Advertisements
Chapter 84 Reading A Lokacin Mu Ke by Zainab Idris Makawa Seenabu BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

A Lokacin Mu Ke by Zainab Idris Makawa Seenabu

Author :  Zainab Idris Makawa Seenabu Category :  Complete Novels

Chapter   84 / 92

249K to 252K   out of 275.8K words

kawai ranan ina marmarin alale na gwangwani don haka na fadawa Iyya Rabi
abinda nake son ci.
Baita kasa a gwiwa ba ta shiga shirin yi min alaila ta samo gwagwani gurin wani
mai shayi a unguwan ta hauyin alalen da nake son ci.
Ba bata lokaci ta gama min ina daki ina shiyawa zan fito falo yau na kokarta na
yi dan kwalliya a jikina don jama,an da suka cika gidan.
Cikin atamfar super nake dark blue dinkin shi mai shara sharan hannuwa half gown
na daura dan kwalin kayan a kaina.
Cikin dake jikina kayan yasa yafito don lokacin ya kai wata shidda a jikina sai
dai ba kowane zai iya ganewa ba sai wanda ya sanni da farko.
Nafito falo na zauna Iyya Rabi tace yauwa yanzun nake batin kiran ki kifito kici
shi da dan zafin shi kada kuma ya fita ran ki.
Zama daidai da shigowan maryam gidan da ita da kannen mijin ta da suka rako ta
gurin sunan.
Suna dauke da danta a hannun su sai wata makwabciyar ta data rakota kuma again
don ita tana hurda da makwabtan ta sosai.
Suna zama aka kawo alalen da ita muka hada hannu muna ci a plate daya naji dadin
shi sosai muna ci muna hiran yaronta irin yadda yake yawan alolayi sosai.
Muryan Baba mukaji a tsakar gida yana kwalawa matan shi kira cikin tashin
hankali.
Gaba daya suka fito daga dakunan su sai gidan yai tsit kowa nason jin kiran don
daji bana lafiya bane.
Mama Asiya tana fitowa ya kalleta yace Asiya kuncuce ni kunci amana keda dan ki
bazan taba yafe maku ba a rayuwana.
Mummy ce cikin karfin hali yadda taga Baba a rude take cewa wai may yafaru ne
Alhaji kuma ?
Yace Ahmed ya sayar da gidan nan yau wata uku ke nan ban sani ba ashe ?
Salati kowa ya saka sai ihun mama Asiya kawai mukaji daga waje abinda yasa mu
fitowa ke na daga dakunan mu duk wanda ke gidan sai da yafito don tashin hankali.
Baba yaci gaba da fadin yanzun haka wanda yasai gidan yana waje yace yazo ne
yabamu notice din tashi don anyi dashi nan da wata uku zamu bar gidan wai .
Lokaci daya aka saka salati masu kuka sunayi masu salati da tir sunayi a lokaci
daya.
Sai ganin kawai akayi Baba yai suuu zai fadi da sauri mama da mummy suka tare
shi bai kai kasa ba sai dai ba rai.
Idanuwan shi a waje inna lillahi wa inna alaihim rajiun,,,
Ihu da tashin hankali a ranan mun gane shi a gidan da gudu wasu suka kwasa zuwa
kiran maza a waje.
Yaya saudauki yana tare da yaya Bashar suna hanya kiran maryam ya shigo wayan shi
.
Yace kai munafukan matar kace fa ke kirana yanzu, bashar yace wa maryam lafiya
kuwa ya dauki kiran tana kuka take ce mai yaya don Allah kazo gida Baba.
Cikin wani irin murya yace Baba may fa ?
Sai kuka takeyi tace don Allah yaya kazo Baban mu ya rasu inna lillahi wani irin
burki ya taka da ya daki motar dake kusa dashi.
Ga you turne din sokoto da tsawon tsiya haka ya kwashe su da gudu Allah dai ne ya
tsare su sai gida cikin yan mintina suka kawo.
Irin mutanen da ya hango sunyi cincirindo a kofan gidan su cikin tashin hankali
ne yasa hankalin su ya kara dagawa sosai.
Wani irin mugun parking sukayi ya bar mota a bude ya nufi cikin gida da gudun shi
irin na yan kwallo bashar tana bayan shi.
Sai wani yaro makwabcin su ne ya kashe motan ya gyara parking gefe yana shiga get
su Sagir sun dauko Baba ya tare su tare da kamashi suka fita zuwa waje da shi sai
asibiti cikin tashin hankali.
Suna zuwa emergency aka nufa dashi nan aka samu da kyat ya farfado duk ilahirin
iyalin shi suna gurin sai yaya Ahmed ne kawai da matar shi basu gurin.
Koke koke kawai ke tashi tashin hankali ne ga duk fuskan wanda ka kalla a
lokacin.
Muna tsatsaye tare da su anty maryam da anty Nafisa don tare muka zo asibitin da
su.
Wani iri nake ji dole ssuka samomin guri na zauna ga alalen da naiwa mugun ci
sai taso min yakeyi ina jin zanyi amai a lokacin.
Maryam ce ta dafani take cewa Fatima ko zaki koma gida ne kinga baki da lafiya fa
a jikin ki gaki da lalura kada tashin hankali ya kamaki kuma ?
Nace ba komai ai anty aiko sai aman da nake taushewa ya taso min nan na duka
naita sharara shi hankalin mutane kuma ya dawo a kaina.
Daga cikin daki da Abdul ya shiga inda su yaya suke a kan Baba da ake neman
jijiyan shi yake cewa ga kuma Fatima can wallahi ita ma a waje sai a hankali sai
amai take shararawa kawai.
Da sauri suke cewa harda ita da bata da lafiya tazo ne yaya sadauki ya dago rai
bace yace may yakawo ta ita da bata da lafiya kuma ?
Bashar ya fita da sauri halin da ya samay ni ciki yace su maryam su kamani muje
gurin likita.
Muna zuwa likita mace ce muka samu tace ina bukatan bedrest a lokacin nan nima
aka kwantar dani asibitin.
Dole rabin yan uwa suka dawo gare ni barci ya dauke ni mai nauyi sosai har ban
san inda nake ba ma.
Da kyat aka samu baba ya farfado tana kiran Ahmed Ahmed ka cuce ni wallahi ka
cuci iyalina Ahmed.
Nan sadauki yake cewa haba Baba yi hakkuri a samo lafiyan ka tunkun na koma may
nene please.
Sagir ne ya jashia gefe daya can kusurwan gadon da Baba yake kwance yace yaya
sadauki baka san may ke faruwa bane ko ?
Yace may kuma ya faru ne Sagir ?
Sagir yace wai yaya Ahmed ya sayar da gidan mu shine ya jawowa Baba wanan
matsalar haka.
Cikin wata murya sadauki yace what Ahmed ya sayar da gida fa kace nan dai Sagir
ke fada mai duk yadda abin yake don a gaban idon shi akai komai.
Yace mai gidan yazo da bukatan yana son a kwashe a bashi gidan shi don wa,adin
aka bayar ya cika.
Innalillahi sadauki yace may yasa Normal yai wanan mugun aika aikan haka da
lafiyan shi kuwa ?
Waye ya sayi gidan ya tambayi Ahmed cikin dago kai da idanuwan shi suka kada
sukai ja a lokaci daya.
Nan Bashar ya shigo yanayin da ya gansu ne ya tayar mai da hankali ya karaso yana
fadin may ke faruwa ne kuma man ?
Yace humm bari kaidai man wani sabon labari nake ji wai Normal ya sayar da gidan
baba ga wani mutum.
Yace what da dan karfi yace no warder ake ce min yanzu anga yana bushasha da kudi
ya samu lafiya.
Kai amma guy din nan baiyi ba wallahi wanan ne ya jawo wa Baba matsala ke nan
ko ?
Bai bashi amsa ba sai cewa yayi yaya ita Fatima din kuma take yanzun ?
Yace itama an bata gado tana bukatar bedrest wai sukace .
Yace o my god wata sabuwa kuma again Allah gamu gareka yace a zuciyar shi amma a
fili cewa yayi tana ina yanzun kuma ?
Tana gany room a can suka kwantar da ita har tayi barci shine na fito zuwa nan
don gaskiya tana jin jiki sosai wallahi.
Sai da yaga komai ya saitu wa baba ne ya fito zuwa dakin da nake kwance ina barci
maryam da Nafisa sun sakani a gaba suna kallo na.
Shigowan shi yasa suka juyo suna kallon shi tare da tambayan shi jikin bana
yanzu.
Yace masu ya farfado idanuwan shi a,kaina ya kura min ido ina barci cikin wahala
ga ruwa daure a hannu na lokacin.
Takowa yayi zuwa bakin gadon ya dan tabo fuskana ban ma san yanayi ba don nai
barci sosai.
Ya dade a tsaye baiyi magana ba ya juya tafita daga dakin ya nufi gurin Baba
shima barcin yakeyi yasa shi fitowa don likita yace kada a shiga dakin abarshi ya
huta haka yasa akabar su mama da umma da mummy kawai.
Fita sukayi daga asibitin shi da bashar bai mashi magana ba shine dai ya karbi
key yajasu barshar din.

****** ********* ******
Ina muka nufa yake tambayan shi kai tsaye yace kaini gidan Normal please inji daga
bakin shi.
Sai gidan yaya Ahmed bashar ya tsaya suka fita gidan yana a rufe amma akwai mutum
don kara kidan disco daya karadw erea din a lokacin daga gidan.
Nocking din kofan gidan sukayi kusan sau uku kamar baza,a bude ba can jamila
tabude kofan gidan.
Tana cikin wani matsatsen wandon jeans da ya matse ta da wani dan riga ja mai
guntun hannu a rubutawa rigan crazy girl.
Tana ganin shi ne tace up UF yau kaine gidan da kanka cikin wani yanayi na farr
da idanuwan ta.
Yace mai gidan fa a taice ?
Baka ma bari mu gaisa sai tambayan dan uwaka watau shi ka sani kawai ko ?
Yace please ina Normal yake nake tambayan ki ?
Normal kan baya kasan ya tafi kwatano dauko mota tabashi amsa ganin da tayi ba
wasa a fuskan shi.
Ok kawai yace ya juya yabar gurin bashar yabi shi a baya mota suka shiga suka bar
unguwan .
Baiyi magana ba da suka fara hanya sai sa hannu yayi ya dafe goshin shi da hannun
shi daya kawai.
Zuciyar shi tana mai wani irin suya don bacin rai hankalin shi a tashe yake
lokacin.
Bashar ne yace yanzu kamata yayi mu nemi mutumin mu fara jin yadda sukayi dashi
first.
Yace wa yasan mutumin sai bashar yace bari mu nemo Sagir ko yasan labarin mana ?
Asibiti suka dawo har looacin Baba yana kwance sharkaf dashi sun dan dade a kan
shi ba wani motsawan da yakeyi sai dai numfashi kawai da zai nuna ma yana raye.
Fita yayi ya kira yaya Imiran da Sagir din shima Abdul ya biyo bayan su dashi da
bashar.
Yace wani mutumine ya sayi gidan baba din hannun Normal Sagir ?
Gaskiya ban san shi ba sai dai ina gani a GRA kamar nake ganin motan shi idan
naje gurin aboki na dake can.
Abdul daga bayan su yake cewa wanan guy din da suka zo dazun yace eh shi yace
dan masani ne mana guy din nan mai sayen gidaje dake GRA ko ?
Mota biyu suka tafi dashi gidan mutumin sai dai baya nan ance masu yafita cikin
gari .
Yanzu yaya kuke ganin zamuyi ke nan ?
Bashae yace lauya zamu fara nema mana shine farko don nasan dole abin sai ya hada
da lauya ai.
Wani lauya kake gani duk garin nan zamu iya samu ya tsaya muna kan wanan magana
don ba karamar case bane fa ?
Nan suka fara kawo sunayen lauyoyi da suka san cewa yakai lauya da zai iya tsaya
masu karshe dai suka tsaya akan barister Nuraddeen mohammed moroki dake zama a
gusau zamfara state.
Shine zai tsaya masu a matsayin lauyan su matashine wanda yasan aikin shi da
sanin darajan tallakawa akan aikin shi sosai.
Sun samu lamban lauyan inda suka kira shi tare da mashi bayanin komai dake faruwa
shima yana tambayan su wasu abubuwan da ya dace ya sani daga cikin maganan.
Haka aka shigar da kara a koto ranan basai ma gari ya waye ba don da zafi zafi
ake buga karfe.
An aikawa dan masani da sammacin sayen gida ba bisa kan kaida ba a hannun dan
maigida da yayi.
Yana karantawa yai dariya yace shi may ye nashi sana,anshine ba yau aka fara irin
wanan ba ai Allah ya kaisu kotun lafiya.

****** ********* ******
Falkawana yai daidai da su Mama suna dakin lokacin ma magariba ya gabato sosai na
bude idanuwa na a hankali.
Sai naji suna sannu Fatima yaya jikin naki nace a hankali da sauki na daga ido na
kalli gurin daki ne na asibiti ashe nake ciki a lokacin.
May ke damunki yanzun Fatima mummy ta tambaye ni ?
Da kyat na bude baki nace mata juwa nake ji tace bari a kira likitan ya dubaki.
Likita sun dawo tare da su yaya nan suke gaishe mu likita yace su dan rage daga
dakin nan aka barmu ni da yaya da likitan kawai.
Bayan yan tanbayiyi idanuwa na suna a lumshe yai yan rubuce rubucen da zaiyi ne
yake cewa dole sai nayi bed rest a cikin asibiti don yana gani baby dake jikina
yayi weak sosai zai iya fitowa indan an matsa mai wanda hakan babban hatsari ne
sosai gare shi.
Idanuwan shi ya runtse tare da tausaya ma halinda nake ciki lokacin nan dai aka
yanke shawaran zan zauna asibiti har wani lokaci a gani.
Iyya Rabi ce zata zauna a tare dani don dama tare muke itace ke ta fama da lalura
na ko a gida.
Hankalin kowa a tashe don yadda baba yake matukar jin jikin shi ko matsi bayayi
sai na,uran taimako da,aka saka mashi ke aiki.
Zancen karan da akayi an tsayar da magana dole sai anga Ahmed anji ta bakin shi
za,a,san yadda za,ayi.
Gashi har lokacin bai dawo garin ba kullun akaje gidan baya gari Jamila take
fadi.
Ashe ta dawo ya samu labari gurin wani abokin shi shine yake boyewa kada su
ganshi.
Sai dare sosai yake komawa gida ya kwanta tun da safe ya bar gidan ya koma
maboyan shi ya boye.
Duk wani dan gidan hankalin shi a tashe yake yadda baba ake hasashen ya samu
faralazy ne barin shi guda na dama.
Gashi har zuwa lokacin yana unconscious bai san inda yake ba sai cewa likitoci
keyi akwai improvement ga lafiyan shi.
An yanke shawaran za,a fita dashi waje wani abokin sadauki likita yace a kawo
shi gurin su su duba shi a Germany.
Komai an cika na tafiyan su waje da baba lokaci kawai ake jira na fita da mummu
kawai sai shi sadauki da,Sagir aka shirya tafiyan da za,ayi.
Ina zaune Iyya tana tsaye a kaina ta wade min lemo zan sha ya shigo dakin zai min
sallama.
Tana ganin shi ta fara gaudashi tare da mashi yaya maijiki yace Alhamdullahi Iyya
zamu tafi yau da,daren nan lagos gobe da safe zamu daga dashi.
Iyya tace kai duniya gaskiya wanan yaron wallahi bai kyauta muna ba wallahi wanan
sallon yaudaran nashi yayi yawa ina zai kai alhakin wanan bawan Allah da,sanadin
shi ya mayar haka ?
Ya tako zuwa inda nake ina tsotson lemun da Iyya ta wade min a hankali yace yaya
jikin naki Fatima ?
Nace naji sauki yaya yaya jikin baba din yake ya dan lumshe idanuwan shi a
hankali yace yaji sauki yau insha Allahu zamu tafi.
Ki kula da shan maganin ki Fatima kin dai ga yadda kike fama ban how long zaki yi
ba anan yadda likita yai min bayani zasu dan rike ki suga yadda jikin naki zai
kasance kafin su sallamay ki daga nan.
Idanuwana na lumshe ina jin wani ba dadi yace naso mu aikawa mutanen gida don su
san halin da kike ciki amma maji ta hana tace kada mu tayar masu da hankslin su
suma.
A bari har aga yaya jikin naki zai kasance tukun sai a fada masu amma ni naso su
sani kila za,a samu wanda yazo daga can ya zauna dake.
Shiru nayi ban da ta cewa sai dai naga aiko yayane ya kamata a basu hakkin su a
matsayin su na mahaifa na.
Don idan sunji bazasuji dadi ba daga baya sai dai banda yadda zanyi don ban da
tacewa ni yanzu.
Muna tare muna hira jefi jefi dashi wanda na lura bai a cikin hankalin shi a
lokacin.
Yace zai tafi gida ya shirya ya bar zancen makarantan Sa,ade a hannun bashar yana
ganin zuwa wani Monday za,a kaita makaran ta.
Musa ma Bashar zai kula da zuwa mai visiting kamar yadda ya saba zuwa mai.
Nace na gode a hankali ya mike yace zai tafi ya dawo idan ya kimtsa nace Allah ya
tsare ya fita.
Da yamman ne wani abokin bashar ke fada masu cewa yaga yaya Ahmed yana garin don
sun hadu dashi da rana a,wani shago yana sayayya.
A gida kuma mama Asiya da yan uwanta suna cikin matukar tashin hankali sosai don
tana gudun wani abu ya faru da mijinsu a sanadin dan ta.
Wanda tasan ba zasu yafe mata ba don halin da danta ya jefa gidan ko yanzu bata
da shakata a gidan kowa sai zagin su yakeyi tanaji tana gani babu yadda zatayi akai
sai hakkuri.



ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU

IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,,,

IDAN KIN BIYA KIKA TURAWA WANDA BAI BIYA BA MUN BAKI GA ALLAH YA SAKA MUNA AKANKI
YAR UWA,,,


Ya dawo acikin shirin shi ina kwance Iyya tana kokarin fita da ta gan shi yace,
Iyya ni zan tafi don Allah mutumiyar ki a kulla da ita sosai naso ace ina garin don
na bata kullawa sai dai hakkan baisamu ba.
Nasan ban da matsalar hakan don ke da maji kuna kusa da ita bana son tana wanan
rashin cin abincin da batayi yana matukar damu na sosai ko ba dadi abata koda kadan
ne please.
Iyya tace uban dakina kada ka damu tsakani da Allah nake zaune tare da ku zanyi
wa Fatima duk abinda kasan zan iya yiwa yar cikina shi insha Allahu.
Ya ciro kudi masu yawa yabata yace ga wanan ki rike a hannun ki ku dinga lalura
dashi a nan din.
Tai mai godiya ta fita daga dakin ta barmu mu biyu dagani sai shi a dakin.
Isowa yayi inda nake kwance yana cewa na,shirya zamu tafi yanzu bakin gadon da
nake kwance ya zauna ya kamo hannuwa na.

84 / 92