Advertisements
Chapter 72 Reading Matar Taj Book 2 Complete Hausa Novel Hausa Novels
Advertisements

Matar Taj Book 2 Complete Hausa Novel

Author :  Queenmerh Category :  Complete Novels

Chapter   72 / 107

213K to 216K   out of 320.4K words

dinshi yanda ya futa ya barshi haka ya dawo ya taddashi, ko dinner din jiya ba a kwashe ba, ganin haka ya tabbatar mashi bata shugo ba.
Sama ya wuce zuwa bedroom dinshi shima yana nan yanda yake dan ya hargitsashi ya watsa papers da yake review din ayyukansa da laptop dinshi, he was never a dirty person kuma yanason ko’ina ya zama organize amma saboda yanason ya kasan ce da ita tunda ya lura idan tazo abunda ya kawota kawai takeyi ta futa wannan yasashi yin haka don ta dunga dadewa yanajin motsinta a kusa.
Bathroom ya wuce shima dai kana ganinshi kasan ba a gyara ba kwata kwata, hakan ya sashi dan jin dadi don yana expecting zatazo tayi gyaran, yamayi tunanin ko tazo ta tafi har allah allah yake ya dawo daga futar dayayi don baiyi niyar futa bama dande kawai yanason ya miqar da muscles dinshi data nannade mashi jiya, ya zama weak lokaci guda saboda kawai yayi kissing dinta.
Haryayi wanka ya sauya kaya ya zauna yana duban laptop dinshi babu ita babu labarinta babu breakfast kuma.
Yakai wajen awa guda shuru, daman saida wata zuciyarshi ta ayyana mashi bazata zo ba, gudun hakan ne ma yasa tun farko ya biye mata data nuna bata sanshi ba, don idanda yayi insisting zata dunga distancing kanta dashi ne.
Samun kanshi yaui da aje laptop din ya miqe tare da sanya bathroom sleepers dinshi ya futa.
Kasa ya sauko daidai nan aka kwankwasa kofar ya kafe wajen kofar da idanunshi don son ganin ko waye zai shugo, basira da allah allah take ta shugo don yaune ta taba shugowa bangaren tana bude kofar tayi saurin dagowa tare da washe baki, tuni tray din hannunta ya nemi subucewa, jikinta ya fara rawa, bata taba ganinshi so close ba sai yau, saidai ta ganshi daga nesa ko taji bilki na maganar sa.
“Wayyo allah” ta fada kamar wata zararriya saitaji kamar zatayi futsari ga wani gumi daya tsatsafo mata tsabar kyawunshi daya kidimata.
Take ya hade ranshi sosai kamar bai taba dariya ba, ranshi ya wani irin mugun baci ya dubi tray din hannunta da gumin fuskanta ke neman duga akai.

“Who d hell are you?” Yayi magana kamar da tsawa tsawa, basira aka sake kidimewa kamar ta ajiye tray din ta ruga a guje, “where’s the other maid??” Da turanci yake magana basira ko turancin babu sai kadan kadan shima don ta taba yin aiki a lagos ne, wannan yasa takeji amma mayarwa ke bata wahala sai dan pigin”
“Good moni sir, me i go wash and clean here today!”
Saurin kauda idanunshi yayi ganin haka yasa basira tunkarar wajen dining jikinta na tsuma zata aje yayi saurin dakatar da ita, not looking at her site cause he feel disgusted yace “take it back, and call the other maid” ya sake magana cikin husky voice dinshi da bai cika fiddata ba sai idan ranshi ya dan baci, wani irin kwarjini yake dashi dakesa hankalin mutun ya tashi lokaci guda.
Tuni tayi saurin juyawa tana janyo dankwalinta dqke neman faduwa don ko hijabi bata saka ba ta taho, gaban rigar duk a jiqe don bata dade da gama yin wanke wanke ba rabi tace mata tazo taje takai breakfast dinsa sanna ta gyara part din nashi tunda sabeehar jikin babu dadi.
Kamar wadda ake ingizowa haka ta dawo main house ta kitchen ta biyo tana shugowa ta aje tray din tana nishi kamar wadda tayi tsere, dakin rabi ta nufa tana faman susar kai tana shugowa rabi ta kalleta a burkice.
“Ke ya haka kamar wadda aka wullo daga sama”
“Anty rabi…anty rabi..”
“Ke nutsu mana, kin gama gyaran ne”
“Billahillazi bazan kara shiga bangaren nan ba,”
“Meysa?”
“Ni wallahi tsoro ma yake bani na rantse da Allah, kin ganshi kamar ba mutun ba, allah mai halitta yanda yaso, koroni yayi yace wai fatima taje”
“Baki fada mashi bata da lafiya ba?”
“Yoh ina zan iya anty rabi? Ko idanunshi kasa kalla nayi, wallahi ko taku biyu banba yace na futa”
Shuru rabi tayi tana nazarin yanda za ayi, ba huruminta bane shiga bangarenshi don ita ke kula danan, kuka tunda fatika ta fara gyaran part din bai taba cewa ta futa ba dukda ba utace ta fara aiki a part din ba wannan yasa ta gane ya aminta da gyaran fatiman don gaskia tafi basira tsafta sosai kuma daga yanda anne tayi bayanin yanda za adunga kula da bangarensa ta gane shi mai son tsafta ne sosai,
Kallon basira tayi ganin yanda gaba dayanta sai a slow, kana ganinta kaga zubin kauye kwata kwata bata wayewa, gashi dai suna samun ci mai kyau da sha mai kyau don harda turare ma ana basu kayan wanka kuwa sabulu mai kyau ake basu amma gata nan dai saika rantse bata wanka ko dan baka ce, fatarta bata gogewa kwata kwata.
“Mtew kema jibeki dan allah kamar wata jaka, matsa dan allah” ta fada tana miqewa ta nufi dakinsu basira inda sabeeha ke kwance.
Da sallama suka shiga dakin basira na biye da rabi, daidai nan ta budo kofar bathroom, rigar dazu ne a jikinta bata sauya ta ba, wato kwanciyar datayi ta dade kafin barci ya dauketa, bayan ya dauketa kuma bata wani dade ba ta farka jin kamar abu na fita daga kasanta wannan ya tabbatar mata baqon watanta ne yazo mata,allah yaso ma bata ciwon mara sai ciwon kafa datake yi duk wata idan zaizo mata, shika bawai ya zama mai tsanani bane, gaba daya tayi wani irin fayau lokaci guda har tayi wata yar rama.
Kallonta rabi tayi tace “sannu ya jikin? Zazzabin ya sauka?”
Dan murmushin wahala tayi kadan tace “eh”
“Masha allah maganin daman yana da kyau sosai hajiya ce ta bani zazzabin dana dunga yi kwanaki inasha zqzzabin ke tafiya,”
Zama tayi bakin gado suka bita da idanu, rabi ta zauna gefen ta, so take ta tabbatar zazzabin ya sauka kafin ta mata maganar gyaran part din.
“Anty rabi kinyi shuru.. ki fada mata”
Basira tayi magana tana duban rabi, “kinga wai basira na tura ta gyara chan bangaren tunda bakyajin dadi toh shine yace a turo wadda ke gyara wa da alamu dai gyaranki yafi so”
Kauda kai sabeeha tayi ko maganarshi bata so ayi kwata kwata, “in bazaki iyaba bari naje da kaina,”
“Wallahi kina zuwa zai koroki kema na rantse da allah” basira tayi magana tana wuce bandaki da sauri karka rabi tace mata ta koma
Tashi tsaye sabeeha tayi muryanta a dishashe tace “ah ah bari naje nayi zan iya”
Rabi najin haka tayi saurin cewa “yawwa shiknn ma allah ya kara sauqi” ta fada tana miqewa ta futa daga dakin don itama dai tsoron nashi take ji harga allah ranar daya tsare sabeeha a kitchen saida cikinta ya kada, kyawunshi mai rikitarwa ne gashi da kwarjini.
Jiki a mace sabeeha ta miqe, wajen kayanta ta nufa ta rasa me zata saka hijabanta daman biyu ne dayan jiya maya ta farkeshi dayan kuma yau tayi amai a jikinshi duk ya baci dole ta jawo wani kayafij doguwar riga da baida wani girman kirki ta dora kan rigar jikinta da basira ta bata ta saka.
Irin cotton rigunan nan ne na zaman gida wanda ake rarraba masu idan sunzo yawanci irinsu basira da ake kawowa daga kauye zaka gansu ko kayan kirki babu haka suke zuwa.
Futa tayi ta nufi hanyar kitchen ta baya ta futo ta nufi part din, slippers ne kawai a kafarta daya bayyana yan kananun toes dinta farare tass jijiyoyin kafar nata sun fito dake farar kaface, tunda ta fito wata iriyar iska ke kadata tana shiga sassan jikinta, duk ni’imar dake lulube da iskar baisa taji saukin abunda takeji aranta ba, da ason ranta ne wallahi bazata taka zuwa inda yake ba da kafafunta saidai kash babu yanda ta iya.
Tana zuwa daidai kofar gabanta ya soma tsananta bugu sosai, kwata kwata tunaninta ya rarrabu kashi kashi, wanda hakan yasa batama san a wani yanayi take ciki ba physically.
Knocking tayi ahankali kafin ta sanya hannunta dake karkarwa wajen handle din tana kokarin budewa aka budo daga ciki, kamar allah allah yake ta shugo yana jin an taba kofar ya karaso wajen, din daman bai tashi daga inda yake ba tun bayan futar dayar maid din.
Jira kawai yake ta shigo ya sanya ta a idanunshi ko zai ji sauqi aranshi, tsakanin jiya da yau ya kasa gane yanayinshi ya kasa gane tunaninshi, ya kasa gane kanshi gaba daya ma, zuciyanshi ne kawai ke controlling dinshi, kuma ya kasa hanata yin hakan.
Maybe kodan ya dade yana son ganinta, jikinshi na begenta, daman ance action speaks louder than words bazai iya expressing komai ba a baki amma gangar jikinsa da zuciyarta taki yarda ya yaudari kanshi.
Har mamakin kanshi yake kamar wanda is obsessed with her, actaully he is din baisan hakan ba sai yanxu.
Kallo daya ta mashi gabanta ya wani irin fadi don saida jikinta ya amsa don a gaskia yau sai taji tana jin kwarjinin sa sosai, abunda ya faru dasu a bakin kofar ya dawo mata sabo fill, yanda ta dunga jin nunfashinsa a kan fusknta,yanda bakinsa ya dunga yawo cikin nata ,yanda ya dunga kissing dinta deep kamar his life depends on it.
Cikin sauri ta dauke idanunta akanshi tana kokarin hana kanta wannan tunani mara amfani, shiko tunda ya zuba mata idanu ya kasa daukewa, a fuska dai bazaka tantance meke yawo aranshi ba, don fuskanshi bai chanza ba, kallonta kawai yake kamar wani sabon kamu tundaga tsakiyan kanta da iska ke kada mayafin, gashin edges din daya kusa cike gefe gefen fuskanta ya bayyana baki wuluk, idanunta yabi da kallo datake jujuyashi, tanada irin hazel brown greenish idanu da saika kureta da kallo sosai zaka gani, shidai bazaice ya taba mata irin wannan kallon kurillan ba duk zamanshi da ita, cause this look is kinda different don akwai affection da attention cikinshi, maida dubanshi yayi ga hancinta daya danyi pointing daidai fusknta daya karama fuskan nata kyau, he find it so attractive, maido da dubanshi yayi ga dan bakinta daya dunga kissing jiya, yanda ta saki lebban nata da suka dan bushe amma they look moist yana hango yan kananun hakoranta, sai guda biyun nan na gaba da aka gyara mata saima ya kara mata kyau.
Gaba daya ya shagala da kallon nata itako sai a lokacin tayi takaicin futowa haka, sanin ita ba ma’abociyar saka bra ba.
Hade rai tayi sosai tana jan mayafin nata don ta rufe sosai, ba tare da ta kalleshi ba tace “good morning sir, if you excuse me i will like to do my job”
Kallonta yake sosai kamar baisan tanayi ba yana mamaki kafiya irin nata, she’s still acting as if yesterday doesn’t happened, kamar yau ta fara ganinshi, baisan cewa the most peaceful people are the ones that are very hard to deal with.
Kamar ba fatiman daya sani ba, yarinyar dayake mamakin yanda take da hakuri sosai.
Baice mata komai ba ya matsa gefe ta shugo ciki ya rufe kofar.
Kitchen din part din ta nufa yana daga tsaye ya saka hannunshi cikin alji’un shi harta fito hannunta rike da vacuum cleaner, pillows din parlorn ta fara tattarawa sannan tayi connecting ta fara goge gogen parlor, yi tayi kamar babu existence dinshi a wajen kamar he’s invisible to her, shiko kallon ta kawai yakeyi duk inda ta gifta akan idanunshi.
Tana gamawa ta kinkimi vacuum din ta wuce sama dashi, aranta tana fatan allah yasa karyace zai biyota don a taorace take sosai dashi gabanta na mugun faduwa soaai allah allah kawai take ta gama ta futa.
Fatanta bai karbu ba don tana shugowa taga yanda gaba daya bedroom din yake a hargitse tasan zata dan jima kafin ta gama, kuma da gayya yayi hakan, haka nan ta fara kokari yaye duvet din gadon tana cikin nadewa kamshinsa data barshi dashi a kasa tajishi a kusa da ita sosai, take gabanta ya sake faduwa ta danne zuciyarta ta cigaba da abunda take,
“Fatima!!!“
Ya kira sunanta ahankali, saida jikinta ya amsa amma tayi kamar batasan yanayi ba.
“Fatima i’m sorry….”
Itace kalma ta biyu dayayi using wajen yi mata magana, chak ta tsaya da zare duvet din da takeyi, hawaye takesonyi amma ta hana kanta, “I’m sorry for not trusting you bibi, I’m sorry for…”
Da sauri ta juyo hannunta na karkarwa tace “sorry????”
Takowa ya somayi tayi saurin cewa “sir please…i don’t know who you’re mistaken me for, i don’t know what you’re talking about, i don’t know why you’re doing this to me, this is so unfair, you touch my body unwillingly to me, why are you doing this to me?”
Ta karashe tana neman fashewa da kuka yayi saurin takowa inda take, tayi baya sosai kiris ya rage bata fada jikin gadon ba.
“Fatima please..this is enough, i know that i have no right to be face you after all you’ve gone through because of me, i have wronged you for not trusting you, for everything..please fatima”
Saurin toshe kunenta tayi kamar zatayi hauka tace “please stop…stop…” jikinta ya soma tsuma, zafin jikinta ya zurfafa ta bude jajayen idanunta tace “I don’t know who this fatima you’re talking about but please ka kyaleni ka rabu dani, why is it so hard for you to just leave me alone? I’m just a mare house-help nothing else, why are you trying to force me while i dont even know what you’re talking about”
Runtse idanunshi yayi ya bude su ya kalleta yace “khaal..khaal is alive”
Karatun bakinta daban na fuskanta daban,don yana hango yanda ta shiga wani shock, “khaal bai mutu ba yana raye, kuma na gane komai, na gane irin rayuwar danakeyi da yan uwana yanda suke fatan ganin bana raye, up until not im hating and regretting not trusting you, for everything youve done for me, for trying to make me understand,..”
karasowa yayi dab da ita soaai saidai akwai yar tazara a tsakaninsu sosai, “na gane komai, kuma up untill the last minute they didn’t hesitate to kill me, fatima you made me who i am today,without you i would have been history fatima, I’m hating my self for letting go of you please….
“Na shiga uku” ta wani fashe da kuka mai tauma zuciya jikinta na mazari, take hankalinshi ya tashi ya wani irin rugumeta sosai tuni ta saki jikinta kamar an zare duk wani energy dinta, turashi takesonyi amma ta kasa ya kamo waist dinta sosai ya sata jikinshi ya rufeta sosai, duk kamshin dake tashi a jikinsa baisa tayi calming kanta ba, ta dunga fizgewa tana kuka sosai.
Shiko babu abunda yake sai dabbing bayanta yanajin zafi soaai, baisan cewa yayi hurting dinta sosai ba sai yanxu, kuma har yanxu yana tuna last kalamn datayi masa daya koreta, maysa bazai bude idanunshi yaga gaskiyar dake gabanshi ba,har sai lokaci ya kure, idan lokaci ya kure he will regret it gashi kuwa yanxu he is regretting it more than anyone else.
Har cikin zuciyarshi yakejin zafin hawayenta da kukanta dake futa ahankli ahankali data gaji da tureshin ta hakura, saida ta natsu ya soma jin zafin jikinta na shigarshi sosai,
Shuru sukayi for about 5-10 minute a haka tanajin bugun zuciyarshi yana jin nata shima ahankali, rankwafo da kanshi yayi daidai wajen kunnenta ya sauke mata wani irin lausassan nunfashi dataji gaba daya jikinta ya sake rikidewa
“Are you sick?you body is hot”
Yanda yayi maganar saida yasa tsikar jikinta tashi sosai, da harta shagala da warm jikinsa sai kuma ta dawo hayyacinta gashi jiri jiri na neman dibanta.
Matsawa yayi yana kallon fuskan ta gaba daya ta wani sauya launi.
Lashes dinta duk sun jiqe da hawaye ta rufe idanun nata, ko gama matsawan baiyi ba tayi baya baya luuu zata fadi saboda wani irin jiri daya debeta yayi saurin taro ta fadi jikinshi, take gabansa ya fadi sosai, ya kara jin temperature din nata nata rising, gashi tana neman rurufe idanunta alamun yana cinta sosai.
Cikin saurin ya dan duqa ya dauketa chass kamar yar baby batada wani nauyi kwata kwata yabi fuskanta da kallo, karasawa yayi bakin gado ya dan hau tare da kwantar da ita ahankali kamar ya dauka kwai.
Tallabe kanta ya farayi ya jawo pillow ya saka yanda she will be confortable.
Sanyi ac dakin yasa ta fara karkarwa, yayi saurin janyo duvet din datake kokarin sawa a gadon ya luluba mata, ya kashe sanyin ac din dakin ya sauyashi ga heater kadan,
Miqewa yayi tsaye yana kallon fuskanta hawaye na sauka ta gefe, bakinta na karkarwa.
Closet ya nufa ya bude jakarshi, normally yana aje self medic-kit a cikin luggae dinshi incase of emergency yana treating kanshi which is good akwai wasu situations din da ba sai an jira likita ba considering anything can happen at any given time musamman shi da yakeda self medication certificate yana treating kanshi.

Daukan kit din yayi ya futo dashi zuwa bedroom din ya aje gefen bedside sannan ya zauna bakin gadon, yanda ya barta haka ya taddata tanata juyi.
Bude medic kit din yayi ya zaro wani dan kwalba da syringe, shi kadai ne pain relief din da zai mata don daga ganin yanayin jikinta zazzabin ya shigeta sosai yanda ya hau sosai kafin ya sauko zata sha wahala, a gurguje ya hada alluran sannan ya janye duvet din, hannunta ya daga ya janye hannun rigar ya fara kokarin neman jijiyan hannunta, bai wani sha wahala ba ya samu yayi injecting alluran, dukda yanayin datake ciki baisa ta danji zafi ba tace “ouchhhh” ta tabe bakinta.
Kamar shi ke jin zafi yayi saurin cewa “sorryyyyyyy” ya shafa kanta, mayafin yayi baya, janye mata shi yayi, ya samu access to gashi ta ya soma shafawa ahankali ahankli kamar yana lallabata.
Wata ajiyar zuciya ta soma saukewa ahankali ahankali tana fidda nunfashi, tana hawaye,

Matsowa yayi dab da fuskanta ya goge hawayen dake sauka kan fuskanta yana kallon fuskanta hawayen na sake futowa kamar ana janshi ya dora lips dinshi kan goshinta da yayi zafi sosai yayi kissing dinta ahankali “sorry bibi..”
tana jinshi fa bawai bata jinshi ba kawai dai abubuwa ne sun mata yawa, ga zazzabin ya dameta sosai babu yanda ta iya sai yanda yayi da ita.
Cire lebbanshi yayi ya miqe ya wuce bathroom ya dauka wani karamin towel ya juqoshi da luke warm water ya fito yasa mata asaman goshinta. Ya tsaya yana kallonta yana duban agogo, cikin abunda bai wuce minti

72 / 107