Advertisements
Chapter 103 Reading Matar Taj Book 2 Complete Hausa Novel BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Matar Taj Book 2 Complete Hausa Novel

Author :  Queenmerh Category :  Complete Novels

Chapter   103 / 107

306K to 309K   out of 320.4K words

ce fa..mayan ki? Wallahi bazan futa ba, bazan futa ba babu inda zanje, nanne gidanmu… nanna anne dan allah karku bari a fita dani…ku yafe min… i wasn’t on my right mind na shiga uku…wallahi bazan sake yunkurin yin komi ba..ku yafe min”
Nanna ta girgiza kai kawai, maya tayi laifin da it’s unforgiving, tsintacciyar mage bata mage, tayi mamakin abunda mayar tayi.

“Mummy I’m pregnant…in kuka koreni bansan ya zanyi ba..ku rufa min asiri..nayi nadama”
Gaba daya Basuyi mamaki ba harma bahijjar,

Hamad na shirin kiran yan sanda anne ta dakatar tashi, “ku futar da ita kawai, taje da halinta, allah ya maki abunda kikayi mana”
“Dan allah ku yafe min…bazan sakeba…”
“Kin makaro maya…you made a very big mistake” nanna ta fada tana hawaye, daidai nan guard suka shugo za a futar da ita, ta soma wani karamin haukan, kamar tababbiya…which duk effect din alluaran da takema kanta ne batama san maganganun da take ba “baku da imani, ku azzalumai ne, mugaye…allah ya tsine maku…wallahi bazqn taba yafe maku ba, saina lalalata sunan ahalin nan..”

Ana fitar da maya suka bi bayan taj da tunda suka sauko ya tafi da sabeeha hankali a tashe, bazai iya tsayawa ba.
Fadila sai jan bahijja tayi data sandare a wajen nunfashunta na nemn rabuwa da sassan jikinta ta turata cikin mota.

Maya na ihu tana kundumama securities dinnan zagi haka suka watsota babu komai hatta takalmin kirki babu a jikinta, ihu take tana sambatu kamu amma ina, haka suka watsar da ita waje, data fara kokarin yi masu taurin kai daya daga cikinsu ya daga bundiga ya buga mata a goshinta ya soma fidda jini, a razane tabar wajen babu abunda ke jikinta sai wayarta data saka a aljihun rugarta.

Ranga ranga aka shugo da sabeeha asibiti, gaba daya jikin taj ya jike da jini, bai taba tsoron rabuwa da ita ba sai yaxu, duk wanda ya ganta a wannan yanayi bazaiyi tsammanin zatayi surviving ba, aka shiga da ita emergency.
Tun kafin akaiga komai jinin data rasa aka buqata, inda yayi insisting a deba nashi, saboda shi universal donor ne.
Bahijja suna karasowa ta zube aka bata taimakon gaggawa, majeed ma suka karaso da su sameer, laila na kuka ta fayyace masu komai, sukayi allah wadai, anne tace babu ita babu gidan har abada, taje da mugun halinta, zasu kyaleta kawai albarkacin rikon da aka mata amma da an makata hukuta.

At that point addua kawai suke ma sabeeha don har bahijja ta farfardo ana kan sabeeha ana kokarin ceto ranta,

After 2-3 hours of waitings doctors suka fito, daga yanda kaga yanayinsu zakasan bad news, daoctor barau yayi shuru bahijja ta karaso gabanahi tace “yataa yata tell me shes alive bata mutu ba, please ku fada min kun ceto ta..”
“Hajiya saidai kuyi hakuri,” yuu bahijja tayi zata fadi jin wani jiri ya debeta,
“She lost the pregnancy due to the excess blood data dunga zubdawa, sannnan state din shock data shiga amma aside from that she’s safe from the cut Alhamdullah!, allah yaso baije deeep ba munyi mata dinki, yanxu she’s unconscious”

Gaba daya suka bishi da wani irin kallo, musamma taj da he’s more shock than anyone else, anne tayi saurin furta “innalillahi wa inna ilaihi rajiun…subhanallah…”
dady sabeehan da hankalisa ya tashi sosai ya karaso gaban doctor yace “pregnancy? What pregnancy are you talking about???”
“Yes sir,, jinin data dunga fiddawa ne sanadiyar shock din data shiga yasa ta rasa 4weeks pregnancy dake jikinta”

Dam gaban taj ya kara bada wa babu abunda yake sai kallon doctor yana nanata maganar a ranshi, “she was pregnant??? Fatima was pregnant this whole time with his child??? Ya rasa cikinsa?? Because of wannan shedaniyar yarinyar..innalillahi wa inna ialaihi rajiun, adaidai wannan lokacin ganinta kawai yakeso yayi, he just wants to see fatima shi” bai tsaya sauraron su ba ya zame yabar wajen

“Wani irin magana kake ne likita?? Fatiman ce takeda ciki?”
Fadila tayi mga tana duban doctor, “baku sani bane hajiya??”
Anne ta katse su jikinta a mace tace “mun sani…ya allahu,allah ya bata wasu masu albarka sannan ya bata lafiya”
Duk sukabi anne da kallon mamaki, duk wani shock news daga wajenta yake futowa.
“Zamu iya ganinta??” Anne ta tambaya, doctor yace “eh an kaita recovery room tana samun rest”
“Thank you dr barau” ya kama hanyarshi suka nufi wajen recovery ward vip, gaba daya rututu suka taho taj suka tadda tsaye akanta ya kama hannunta yana kissing sannan ya duka goshinta ya hade da nashi ya shiga wata duniyar, su da shigo suna ganin haka suka tsaya babu wanda ya tunkari wajen,bahijja ta kauda idanunta abubuwa da dama na yawo a qwaqwalwarta, anne ta samu waje ta zauna.

Anne tayi gyaran murya tace “alhamdulillah tunda bata samu wani rauni sosai ba”
Fadila tace “anneeee!!!”
“Toh yanxu ma karin bayanin kuke nema? Bayan gasu nan a gabanku?“
Kowa yayi shur chan kuma anne tayi gyaran murya tace “tajudeen mijin sabeeha ne,”
“Mijinta kuma? Auren da ba ayi shi ba? Ko a bayan mu akayi bamu sani ba?”
“Ah ah da ma chan da aurensu, gashi nan gata,ay,”
“Anne ki mana bayani yanda zamu gane” fadila ta sake a natse, gaba daya daga nanna har bahijja da sameer kamar ruwa ya cisu bakinsu ya rufe, nanata maganar anne kawai suke aransu.

Nan take ta fada masu komai yanda taj ya fada mata tundaga farko har karshe idanun nanna yayi jaa sosai, ta soma innalillahi a zuciyarta tayi tawakkali ta danne abunda ke zuciyarta kowa ayayi shuru da abunda ke ranshi, amma mamaki bai barsu ba.
“Shiyasa nace zan aurar dasu, banso wannan zancen ya futo ba, don shi da kansa ya roki kar hakan ta faru, toh saidai kuma komai da yanda allah ya tsara, baiso kuji irin rayuwar da yayi ba saboda we had gone through alot, amma allah yana tare damu, we are still together no matter what alhamdulillah komai na cikin tsarin allah, ke bahijja yanxu kinga duk abunda ya faru ishara ne a garemu, kina matsayin uwa baki ma san yarki nada ciki ba, kin sakankance akan wannan shedaniyar, har kina rokon dole saina hada aurenta dashi,”
Bahijja tayi ahuru abun tausayi kanta a kasa ta doka uban tagumi.

“Hmm ay ni nasan yarinyar nan babu alkairi a tattare da ita yar hadiza ce fa??” Fadila ta fada tana tabe baki.
“Allah ya bata lafiya” majeed ya fada yana futa daga dakin.
Hamas ko tun kallo daya daya mata daga nesa shima ya fuce daga dakin, zuciyarsa na zafi, tabbas fatima ta haramta a gareshi, ya rigada ya karbi hakan.
Laila ko tunda ta kafesu da ido ta kasa daukewa, sai kawi ta fara murmushi, fadila ta dubi bahijja sannan ta dan kauda idnaunta tace “oh yanxu daman da aurensu shine suka boye mana? “
“Toh idan kukaji ba lallai ku fahimce su ba, kamar nima yanda da farko ban yarda ba saida ya zauna yamin bayani, wa zai taba tsammanin fatima taje aikatau saudiyya , kuma har ya kasance gidan su tayi aiki ta kula dashi? Har sanadiyar hakan yasa kawunshi ya masu aure? Just to protect him? Ay babu wanda zai yarda da wannan cikin sauqi” nanna ta bata ansa
“Kai amma mutane mugaye ne, kana kallon naka inkaga na wani saikaga naka ba komai bane, yanxu meya tsaresu dashi taakani da allah? Dan uwanku jininku? Wannan zalincin ay yayi yawa”

Nanna dai tayi shuru tana matsar kwalla, taji wani irin soyayyar sabewha na ninkiwa a cikin zuciyarta, she did the duty of a mother, she protected a lokacin da yafi buqatar uwarsa a tare dashi,

Lokacin sallar asr nayi anne ta tashi ta dafa taj sannan tace “tashi kaje kayi sallah, zata farfado insha allahu deeni kaji ko?”
Haka nan ya tashi idanunshi sunyi jaa sosai ya futa daga dakin, wanda hakan ya bama bahijja sakewa ta karaso kusa da sabeehar ta kama hannunta tana hawaye.
She can’t imagine loosing sabeeha, wallahi zuciyarta zata iya bugawa lokaci guda.
Haka zalika shock din maganar aurensu da taj bai barta ba.


Anne na zaune gefen nanna tana bata baki tana tausasa ta suka soma jin maganar bahijja, tana kiran sunan sabewha a daidai lokacin kuma sabeehar ta soma bude idanunta laila ta futa da gudu ta kira doctor yazo.

Taj bai shugo ba bayan futar dayayi sai wuraren bayan sallar magrib, kusan a tare suka shigo sa hamad da sallama.
Anne da nanna na zaune while anty fadila na sallah.
Bahijja kuma na gefen sabeeha dake kwance amma an dago gadon nata kamar tana zaune, anesthesia da aka mata yasa batajin zafin komi kwata kwata saidan abunda baza a rasa ba donma alluran ya soma sakinta amma tayi shuru.
Babu wanda ya mata magnar cikin da bata san dashi ba, haka zalika babu wanda ya fada mata cewa sunsan da aurensu ita da taj din.
Sallamarsa yasa taqi dagowa balle ta kalli inda yake, bahijja tayi saurin miqewa ta bashi guri don kamar baisan wani abu wai shi kunya ba ya tunkaro inda suke.
Kana ganin expression din fuskarsa zakasan he’s relieved daya ganta zaune.
Ya karaso har gabanta ya kafeta da idanu, ya rasa ma me zaice mata, sai tunanin cikin nan yake, abunda ya hanashi dawowa asibitin kenan ya tsaya a masallaci yana addua akan allah ya kawo masu wani mai albarka, balarbe dai akwai son yaya, baima san da cikin ba amma barewarshi dayaji abun ya mashi zafi sosai.

Tana jin yanda idanunshi ke yawo akanta amma taqi kallonsa ya dan duka kadan ya kamo hannunta, cikin Sauri ta juyo ta kalleahi ta kalli mutanwn dake daki, taga kowa harkar gabansa yake banda laila datake guntsw dariyarta ya dan rankwafo ya soma mata magana cikin sanyi with so much care affection and love..”how are you feeling?akwai inda ke maki ciwo?”
Kasa kasa yake magana yanda dagashi sai ita ne zasuji, kuma yana kashe mata murya,mamaki ya gama cikata,
Ta soma kokarin kwace hannunta yayi pwcking hannun ta kwalo idanu, kasa kasa ta soma magana itama “menene haka, idan aka ganmu fa? What is this?”
Yatsanshi yakai bakinta “shiiii” alamu tayi shuru tayi saurin ture hannun nashi gaba daya rai a bace tace “don’t ever touch me…”
“This touch or the other naughty touch uhmmm???” Ya fada in a naughty way yana mata wani irin mayen kallon flirtingly
Ta kauda kanta, gaba daya a furgice take, shin ya mance da su mummy na wajen ne ko kuwa, ta lura tunda aka fara maganar aure shikenan yake neman zaqewa, itako ayanxu babu abunda ta tsana kamar maganar auren.
Anty fadila na idarwa ta soma magana “toh toh…akwai dai iyaye anan..sai ayi maintaining basai kun nuna mana kunsan juna ba”
“Kai mummy..”
Laila ta fada tana murmushi, sabeeha ta sunkuyar da kanta tsabar kunya da takaici, gashi yaqi barin wajen kamarma baisan abunda take cewa ba.
Anne tayi breaking silence din, “toh alhamdulillh tunda ta farfado sai ayi tunanin wanda zai zauna da ita ko?”
Bahijja dai tayi shuru batace komai ba,nanna tayi saurin cewa “kuje ni saina zauna da ita…”
“Ah ah baza ayi haka ba, keda kike fama da kanki, kubar bahijja ta zauna da ita”
Fadila tace “toh shikenan”
Suka shirya komawa gida a daidai lokacin kuma majeed ya karaso asibitin.
Nanna ta tunkari inda sabewha take ta shafa kanta sannan tace “allah ya maki albarka ya baki Lafiya fatima”
Sabeeha ta sunkwi dakai ta kasa cewa ameen dinma.
Haka suka fita gaba dayansu, harda taj.
Ya rage daga bahijja sai majeed, daya tako gaban sabeehar ya zauna yana tambayarta ya jikinta sai faman lallabata yake uba mai dadi, bahijja dai ta kasa cewa komai tana kallonsu duk jikinta yayi sanyi gaba daya.
Sai wajwn karfw sha daya majeed ya koma ya rage daga bahijja sai sabeehar.
Nan ne bahijja ta zauna ta soma mata tambayiyi, “meysa baki fada min ba?”
Sabeeha tayi shuru ta kasa bata amsa don ta gane sun san komai.
“Dan allah fatima karki dunga boye min komai na rayuwarki, inason na kasance mutun ta farko da zaki sama da maganar daya shafeki, mai dadi ko mara dadi, I’m here for you, i will never judge you, banida wadda ta wuceki, i was so scared of loosing you, idan na rasaki diyata bansan ya zanyi ba” bahijja ta soma hawaye, sabeehar ma na kuka ta share mata hawayen tace “mummy im sorry…bazan kara boye maki komai ba Insha Allah”…
Sun dan jima suna magana bahijja na bata abunci tanaci chan sabeeha ta dan dakata tace “mummy…maya…”
“Karki sake ambaton sunan ta… sunanta ya haramta a gaba “bahijja ta katse sabeeha, wanda hakan yasa jikin sabeeha mutuwa tace “kiyi hkuri mummy…” sai kawai ta fashe da kuka, “sanadiyarta na kusa rasaki, bazan taba iya yafe ma yarinyar nan ba, da wani abun ya sameki shikenan, gashi tayi sanadiyar zubewar…”
Sai kuma ta dakata daga nan bata karasa ba, sabeeha ta goge hawayenta ta soma kokarin kawar da maganar mayar..
Haka suka kwana bahijja na jin mostinta zata tashi, baiwar allah ta kasa barci gaba daya.

Bangaren maya bayan wannan korar da aka mata, mutun na farko daya fara zuwa ranta shine salim, tana kiranshi a waya kuwa ya dauka, ta umarceshi dayazo ya daukwta.
Aikuwa yazo yana zuwa yaga yanayin da take ciki ya gane akwai matsala.
Tunda ta shiga motar nan babu abunda take sai sambatu da bababi iri iri,shidai baice komai ba abunda ke damunsa ya ishesa kawai, gashi ya kasa gane kan magnganun da take, daga yabda take magana ya gane tayi ma kanta allura.
Suna zuwa hotel ta tadda wani sabon tashin hankali, daman daga asibiti yake ta kirashi yazo ya dauketa, an dubashi aka tabbatar mashi yana da HIV/AID, which tabbas yasan itama yanxu haka tana dauke dashi, da farko baiyi niyar fada mata saida yaga ta nadu ta nadu ko tsoron zubewar cikin jikinta batayi inama take ta cikin yanxu neman abunda zai dauke mata damuwa kawai take tana farkawa doshin asuba taga babu shi babu labarinsa sai takardar report din test dayayi.
Nan ta shiga sabon tashin hankali, iskanci baiyi rana ba, ta dunga kuka tana kiran wayanshi baya shiga, ragiwar allurar data aje ta kara makawa kanta ta fita hayyacinta gaba daya don ta jikinta bata gama futa ba ta kara sama kanta wani.
Wuraren karfe sha biyu na rana aka zo karban room, don kwanakin daya biya sun kare, ana shugowa suka ganta unconscious, cikin gaggawa aka kira anbulance sukazo aka tafi da ita asibiti.
Chan asibitin ma aka kasa daukan ta saboda babu guardian dinta, shi salil data kira last da aka kira sa bai akaji wayar ma bata shiga, sai number mummy da aka gani shima yana cikin recents, kiran duniya shima akayi da farko ya shiga sai kuma daga baya yaqi shiga gaba daya.
Ana kanta ana kokarin daidai ta nunfashinta da ya tafi saboda buguwar datayi call ya shigo.
Cikin yan mintuna qalilan hamad ya karaso asibitin hankali a tashe, ta kirashi wajen sau goma ashe doshin asubar nan bai dauka ba ta mashi message kamar haka, “ka taimakeni ya hamad, zan mutu” harga allah baiyi niyar bin bayan call din ba ko message din sai kuma kawai ya kira, wannan yasa nurse sun suka sameshi a waya.
Yana zuwa aka mashi bayanin komai, tabbas akwai ciki a jikinta, sannan tana dauke da hiv aids da yan cucututukan da baza a rasa ba stds,but the most shockingly part shine effect din da allurar nan datayi ma kanta within the range of 16hours, sannan tayi consuming 10 dosage cikin awannanin bayan ga wannan report ya nuna ta dade tanayi ma kanta allurar ta jijiya gashi tayi compulsing which might affect or damage her brain.
Tunda hamad yaji wannan masifa babu abunda yake sai innalillahi, tabbas maya ta lalata rayuwarta, ta cuci kanta da kanta, kuma ya tausaya mata batun yanxu ba yasan kanta na rawa amma bai taba tsammanin zata jefa kanta ga halaka haka ta hanyar shaye shaye mara amfani, above all ciki? Tana dauke da cikin shege a jikinta? Sannan ga cutar HIV?
Tabbas abun a tausaya mata ne dukda ita ta jefa kanta a cikin wannan rayuwar amma bayajin ko dan wannan zaisa su yafe mata abunda tayi, har tanada audacity din daukar wuka zata kashe sabeeha? Tabbas zata iya yin komai and she can never be trusted.

Shi ya biya bill din medication dinta komai, sannan yabar kulawarta hannun likitocin da suka dukufa akanta don ceto ta.
Koda ya koma gida baiyi gangancij fadama kowa ba yanayin da take ciki musamman anty fadila wato mami, idon idan taji yasan ranta zai baci sosai.





MATAR TAJ (destined with you)
   Written by 
          Queenmarh

Book2 
PAID
Chapter 117


Washe gari..
Sabeeha ba karamin kulawa take samu ba wajen mahaifiyarta, duk wani motsinta akan idanunta, yan gida ko yanda sukazo runduna gaba daya jiya haka yauma suka zo.
Sun dade sosai anata haba haba da sabeeha, itako babu abunda take sai murmushi, ada chan idan tana rashin lafiya tsakaninta da hadiza ko sannu wani sa’in ma saitayi cuta ta cinyeta babu wanda ya sani, saima inna kawai datake dan nuna kulawa akanta.
Tana cikin wannan tunanin bata san hawaye na saukowa akan fuskanta ba sai jin hannu tayi kan fuskanta, dagowan da zatayi kenan idanunta ya sauka kan nashi, cikin hanzari ta dubi mutanen dake dakin, hirarsu kawai sukeyi abunsu babu wanda yakai hankalinsa ga inda suke sai laila data kalleta ta kashe mata idanu cikin tsokana,

Cikin sauri ta kabe hannunshi dake kan fusknta ta hade rai sosai, ya dan matso gefen gadon kamar yana duba ruwan da ake kara mata.
“How are you?”
Tayi banza dashi ya sake tamabayata.. “akwai wani abu da kike buqata??”
Nanma tayi banza dashi tana fakar idanun mutanen dake zaune musamman nannan,shi ko kunyanta ma bayaji kwata kwata.
Hannunta ya nemi rikewa ta mashi wani kallo mai tafe da harara chan kasa kasa ta soma magana “please stop it…stop pretending as if you care”
Dan jinkirtawa yayi yana nanata maganarta aranshi, gaba daya jikinsa sai yayi sanyi sosai ya matsa kawai ya hade hannayenshi a kirjinsa.

Nanna dake zaunw jefi jefi take dagowa tana kallonsu, daga haka inka kallesu saisu baka sha’awa sosai, jiya bata iya barci ba dan murna, wani irin mixed feelings ne yazo mata, she was very happy da sabewha ta kasance MATAR TAJ kuma ta kasance tare da shi alokacin dayake cikin hadari, wani ikon allah kenan, da allah ya tashi ikonsa saiya hadasu tun basu san cewa yan uwan juna bane.
Tana farin ciki, da wannan alamari, tamafi kowa farin ciki, don samun sirika kamar sabeeha sai

103 / 107