Advertisements
Chapter 31 Reading Matar Taj Book 2 Complete Hausa Novel BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Matar Taj Book 2 Complete Hausa Novel

Author :  Queenmerh Category :  Complete Novels

Chapter   31 / 107

90K to 93K   out of 320.4K words

san yayi subutar baka ba, dariyar manyanta ammu tayi tace “it happens sometimes, probably she’ got scared of something ko she’s stressed, yanxu haka na bata magani tayi barci..amma mey ya faru jiyan naji kana cewa its your fault”
Shuru yayi ya kasa bata amsa sai miqewa yayi yana zuban agogon hannunshi yace “zan dan fita”
Yana kaiwa nan baima jira amsarta ba ya fuce.
Girgiza kai kawai ammu tayi bayan futarsa tana mamakin abubuwa da dama.
Shidai ya gama confusing dinta da maganganunshi.

Anan kasa har zai haura sama hidaya ta sakko tana waya, yanda ya saba haka ya gaisheta sannan suka nufi dining badan yaso ba don yaga nan ta nufa itama.
Su afiya da sonata da suka ganshi kamar daga sama ba karamin mamaki sukayi ba.
Suna cikin cin abunci saiga ammu ta shigo dining din rai a bace, gefenta maida ne har guda biyu.
Kallon inda sonata take ammu tayi tana gefen taj sai wani shigige mashi take, “keee”
Yanda ammu ta kirata saida kowa ya fuskanci tana cikin bacin rai, maids din dake gefenta ta kalla suka watsa akwatin sonata a kasan.
Gaba daya miqewa sukayi sonata tayi gaggawar zagayowa wajen kayanta ta tsaya, suka duk suka karasowa wajen banda taj dake zaune yana cin abuncinshi hankali kwance kamar baima san me suke ba.
Kallon afiya ammu tayi rai a bace tace “ke kika kawo wannan tsigaggiyar gidannan ko? Na dauka iya badala da iskanci ne kawai akanta ashe har sata takeyi?Bakusan mutun ba bakusan daga inda yake ba kun kwaso kun kawo shi cikin gida,“
Afiya ce rai a bace ta soma magana “ammu menen haka? Waye tayi ma sata?“
Zaro wani tambatsetsen gold bars ammu tayi daga cikin akwatin harda sarka tama afiya nuni dashi tace “meya kawo wannan cikin kayanta”
Ba karamin mamaki afiya tayi ba ganin sarkarta cikin kayan sonata, sarkar dake cikin safe dinta kuma babu wanda ke shiga dakinta sai sonata, gold bars din kuwa daga dakin hidaya suke, itama tayi mamaki sosai yanda akayi suka shiga cikin akwtin.
Sonata da mamaki ya gama cikata kasa cewa komai tayi, nan ta fara zazzaga masu turamci, “who dares to lie on me? I didn’t do that..impossible i will never do that”
Ammu dai hannu tasa ta kwade ta da marin da saida taga taurari, sonata na rike da kunci ta dau hannu zata rama taj ya daka mata tsawa, ashe yana kallonsu ta gefen ido, tuni tasha jinin jikinta, ammu ta dubu afiya tace “zan mata karya ne?” Kallon maids din ammu tayi tasa suka bude wani sashe daga jakar suka kwaso wasu kwalabe, da kwayoyi, abortion pills ne, harmfull drugs ne harda poison
“Idan su bazasu koreta ba ina fata wannan zaisa ka kaika koreta ko, tunda a gabanka ta kusa kashe barad da sabeeha”
Ay hidaya najin an kira sunan danta hankalinta ya tashi ta kalli ammu tace “whats going on here ammu? Ta kusa kashe barad? Wani barad din?”

“Danki mana, ranar suna backyard shida sabeeha ta aiko da wannan maid din da juice da sunan ni na aiko masu susha su mutu, allah yaso taj yazo wajen kuma yayi gaggawar hanasu sha da tuni ta kashe su.”

Rai a bace hidaya ta kalli afiya da sonatar, tabbas ta tuna sanda suke qulle qullen su na ganin sun kawar da sabeeha saidai batayi tunanin zasu hada da danta ba, lallai yau mai rabata da sonata sai Allah.
Afiya babu abunda take sai juya kai alamun babu ita cikin wannan,
“Head maid”
Hidaya ta kwala kira nan take ta karaso, “call polisey, rn”
“Basai kun kirasu ba suna waje” ammu ta dakatar da hidaya.
Afiya dai ammu ta bata mamaki sosai ba kadan ba, don shedun data kawo cikinsu babu wanda yasan da maganar juice din da suka saka poison a ciki, kuma poison din a cup din sabeeha ne kawai banda na barad, hatta maid din ma da suka saka takai ma su sabeeha juice din saida suka tabbatar maid din tabar gidan, wato tana ma ammu wani kallo kallo she’s actually a sniching old rag, tasan me takewa and she knows how to play dirty as well, dole tayi laying low for now kar a gane tare suke yin duk wannan katabarar da sonata, kuma yanxu ta kara tabbatar da sabeeha da ammu are planning something..kuma cikin nan dole ta tabbatar babu shi a jikin sabeeha, daman hidaya cw kawai zata samu da maganar amma yanxu batajin hidaya zata saurareta, tana kallo police mata suka shigo suka tarkata sonata daketa faman turanci, turancin da ya kasa fiddata daga tarkon da ammi ta dana mata.

Ana fita da ita taj ya miqe yabar wajen ammu ma tafita suka bar hidaya da afiya, hidaya ta soma zazzagawa afiya masifa, “wallahi wallahi yanda tabar gidan nan zaki iya barinshi i will forget you are my blood sister akan barad, how dare you collide with that bitch? Har zata kashemin dana..toh wallahi zan iya komai akan dana, be warned”
Tana kaiwa nan tabar afiya tsaye rai a bace, bata taba tsammanin hidaya zata gaya mata wannan maganganun ba sai yau a matsayinta na yar uwata, har tana cewa zata iya yin komai akan danta kuma zata iya mantawa da ita yar uwarta ce ta koreta??????hmmm

Sonata dai an kara gaba sai aje chan ayi zaman jail, bayan an yanke mata hannu don hukuncin sata kenan anan saudi ga attempt of murder and she deserves it.

Ammu kuwa tana barin wajen dakinta koma wajen sabeeha data tashi har tayi wanka taji jikinta ya daina mata ciwo sosai.
Sama ne dai taqi yarda ta koma don gaba daya fargaba take ji.
Ammu na shugowa suka gaisa sannan zaunar da ita ta soma mata bayanin abunda ya faru jiya don tasan itama tana cikin rudu, nan ta shaida mata maganganun dataji sonata da afiya nayi na abortion pills da suka bata da plan din da sukayi na drugging dinta don su deba jininta ayi binciken ko akwai ciki a jikinta don su tona masu asiri wannan yasa ta san yanda tayi ta kori sonata daga gidan, abu daya ne bata gaya mata ba maganin data saka masu cikin dessert dinnan, sabeeha dai daga maganganun ammu ta fuskanshi komai saidai batace komai ba, lokaci guda ta zama wata shuru shuru.
Ganin batace komai ba yasa ammu tace “ki kwantar da hankalinki kinji, kome ya faru taakanin ki dashi ba haramun bane fatima, mijinki ne, kuma wannan maganar cikin danake ta kokarin rufewa kar a gane saboda karsu wulaqantaki ne kuma karsu koreki bazan gaji da fada maki cewa kece haske a cikin rayuwar tajudeen ba, kece katangar dake bashi protection daga sharrin yan uwan, komai zai wuce kinji”
Hawaye na sauka idanun sabeeha kamar bazatayi magana ba chan tace “ammu ya tsaneni, bazai taba karbana a matsayin matarsa ba, ni zan fada mashi gaskia kawai”
“No fatima bazai yuwu ba, dun abunda mukayi ya tafi a banza kenan, yanxu dai kinga ahankali ahankali yana ganin komai duk abunda ke faruwa a gidan nan, kuma yasan gaba daya yan uwansa ba abun yarda bane tunda kinga a gabanki ya kubutar dake daga sharrinsu”
Sabeeha dai bata ce komai ba kawai ta jinjina kai.


Bangaren tareeq tun yabar gidan nan ya kasa sukuni, wajen abokinshi ya fara zuwa ya zayyane mashi komai da abunda ya gani garda recoridings din daya gani, nan abokin ya bashi shawarar kawai su tona mata asiri, its a win win for him, yaje wajen yar uwarta hidaya ya nuna mata, tareeq dai dayasan halayensu gana daya bai dauka shawarar abokinsa ba, mutun daya ne kawai ya kamata yaga wannan which is tak shima yasan idan ya nuna mashi bazai taba yarda ba, don yanda yaga hotunanshi a dakin ya tabbatar akwai wani abu tsakaninshi da fadwa.
Toh ina ma amfanin nunawa, he will just use it and threaten her don ya samu abu a wajenta ya kara gaba.
Da wannan ya kwanta barci dakyar a gidan abokinsa.
The next day bayan ya farka a barci yazo shiga bathroom kenan yaji muryar abokinshi yana waya, baisan dawa yake ba amma yanda yakejin abokin na responding yasa hankalinshi tashi.
“Zaku iya zuwa yanxu yana barci, zanyi kokarin ganin bai fita ba..but as you promise zaku turamin complete kudina”
Daga chan bangaren aka amsa kafin ya kashe wayar ya kyakyace da dariya, yana magana da kanshi, “hahah kaifa dan iska ne..akan kudin ka saida abokinka, who cares, inma kasheshi zasuyi nidai idan kudi na yashigo hannu na shikenan”

Tareeq feels betrayed bai taba tsammanin haka daga wajen babban abokinshi ba, they have been together since childhood tare suke duk wani shaqiyancinsu, kuma sun san sirrikan juna ya tabbatar yanxu haka fadwa ce ta nemeshi tayi bribing dinshi with her power don tasan su tare shikadai yayi mata introducing as his closest friend, baiyi tunanin she can go to this extent ba, which mean he’s a threat to her kennan,

Ganin bashida sauran time yasa ya dauka wayanshi da gold bars dunshi da sauran abubuwan sa mai amfani ko kayansa bai dauka ba ya fuce daga gidan bayan ya tura report zuwa ga civil force defence harda evidence na scams din da abokinsa keyi da illegal abubuwan da yakeyi ya kara gaba.

Tareeq na futa akazo aka tafi da abokin sa,san abun duniya ya jawo masa yaci amanar abokinsa gashi ya koma kansa.

Tana tsaye bakin motarta taji wani baqin shade akan fuskanta babu abunda take jira sai call, ayko yana shugowa ta amsa wayar maganganun da akayi mata daga cikin wayar yasa ta doka tsaki…”you’re fucking useless…ku nemoshi na baku nan da awa daya adul inda yake”
Tana kashe wayar wani call din ya shigo taqi dagawa saida ta shiga motarta ta kunna wani call din ya sake shugowa ta amsa dake wayar is connected to motar anajin me ake cewa.
“Calm down my baby..za a na maki alkawarin bazai fita daga kasarnan ba kuma duk insa yake zasu kawo maki shi”
“Just handle him” ta daka wata tsawa kamar mahaukaciya kafin ta fuzgi motar ta kara gaba.

Tareeq na shiga motarshi ya cire sim dinshi ya yarda, yama rasa ina zaije dake yasan hanyoyin smuggling a cikin kasar don yayi harkar nan ba sau dayaba ba sau biyu ba wannan yasa ya shirya ma barin kasar da daddare zuwa london to secret route da akebi illegally, kwata kwata bai duba internet ba daya duba zaiga an sakashi he’s wanted nemanshi akayi, saida yaje zai sayarda motarshi yagane neman shi akeyi, allah yaso sun bashi kudinsa kafin su kira line din da aka saka idan an ganshi a kira, haka nan ya zama abun tausayi yana boye boye kanshi, bai taba tunanin fadwa will go to this extent ba, da farko yayi niyar ya kara gaba ne kawai bazai sake dawowa kasar ba daga baya kuma dayaga abubuwan datayi mashi da yanda ta nemi tona mashi asiri ta fallasa duk wani abunda yakeyi that is not legal yasa yaji haushi shima, don ta gama yi mashi iyaka da kasar, kasar haihuwarshi bazai taba dora kafarshi acikin garin ba idan ya fita nan yayi alkawarin he will take his downfall along side with hers kafin yabar kasar.
Misalin wajen karfe biyar ya shirya cikin wasu baqaqen kaya ya saka facing cap ya rufe fuskanshi sannan ya dauka jakar kudinshi, bai tsaya ko ina ba sai wajen wasu gang leaders da suke wata harkalla data babe masu suka rabu baran baran, su daman nemansa suke sucu ubansa suka kasa samunshi sai gashi yazo da kafarshi wajensu.

Bai wani jima ba wajensu ya kara gaba, tunda ya shiga taxi zuwa inda zaije babu abunda yake sai kallon wayarshi, abubuwan dayayi recording da wanda ya dauka yake kallo, hankalinshi yayi nisa yana tunani acikin zuciyarshi baima san ya fito fili ba.
“She’s worst, she’s a devil disguise”
Tareeq dayake tantiri macuci, scam, satan kudi da sauransu, duk abubuwan nan da yakeyi baisa yaji zuciyarshi ta mace ba gaba daya.
Yana cikin tunanin nan taxi driver ya tsaida motar a filling station ya dubeshi ta mirror yace “excuse me for a minute sir, zanyi filling tank”
Girgiza mashi kai kawai tareeq yayi shi kuma ya fita ya saka pump din cikin wajen saka mai sannan ya wuce cikin super market din wajen dake daga chan nesa don ya saya ruwa.
Cikin abunda bai wuce minti goma ba wajen yayi exploding booomm motar tayi sama ta fadi kasa, ataqaice dai motar da tank din wajen duk suka kama da wuta wuwuuuuuu, lokaci guda mutane suka firfido suka bar wajen mai taxi kuwa shima sai aka nemesa aka rasa.

Cikin abunda bai wuce minti biyu ba saiga motar kashe wuta, few minutes ago tun kafin ma wutar ta kama aka kirasu akan wuta ta kama a kusa da filling station.
Suna zuwa aka fara kokarin kashe wutar kar yayi affecting sauran stations din wajen, motar ma bayan an kashe aka fitar da gawar dake ciki.
Allah ya jiqanka tareeq……
Kan kace me tv stations sun dauka labarai ko’ina ya dauka, yanda explosion din ya faru ya tada hankalin mutane sosai, saida driver ya futa motar ta kama da wuta kuma aka rasa ta ina ko kume menene ya jawo explosion din.

Fadwa na zaune a wani katafaren gida taga news din, tabe baki kawai tayi tace “you deserve worse than this..”
wayarta ta zaro takai kunnenta daga chan aka soma magana, are you happy princess?”
Murmusawa kawai tayi tace “yessss i love you papi”
Tana kaiwa nan ta aje wayar ta cigaba da shan wine dinta.

Kawayenta mutane da yawa kiranta aka somayi a waya, taqi daga kowanne daga ciki, already daman tasan outcome din haka wannan yasa ta shirya document dake nuna sun rabu shida ita tun shekara daya data wuce kan ta gano qasurgumin armed robber ne kuma scammer ne yayi hiding identity dinshi ya shugo rayuwarta.

Mutane da sukaga wannan labari sai aka soma pitying dinta allah yaso bai cutar da ita ba kuma baici galaba akanta ba allah ya kubutar da ita daga tarkonshi don kowa yasan yanda suke da arziki.

Tana zaune tana shan wine tana kallon newss din harta fara zama high akayi knocking kofa, ta amsa, nan ya bude kofar ya shugo, takowa yayi har inda take ya tsaya gabanta,dagowa tayi ta kalleshi ta ya tsaya qiqam fuskarshi duk zanen suka, bakinsa baqin qirin ba kyan gani black kennan the most dangerous thug kuma na hannun damanta, the only dog din da take juyawa son ranta, black dake ma hidaya aiki amma karkarshin iko da umarnin fadwa…….
Mikewa tayi ta tako gabanshi ta soma shafa kirjinshin sabda yanda ta zama high sosai, rungumeshi tayi tana jin kamar taj ta runguma, chan kuma ta matsa baya ta turashi tayi wani irin tangani yayi saurin tarota ya zaunar da ita sambatu ta soma “i need him i want him so bad…saina sameshi, waye shi? Shi din waye shi? Saina sameshi kota hali qaqa ne”
Shuru black yayi yana jinta saida tayi sorber kafin ta kalleshi da jajayen idanunta ta soma magana “hope you wipe the mess you created”
“Yes ma’am”
Ya amsa ta, “good”
Ta daga mashi hannu alamu ya kara gaba.

Achan office kuwa hidaya neman duniya tayi ma fadwa ta kasa samunta, dalilin wannan news din mutuwar tareeq ta janyo masu asara sosai don dole sai an samu competitor dinsu da zasuyi using din mutuwarshi against dem, ji kake anata ay taheel family criminals ne sun ajiye criminal a cikin family dinsu don haka suma criminals ne, da kyar hidaya ta samu ta toshe rade raden da akeyi.

Su afiya ma duk sunga komai a internet, maida din gida da mutane da dama kowa.
Abokinshi ma dake cikin jail shima an tashi wahse gari anga gawarshi a jail bama asan mey ya kashe shi ba.



✊💋BOSS LADIES WRITERS💋✊

MATAR TAJ (destined with you🩵🤍)
Written by
Queenmarh✍️
Book2
PAID
Chapter 79
Sabeeha dai batayi gigin komawa saman nan ba sai washe gari, gaba daya tabar taj cikin zulumi, dukda yasan tana cikin koshin lpy so yake kawai ya ganta, idan da da ne abu yashiga tsakaninsu blaming dinta zaiyi, don yana tunanin abunda take so kenan shiyasa tayi using dinshi lokacinda baya cikin hayyacinshi yanxu kuwa ya hana zuciyarshi dayin haka kodan albarkacin cikin dake tsakaninsu, he wants to care for her, give her attention and remove duk wani bad energy dake sashi yake pushing dinta from him.

Saida ammu tayi ta tausasa ta ta kwantar mata da hankali ta nuna mata dalilan dayasa they have come this far tukunna ta samu courage din komawa saman, tabbas ta damu dashi sosai, tana jinshi har cikin ranta saidai ta farar daya ya sauya mata daga taj din data sani a baya, wannan taj din kwata kwata hates her, baya kaunar ganinta,abu daya kesawa take danne zuciyarta inta tuna yanda yasha wahala a baya, ayau da zai gane halayyan yan uwansa gaba daya da yanda suke nuna qiyayya a tattare dashu databar rayuwarshi gaba daya, aaidai inta tuna da maganganu ammu ne yakesawa take hana zuciyarta tunanin.

Koda ta shigo part din nasu tsayawa tayi ta kasa yin gaba, tsoro da fargaba ya dirar mata, moments din ranar na yawo a kwanyarta dukda ta hana kanta tunawa, idan ta tuna yanda yake dirzarta sai taji tsikar jikinta na tashi zirrrr sosai..

Anan parlor tayi zamanta ta doka uban tagumi, tayi nisa sosai cikin tunani ta soma jin kamshi na shiga hancinta, wanda ta tabbatar nashi ne, dagowa tayi da sauri suka hada ido dashu tayi saurin kauda nata saita fara neman daburcewa, yana ganin yanda ta daburce ya gane a taorace take dashi, wannan yasashi takowa ya samu waje ya zauna yana facing dinta
Gyaran murya yayi yanayinshi bai wani sauya ba cikin sanyi ya soma magana.
“Uhm..abunda ya faru the other day”
Ya dan dakata sai kuma ya cigaba “it was a mistake, lets pretend it never happens”

Sabeeha na jinshi batayi responding ba haka zalika batayi gigin dagowa ta kalleshi ba “im sorry”
Itace last kalma ta karahe dayayi wanda yasa ta dago ta kalleshi, hawaye na kokarin sauka akan fuskanta har ya sauko,
Saida ya runtse ido ya bude, yaji babu dadi wallahi sosai, he must have hurt her feelings sosai.
“Stop crying..did i hurt you badly?”
Girgiza mashi kai kawai tayi a shagwabe yanda yake mata magana dadi yake mata, saidai tayi mamki sosai kamar bashiba, shidai kamar wahainiya, yau he’s soft gobe ya gaya mata

31 / 107