Author : Queenmerh Category : Complete Novels
wajee”
Ta daka mata tsawa tana fita ta soma kiran jamila a waya tana dauka kamar tayi hauka ta soma magana “jamilaaa…”
Sabeeha na fita daga dakin tayi kicibus da maya data dawo, kallonta tayi sai kawai ta soma dariya wani irin dadin takeji sosai,
“Ay wallahi bakiga komai ba, ni nan sainayi sanadiyar barinki gidan nan, this is just the beginning”
“Meysa kika tsane ni me nayi maki?”
“Ke har kin isa na baki dalili?”
Murmushi sabeeha tayi tace “takamarki bata wuce saboda kunada arziki ba, amma inaso ki sani baki fini da komai ba, kina ganina a wulaqance ko? Toh babu wulaqattace sai wanda Baisan darajar dan adam ba,”
Mari maya taso yi mata ta kama hannun nata gamm tana kallon cikin idanunta babu tsoro tace “kinyi kadan ki taba wannan fuskar, mahaukaci mara tunani”
“Ubanki ne mahaukacin, auu sorry qila ma
Bakida uba”
Ji kake tassssss sabeeha ta dauketa da mari, har sharin hannayenta na futowa akan fuskar maya.
Saida maya ta daidaici isowr mutun kawai tayi baya ta fadi kasa, da gudu yar aikin dake labe ta wuce don kiran maman maya.
Suna isowa maya data kama wuyanta tana kakakin amai sabeeha na tsaye na kallonta tana kallon makirci iya makirci.
Bahijja na ganin maya a kasa hankali tashe ta tunkareta “baby menene? Menene?”
“Mummy shake min wuya tayi wai saita kasheni saboda na tona mata asiri”
Bahijja batayi wata wata ba ta dubi sabeeha ta kwasheta da mari tass tass, wajen sau uku, idanunta sunyi jaa sosai sabeeha tayi baya zata fadi
“How dare you lay your hands on her eh???? Ina uwar taki hadizaa hadizaa”
Rabi dataji hayaniyar tayi yawa sosai ga abunda ke shirin faruwa tsoro yasa ta wuce sama don shaidama anne abund ake faruwa.
“Ay daman nasan zuwanki bazai taba zama alkhairi ba, a da chan baya ma bai zama alkahir ba balle yanxu?”
Maganganu fa sosai bahijja keyi tsabar bacin rai, masu aikin gidan kowa yabfito, hadiza kamar ruwa ya cita.
Bahijja nada ahkuri sosai ba kadan ba amma idan aka tabota babu sauqi tanada zafi sosai, musamma akan maya da abund aya shafi maya.
Wayanta dake hannunta ne ya soma ringing ta kaasa dauka saida rabi ta karaso tana bata hkuri ta miqa mata wayanta tace “ hajiya na magana”
Ko kallonta bahijja batayi ba taja maya suka wuce sama.
Suna zuwa ta tabbatar mayar is not hurt kafin ta wuce wajen anne.
Tana zuwa batama bari anne ta tambayeta meya faru ba ta soma magana “ anne wani ganganci ne yasa kikabar hadiza zuwa agidan nan a karo na biyu? Bayan kinsan abubuwan datayi min a baya? Bama ni kadai ba wani abu hadiza batayi ba? Amma a karshe taci amarnarmu,? Wajen zama da aka basu bai isa ba abu har yakaiga sata yanxu yarta na kishi da maya? Har tana ikirarin zata kasheta? Toh wallahi saidai subar gidan nan kona dauki maya mu koma”
Saida anne ta barta ta gama babatunta tass har tana cewa “ ba tun yanxu ba na lura ba indai akan abunda ya shafi maya ne akwai banbanci akan komai ma, at this young age har tasna an takurata an tsaneta, dukdan saboda tana ganin banbanci, kuma badan komai saidan ubanta bare ne a cikinmu, zan dauki yata mu koma kawai bazan iya barin ta ba”
Ran anne ya baci sosai ta dakatar da ita “lallai bahijja kin bani mamaki, ashe kece kikayi contributing wajen lalacewar yarki, kikace an tsaneta? An takurata? Duk abund aya shfeta akwai banbanci saboda ubanta ko toh bari kiji, banbancin daga tarbiyyar da kuka mata ne,baku mata tarbiyya mai kyau ba sam sam batasan darajar dan adam ba dana gaba da ita, a kananun shekarunta hartasan taje hotel? Duk cikin zuri a ta wake zuwa hotel da wani eh???? Sau biyu ana kawomin wannan korafin, what did you do as a parent about her upbringing eh?
You failed bahijja as a mother you failed saboda son yarki ya rufe maki ido, abun ai ba hauka bane, maya is going no where, idan har nina haifeki baki isa ki tafi da ita ba anan zata zauna,”
Idanun anne yayi jaa sosai tsabar bacin rai, bahijja ko jikinta lokaci guda yayi la’asar da jin batun anne babu abunda take sai innalillahi, maya a hotel? …
✊💋BOSS LADIES WRITERS💋✊
MATAR TAJ (destined with you🩵 🤍)
Written by
Queenmarh✍️
Book2
PAID
Chapter 97
Bahijja da maya na barin wajen hadiza ta koma daki tana sababii.
Sabeeha na tsaye tana jin sauran yan aikin gidan suna tsgumin abunda ya faru, “gata dai kamar bazatayi ba allah ka raba mu da dauke dauke, chap ina mata kallon mai hankali ashe ashe, lallai ma”
Kallonsu rabi tayi cikin bacin rai tace “ku wuce daki”
Sabeeha daketa faman hawaye har zuwa lokacin jikinta tsuma yake, fuskarta har tayi jaa sosai saboda haske da take dashi har yatsun bahijja na futowa a cheeks dinta, ga gefen lips dinta daya fashe don har jini ya dan fito.
Gaba daya ji tayi kirjinta na mata nauyi,ayanxu ta gwammace kawai a kaita nasarawa lafiyan kawai wajen dangin babanta, don rabonta da dangin babanta harta manta.
Tun suna dan zuwa lokacin da inna na raye har saida hadiza tayi sanadiyar daina zuwansu, don duk abunda ya shafi mahaifin sabeehar ba qaunar ganinshi take ba balle jinshi.
Inda take yawan zama ta tafi taci kukanta sosai don takai wajen karfe sha biyu a wajen, gashi garin akwai dan sanyi musamman na idan dare ya raba.
Dakyar ta tashi jikinta duk yayi tsami ta shugo cikin gidan tare da rufe kofar entrance din kitchen ta baya.
Gaba daya ko’ina an kakkashe babu wani hasken kirki saina censor idan an taka wajen, dakinsu ta nufa ta sanya hannu zata bude taji bamm an rufe, sake murdawa tayi taji a rufe, har zata kwankwasa taji tsoro ta hakura tare da zama bakin kofar ta tankware kafaunta tana hawaye kamar ranta zai fita.
Har wajen karfe sha biyun dare bahijja takasa sukuni, maganganun da anne ta fada game da maya ya tsaya mata arai sosai, saita fara questioning din kanta da irin tarbiyyar datayi ma maya, tabbas tasan cewa soyayyar da take mata baya boyuwa don shike hanata tsangwama mata amma harga allah bazata taba bari taga yarta ta lalace ba.
Kuma tarbiyya daidai gwargwado a ganinta tayi mata, kama ga sallah, abunda ya shafi a sani game da ya mace, tasowarta da girmanta, abu daya ne tasan cewa she’s guilty of it, shine rashin kasancewa da batayi da mayan due to ayyuukanta, wannan yasa tayi sake sosai akan mayar.
Maganr hotel ya tayar mata da hankali sosai ba kadan ba, ba irin tarbiyar datayi ka maya ba, sangartata da tayi bashi zaisa ta fara zuwa hotel ba, she couldn’t believe it kwata kwata.
Wannan yasa ta kasa barci, gashi ta kasa samun majeed balle ta samu tayi pouring heart dinta, shi take kaima kukan koda yaushe idan tana cikin damuwa.
Kiran sallar subh a kunnen bahijja da bata runtsa ba, ta tashi gaban Allah tana yima mayar addua sosai.
Miqewa tayi ta nufi kan gadon tana kallon yanda maya ke barci peacefully, ta dade a tsaye tana kallon nata.
Tunda tazo nigeria bata taba ganin maya ta tashi sallar subh da kanta ba, kuma bata taba damuwa da tashinta ba, ko a london daddy ne ke kokarin wajen tracking ibadarta, sai yanxu abun ya sake karyama bahijja zuciya, maganar da anne ta fada babu komai a cikinta sai gaskiya.
“Maya maya, wakeup tashi kiyi ra’atainul fajr”
Maya ko gizau, sake tashinta bahijja tayi sai kawai ta fara kuka, “mummy please wuyana ciwo yake kaina na ciwo zan tashi anjima”
“No maya!!!
“Tashi, zan baki magani kisha inkinyi sallan saiki koma bari na dauko ruwa”
Dan dolenta ta miqe zaune tana qunquni, bahijja na fita tayi kwanciyarta.
Kasata sauko, ko’ina shuru wannan yasa ta wuce kitchen ta dauka bottle water biyu da glass cup, tana shirin futowa ta soma jin sheshekar kuka kadan kadan, bin wajen inda take jin kukan tayi don walkway ne tsakanin wajen da kitchen tun bata karasa ba ta hango sabeeha zaune ta sanya kanta tsakanin cunyoyinta.
Ta dade tsaye tana kallon sabeehar da mamaki,kamarma a haka yarinyar ta kwana, saitaji babu dadi gaba daya, badon ta duaka abu dazu ta mareta ba saidan furucin datayi kan maya.
Kwakwata bai zo mata cewa ba lallai sabeehar ce ta dauka bangle dinba tunda a dakinsu aka gani, duk yanda suke yar tsaba da hadiza baisa da taji ance yarta bace ta mata wani kallo daban, yarinya ce kamar maya, probably insa ta taso ne taga anayi.
“Fatima!!”
Da sauri sabewha ta dago jin an kira sunanta, tana ganin maman maya ce tayi saurin miqewa tsaye jikinta na tsuma taqi kallon bahijjar.
“Me kikeyi anan?”
Shuru ta kasa bata amsa, saida ta sake cewa “anan kika kwana?”
Girgiza mata kai sabeeha tayi babu bakin magana tsabar ciwon kai daya addabeta shi ya hanata runtsawa kuka ya sata kuka sosai.
Mamaki sosai bahijja tayi ga tausayin yarinyar daya kamata lokaci guda batasan sabda tace “meysa kika dauka abubda ba naki ba? Kinsan laifin sata kuwa?haramun ne daukan abunda ba naka ba, and no one will trust you idan kika cigaba da yin haka, da kananun shekarunki bai kamata ace har kinada urge din daukan abunda ba naki ba”
Bakinta na karkarwa ta soma magana, “wal..lahi bani na dauka ba ban taba daukan abunda ba nawa ba, ba halina bane”
“Maya zata maki karya ne? Ya akayi yazo dakinku?, ba sata kadai ba har karya ma haramunne”
Sauke kanta kasa tayi a ranta tama daina tunanin kare kanta, to wama zai yarda? Wanda ta tsugunna ta haifeta ma bata yarda da ita ba balle su.
“Kiyi hakuri hajiya”
Kofar dakin su rabi aka budo rabin ce ta futo, tana ganin bahijja tace “ina kwana hajiya,”
“Lafiya lau rabi, ta biki dakinku, naga kamar anan waje ta kwana” tana fadin haka ta juya ta barsu tsaye.
Rabi ta kalli sabeeha tace “shugo fatima”
Shugowa tayi rabi ta tambayeta meysa ta kwana waje nan ta shiada mata kofan dakinsu ne a rufe.
Tausayinta sosai rabi taji, duk laifun da tayi baici ace hadiza ta barta ta kwana a waje ba tana matsayin mace kuma yarinya, kai sha’anin hadiza sai Allah.
Yanda takema yarta kamar ba wanda ta haifeta ba, idan akace yar kishiyarta ce zata yarda.
10am daidai kowa yazo sallama da bahijja, anty fadila tun wajen 8 tazo part din anne, kusan ma gaba daya sukayi breakfast.
Maya ko bata tashi koke koke ba saida taga da gaske mummy nata tafiya zatayi.
Gaba daya futowa sukayi aka rakota bakin mota, anne bata samu futowa ba saboda kafa, sai anty fadila da nanna da maya ne kawai da zasu rakata airport.
Maya na kuka haka mummy nata ta tafi.
Fitowa hadiza tayi cikin shiri ta jawo jakar kayan sabeeha data tattara, bata tsaya ko’ina ba sai kitchen taba zuwa ta tadda su bilki na wanke wanken plates da akayi break dasu.
“Bilki Ina sabeehaa??”
“Tana dakin rabi”
Tana jin haka ta juya zuwa dakin rabi, ko kwankwasa bata yi ba bude tare da afka kai ciki, kamar an jehota haka sabeeha dake zaune da abunci gabata ta kasa ci ta ganta.
“Tashi ki fito munafukaaa!!!” Ta daka mata tsawa.
Hankali a tashe sabeeha ta miqe, hadizq ta futo waje ta bita a baya har tana tuntube.
Hanyar main entrance tabi suka hau sama zuwa part din anne, suna isowa hadiza ta kwankwasa tare da neman iso.
Rabi ta bude masu kofa suka shugo suka zauna a parlorn a kasa.
Futowar anne yasa hadiza gyara zama harda kwalla.
Zama anne tayi tana kallonsu “lafiya dau hadiza da safiyar nan?”
“Ba lafiya ba hajiya” ta dan dakata harda share hawaye, “wallahi bansan cewa yarinyar nan sata ta koyo ba dana turata aikatau saudiyya, na mata tarbiyya mai kyau ta watsar allah kadai yasan irin ta’asar datayi achan, dan girman allah kuyi hkuri yau zan maidata garin dangin ubanta”
Duban sabeeha anne tayi kafin ta kalli hadizar, “kin zaunar da ita kin bunciki itace tayi satar da kanta?”
Shuru hadiza tayi ta rasa answer da zata bata, rabi dake tsaye tana jinsu, duk abund aya faru saida ta fada ma anne da yanda hadizar tabar sabeehar ta kwana a kofar dakinsu, kuma dazu data zauna a dakinta cikin lumana ta tambayeta meya faru, sabeehar ta fada mata iya gaskiyarta, wallahi harga allah duk wanda ya zauja yaji batun abunda sabeehar ta fada zai gane akwai kulalliya a cikin ala’amrin, na farko dai ya akayi maya tasan sarkan na dakinsu harta iya fiddota, duka gidan akwai yan aiki kamar sabeehar kuma akwai chances din sune
suka dauka, cikin yaran ma akwai wadda tayi gyaran dakin, ita ba ace itace ta dauka ba sai sabeeha?, abun akwai tambaya a almarin.
Ganin hadiza tayi shuru ta kasa cewa komai yasa anne cewa “ke karaso nan”
Ta rarrafa ta karaso wajen anne, kallon cikin idanunta anne tayi tace “ke koka dauka? Fada kin da bakinki”
“Wallahi bani na dauka ba, kayan da akace na kwaso na wanke su kawai na dauka na wanke, ban taba yin sata ba,”
“Kinsan wadda ta dauka ta saka a dakinku?” Ta sake tambayarta
Shuru sabeehar tayi wannan ya tabbatar ma da anne ba yarinyar ce ta dauka ba, kuma sai taji ta kara yarda da yarinyar.
“Rabi jeki kira mun maya, ke kuka hadiza Babu inda zaki maidata tana karatu, kuje kawai”
Hankalin hadiza ne ya tashi, badai anne ta gano maya ce ta dauka bangle dinnan ba ta qala ma sabeeha,don sarai hadiza tasan maya ce ta kawo abun hannun nan, don lokacin data shugo dakinsu tana kallonta tasan batada gaskia a lokacin amma tayi shuru batace komai ba, gudun kar ayima mayan fada ko a gano ta, ta hanyr nan ne kawai zatayi gaining trust din mayar.
Suna fita hadiza ta kasa sukuni,chan sama kuwa anne datasa a kira maya, daga tambayoyin data mata ba’aje ko’ina ba ta gano gaskiya, as always itafa ba a ha’intar kowa a gabanta wannan yasa tayi ma mayar warning kan cewa idan ta sake ta sake irin wannan zata saba mata sosai ba kadan ba, and she will punish her.
Weekly allowance da take basu ta yanke na mayar sannan ta sata dole ta kira mamanta ta fada mata gaskia.
Ko sama da kasa zata hade bazatayi hakan ba, allowance ko da aka hanata tanada hanyoyin samun su daban daban, tsakanin shekaran jiya da jiya yarinya kankanuwa tana shirin haddasa fitina, tunda mamanta tazo babu abunda take fada sai an tsaneta ba a sonta anne bata qaunarta, ba a janta jiki, har bahijja na tunkarar anne da maganar.
Maya na shiga dakinta ta kudiri aniyar saita illata sabeeha, ta tsaneta ta tsaneta kamar ranta, duk duniya batajin akwai dan adam data tsana sama da sabeeha haka kawai bata mata komai ba.
Duk mai sauraro idan ya dubi hakan da kyau zai gane cewa ba komai ne kesa maya jin tsanar sabeeha ba saidan ganin ta fita da komai, hasalima itace take kishi da ita, ta futa kyau, ta fita basira, uwa uba hankali ga girmama dana gaba, school dinsu ko kowa son kawance yake da ita musamman a department dinsu sabeehar, wannan yasa maya ta tsanaeta kawai. Babu yanda za ayi yar aiki ta fita da komai.
After few weeks…
Tahudeen dai ya zama dan gida Masha allah, su abal an koma school, sufyan ma da matarshi sun koma kasar da yake aiki achan.
Tsakaninsa da mahaifiyarsa kuwa wani irin kusanci ne mai karfi tsakaninsu.
Anne ko data maidashi kamar abokin shawarar ta duk wani abu daya danganci kasuwancin su sakashi take a ciki, yanxu haka ma tace ya dunga zuwa don har an bashi office achan.
Har zuwa lokacin abunda ya shafi rashin lafiyarta babu wanda ya sani saishi kadai, kuma baiyi sake da zancen ba ya tsaya kan gaba dukda ta nemi karya fada ma mahaifiyarsa.
Bangaren anty fadila ko har ya saba da zuwa cin tuwo, baya gajiya dacin signature tuwon shinkafanta da miyan zogale.
Da farko idan an kawo mashi lunch part dinshi saiyaqi cin na bangaren anne saidai azo a kwashe warmers din, da anne ta lura da yafi son girkin fadila wannan yasa ake mashi.
Da anty fadila ta gaka take kiranshi a waya yazo yaci.
Maya duk yanda zatayi ta samu chan din haduwa dashi bata wasa da wannan, breakfast ko baya wuceta, duk sanda yayi deciding yayi a bangaren nanna kuwa ji take kamar tayi kuka, bahijja ko duk tighness din aikinta saita nemi lokaci everyday ta kira maya taji ya take.
Sun cigaba da zuwa school gaba daya yanda suka saba saidai an samu sauyi daga wajen maya data daina kula laila ma saboda har zuwa lokacin haushinta takeji don ta fadi abund aya faru ranar da suka tafi suka barta a school, wai a cewarta tabi bayan yayanta da sabeeha.
Duk hkurin da laila ta dunga bata amma kiff taki kulata, ta daina zuwa part dinsu ma gaba daya sai bangaren anty laila.
Achan saudi ko abubuwa da dama sun faru a wannan kwanakin, tundaga ranar da jamid yayi visiting dinta bai sake komawa ba, gashi batasan meke faruwa ba, shin dabta na ciki. Qoshin lpy ko akasin haka.
Akwai ranar juma’a da afiya ta dawo kasar daga yawace yawacenta, duk abubuwan nan da suka faru kwata kwata bata sani ba saida ta dawo.
Koda taje gida kiri kiri fadwa tayi brainwashing dinta, ta zuzugata sannan ta fayyace mata cewa hidaya kanta ta sani kawai kuma dole su hada hannu don ganin sun tabbatr bata futo ba, dama chan itama afiyar akwai son abun duniya akanta wannan yasa taji tanason irin daukakar da hidayar takeda ta hanasu suma su samu, wannan yasa ta amince in support of fadw ata karba taheel ita kuma saita zama mabiyarta.
Fadwa batasha wahalar amfani da afiya ba don ganin ta samun abunda takeso, tana samu kuwa ta futo mata da true color dinta.
A Ranar bidding za a saka taheel company a kasuwa afiya ta gano shirin fadwa, fadwa ko saida tasan yanda tayi ta rufe bakinta, ta hanyar threatening dinta don itace sanadiyar mutuwar wata maid da suka sa ta zubama taj poison.
Afiya tayi understimeting fadwa sosai, sai a lokacin ta tabbatar fadwa maqira ce ta karshe,
Duk san abun duniyar afiya bazata taba son kamfaninsu ya tafi a banza haka ba, don legacy dinsu ne.
Gaba daya komai fadwa tayi legalizing ya zama nata hatta gidajen su gaba daya duk wani propety dake karkashin sunan hidaya.
Neman khaal ko har yanxu bata