Advertisements
Chapter 88 Reading A Lokacin Mu Ke by Zainab Idris Makawa Seenabu BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

A Lokacin Mu Ke by Zainab Idris Makawa Seenabu

Author :  Zainab Idris Makawa Seenabu Category :  Complete Novels

Chapter   88 / 92

261K to 264K   out of 275.8K words

yai nadaman zaman Ahmed da,wanan
yarinyar mara mutunci da ita.
Yana fita gurin baba bayan sun gama magana dashi kotu suka nufa shi da yaya
bashar sun samu danmasani ya ce idan zai samu kudin shi ya janye maganan shi.
Ba bata lokaci sadauki ya saka hannu akan zai ba mutumin kudin shi miliyan bakwai
da Ahmed ya karba a hannun shi.
Nan aka zauna ranan ya biya kudin a ka rufe case din tare da sako yaya Ahmed
yakai shi har gidan shi gurin matar shi ya nufo gida don lokacin har duhu yafara yi
ko.
Bai shigo gida ba sai da aka sallamay sallah yashigo gida agajiye dashi.
A sanyaye ya samay mu a falo muna hira Amir yana hannun Sa,ade tana mashi wasa.
Sannu muke mashi yana karbawa da kyat ya fada saman kujeran dake kusa da wanda
nake zaune.
Na kalle shi yadda na ganshi a wahale dashi nace ko zakai wanka ne ka ji dadin
jikin ka ?
Yace shine daidai tun safe muna koto ana zirgazirga kan zance yanzun dai mun samu
ankashe case din mun karbi takardun mu ko.
Nace masha Allahu yau baba idan yaga takardan shi a hannun shi kila hankalinshi
zai kara kwantawa hakanan.
Ya lumshe idanuwan shi yace ban tafi na,kai mai ba,sai da,safe idan Allah
yakaimu.
Nace Allah ya kaimu na mike na nufi dakin shi na hada mai ruwan wanka a can kafin
ya taso yayi.
Sai washe gari ne ya shirya tafi gurin baba ya kai mai takardan gidan nashi
da,aka anso gurin mutumin da ya sai gidan hannun Ahmed din.
Sai da baba ya tara kowa diyan shi da matan shi da,aka kirasu a,waya yake cewa
dama akan zance gidan nan ne gashi yau Allah yayi Sadauki ya karbo gidan a hannin
azzalumai macuta.
Don haka daga yau ina son ku sani gidan nan ba gida na bane gidan sadauki ne da
uwarshi don haka ko bana raye kowa ya rike wanan zancen a ran shi.
Duk suka dago kai suna kallon baba da mamaki don jin abinda yace wai gida na
sadauki ne da uwar shi yanzu.
Sadauki ya tare baba da cewa haba baba gidan nan na kowa ne baba tunda gida
nakane har yanzu ni bawai na karbo bane don ya zama nawa ba.
Baba ya daga mai hannun shi da kyat yana cewa wanan magana danayi ba fashi a
cikin shi sadauki gida nakane yanzun ba nawa ba.
Idan kuma kana,son ganin bacin raina ne a yanzu sai ka matsa da magana mu gani.
Dole yaja bakin shi yai shiru yana gudun yai magana wani matsala ya faru da baba.
Baba yace Ahmed dai yanzun sai kuyi kuka dashi da uwar shi don shine yaja ma kowa
wanan bani ba.
Don ni Allah ta gani nayi yadda ya dace nai maku muhalli wanda ko bayan raina
iyayyen ku daku zaku iya zama a ciki am.a ya,sa kafa ya take tausayin kowa dani
daku yasayar wa banza irin shi macuci.
Don haka yanzu na fada maku gida yana a zaman sadauki ne bani Abubakar ba kuma.
Sai kowa ya,watse na gama magana na ke nan ya juya inda mummy take zaune tai
tagumi sai sauraren shi ta yake yace ke turani ki maidani dakina nagama maganan da
zan yi kenan.
Mummy ta mike duk jiki ba kwari ta fara turashi zuwa uwar dakin shi cikin rashin
kuzari.
Nan ya barsu a,zaune kowa jikin shi ya mutu ana shigewa dashi Nafisa ta fara
mikewa tana fadin yau dai shi ke nan tafaru ta kare kurun kus kan kutsu sai kowa ya
fara neman madafa.
Maganan ta yai matukar ba kowa haushi uwarta ta kalle ta tace ke kan anyi
sakariyar yarinya wallahi nan.
Ke kan baki san ciwon kanki ba ko kadan yau wanan abin tashin hankalin da may yai
kama harda kike fadin wai takare.
Takare mawa ke nan kike nufi yanzu mu ko ku da baku da madafa kamar kowa.
Ai mu muna da gidan iyayye sai mu koma can mu zauna ku kuwa ina zaku kuda baku da
gidan uba.
Mu dai wallahi ancuce mu anzalunce mu sai dai muce Allah ya isar muna kawai
ancuci na kauye.
Saboda hainci da zalunci dan gidan ma da za,a tsira dashi akama a sayar wa mutane
su rasa matsuguni sai rabe rabe.
Sadauki ya mike tsab ya fara fita daga dakin bayan fitan Nafisa yabi bayan ta.
Sai mama da Amira da maryam suka mike suma suka fice daga dakin ran su a bace.
Lokacin Umma ke fadin muna fukai kawai kun kai ga yadda kuke so ai dama gurin ku
su ke nan duk su mamaye gidan to gashi Allah ya cika maku ai gida ya zama naku.
Sagir dake zaune kasa saman carpet yace haba haba Umma yanzu may yw laifin yaya
sadauki a gidan nan.
Mai laifi daban wanda bai da laifi ya taimake mu ya raba mu da gararanba a saman
titi kuma za,aga laifin shi a banza.
Gaskiya wanan ba adalci bane kuyi wa kanku nasiha ku san may ke a gaban mu ba,wai
mu zauna kuma muna cusa kiyayyan junan mu ba a haka.
Ya mike yafita daga falon shima,ranshi a bace ya,saka takalman shi ya bar falon.
Nan dai sukai ta watsewa daya bayan daya a falon kowa jikin shi ya mutu don basu
taba zaton wanan hukuncin baba zai iya yankewa akan su ba.

****** ********* ******
Da,sannu yau Allah yayi mun gama exam din final din mu gaba daya sai dai fatan
alherin Allah ya ba da sa,a kawai wa kowa daya zana exam din shi a matsayi
finalist.
Muna gamawa da sati biyu muka daga zuwa waje da yaya sadauki inda ni kaina ban
san tsawon lokacin da zamu dauka a can ba indan mun tafi.
Mun fara zuwa kasar hongkong, inda muka share kusan wata daya a kasan muna hutawa
kawai.
Dani dashi sai dan mu Amir da yanzu yayi wayo sosai zakace watan nin shi ya zarta
ya kai shekara ma.
Sosai nake jin dadin yadda muke rayuwa a wanan kasan a tsakanin mu ukun nan inda
sone da kauna tsantsanta ake gwadawa junan mu.
Don kowan mu yana son dan uwa mun shaku da juna fiye da tsanmani komai a tare
mukeyin shi.
Zai kwashe yai ta yawo da mu muna ganin gurare tare da yin photuna masu kyau.
Mun bar kasan zuwa kasar Beselona inda zasu buga kwallo da,aka dauke shi wani
contarack mai tsada da kudi masu yawa.
Ina zaune ina kallon shi yana shirin abubuwan da yake bukata da zamu tafi dasu a
gurin wasan
Can ya dago kai ya kalle ni ya sake min laulausar murmushi ya ce kina kallon
yadda mijin ki ke fita,gurin neman kudi halaliyar mu ko ?
Tsab ya,shirya cikin wasu kananan kaya sai ga wani abokin shi Daniel yazo dashi
zamu tafi na,dauki dan jakkan da na saka kayan mu a ciki muka kama hanya sai gurin
da za ai wasan ball din.
Muna isa ranan naga inda,akasan muhinmancin wasan kwallon kafa don naga taron dan
mutum da ban taba gani ba a duniya.
Wata baturiya ta karbi Amir a hannu na da sauri tace nima na biyo ta nan muka
shiga wani daki ta miko min riga mai tambarin yan wasan inda shima Amir din ta saka
mai rigan yan kwallo na yara mai tasu tambarin.
Hijjab ne a jikina irin dan karamin nan ta karba taje ta sa aka buga mai
tambarin su nasaka rigan saman dogon rigan dake a jikina tare da hijjab din na take
na saje da duk wanda yake a gurin.
Suka miko min wani dan abin wasa kamar hure wai na rika nikan na samu abin yiwa
Amir wasa dashi.
Muna fitowa a wani guri da,sai wanda aka yarda dashi zai shiga gurin nan naga yan
wasan kwallon duniya birjit dasu suna ta mota jikin su kafin a,shiga filin.
Can na hango sadauki rana,na,farko dana fara ganin shi saye da kayan su na yan
kwallo yana ganina ya bar abinda yakeyi yanufo ni yana murmushi.
Nan sauran abokan shi ke tambayan shi wai matar shi ne da dan shi yadda ya
rugumay mune ya tabbatar masu da amsan da suke son ji daga bakin shi.
Don hada kaina da nashi dana,Amir yayi guri daya a hankali yake fadin kiyi min
addua Fatima Allah ya bamu sa,an wanan wasan da za,a buga a yau.
Nace yaya Allah ya tabbatar da alheri yasa a,dace da abinda akazo nema ta hanyan
alheri.
Yace amin nan yan jarida da sauran median suka shiga daukan mu hotuna kalakala.
Kyau, kudi, ilimi yanzu duk Allah ya bani don haka gwargwado zan iya gogaiya a
cikin wa yan nan mutane.
Muna sahun gaba cikin officials muka fara fitowa bayan yace wa matar nan ta kula
damu amana please.
Muna futowa guri ya kaure da wani irin ihu wanda yasa na daga kai na kalli fadin
gurin sai da gabana ya fadi sosai naga gurin yana juya min.
Kujeru aka bamu muka zauna bamufi minti biyar da zama ba suka fito a jere dasu
ana taken team din su.
Sai flowers ake watso masu ta ko ina can na hango wasu da irin furen da aka bani
a hannkali nakewa dana wasa dashi yana dariya.
Sai daukan mu hutuna akeyi tako ina nan bayan sunyi taken kasan tasu aka fara
shirin fara wasa.
Wasa yakai wasa guri ya rude sosai mutane sai faman ihu suke inda sai ranan nan
nasan muhinmancin kwallon kafa da kyau.
Tun ina kallo ban damu ba,sai gashi da,wasa yai wasa da kaina nake daga Amir ina
nuna mai wasan .
Wanda idan mutum.ya gani zai dauka cewa wani wasan jin dadi nake mai a lokacin.
Har aka tafi half time suka dan huta suna dawowa wasa ya tashi sosa kafin atashi
wasan sai da sadauki da wani farin fata suka ci cibiyu babu ko daya .
Haba aiko guri kaure da ihin murna nan muka kutsa muka shiga filin akai ta muna
hutuna tare dasu suna ta daukan Amir kowa da kalan maganan da yake idan ya dauke
shi akai masu photo suna kiran shi little UF.
Washegari Naga karamawa ranan sai shaye shaye da lashe lashe da tsotson juna
akeyi.
Abinda yaban mamaki shine ina zaune na dawo a gajiye wayana ya nuna min sako
yashigo.
Ina dubawa yaya sagir ne ya turo min da photuna da akai muna a gurin kala kala
wasu ma ban san anyi suba ni.
Yana tayani murna na mayar mashi da amsa dana gode yayana kawai.



ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU

I'mIDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,,,,


IDAN KIN BIYA KIKA TURAWA WANDA BAI BIYA BA MUN BARKI GA ALLAH,,,,



Washegari aka hada lifaya, don taya murnan samun nasaran da sukayi akan wasan su da
suka buga na kwallo.
Mun sha kwalliya sosai a lokacin in cikin wani dogon riga mai launin dark blue
wanda yaji duwatsu a jikin shi sosai.
Nai rolling din kaina da dan kwalin shi wanda shima yana da duwatsu da aka jera
mai a jikin bakin shi.
Ga zobunan gold sun cika min yatsu na dama duka hudu, daya sayo min wuyana saye
da English gold.
Na saka wani takalma mai dan tudu akafana sai yar karamar jakar hannu dana rike.
Shigar tawa duk wanda ya ganni sai ya yaba da ita shi kan shi sadauki dana fito
sai da ya kasa boyewa a ran shi ga kamshi dake tashi na jikina saboda mayukan
danake amfani dasu a can yanzu.
Haka Amir shima yaji kwaliyan shi irin ta yara maza mai tsada sosai tare da saka
mai hula irin ta yaran turawa.
Wayan shi ya dauko ya fara daukan mu hoto dashi, yana yaba kyawon mu ni da
yaron.
A cikin wata irin dirkekiyar mota muke tafe dagani sai shi sai Amir wanda yake
rike a hannun mahaifin shi yana waya.
Muna Isa gurin munga karamawan ban girma a gurin mutanen da muka samu suna jiran
isowar mu gurin.
A gaskiya wanna mutane suna matukar girmama yan was an kwallon a rayuwan su.
Yana fitowa ya zagaya a bangaren da nake zaune ya bude min motar da kan shi yayin
da idanuwan mutane yake a kan mu caaa.
Wasun su da yawa a gurin basu san cewa sadauki yana da aure ba don su ganin su a
gurin su shekarun shi yai karami da aje iyali haka.
Hannun shi harde acikin nawa muka shiga babban holl din wanda yake makil da
jinsin mutane kala kala.
Duk wanda yake da iyali acikin su tafe yake da iyalin shi a gurin.
Nan aka shiga gaisawa da mutane ana introducing din juna ga manyan masu kudin
kasan turawa.
Inda matan dake gurin suka shiga kallon kalar shiga ta wanda ke baiyyana
musulunci a fili.
Don haka aka shiga gimamani don suna matukar daraja matan musulmai sosai.
Ga wasu flowers da ake watsowa daga sama sai shagali suke suna shaye shayen su
irin na al,adan su.
Nan sadauki suka hade da wani balarabe mai kudi dan kasan Dubai mutum ne mai
tsananin arziki da tarin dukiya acikin nahiyar Arab side.
Gaba daya shine mutum na farko da yazo na daya a duk duniya arziki da tarin
dukiya.
Gashi da ra,ayin son wasan kwallon kafa don matashi ne shima haka yasa ya kyasa
taimakawa yan kwallo musanman matasa musulmai irin su sadauki.
Yana kuma da kamfani na kera gwala gwalai da diamond nashi na kanshi ga rijiyoyin
mai da yake dasu kasa kasa na duniya.
Yana da kamfanin kera jiragen sama da na ruwa wanda yake mallakan shi na kansa.
Hannu Abu sufiyanu ya mika ya karbi Amir dake a hannu na ya dan yi mashi wasa
tare da sumbatar yaron.
Cikin wasa yake cewa sadauki ya bashi Amir don yaron ya shiga ranshi.
Sadauki yake cewa ya bashi yace ya gode tare da kissing din yaron inda ya juya
gurin na hannun daman shi yai mai magana.
Mutum ya amsa da insha Allah.
Nan yaja hannun sadauki wanda nake biye a bayan shi sun dan jima suna magana irin
ta Siri a tsakanin su.
Wanda ashe alakace ta business suke kullawa a tsakanin su a lokacin, mutane da
yawa sun San ba kebewar banza Abu sufiyanu yake da sadauki ba a lokacin.
Da hannu ya yafito na nufin na karaso inda suke a tsaye, yake ce min nai wa
mutumin godiya.
Duk da ban San ko na may ye ba amma nai mashi godiya irin ta addinin musulunci
wanda ya kara sawa mutumin jin dadi a ran shi.
Don shi mutum ne wanda yake son mutane masu yi mashi godiya da nuna farin cikin
su gare shi.
Nan dai sukai ta gaisawa da mutanen arziki na duniya kala kala ina rike a hannun
shi har taro ya fara watsewa.
Muka Fara ficewa daga sahun farko muka bar gurin don a lokacin a gajiye nake
sosai ga Amir da nauyi ba kadan ba.
Muna a mota ya dan sasauta tie din wuyan shi yana juyowa inda nake zaune yana
cewa my queen kin gaji ko don nasan baki saba irin wanna kwaram din namu ba ke.
Idanuwana na Dan lumshe nake cewa nauyin daukan wanan din dai ya isheni .
Yace Kai ni dake son na samu ma yafi haka girma idan son samu ne a gurina.
Nace kai Yaya idan Amir yafi haka kiba kuma ai sai dai na dinga barin shi a zaune
guri daya don ina zan iya daukan wanda yafi wanna girma haka.
Yanzun ma a Yaya nake iya daukan shi balle ya kara yafi nan kuma ?
Ya dan juyo a mamaki yace Queen baban nawa zaki bari a zaune don tsaban mugunta
kuma ?
Nace ai nima babana ne ko ko kamanta nima shi ya haife ni ne wai ?
Nace sune fa gata yanzu a duniya don sune sillar wanna rayuwan da nake a ciki
yanzu.
Murmushi yayi don jin abinda na fada yasan ba karya na fadin ba haka zancen yake
ko yaushe Ina matukar godewa mama da baba din.
Yace tare da kwantar da kanshi saman kafada ta nauyin ya karu min biyu wanda a
lokacin ba nauyi naji ba sai wani sanyin dadi da naji a raina kawai.
Don farin cikina yanzu karuwa yake a kullun Ina mai godewa Allah na da biyayyan
da yabani iko nai wa Maji ban butulce mata ba ga bukatan ta a gare ni na auren dan
ta da duniya kewa kallon lalatace.
Matsalata daya yanzu shine ban gama tantace ko sadauki ya daina halin shi ba ko
yanayi har yanzu.
Haka ne yakan rage min jin dadina a kullun na tuna da wanna rayuwan nashi na
shaye shaye.
Ai fa tuni idanuwana ya ciko da hawaye yana magana jin nai shiru yasa shi dago
kanshi daga kafadata ya kalleni.
Ganin da yai min a cikin rashin walwala komai ma na duniya yafita min arai a
lokacin.
Da sauri ya Kara dagowa yana kallona acikin mamaki tare da kamo hannuna ya rike
gam a cikin nashi yana tambayana may kuma ya faru haka queen ?
Na sauke ajiyan zuciya tare da zubo hawayen dake a cikin idanuwana kasan fuskana.
Yasake maimaita tambayan shi da wai may ya faru bana son ganin ki ko kadan a
cikin damuwa queen.
Na sauke ajiyan zuciya tare da mayar da kaina ga nashi kafadan ina sauke ajiyan
zuciya a hankali a karo na biyu.
Da sauri ya kara jawoni a jikin shi ya rugumay mu yana cewa kada kimin haka
Fatima kinsan kwanciyan hankalinki shine nawa yanzu.
Na dauka yanzu zakifi kowa farin cikin gani da idon ki da kikayi na irin baiwan
da Allah yai ma mijin ki.
May ye kuma ya samay ki a lokacin da nake tsanmanin farin ciki a gare ki Kuma ?
Na goge kwallan da suka fara zubo

88 / 92