Author : Zainab Idris Makawa Seenabu Category : Complete Novels
wani abu don lokaci yana
ja gashi ina son zuwa umurah cikin watan nan.
Nace to Allah ya kara baka lafiya yaya yanzu may kake ganin za,ayi ne ke nan ?
Naci gaba da cewa su baba ma nasan kaine mai tallafa mashi yanzu gashi kuma
lalura yazo ya gifta akai.
No ki bar zancen na su baba da mutanen Rabah na riga nai masu tana din nasu ko
yanzun dai ina son ki taimaka min ki yi list din mutanen da kika ga yadace aba wani
abu sai na gani nace to bari na dauko pepper da biro sai na fara a gaban ka ko ?
Sai dana je gurin Iyya a kitchen na bata hakkuri taci gaba da aiki zan dan yi
wani abu yanzun ne.
Tace haba hajiya dama dai aike ce baki zama amma komai da kuke bukata ai na iya
yanzu wanda ban iya ba zan kiraki ki duba min .
Na dawo gurin shi ida na fara rubuta sunayen makwabtan su na can gidan baba.
Inayi ina lissafo mashi wa yanda nake rubutawa har na kawo gurin na ugun da muke
zaune a yanzu shine ma yake kara tuna min da wasu gidajen idan na manta.
Yace banji kin sa sunan mutanen ki ba mana suwa ke nan yaya na tabaya cikin sonji
su ?
Yace masu gadin ki mana nace Allah sarki wallahi har na manta dasu nan rubuta
sunayen su ciki.
Nace shike nan ko ina ga an gama ya dan dago kai yana kallo na, yace kin san ban
san mutanen arzikin ki na can gida ba fa ?
Murmushi nayi nace har dasu yaya za ,a rubuta yace ki rubuta su mana su ma.
Mutum kusa goma na rubuta mai yan uwana dana mamana har da yayan mama tabawa
ciki.
Yace motan da nai odan kayan sun shigo sukace don haka bashar zai zo sai a bashi
list din kinga ga musa ya dawo sai yakai na mutanen ku shi da driver ko ?
Yadda ya fada haka akayi washegari nan gida ya kace may su yaya Sagir yaya Abdul
da yaya Jibrin kannen shi sai yaya bashar da wasu ma,aikatan su ne sukai ta faman
rabon wanan kayan shi yana daga ciki tare dani ina kula dashi sai dai duk wanda ke
son ganin shi yaya Bashar ya hana a shiga gidan sai da shi da kannen sadauki kawai
suke shigowa gidan.
Take labari yakai ko ina sai ga al,uma bayin Allah masu bukata sun yo caaa a
gidan.
Nan yace ma bashar da ya shigo ya fada mai araba masu sauran sai a karo buhu
hamsin a hada masu dashi.
Ba karamin mamaki nayi ba da irin wanan abin alherin da yaya sadauki yayi ba koda
yake ba mamaki don yagaji alheri ga uwa da uba ne.
Ankai kayan azumi a gidan mu ida abin ya zama abin magana a gari ashe ya ba da
buhu biyar na shimkafa yace a rabawa mutane gari kuma ban sani ba sai da musa ya
dawo ne yake fada min.
Nai matukar mamaki duk da ba,a mamaki da ikon Allah wai a kwallon kafa ne yaya
sadauki ya samu wanan kudin haka.
Ikon Allah ke nan yau sadauki ne da,wanan irin alheri ga al,umma haka ubangiji
Allah ya kara albarka.
A kwana na shidda ne da azumi yace zai tashi da azumin naso yadan kara sha amma
yace zai gwada ya gani.
Lafiya yakai azumin shi ranan haka yaci gaba da azumin shi kuma yanzun yana fita
zuwa site din su ya dan duba su.
Ranan ya dawo da dare bayan mun gama buda bakine yake cewa ina fatan kin fara
shirin tafiya ko ?
Nace zuwa ina yaya ?
Yace umurah mana daga can kuma zamu wuce chaina akwai wani aiki da zanyi don ina
son bude kamfanin karfe anan sokoto insha Allahu.
Ban san lokacin dana fada jikin shi ba na ma manta da wata Iyya Rabi a gurin
lokacin.
Shima rugumoni yayi yana murmshi yace cikin harshen turanci kin san dama fa
bamuje honey moon din mu ba kin ga sai muyi shi acan tunda kuna hutu.
Dan jaye jikina nayi tare da cewa kai haba yaya wani honey kuma bayan wanda ka
lashe a nan cikin gidan ka yace to bari kigani idan mun tafi ai.
Koda na farga ashe iyya dake zaune tana kallon sallah a kasar makka ta bar
falon .
Nace lah ashe iyya bata falon nan ban ma san tashin taba wallahi kaga ka koreta
ko yaya ga Iyya da son kallo wallahi.
Yace kin dai koreta ke bake ce kika rugumay ni a gaban ta ba ya kamata fa ace an
saka tv a cikin dakunan nan don kallo kinga ko musa na lura idan ina falon nan
kamar ina takura mashi shima.
Washe gari kuwa sai ga masu hada starlight sunzo gidan suka hada ako wani daki na
gidan kowa da nashi receive din a dakin shi.
Nan naita faman koyawa iyya yadda zata dinga kamo tashan da take so a dakin ta ita
kadai.
Ashe tafiyan har su babane da su mama za,ayi shi sai da tafiyan ya matsone saura
kwana biyu mu tafi naga ya shigo da passport din masu tafiya.
Daga iyya sai Musa na muka bari a gidan na fada mata don Allah kada a manta da
masu gadi gurin girka abinci idan sunyi.
Naje gidan gurin su mama na samay su suna shiri gaba dayan su ban fita ba sai da
na gyara mata kayan ta da daki da yake wuni zan dayi masu a gidan take ce min ai
gwagona ce zata zo ta zauna mata daki da Amira don bata tafiya ta barta ita kadai a
gida hakana.
Anty Amira sama sama muke don haushina da take ji babu abinda ya canza a ciki
sai ma ince ya karu ne kawai yanzu.
Sai bayan la,asar na bar gidan zuwa gidan anty maryam can muka lalace da ita
wanda hiran namu akan mazajen mu ne mukayi shi.
Na dawo gida na samu Iyya ta gyara ko ina ta gama komai yadda ya kamata sai
bayan sallah magariba ya shigo gidan.
Muna falo gaba dayan mu sai mashi sannu da shan ruwa mukeyi a kasalance ya zauna
don har yanzu ba wai karfin jikin nashi yake ji ba sosai.
Nan muka shiga jera mai kayan buda baki a gaban shi bai ci wani abu ba sai kayan
fruits din da ya sha kawai ya kai kwance fuskan shi yana kallon tv ana sallah asham
a saudiya tv.
Yace iyya Rabi gobene fa tafiyan mu insha Allahu zamu tafi mu barki da Musa
sarkin son yawo kingan shi kada ki bari ya wuce takwas bai shigo gida ba kun rufe
don tsaro.
Tace insha Allahu nawaje na za,ayi yadda kace yace kai kuma kaji may nace ko?
Musa yace naji yaya ai ba inda zan tafi ga tv nan muna kallo ai da rana ne kawai
nakan dan fita can bakin shagon.
Daga haka yai shiru idanuwan shi suna a lumshe sai da akai kiran sallah suka fita
tare da MUSA.
****** ********* ******
Washe gari da azahar muka bar garin sokoto zuwa sadauya mun sauka da dare inda
akai muna screening motan da ke jiran mu muka shiga sai wani hotel nan muka kwana a
jidda sai da safe muka wuce zuwa madina.
Ibada sosai mukeyi ba kama hannun yaro har su umma da mama sun bani mamaki sosai
yadda naga suna ibadan su sai dai bawai sun bar halinsu bane ko acan.
Adduoina sun fi yawa ne akan Allah ya shirya min yaya sadauki da samun zuria
masu albarka dam yan uwa musulmai da suka fada cikin irin wanan halin .
Sai dai a can ni da mummy muka zama kamar kawaye sai mama da muke tare da ita
wani lokaci don mama bata da time din wasa ko kadan ko yaushe cikin ibada take .
Mun bar madina mun nufi makka a can mukai kwana goma muka fara shirin dawowan su
gida mu anan zamuyi sallah two days after sallah zamu wuce chaina din.
Ana gobe zasu tafine ina makale da mama da mummy da wani iri shakuwa ya shiga
tsakanin mu yanzun da ita.
A can nice mama take sakawa na zaba masu abubuwa ni da mummy wanda kusan sayayan
na Amira ne da naji ance wai zatai aure bada dadewa ba.
Har gado nice yaya yasa a gaba na zabi gadaje har guda biyar masu kyau.
Da,safe mukai masu rakiya suka tafi muna tsaye muna kallon su ba yadda zan yi ban
san lokacin da hawaye ya zubo min ba.
Muna motane yai dan murmushi tare da rungumoni zuwa jikin shi na langabe kaina
ina share hawaye a hankali yace baki son rabuwa da mama ko?
Ban yi magana ba sai ajiyan zuciyar da nayi kawai muka kai masaukin mu wanka
mukayi muka nufi masallaci gurin sallah sai dare sosai muka dan huta kwana biyu duk
a cikin masallaci mukayi shi.
Ranan sallah na saka wani dogon rigan mai tsananin tsada da ya sayo min a wani
katon shago na kayan mata.
Rigan da gani ta matan manya ce irin tasu sai wace ta isa take sayanta
Na yafa mayafin rigan take na koma kamar irin matan manyan larabawan da muke gani
ko kuma matar wani kusa a kasan mu.
Ga zubbunan gold da na saka guda biyu a yatsuna wuyana kuma Diamond ne kiran
Dubai sai takalma mai tudu da yar karamar jakan takalma dana rika a hannu na sai
wani kamshin turaren larabawa ke tashi a jikina.
Yana falo zaune na fito a cikin shirina wani irin mugun kishina ne ya darsu a
zuciyar shi.
Na karaso inda yake zaune shima kayan maza yasa na larabawa masu tsada na karaso
inda yake zaune cikin wani takon da ban san inayin shi ba.
Wani kamshi ne ya daki hancin shi har ya saukan mai da kasala a lokaci daya.
Ya sake idon shi yana kallona har na karaso gare shi tare da,dan fadawa jikin shi
ina cewa yayana barka da sallah.
Yace Fatima anya kuwa kece haka ko dai an canza min matane nace bari ka tabbatar
da ni dince to na dan kai mai wani guntun cizo a kunnen shi ya dan saki wani dan
kara yace muguwa.
Na mike ina dariya yace Fatima kinyi kyau kinyi kyau sosai wallahi ban san may
yasa duk dogon rigar da zaki saka sai naga tai matukar karban ki kaman don ke aka
dinkata ba ?
Gaskiya kafin mu bar garin nan sai na kara saya maki irin dogayen rigunan nan da
yawa koda mun koma gida ki dinga min kwaliya haka dasu.
Nace kai haba yaya kaface da tsada ka,sayo su fa ai biyun nan ma sun isa haka
please.
Yace Fatima shigan ki a cikin suturun alfarma shine mutunci na ga idon idon
jama,a shigar ki shine zai nunawa duniya ni Umar ina sauke hakkina akan iyalina.
Ya jawoni da hannu daya na fada a jikin shi yace bakin san ko waye mijin ki ba ko
bakin U F ba ko Fatima ?
Nai dariya tare da dan shafo fuskan shi da hannu daya yai murmushi nace niko
nasan waye mijina don ni nasan kayana.
Yace to ki godewa Allah daya baki Umar a matsayin mijin auren ki uban diyan ki nan
gaba kuma.
Yace Fatima mijin ki mai tsada ne mai daraja kuma a idon jama,a sai dai a idon
mutum biyu zuwa uku ne kawai yake mai rauni.
Dariya nayi nace idona dana mama ke nan na ukun ne ban sani ba yace na ukun shi
ne baba.
Kai yaya kada kaiwa baba haka wallahi tun haihuwan ka har yau baba baida wani da
dayake ji dashi kamar ka a duniyan nan.
Iyya fa ta fada min irin son da baba ke maka tun haihuwan ka har ya kai su Umma
suna kishin ka tun kana karami har yanzu.
Murmushi yayi tare da jawoni jikin shi yana sinsina na kamar ya samu handkici mai
kamshi yacs nasani Fatima nima nasani wallahi.
Iyya Rabi batai karya ba son da baba ke min yasa su imma suka sakani a gaba da
horo tun ina karami ga mamanki da shegen hakkuri duk abinda akai min kona fada mata
bata cewa komai sai dai tace min inyi hakkuri kawai.
Ya kara motsoni a jikin shi yace kin san may fatima nace ,a,a yayana yace
watarana har nakan zargi su Umma a raina akan da hannun su a cikin lalacewa na a
baya.
Sai dai zato zunubine koda ya zama gaskiya Astagafullah amma yadda suke gwada min
bana jin dadi Fatima.
Sun hana diyan su hurda dani sun hana mutanen shiya ma hurda dani haka yasa na
kasance ban da aboki sai bashar.
Bashar yai min kokari a rayuna na Fatima banda kamar bashar a duniyan nan kuma na
san har gobe banda kaman shi wallahi.
Yace humma Fatima idan ina tuna wasu abubuwa bazan iya koda gaisawa da Umma da
mama a duniyan nan.
Yace akwai lokacin da maji tai tafiya wallahi abinci hana min shi sukayi haka
nake takawa da kafa har gidan su bashar a can zanci insha sai dare zan kamo hanya
na dawo gida da kafa.
Wata rana ruwa ya hana naje gidan su bashar cin abinci na shiga gida ko zan samu
wanda ta tausaya min cikin su ya bani ga abinci ina gani amma sukace min wai na
Ahmed ne da Imirana.
Nadawo dakin mu da yuwa sai ga Bashar cikin ruwan nan ya aro mashin din makwabcin
su bai ko iya tuki sosai ba yakawo min abinci shi naci har dare na kwanta.
Ga maji bata dawo ba aai ashe tayi yaji ne ta tafi gida ban sani ba lokacin tana
goyon Amirah.
Kin san may nacece mai a,a lokacin duk jikina yai sa yi ga labarin da yake bani
yace wallahi a lokacin ne na fara shaye shaye tun ina da fifteen year Fatima.
Idanuwana na runtse don jin abinda ya fadi nan yai ta bani labarin irin musguna
mashi dasu Umma sukai tayi har mama ta dawo.
Yace ni mummy batai min komai ba wallahi don daidai da rana daya duk da nasan
itama tana kishina kan wai baba yafi so na da diyanta amma tana boye zafin kishin
ta akaina.
Don Allah Fatima duk zafin kishin ki a kaina kada ki mu,amula da masu sihiri
bala,i ne da fadaqa halaka ga mai irin wanan halin daga karshe.
Kara shigewa jikin shi nayi nace kada Allah ya bani kwandalan zuwa gidan boka ko
malam wanda zan illanta rayuwa wani bawan Allah.
Munje sallah idi muka dawo bamu sake fita don ansha ruwa ba azumi muna gida muna
farautawa nunan mu rai.
****** ********* ******
Mun sauka a China inda na kara tsinkewa yaya ke nan irin abokan da nagan shi da
su can har sun so sufi na saudiya ma don ko a can naga yadda yake hurda da yaran
masu kudin kasan ga kyautan dana samu har tsoro abin ya bani.
Mun tafi wani katafaren hotel mai shigen tsawo da kyawo sosai kauyanci kan
wallahi nayi shi sosai na lumshe idanuwa na daga inda muke zaune a bayan mota nace
Alhamdullahi Ala Kulli Halin.
Yace jawoni yace may kikace Fatima nace godiya nake mikawa ga uban gijina da ya
nufe ni da hakan .
Tsayawa bada labarin hotel din zai bata muna lokaci amma gaskiya nasha kallo
Allah ya horewa mijin kowa yakaita kashen duniya tai kallon abin mamaki a can.
Munga karamawan ta ban girma a gurin abokan shi na can nikan sai faman godiya
nake ga Allah da ya daukaka min rayuwana haka.
Ina rungumay a jikin shi muka bar gurin haraban hotel din zuwa masaukin mu a tare
muka zube agado dashi.
Na lumshe idanuwa na tare da ajiyan zuciya yace yaya akayi ne Fatiman yaya ?
Nace ni may ma zance yaya dariya naji yayi yace kice kina son U F dinki sosai
Fatima .
Ki dinga gyara min kanki ina kallo ko yaushe gadona yazama ready ba sai na nema
ba abani idan kin min haka kin gama min komai Fatima a rayuwana.
Murmushi nayi nace ai baka da matsalar haka din ko yanzu yaya .
Yace umm haka din ne amma ba sosai yadda nake so a raina na ba jinayi ya shiga
zuge min zif din rigar dake jikina a hankali tare da fada min wasu kalamai da bazan
iya fadin su ba anan.
Nace ko wanka ba zamuyi ba yau kuma yace wanda mukayi kafin mu fita may mukaci
dashi kada fa ki manta honey moon dina nake yanzu.
Rugumashi nayi nace ai kayi abinka tin a gidan ka na sokoto sai dai ka dora inda
ka tsaya kawai.
Yace hakan za,ayi ranan kan nafitar da duk wani kunyan shi a idanuwana na nuna
mashi nifa ba yar kauyen da yake kirana da ita bace.
Rayuwa sosai na jin dadi mukayi da yaya a kasan China satin mu biyu a can ya
sanya hannun jari a kamfanin yin karafuna da yake son yi a sokoto.
Mun dan kara kwanaki muka wuce har Hong Kong nasha mamaki sosai yadda yaya yasan
kasashen duniya haka da mutane kuma cikin yan shekarun kwallon shi.
Daga karshe muka dira a Dubai a lokacin banda matsalan komai a raina ban da na
tuhumar ko yaya yabai daina sha ba har yanzun .
Don wanan irin mutanen da naga yana hurda dasu haka dole ne idan mutum.baikai
zuciyar shi nesa ba ya yi aikin sabawa Allah.
Amma sai naga shi akan ibada baida wasa ko kada ko wani kasa yana da time din
sallah su ko baya gida zai bugo min waya yace lokacin sallah yayi na tashi nai
sallah.
A kasan Dubai kan kamar a gida Nigeria muke don yan Nigeria dake kasan maza da
mata gasu nan manya da yara kana gani.
Nan naga matan manyan kasan mu yadda suke hurda da matasa ko