Advertisements
Chapter 46 Reading A Lokacin Mu Ke by Zainab Idris Makawa Seenabu BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

A Lokacin Mu Ke by Zainab Idris Makawa Seenabu

Author :  Zainab Idris Makawa Seenabu Category :  Complete Novels

Chapter   46 / 92

135K to 138K   out of 275.8K words

da ya rabane yai maki cin fuska kin ce a,a.
Wallahi Allah mama bashi bane kuma ba komai, ikon Allah inji maji ba komai kike wa
kuka ba to may yakawo kukan?
Mama yaya ne sai kuma nai shiru don, na tuna da zancen alkawarin da nayi bazan
fadawa kowa ba.
Hakali a tashe tace yaya yai maki may hankali a tashe take tambaya may yai maki
Fatima ?
Fada min mana nace may sadauki yai maki ne wai,?
Taba ki yayi ko may ?
Nace da sauri a,a mama don nagane may take nufi da tambayana tabaki yayi.
To may yai maki nai shiru nace mama ba komai bane cewa yayi wai na faye yau
shiyasa maza ke ganina .
Sai naji tai ajiyan zuciya tare da dafa ni tace kyaleshi ai munyi maga in don
zancen Usman ne ya fada min yaron ba mai gaskiya bane.
Nace cikin kuka tau mama ta ce ki kwantar da hankali Allah zai kawo maki wani
wanda yafi Kabir insha Allahu.
Tace karbi wanan kayan daga cikin kayan lefen da ya aje ne na debo maki kema a
matsayin naki tsaraban.
Da sauri cikin girgiza kai nace mama a barshi wallahi ko kadan raina bai baci da
rashin kawo min ba don ai yasaba kawo min.
Au kyautana ne kuma baki bukata ko may na girgiza kaina da sauri na sa hannu na
karbi kayan dogayen riguna matsu kyau da masifan tsada har guda hudu.
Nace amma mama kaman kayan su yi yawa fa tace nifa na baki Fatima nace na gode
mama.

****** ********* ******
Da yamma daya daga cikin rigunan nai kwaliya dashi kaman yadda suma su maryam shi
suka saka sai dai nawa yafi nasu tsada da haduwa, nisa ba kusa ba.
Sam ban san yana cikin falon ba nafito cikin dogon rigan mai maroon clour sai
tsakiya a bude yake an yi mai kwalliya da wani silk dark blue da duwatsu har kasa,
hannun rigan manya manya ne shara shara dashi .
Kwaliyan yai matukar karbana fa kamshi turare na na white musk da ko yaushe shi
nake shafawa a jikina da tufafina.
Haka kawai ganin shi zaune yasa kirjina bugawa a lokaci guda yana zaune cikin
shiga ta kamilan mutane.
Masangalin kujera kawai na dafa nace ina wuni yaya ?
Kamar kullun wanan yaudararen idon nashi ya watso min ya na kallona a fakaice, da
su.
Kai Bintu wanan hadaden rigan fa kuma maryam ke tambayana don bata san dashi ba.
Nace daga mai kauna na, a takaice.
Kan shi kawai ya girgiza don jin amsan dana ba maryam din a lokaci guda,
wayancewa yayi don yasan inda magana ta dosa.
Na kalli maryam nace akwai wani tambaya ne kuma anty ?
Ai ni dama nasan da,wata a kasa tunda naga ba,a baki taki a fili ba nasan zance
ya canza ke nan.
Nace wanan kuma zargin ki ne anty ni uwata mai kaunata tabani shi don tasan nina
dace dasu.
Da sauri suka juya gurin Maji da idanuwan su suna mamaki wanan riga mai bala,in
kyau yaya akayi tabani shi gasu.
Maji bata bada fuskan tambayan ba balle su san gaskiyan maganan don haka sai kowa
ya share zancen.
Ganin yanayin shi duk a tsarge ya ke lokacin saboda yana ganin sai na fadawa mama
zancen kwayoyin dana kwaso daga gurin shi.
Yana zaune ya rafka uban tagumi sai sauraren zancen, kanne shi yakeyi ba tare da
yai magana da kowa ba sai kace wanda aka aiko ma wani sakon tashin hankali.
Daga inda mama take a zaune muka ji muryan ta tana cewa ku tashi ku bamu guri
zanyi magana da yayan ku.
Hakan yasa muka mike daya bayan daya muka koma daga cikin dakin mu.
Shiko jin abinda mama ta fadi yasa shi saurin dago kan shi da sauri yasan ta faru
takare kenan yanzu sai da munafukan yarinyar nan ta tseguntawa maji zancen nan aiko
sai ball da yar iska gidan nan algunguma kowa ya huta.
Tace Baba na magana nake son yi da kai akan Fatima, yace shike nan yar iska
tafadi ashe.
Ba karamin kokari yayi ba gurin gyara natsuwan shi tare da dan dagowa daga
kujeran yana fuskantar uwar.
Mama tace ina son ka fada min gaskiya may ya hada ka da Fatima dazun da rana
tashigo gidan nan tana kuka?
Yace maji ita may ta fada maki nayi mata da ta shigo?
Kai ma kasan halin Fatima da zurfin ciki da kyat na samu ta dan fada min wai kace
tana kwaso samari kala kala a gidan nan.
Yanzu har wasu samari Fatima ke dasu ina bayan wancen da Allah baiyi auren su
dashi ba sai wanan da kace baka amin ta dashi ba kuma ta daina nagani.
A jiyan zuciya ya sauke yace ta rufani ke nan ashe ai nazaci bata da,wayo ne ?
Tace tunda kai mata fada kuma taji banga abinda zaisa kuma ka kara matsa mata ba
akan zancen.
Murmushi yayi yace maji ni fa duk abinda nake mata a saboda ke nake matashi don
tana karkashinki ne.
Idan da a, wani dakin take mai zai kaini saka mata ido da daukan mataki a kan ta
amma tunda bata son fada ai shike nan.
Maji tace dakata malam yarinyar nan fa amana take a gurina ka sani amma irin
yadda naga ka dauko tsangwama mata bazan lamunci hakan ba gaskiya.
Yanzu irin cin fuskan da kai mata ka bawa kowa tsaraba a gidan nan amma ita ka
hana mata kayi daidai ke nan Baba ?
Amatsayinta amma a guri na ina duk abinda kaga naiwa yan uwanka ita ma ya dace
kai mata tunda ni bani banbanta tsakanin su.
Waya san ta hanyan da zata taimaka muna itama watarana shi mutum fa rana garw shi
ta inda ba,ai tsanmani ba.
Yace maji yin haka bada wani manufa nai mata hakan ba kawai dai dama alkawari nai
mata cewa idan bata gayar da mutum bazan mata tsaraba ba.
Tace wanan matsalar kace don ni na bude akwatin kayan lefen dake aje na zaba mata
wanda ta dace da ita.
Ya dago kai kamar zaiyi magana sai kuma yai shiru can yace ai shike nan ko?
Idan kuma akwai abinda ya dace akara mata daga ciki sai abata suma su Amirah
abasu man shafin da turare da sauran abubuwa suyi amfani dashi.
Tunda ba wani abin kuma za,ayi da kayan ba yanzu ai, ko ?
Kamar yaya ba wani abin za,ayi da kayan ba ka manta da maganan mahaufin ku ne da
yace nan da wata daya ku fitar da matan da zaku aura.
Murmushi yayi yace maji ni ina zani na nemo mata nan da wata daya hakkuri dai
Baba zai yi muna har lokacin yayi.
Mama tace wanan kuma maganan ku ne da mahaifin ku idan baka fitar va ai shi ya
maka mata da kan shi.
Ya zaro ido yace haba maji kamana za,ace za aiwa mata kuma ai ni yanzu na wuce
wanan ko.
Wancan ma da kukayi da farko ba,aji dadin shi ba balle yanzun ace za,a sake wani
kuma again idan lokacin yi yayi ai za,ayi din ne maji.
Ina ruwana ina zaune ni a dakina matsalan ku ne da mahaifin ku ni banda na cewa
ai.
Duk hiran da suke da uwan hankalin shi yana akan zancsn abinda ya faru da rana
tsakani na dashi.
Mama ta kwala muna kira tace ku fito tun dan uwan ku bai fita ku kara mashi
godiya ya baku kayan kwaliyan dake cikin akwatinan shi gaba daya wai ku raba ku
uku.
Godiya mukai mashi sai dai yana kokarin ganin idona danake boyewa a bayan Amirah.
Mikewa yayi don wayan da akai mashi yafita lokacin naji dadin sakewa sosai a
falon.

****** ********* ******
Sannu sannu na dan sake jikina na koma normal na bar zancen komai a raina sadai
kallon mai bisa ruwa nakewa sadauki doni na tsinke da lamarin shi yanzu.
Maryam tafito tana tambayana na bata wani handout din muna chemistry na 200
level nace ta duba a cikin jakad litattafaina yana ciki don ina kitchen ina aiki.
Zaro takardan da zatayi sai ganin roban wanan drugs din dana dauko a dakin yaya
tayi.
Saman gado ta zauna tana kallon maganin tare da karanta shi a fili ta furta drugs
kuma a jakkan Bintu.
Hankalin ta ya tashi sosai a kitchen ta samay ni tace Bintu zo nan ganin hankalin
ta a tashe yake yasa ni bin bayan ta zuwa dakin mu.
Sai da muka kai zaune ta zaro roban daga inda ta boye fuska a daure take ce min
Bintu may ne ne wanan nagani a kayan ki?
Cikin kura min ido bata ko kiftawa don son jin bayani daga gare ni cikin damuwa.
Nace ba nawa bane anty nima dauko shi nayi a wani guri na boye shi a nan da kika
gan shi.
Bintu fada min gaskiya a ina kika dauko wanan roban in ba naki bane ?
Na nisa nace wallahi anty ba nawa bane nagi maki kama da mai wanan halin daidai
da rana daya ne ?
Tace shi ya bani mamaki ai nake son sanin nawaye ?
Nace na dauki alkawarin boye zancen anty don Allah kiyi hakkuri amma,wallahi ba
nawa bane Allah.
Sai naji tace na yaya sadauki ne ko ?
Da sauri na kalle ta nace ni ban ce ba anty.
Amma kin san zaman su haka a gurin ki hatsari ne babba kuwa a gare ki ?
Yanzu dabanice nagan su akayan ki ba kuma nasan halinki may kike ganin zai faru ?
Nace nayi kuskuren barin su a tare dani amma na aje su don sheda kawai.
Tashi kiyi flushing din su yadda kikayi a ranan tun wani bai gani ba hankalin maji
ya tashi.
Yadda tace din haka nayi na zubar dasu a cikin toilet suka bi ruwa suka wuce.
Nan na barta zaune tayi shiru tana tunanen dalilin da yasa na boye mata tasan
cewa na yayan sune duk yadda akayi.
Da dare da Bashar yazo ta samay shi yadda ya fahinci bata cikin hayacin ta ya sa
shi matsa mata da tambaya may yake damun ta hakane wai ?
Tace matsalan yayan mune yayana ina ganin kamar bai daina shaye shaye ba har
yanzu.
Da sauri yace, kai may kika gani ban tsan mani yana sha ba kuma har yanzu gaskiya.
Tace koma may nene Bintu ta san komai sai dai tana boyewa ne, nan ta bashi
labarin yadda mukayi da ita da rana.
Ya nisa bayan yaji maganan ta yace tabsa tunda kikaga taki fadi akwai magana
gaskiya amma yaya akayi ta samu wanan abin a gurin ta in ma nashi ne.
Tace nima shi nake ta tunane nasan tayi hakane don farin cikin maji don kada
hankalin ta ya kara tashi kuma ?
Tace nima abinda na fhinta ke nan hakan take boyewa don kada aji hankalin shi ya
tashi amma ba matsala gobe da safe zanzo na kaiku makaranta anan zan fito mata da
zancen muji.
Yadda suka tsara haka din ne kuwa da safe sai ga Bashar mun gani a jenction din
gidan mu yana jiran mu.
Muna shiga muka gaida shi yafara hanya sai dai tuki yake a hankali, sai naji yace
malama Binta ya garin dai nace lafiya kalau yaya Bashar.
Ya ce ranan sai mutumina ke fada mai ta,asan da kikai mashi da kayan shi ?
Da sauri na dago kai na kalli maryam sai na dukar da kaina nai shiru bance mashi
uffan ba.
Yace Binta yaya akayi kika kwaso abubuwanan a gurin shi shiru nayi babu amsa.
Yace look Binta ba boyo ki fada min komai nai maki alkawarin bazan fada mashi
komai ba akai don hanyan da zamu ceto rayuwan shi nake son mu bida a cikin sauki.
Nace shi may ya fada maka don nasan na daukan mashi alkawari bazan fadawa kowa
ba wanan magana.
Sai Bashar ya nisa tare da buvun sitiyarin motar shi yace ina ganin baki fahince
mu bane kawai.
Nace yaya Bashar kadai gane cewa nashine ne ko to abar maganan don Allah, kyau
alkawari cikawa.
To shike nan na fahince ki yanzu, amma don Allah yadda Allah ya hore maki gane
irin halin rayuwan da yake shiga ina son muyi amfani da wanan daman naki guri gano
abinda ke saka shi a irin wanan halaiyar.
Sai yai kaman ya bari sai kuma ya koma ciki tsunbul dashi al,amari gaskiya akwai
daure kai a cikin sa sosai.
Nace nima na fahinci haka amma gaskiya ban tsan mani zan iya ci gaba da wanan
aikin ba saboda yai min warning sosai akan mashi shishigi ga al,amarin shi.
Zaki ya mana inji Bashar abinda nake so dake shine kamae yadda baki tsoron fada
mashi gaskiya haka zaki daure ki ci gaba da fada mai a kai tsaye.
Murmushi nayi nace anya yaya zan iya hakan kuwa yace kwarai kuwa Binta ai zaki
fitar da tsoro ne ga komai ki kama aikin ki,amma fa kuma kin san aikin nason jan
mutum a jiki sosai.
Nace da sauri yaya zanhi in ja yaya sadauki a jiki mutumin da kullun yake cikin
hattarana da tsangwama.
Yai murmushi kafin yace wanan kuma,wani haline nashi nan dai ya fara fada min ga
yadda zanyi akai nace to ba matsala zan gwada nagani amma idan naga da,wahala
gaskiya bazan yi ba.
Yace zakima iya tunda kina da hakkuri kawai ki dan sake dashi shine farko.
Muna kaiwa school ya sauke mu tare da min fatan alheri nace Allah yasa muyi
nasara dai.

****** ********* ******
Yana tsaye ya bada baya waya yakeyi kuma a handfree yasaka wayan nashi a lokacin.
Magana yake da wata mace sai dai magan tankar fada sukeyi yake cewa na fada maki
ni mace bata a gaba na yanzu.
Don haka ki daina yaudaran kaki don baxan aure ki ba koma zanyi aure yanzu akwai
qualities din abubuwan da nake so ga matar da zan aura ke kuma baki da ko daya daga
cikin su so kima daina yaudaran kanki a kaina.
Ban san may yarinyar tace ba sai ji nayi tace wanan kuma matsalar kine ni da kika
gannin ban taba zina ba a rayuwa ta kuma akanko ba zan fara ba.
Da sauri na juya don nashige ciki sai nai karo da dutse ina batun faduwa naji ya
riko ni bai bar wayan ba kuma bai sake ni ba.
Nace a kakausan murya sake min hannuna kaji malam, wani kallo ta watso min na ki
shiga taitayinki kinji ko.
Sai da ya gama wayan ya juyo gare ni yace ashe kuma banda sa ido harkin fara lebe
ne kuma ?
Cikin tsiwa nace, akan may zanyi labe Allah ha rabani da annaminan ci ni fita
zanyi nagan ka kuma zan koma.
Murmushi yayi yace idan ma baki taba ba ai yau gashi kinyi ko?
Amma anyway zan baki bashin na yau don kin min alkawari a baya don haka nima ya
kamata nai maki uzurin na yau.
Nace aini ba don ka nayi ba don mama nayi amma ba saboda kai ba sake min hannuna
na wuce.
Yai dan murmushi kadan abinda bai saba yi min ba yace ba abinda yakamata kice ke
nan ba Fatima kice dai kin boyeni don baki son ace ni din mashayi ne ko ?
Amma ko banza dai ni koma maye aikin min alheri ko Fatima don haka nima zanso ace
nadan yi maki ko na rana guda nane kamae yadda kikai min din.
Cikin wani shu,umin murmushi yace min tafi sai kin jini nan gaba, nima,
Na dan kalli hannuna da yai ja saboda riko da yasha a hannun shi nace mugu kawai
ashe yajini yace may kikace da gudu na zura zuwa cikin gida kada ya kamani sai
ganin mama nayi a gaba na tsaye.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU

IDAN BA KI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,,,,


YA ALLAH DUK WACE TA TURA MIN NOVEL GA WANDA BAI BIYA BA ALLAH KA ISAR MIN AKAN MAI
SHI,,,,


Suna zaune sai hayaniya suke a tsakanin maryam da Amira suna hiran wai sun kalli
wani film din biri jiya da,dare shine suke hira a tsakanin su.
Ina zaune a kan kujera na jingine jikina saman makarin kujeran nai shiru ina
sauraren hiran su.
Sai dai anihi na sha jinin jikina sosai daga irin kallon tsana da yaya sadauki
yake min daga gefen da yake zaune.
Na fahinci wayan da nayi ne yanzu ya jawo min wanan tsanar haka to amma ai saboda
shine ,aka gaisa dani din.
Hannun shi saman goshin shi ya dan dafe kai yakai bayan shi a makarin kujera yai
kwanciyar balance saman kujera ta hanyar mike kafafuwan shi.
Ganin haka nima na murde nawa fuska babu wallawala acikin sa ko kadan.
Ganin yaki ya bar falon yasani mikewa ina tafiya cikin dan dan gyasawa na nufi
kofan shiga daga ciki.
Yabi bayana da kallo a hankali yana duban yadda nake taka kafana still a cikin
wahala.
Yace ke zo nan kawo kafan nan nan na kara ganin yadda yayi sai a shafa magani .
Kamar na wuce don yadda yake magana cikin nuna isa, da gadara kamar dan wani
sarki shi mutum ne muskilin karshe kilama shiya sa yake cin kwallo don in ya kama
sai ya kai gola kamar abin tsafi sai yaci kwallo.
Shigowan Maji falon ne, shi ya katse min zancen zucin da nakayi tsaye .
Sai maryam ke fadi lah Bintu ba dai wai tsoro kike ji ba haka tun dazun yaya yace
ki kai kafan ya duba ya gani, ko sai an koma asibitin ne ?
Nace cikin daurewa ni kafata normal take don banjin komai yanzu,
Yadda nai magnan tare da dan murguda baki kadan yasashi cewa cikin takaici wanan
yariyar typical yar kauye ce wallahi.
Shigowan mama

46 / 92