Advertisements
Chapter 1 Reading A Lokacin Mu Ke by Zainab Idris Makawa Seenabu BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

A Lokacin Mu Ke by Zainab Idris Makawa Seenabu

Author :  Zainab Idris Makawa Seenabu Category :  Complete Novels

Chapter   1 / 92

1 to 3K   out of 275.8K words

A Lokacin ne,,,,

IDAN BAKI BIYABA KADA KI KARANTA YAR UWA DON HAKKIN WASU NE,,,



Zaune take a kofan dakin ta tai tagumi sai faman tunane take tana kulawa tana
warwarewa ita kadai a gidan don mijin ta ya fita tun safe zuwa gurin aikin saukalen
da yakeyi gurin manyan motoci ,
Sai idan ya dawo ne suke dora girkin abinda zasuci kullun a haka suke wanan
rayuwan wahalan ita da iyalin ta,
Yanke shawara tayi a inda take zaune gara ta hada kayan dakin ta ta,sayar ta,dan
samu koda tsohon fridge ne ta,saya tana sana,an kayan sanyi ko zata samu kobo yana
dan shigo mata a hannun ta,
Ba bata lokaci da mijin nata ya,dawo gida batai nauyin baki ba tafara fada mai
shawaran da ta yanke,
Shiru yayi tare da nisawa inda yake zaune saman tabarman shi, da yake shan iska a
kai, yace
Halima banki shawaranki ba gaskiya amma ni a nawa tunanen da kiyi hakkuri ki
zauna da kayan ki don wanan lokacin da muke ciki lokaci na lahaula ga kowa ba masu
kudin ba ba tallakawan ba kowa wiwi yake yi da wanan karnin,
Koda kin sayar da kayan dakin ki don kiyi sana,a ina mai tabbatar maki rayuwa
bazai bari ka mayar da ko kwatankwancin abinda ka rasa ba a baya kinga hasara da
dana sani sai ya hau mutum,
Ke dai kawai ki bar kayanki tunda Allah bai hana muna dan abinda zamuci ba a
rayuwan mu to ai alhamdullahi komai yanzu sai hakkuri don ba kowa ke samun yadda
yake so ba,
Matar tanisa tace ni dai gaskiya nayi niyya da kabarni kawai na sayar a samu, dan
gurin rage wani hanyan kuma.
Ya fahinci bazata dauki shawaran shi tayi hakkuri da jarabbatar talaucin da suke
ciki ba don haka sai ya kyale ta tayi yadda take so kawai.
Don yanzu ba matan birni ne kawai ke bijirewa girmama wa dokan mazan su ba har ma
da matan kauye haka suke don yadda zamani ya juya a lokaci ne muke ciki,
Bai gida washe gari baya gida takira dillaliya sukai cinikin kayan dakin ta tazo
ta kwashe akan dan kudi kalilan tabar mata su,
Ba bata lokaci ta hada kudin tana jiran dawowan maigidan ta ta fada mai ya barta
taje ta dan samu abin da tai niyar saye da kudin,
Bai mussa mata ba don yasan kudin ta ne don haka ya kyale ta tayi yadda take so
da abinta don yana gudun yai magana ta ga kamar yana son wani abune daga cikin
kudin, nata.
Bata tsaya bayan sallah magariba ta shirya sai gidan wata dillaliya mai sayar da
kayan hannu, inda tai sa,a tasamu fridge har guda uku a gidan da akasa a kasuwa nan
sukai ciniki ta samu dan babban wanda bai tsufa ba sosai ta saya da kudin nata,
Suna barin gidan ta turo mai baro ya daukan mata shi zuwa gida zuciyar ta fam da
farin ciki a ran ta,
Da mijin nata,ya,dawo yai mata fatan alheri da,daukaka a cikin al,amarin.
Tun daga wanan lokacin ne tafara dan sana,a da fridge din nata tana dan samun
kwabon kashewa ta fannin ta ita ma,
Hakan ne ya kawo mata saukin yan damuwan yau da kullun da take ciki don tana dan
samun kudin kashewa a wanan fannin nata.

****** ********* ******
Safiyane duk jama,an gari sai faman zirga zirga suke kowa harkan ga ban shi yake
yi ba mai kama hannun yaro daga cikin su.
Sai faman sallama ake a gidan gwago Asmau da manyan kuloli gurin sayen masan da
take soyawa tun da farar safiya.
Gwago Asmau taji dadin kasancewar Bintu da ita a yau din don ba karamin taimaka
mata takeyi ba.
Komai cikin natsuwa Bintu takeyi ga tsabta sai ta wanke hannu da da kayan aiki
kafinta taba shi,
Sannu sannu tafara gyara ma gwago aiyunkan ta sabanin yadda take aikin ta a baya
in local way,
Bintu taba gwago shawaran cewa ta mayar da masan ta na zamani don yanzu akasarin
mutane suna fama da lalurar ciwa gyambon ciki watau ulcer,
Gwago Asmau tai mamakin yadda Bintu karama da ita tasan wanan dubara gashi kuma
daga kauye take zaune,
Don Bintu ta bata shawaran cewa yanzu da safe zasu dinga kai nika kuma su toya
shi, a lokacin,
Gwago Asmau tace kai haba Bintu ni kada ki jawo min hasaran kudi yaya zaki ce na
kai nika ranan kuma na soya masa a ranan,
Bintu tace wallahi gwago ki gwada masan ki zata samu karbuwa sosai wallahi don
duk masu tsoron cin masa don tsamin shi zakiga sun fara sayen shi,
Gwago tace yaya zan yi wanan aika aikan haka Bintu na,
Bintu tace gwago zamu wanke shimkafan mu fara sai mu barta a jike cikin ruwa ta
kwana da safe zamu tsamay mu hada da dan falawa dai yadda muke son shi sai mu hada
da dafafan shinkafa da yis da baking powder,
Sai a kai nikan shi ayi muna kullun shi na ruwa amma kada a cika ruwa da yawa
gurin nikan shi idan an dawo sai k8 dan kara gurorin dafafan shikafa da kaurin shi
yadda kike bukatan shi,
Sai kawai a fara soyan shi kamar yadda ake masa a koda yaushe,
Kai yan nan akwai ki da dabara kamar wata babban mace ke a ina kika koyo wanan
masan kuma,
Bintu tai murmushi har dan dimple din ta ya lutsa kadan tace nima a gurin wata
makwabciyar mu dake masa a bauchi sukai zama, naga tana hakan.
Yadda Bintu ta fada hakan sukayi sai dai gwago Asmau sai Allah Allah take kada
abin ya bashe su sai da taga zubin farko masa yafito da kyau hankalin ta ya kwanta,
Nan da nan masa ya kare masu washe gari masu sayen masa sai yaba dadin masan
jiya sukewa gwago Asmau, suna cewa kai masan jiya ga taushi ga dadi wallahi babu
tsami ko kadan, don har miyan sai da bintu ta sa aka dan zuba mai dan baking powder
kadan,
Nan da nan labarin dadin masan gwago Asmau ya dan kewaye shiya, don dadin shi.

Daga gidan malam Habu aka aiko asai masan dubu da dari biyar sai aka samu akasi
babu canji a gurun gwago don haka aka ba su masa kawai, sun biyo canjin .
Sai da yamma ne gwago ta ba Bintu canji ta kai gidan rayuwan Asmau bai so ba don
bata son dabi,ar shiga gidajen mutane ita.
Haka yasa tun zuwan ta garin bata je gidan kowa ba, tana cikin gida gurin gwagon
ta kawai sai nikan da tafita da,safe tabi almajirai, don taga yadda za,a nika masu
kullun masan su.
Hijjab din ta ta saka tare da sa dan sifas din roban ta sai gidan duk da dai
kwatancen gwago tabi don shiga gidan,
A hankali tai sallama daga kofan farko na shiga gidan babu kowa sai flawer a
shuke daga can nesa ta hango wani saurayi a duke yana sa takalman kwallo a kafan
shi da alama shigar shi ya nuna cewa gurin wasan kwallon kafa zai tafi.
lna wuni tace tare da dan duka mashi har kasa batai tsanmani ya amsa mata ba sai
cewa tayi don Allah ina hanyan da zan shiga cikin gida canji na kawo na masa.
Fuska a murtuke ya nuna mata da hannun shi, ba tare da yai magana ba,
Inda ya nuna mata ta nufa a hankali sai dai tana shiga duk ta daburce don gina ne
na part din mata hudu ko wace da nata daban,
Yanzu ni ina zan nufa ta fadi a ranta batare da tasan wanda zata kaiwa canji ba.
Tana shiga tai tsaye tana ta faman kwada sallama ita ka dai a tsaye shigowan
wata mata gajera fara mai kiba yasa ta mayar da hankalinta ga matan,
Ina wuni take ce mata cikin ladabi matar ta,amsa a,dadare da fadin lafiya,
Bintu tace canji aka ce na kawo daga gidan hajiyan masa, kamar yadda ake kiran
gwago Asmau, dashi a uguwar,
Cikin wani irin kushe fuska take cewa isa mana ki tambaya ciki tun nan ta
fahinci akwai kishiya a gidan ke nan ,
Tanan tsaye sai sake, sake, take a zuciyar ta, tana niyar juyawa ta koma ne taga
wata mata baka, tafito daga wani shiya dake daga can gefe tsabare da sauran shiyan
,
Hannun ta dauke da bukiti da mopa da tsiyatsiya da alamar da ga shara take futowa
matar.
Itama dai cikin ladabi ta gaida matar da ta gani ta amsa mata cikin sakin fuska.
Tana cewa sannu ko kina neman wani ne ko Bintu cikin murmushi don taga fuska,
tace dama canji ne akace in kawo inji Hajiyar masa,
Au daga gidan hajiyan masa kike ne, ?
Eh a nan nake tana kokari miko canjin dari biyar din dake hannun ta din,
A shigo mana daga shigowa har zaki tafi zo shigo daga ciki kinji ba mussu Bintu
tabi bayan ta zuwa part din da matar ta nufa.
Suna shiga dakin taga ashe daga ciki a kwai dakuna da kuma kitchen, a cikin su.
Kujeran dake a falon gidan ta nuna mata ta zauna tare da kara gaisawa da ita,
Amira Amira matar ke kira daga falo, sai ga wata yarinya doguwa zata dan girmay
ma Bintu tafito daga dayan dakin dake part din,
Tana ganin Bintu zaune sai kallon ta take da mamakin ko wacece ita, gaida
yarinyar mai suna Amira Bintu tayi.
Maji gani inji Amira din tana mai kallon uwarta, don son jin mai zata ce mata.
Karbi canjin nan jeki sauran dakuna ki tambaya wa hajiyar masa take bi canji
dazun da safe,
Amira ta turi baki gaba tana cewa ni wallahi in ba dole ba ban sin shiga gurin
kowa a gidan nan don dai kawai da mutum ya shiga yanzu za,ace ga abinda yayi kuma.
Aiken ki fa nayi Amira kika tsaya mai da naki ba,asin son raki haka Amira taja
kafa ta,wuce zuwa sauran sassan gidan,
Inda Bintu take zaune maji ta dan kalla tana fadin yi hakkuri kinji har ta dawo
muji ko canjin waye,
Andan jima kadan sai ga Amira ta dawo tana konkwami tana fadin wai, maman su
Hadiza tace takawo ta aje ko na baba ne amma taki bata ga kudin tana kokarin mikawa
mahaifiyar ta kudin hannun ta,
Amira mai yasa baki bata ba da kika dawo da kudin nan may zanyi maki dashi a nan
,
Maji cewa fa tayi wai zata ajewa Baba ni kuma nasan ba,bashi kudin zatayi ba
shiyasa nace mata tabari na tambaya sauran shiya muji in ba nasu bane,
Yadda maji take magana da yar ta acikin lumana ba daga harshe ya ba Bintu shawa
sosai sai faman bin su da kallo take yi, na sha,awa.
Yadda uwa takewa yar ta magana a cikin kwantar da hankali da fahinta,
Inda Bintu take a zaune Maji ta,waiga tana fadin inaga canjin Alhajine idan ya
dawo zan tambaya muji in har ba nashi bane zan sa su dawo mata da kudin.
Bintu ta mike don fita daga dakin a daidai lokacin da Umar ya shigo dakin ke nan
babu ko sallama.
Sai cewa yake ni zan tafi ball kada kuma ace ban fada ba natafi , yana,wani cicin
magani cikin dakewa,
Haba babana kai wai yaushe ne zaka girma zaka shigowa mutane daki babu ko sallama
kana wani shan kamshi da cin magani.
Kamar wan da zai tafi gurin wani abin arziki wai ball, ball din mai zai tsinana
maka a rayuwanka ne wai,
Maimakon ya tsaya yaji karshen maganan ta,sai juyawa yayi kawai ya fita daga
dakin,
A hankali maji ta sauke ajiyan zuciya tana furta Allah ya shirye ka babana,
Bintu dake tsaye ta amsa da Ameen Mama sosai har cikin ran maji taji dadin Ameen
din da Bintu ta amsa mata dashi.
Mama ni zan tafi sai anjima ke nan zan fada mata yadda akayi, to kin ji yar
albarka ki gayar min da Hajiyar masa din kinji ,
Bintu takai kofa Maji tace may ye sunan ki ne bakuwar hajiya ?
Cikin murmushi Bintu ta amsa da Bintu nake mama Allah sarki sunan mai kyau sunan
mahaifiyar maigidan nan ke nan ai.
A waje ta samu wanan mai bakin ran yana tare mashin zai hau ko kallin shi batayi
ba don tsoro ma yake bata, ita,
****** ********** *****
Kida ke tashi daga cikin waya daga daki yayin da uwar ke daga gurin wanke wanke
tana wanke kwanukan da suka ci abinci dashi na daren jiya,
Ganin hankalin uwar yana ga aikin da takeyi yasa Raiha mikewa a hankali zuwa
gurin da ta boye kayan harkan ta a ciki ta jawo wani kwalba ta kwankwada son ranta
tai wani jan iska da tsuke bakin ta a hankali.
Ta koma saman gadon da ta tashi a kai, ba bata lokaci sai barci ya dauke ta a
gurin.
Uwar na shigowa daki taga yadda ta kwanta daidai da ita, a hankali uwar ta kada
kan ta don takaici tana dan kiran sunan ta ,
Ke Raiha Raiha fa wai bazaki tashi ki yi abinda zakiyi bane ki kwance haka galala
tun safe kamar mara lafiya.
Cikin murya irin ta mashaya Raiha tace kai haba mama please easy please easy
barci nake ji fa.
Ikon Allah barci dai barci dai kamar wata malalaciya sai kin tashi ki ce wai ke
yunwa yunwa kamar zaki hadiye mutane, lokaci guda.
Nan uwar ta barta ta,tafi tana mita a kanta a lokacin ta gyara kwanciyar ta da
kyau taci gaba da barcin ta.
Bata farka ba sai yam lis ta farka sai bandaki tafada tana sauri don fitsari da
kashin da take ji a lokaci daya.
Bayan ta dauki lokaci tafito ne daga ban dakin shine ta debi ruwa a randa ta
watsa don ta dan ji jikin ta ya sake mata don nauyin da yai mata a lokacin.
Tsab ta shirya cikin wasu kananan kaya ta,dauko hijjab din ta tayafa a kan ta
kamar wata ta kirki can.
Inna ni zan fita tace a gadarance uwae tace ina kuma zaki yanzu ana batun yin
magariba kuma ?
Ba nisa zan tafi ba zan dan je can kasan layin mu ne na,dawo .
To ki daiyi sauri kafin mahaifinki ya dawo bai samay ki ba.
Yanzun ai zan dawo ba dadewa zanyi ba Inna, tana fita ta tare mashi sai wani
uguwa da ke da yawan mutane akasarin su duk matasa ne maza da mata birjit a gurin.
Kutsawa tayi itama tashige gurin can wani dan lungu wani gaye ne ta nufa yana
zaune tsakiyan su sai busa hayaki yake,
Yana saye da,riga blue mara hannu a jikin shi duk mozuqu din shi sun fito wahe
sosai.
Yana ganin ta tace yar halas yanzu fa nake zancen ki a,raina nace ko kayan basu
kare bane har yanzu don tun shekaran jiya baki leko mu ba nagani,
Ina tafe ai na tsaya ne har na karasa sauran wanda ya dan rage min don gudun
kada na tara kwalabe a dakin namu yai yawa.
Kasan gyatumar ba sanin kai tayi ba har yanzu bat da sau nake mata koda ta
rutsani nakan ce mata maganin mura ne nake sha ai,
Shegiya baby watau dai a kwana kike sakata ke nan dai ko?
Kai ma kagane ke nan ai don abin sai da kwana don ba,a,bari ai saurin sani abin.
Nawa kiia zo dashi don kin san ranan ma na biyo ki canji dai ko?
Nawa ka biyoni brosha ina dari uku ne dai kawai ko?
To dari uku ba kudi bane dasu ne ai muke karawa muna business din ga,shegun
kwalawan nan kullun sai kokari suke suga,sun kama mutane don kawai su caji mutum
dan canjin kashi badon a,daina harkan ba.
Ni dai kaji miko min kaya na natafi don yau ba dadewa zanyi ba ina sauri ne.
Wasu kala za,a baki akwai fa,sabbin fitowa masu aiki sosai wallahi tace cikin
tsiwa bani dai wanda ka saba bani kawai na,wuce na biya shagon Samuel na kara dan
kwalabe a can,
Daidai lokacin Umar yazo baiyi magana ba,sai kudin da ya miko mashi yace kaibani
nabar gurin nan don ban son sa ido da yawa.
Brosha amma kasan sai ka sallameni zaka sallami wani can ko?
Umar yana daga gefe ya harde hannayen shi a kan chest din shi ya zuba masu ido
yana sauraren abinda sukeyi kawai.
Sanin ko waye Umar yasa brosha fara hado mai kayan shi don yana kai wata biyu
baizo gurin ba yafi aikowa a,saya mashi,
Yana kokarin miko mai canji tare da kayan shine fam cike da leda, yaji muryan
Umar yana fadin ka bata da sauran canjin sai wani lokaci kuma ya juya yatafi a bin
shi bai tsaya jin may zasu ce ba,
Binshi da ido Raiha tayi tana,mamaki mutum haka ga alheri ga kuna ta hango jin
kai a tare da shi.
Mtwee tace tare da juyawa tace kai bani na,wuce kaji ban son bata lokaci nace
ma,
Aike yau kin taka sa,a wallahi haka yake in har yazo sai yai wa wani alheri a
gurin nan, sai dai kuma ba kullun ne yake zuwa ba,
Tana karba ta juya tabar gurin don zuwa chemist ta sayo sauran abubuwan ta.
Tana fitowa yana,shigewa mota ya harba yabar erea din don gudun wani ya ganshi
idon sani yasa yake zuwa wanan uguwar sayen kayan mayen shi can nesa da gida.
Ko da Raiha ta isa gida lokacin har takwas da rabi na dare.
A lokacin mahaifinta har ya dawo daga

1 / 92