kanshi fal yake da tambaboyi kala kala, duk wani activity da zaiyi yanxu saiya tuna mashi da abubuwa sosai, abunda yafi damunshi sosai shine yarinyar dayake yawan having memories dinshi da ita, ya kasa gane ko ita wacece, how did she end up a gidan sannan ya akayi ya samu kusanci da ita sosai, har zuwa yanxu baisan cewa yarinyar daya gani a asibiti itace yake having memories da ita ba,shiba ma'abocin sanya abu bane arai saidai yanxu ya kasa hana kanshi da tunanin abubuwa da dama, he really wants to know rayuwar da yayi abaya, shekara dayan da ya kasa tuna komai.
baima san hidaya ta kirashi a waya ba saboda a mota ma yabar wayar saboda bai saka icloud dinshi ba, baima fara amfani da wayar ba yanda ya kamata, ya dade sosai a tsaye cikin shower kafin ya futo ya sauya kaya zuwa kayan dake cikin jakarsa wanda suka amshesa sosai.
futowa yayi ya nufi inda motarsa take wajenda yayi parking, ya budeta sanna ya jefa duffel bag dinshi a bayan seat sannan ya zauna mazaunin driver yaja motar.
ahankali yake driving, babu sautin dake tashi sai na ac daya kure sosai, peacufully yake tafiya babu wani hayaniya, harya nufi hanyar gida lokaci guda khaal ya fado mashi arai, tunda suka dawo daga asibiti bai ganshi ba, lokacin daya dawo daga london kusan kullum saiyazo gidan donya ganshi, bashida kusanci sosai da khaal hasalima shike jawoshi jikinsa dukda shi yana baya baya dashi hakan baisa yasan irin son da khaal yake mashi ba, kuma ya damu dashi sosai don ko achan london din khaal yana kokarin zuwa don ganinshi, shi dinne ma bai fiye sakin jiki dashi ba.
samun kanshi yayi da juya akalar motarshi ya nufi gidan khaal din, cikin natuswa yake tuqin motar tashi lokacin wajen karfe tara ta gifta ana neman wajen karfe goma, tafiyar minti goma ta kawoshi street din gidan khaal, tun daga nesa ya soma hango yanayin gidan harya karaso, anan bakin gate din gidan yayi parking ya futo yanabin gidan da kallo, an zagaye gidan da wani rope sai sign din SAMA (saudi arabia monetary authority)da aka kafa a kowanne sashe na gidan, bin ko'ina ya soma yi da kallo kanshi gaba daya ya kulle, kodai he's mistaken ba nan ne gidan ba?, tabbas gidan khaal ne nan don washe garin ranar daya dawo khaal din da kanshi yayi insisting saiya kawoshi gidan, he cant be mistaken but meysa yaga an kafa SAMA, (sama kungiya ce ta gomnatin kasar da take kwace gidaje daga wajen masu laifi waenda sukayi laundering kudi ta banki ko kamfani) sanin me hakan ke nufi yasashi jin akwai matsala,
yau kwana biyu da bai ganshi gidan ba ya tabbatar mashi akwai abunda ya faru kenan, cikin motarshi ya shige, baima bi takan tons of misscalled din daya tadda cikin wayar ba ya shiga setting wayar, icloud dinshi ya saka ya fara kokarin shiga contact yaga wayam, babu contact ko daya akan icloud dinshi, da mamaki yake kallon wayan, yana tambayar kanshi how is that possible?,abun mamaki bama contact dinshi kadai ba hatta messages dinshi anyi wiping tass babu komai kan cloud din, lokaci guda yaji this is not right, wakeda access da icloud dinshi da har zai mashi wiping up komai?,
kunna motar yayi kawai tare da yin reverse yabar wajen yana nazari.
gida ya wuce direct yayi parking motarshi kafin ya fito da jakarshi a hannu, cikin gidan ya nufa ya bude, yana shugowa main sitting room ya dakata ganin hidaya a tsaye ta harde hannayenta a kirjinta, yana hangota ya sauke kanshi kasa tare da karasowa inda take, yanayin fuskanshi na nan yanda yake kamar nata shima bai fiye murmushi ba sannan baka sanin yanayinshi, yana cikin farin ciki ko baqin ciki, expression dinshi is very hard to guess
tunda ya tunkarota take binshi da idanu, tun kafin ma ya gaisheta yanda ya saba ta jefo mashi tambaya ''ina kaje?, meysa ka fita da sassafe, and why didnt you pick up your call inata kiranka?''
yanda take magana zaka dauka kamar da danta