Author : Zainab Idris Makawa Seenabu Category : Complete Novels
da ita muna hira sai dare sanan yazo ya dauke
ta.
Mama ma takanzo sosai kuma abinci dare da rana yana saman hanya ana kawo muna duk
abinda muke so.
Ba laifi don yanzu da cikina yake wata shidda da yan kai saura kiris ya cika wata
bakwai ina dan iya cin abinci kadan.
Sai dai ba mai yawa ba don idan har naci mai yawa ranan sai na fadawa aya zaki
gurin wahala.
Haka dai nake zaune Iyya tayi min halarci matuka a rayuwan na don komai itace ke
min shi iyakana naiwa kaina wanka kawai.
Bayan shi duk wani abin bukata na itace mai aiwatar dashi da kan ta zatai min
komai.
Yan uwa sai faman zarraiya suke zuwa gurina duba ni zuwan Baba na biyu yana duba
lafiya na a,asibitin.
Haka ma a bangaren mamana saida sukayi mota daya ita da abokan arzikin ta da yan
uwa sukazo duba ni.
Don haka ban da wani damuwa a tare dani sai na kadaicin mijina a kusa dani kawai
zance yana damuna.
Acan ma Germany ya wuce gurin buga wani wasa da akayi mai zafi inda kuma team din
su na basilona da yai ma,wasa yai nasaran lashe wasan da suka buga.
Ba karamin kudi ya kwaso ba sai dai bai dawo gida ba ya koma gurin su baba
asibiti.
Baba yanzu ya dan samu lafiya don likita yace zasu iya dawowa dashi nan da sati
biyu masu zuwa idan an tantance lafiyan jikin nashi da kyau.
Sai kuma ga,wasa ya taso mai zai tafi arabian kingdom ya bufa,wasa wanda ake
tsanmanin zasu samu makuddan kudi idan har sunyi nasara ga wasan da zasu buga.
Jirgi ya samu ya kammala komai akan tafiyan su Mummy da baba sai yaya sagir da
zasu dawo gida.
Ya basu kudi kowa ya sawo tsaraban da zai zo gida dashi inda,zasu dawo tare suka
fita dashi ya kaisu sukai sayayya inda yaya sagir ya kwaso laptop da kudin shi
zaizo dasu ya,sayar itako mummy kayan yaranta da,wasu abubuwan anfanin ta ne ta
sayo acan kasan.
Ranan da zasu dawo kowa yana cikin farinciki da dawowan su gida anshirya ma
dawiwan baba din sosai yanzu.
Muna asibiti labarin dawowan shi ya riske mu sai dai ance bari dayan baba bai
aiki gaba na ne ta yanke yafadi ras.
Amma Rukaiyya tace min sai dai gaskiya idan kin ganshi ya samu lafiya sosai
wallahi.
Tun bayan fitanta nake jin marana yana dan yanka min kamar zanyi period nake ji.
Sai ban damu ba don nasan tunda ina da lalura mai zai tayarwa kaina da hankali
dashi.
Wasa wasa ban daina ji ba har cikin dare sai barci ya gagare ni ina kallon iyya
da ta samu barci tana barcin ta hankalinta a kwance abinta.
Jin mara din ya matsa min ne na mike zaune aiko zama yace bai sanni ba can da
naji wani iein ciwo na sauko na kama karfe gadon na dan nisa tare da murde bakina
don dan zafin danaji a lokacin.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,,,
IDAN KIN BIYA KIKA TURAWA WANDA BAI BIYA BA MUN BARKI GA ALLAH YA SAKA MUNA,,,
Kukan dan jarin da ya fado ne ya saka Iyya dake kwance dan bude idon ta a hankali.
A lokacin da nake fadin Iyya Iyya tashi ki gani abin cikin cikina ya fito Iyyah
ko na haihu ne ?
Tamike tana fadin subbahanallahi ikon Allah uwar dakina kin sauka ne ?
Sai kuka yaron dan karami dashi sosai yake tsalawa duk Iyya tabi ta rude taje
inda ake kunna wutan dakin ta kunna tana cewa.
Kinko haihu wallahi uwar dakina amma sai dai killa bakwaini ne kika haifa don
yaron yai kankanta da yawa.
Ta dan taba yaron yakara tsala ihu tace namiji ne sai dai bakwaini ne da sauri
tafita daga dakin zuwa inda nurses suke kwana ta kira su.
Sai gasu da saurin su sun shigo tare da ita taimakon gagawa suka fara ba yaron
nan suka rabashi da uwar tafiya Allah yasa akwai reza da na anty Raiha ta sayo min
sai ta sayo parked din shi gaba daya.
Dayar nurse din taje dakin doctors takira likita mace wacce tai adimin dina
a,asibitin ranan ita ce akan duty.
Tana zuwa ta danyi dube duben da zatayi ta tambaye ni banjin komai na fada mata
komai bana ji.
A cikin daren akaiwa yaron wanka nima nai wanka Iyya tace a kira gida ne a fada
masu nace tabari harda safe sai a kira gida don yanzu kowa yayi barci hankalin su
zai tashi tunda ina lafiya.
Sosai likitan taita gwada yaron tace min lafiya yake sai dai premature baby ne
idan da rabo zai rayu insha Allahu.
Nace daga inda nake zaune a bakin gado anty zai rayu kuwa ?
Tace insha Allahu zai rayu ai seven months ne yanzu kike da kwana biyu.
Sai dai da,safe zan so muyi shawara muji idan zai yuyu sai a dan saka shi a
kwaba yadan kara tasawa tukun.
Bamuyi barci ba sai da,asuba muka dan runtsa kadan shigowan nurse din dakin
ya,samu falkawa Iyya ta tafi sallah ni kuma ina kwance ina kallon yadda sukewa baby
din.
Bakwai da yan mintina Iyya tashigo dakin nace ta bani wayana , numban mama na
fara kira har ya kusa tsunkewa ta daga da,sauri ba ko gaisuwa hankalinta ya daga
don ta ga ban kiran ta da farar safiya irin haka.
Tace Fatima lafiya dai ko ?
Nace a hankali mama na haihu ne.
Cikin wani murya tace kinyi may fatima nace na haihu ne mama.
Sai naji ta kashe wayan maryam na nema tana barci wayana ya tayar da ita na fada
mata na haihu sai Nafisa.
Koda na kira nafisa ina jin muryan mutanen gida a na yaya nasan zancen ne mama ta
fada masu a lokacin.
Kafin wani lokaci naji kiran sadauki ya shigo yace batare da gaisuwa ba Fatima is
that true o you are joking yanzu bashar ya kirani.
Kafin na bashi amsa yaron da nurse din ta daga ya dan yi kuka na kara mashi a
waya yaji.
Yace it means yaron yana da rai har yanzu ke nan nace mai eh kawai sai aka turo
kofa su mama ne da mummy da mama Asiya suka shigo dakin a rude.
Idon su akan nurse din dake shirya yaron za,a kaishi pediatric asaka a kwalba.
Gurin nurse din suka nufa suna kallon yaron dan karami dashi a cikin zani na da
aka nade shi.
Muna kallo suka fita da yaron mummy da,su sagir suka bi bayan su harda mama
Asiya.
Sai lokacin mama ta karaso inda nake zaune a bakin gado take cewa Fatima lafiya
dai kike ko ?
Na kakaro murmushi don hankalina a tashe yake nake cewa lafiya kalau nake mama.
Tace to ki kwantar da hankalin ki idan yaron Allah yayi shi rayayye insha Allahu
zai rayu.
Nakoma a hankali saman gado na kwanta na lumshe idanuwa na shigowan su maryam ne
yasa na bude idanuwana a lokacin.
Maryam tana fadin tare da,waige waige ina yaron yake maji ?
Tace sun tafi dashi nan tafada masu komai basu tsaya ko a gaisa ba suma suka bi
bayan su da sauri.
An saka shi a cikin wani dan karamin gado mai naurori tare da saka mai wani dan
rigan sayi a ciki.
Kafin likita ya shigo dakin sun fada min zan tashi daga wanan dakin da muke na
gany room zuwa maternity room.
Sai da,aka gyara komai suka mayar damu dakin lokacin yan uwa da,abokan arziki sun
cika a dakin ko.
Sai hira ake yayin da niko zuciya na duk a cunkushe yake min ban majin farin ciki
ko kadan ni.
Duk da kowa yazo fadin yake ai anyi arziki wata bakwaine insha Allahu zai iya
rayuwa da yardan Allah.
Barci ne ya dauke ni a lokacin mai nauyi sai mama Asiya ne naji tana tayar dani
wai na tashi na sha tea da aka hada min.
Na mike zaune ta miko min tea din yana wani irin tururi tace na kafa kai nasha
shi hakanan.
Har na daure na kafa kai zafi ya konani nai saurin cire bakina daga cup din ga
tea din gudan mai yawa dashi.
Lokaci daya suke ce min a,a a Fatima anya kuwa kafa kaifa zakiyi ki shanye shi
duka yanzu.
Nace a dan marairaice mama duka fa wallahi akwai zafi mummy tace kin manta cikin
ki akwai miki a cikin shi maza shanye shi don Allah kinji.
Haka na shanye tea din ina zufa take naji bakina ya dauki zafin kuna sai dai tea
din yana shiga cikina naji wani irin dadi a jikina da nake jina yau kamar banawa
ba.
Ban dade ba na koma barci mama Asiya da mummy sukace a dan rage a dakin don na
samu barci.
Barci nayi sosai sai zuwa sha biyu da rabi na rana wata nurse tashigo dakin wai
na tashi naje naba yaron nono.
Tare muka tafi da maryam da Nafisa da mummy a ka dauko shi na zauna na fara bashi
nono sai dai bai iya kamawa.
Mummy ce ta gyara shi da dan kyau ya dan tsosa kadan ya koma barci don ba komai a
nonon ma lokacin.
Likita ya shigo yana cewa sannu madam ashe haka abin yazo muna kuma dai.
Allah ya raya muna,shi ga baban shi yace yau yana da ball da mungashi yazo.
Haka muka wuni yan uwa da abokan arziki sai zuwa suke gaishe ni allura akai min
sai magani da,suke bani kawai.
Bayan shi ni banda wani matsala a tare danj gaskiya mama ta bugawa iyayyena waya
ta sheda masu yadda haihuwan yazo min haka.
Sai dare aka rage a gurin mu inda aka barmu da Iyya sai mama Asiya da tace itama
zata tsaya wai.
Nafisa bata bar gurin mu ba sai zuwa sha dayan dare wani yazo ya dauke ta tafi.
****** ********* ******
Bayan kwana biyu da haihuwa ne likita yace zasu iya sallamana na koma gida sai
dai zasu bani time da zan dinga shigowa ina bawa yaron nono.
Karfe biyar na safe , tara na safe sha biyun rana karfe biyu na rana zuwa hudu
sai shidda na yamma kuma zuwa takwas na dare idan da hali sai na dawo da,sha biyun
dare ko sha daya da rabi.
Yaya bashar yace insha Allahu za,a kiyayye zan dinga zuwa ina bashi nono din.
Haka na dawo gidan don da aka bugawa sadauki waya cewa yayi na koma gidan shi
kawai tunda ance lafiya na kalau.
Gwagona ta zauna dani tare da Iyya a gidan tana min wankan jego gadai jego ina yi
haikan amma babu baby a gida.
Sai time yayi yaya bashar zaizo ya dauke ni ya kaini asibiti aba yaron dake
karkashin kulawan likitoci nono ya sha.
Satin mu daya Alhamdullahi yaron yana ta kara murmurewa sosai don yana samun
kulawa gashi ba,a barin kowa ya dauke shi sai ni idan zan bashi nono ko ganin shi
ba,a bari yan uwa suyi yana ciki a rufe.
Kwanan mu goma da haihuwa yaya sadauki yashigo Nigeria da,tarin arzkin da yasamo
a rayuwan shi sosai.
Don andage suna sai yaron yayi kwari sosai zaa saka lokacin yin suna bisa
shawaran da likita ya bayar ayi.
Koda ya,shigo sokoto ya samu ina shiri ina jiran zuwan yaya,bashar don time din
zuwan mu ba yaron nono yayi lokacin.
Ina saye cikin atamfa zani da riga don nafi jin dadin ba yaro nono hakanan.
Yana rataye da corth din shi a kafadan shi daganin shi a gajiye yake a lokacin.
Direct dakina ya nufo da ya,shigo ina zaune a bakin gado nayi kyau dani don jego
ya karbi jikina sosai a lokacin..
Jin shigowan shi dakin ne yasani daga idona na kalle shi shima dai ido ne
ya,tsura min a lokacin yana takowa zuwa inda nake zaune.
Sai da ya karaso inda nake nake ce mai sannu da zuwa yaya.
Yace aikece da,sannu Fatima ya kai zaune gap dani yana cewa yaya kike nace
lafiya kalau yayana.
Yace yaya baby din yake kuma yanzu nace lafiya yake yanzun ma can zamu tafi bashi
nono yaya nake jira yazo.
Yace to na tashi mu tafi tare dashi nace bazaka huta ba tukun yace ina zan huta
banga baby na ba Fatima.
Tare muka tafi dashi da yaya bashar daya ja motan ranan an barsu sun shiga don
shi.
Shiya fara daukan yaron da muka samu idon shi biyu a lokacin sai watsalniya yake
da kafafuwan shi.
Ya dade da yaron dauke a hannun shi yana mashi addua ga sauran yara a gurin
kwance suna barci zasu kai su biyar a lokacin.
Mun ba yaron lokaci sosai muna tare dashi muna kallon shi muka aje shi ba don mun
so ba muka fito daga dakin.
Haka na dinga zuwa yaya ya na kaini har akai wata daya yaron ya dan yi wayau
sosai a lokacin.
An saka mai sunan Baba watau Abubakar an yanka rago da shanu anyi sadaka da naman
wa mabukata.
Likita ya bada shawara da yaron ya kai wata takwas akan zamu iya tafiya dashi
gida a lokacin.
Ranan da muka dawo gida da yaron naga dan mutum sosai a gidan masu zuwa min barka
aka saka suna sati mai kewayowa za,ai taron suna irin na al,ada hausawa musulmai.
Sai faman shirin suna akeyi Jamilan yaya Ahmed da ita ake komai a taron wanda
mama ce ta saka ta yin haka dole.
Don su taushi zuciyar sadauki akan maganan gida dake aje a kasa ba,a tayar ba
tukun don wanan al,amarin sunan dake gaban shi.
Ranan suna gidan ya cika makil da jamaa masu zuwa taron suna wanda na sani da
ma,wanda ban sani ba yazo gurin taron sunan.
Anyi walima sosai tare da ciye ciye da lashe lashe yan uwana sun zo da yawa sosai
gurin sunan.
Yan uwan mama ma sun zo da yawan su daga Niger state dasu akai sha,anin bukin
sunan yaron wanda muke kira da Amir.
Yai wayo sosai amma gwago bata bari ana daukan shi kamar yadda mukeyi ranan suna
duk wace tazo sai ta dauki yaron ta ganshi.
Likita ya hana haka yasa itama gwago ta hana a dauke shi yana gurinta a wani
dakin da suke kwance a saman gado.
Duk wace tace ina yaro sai dai ace mata yana lafiya yana can gun kakan shi anyi
rabon kayan buki masu armashi da tsada aka saka acikin ko wani jakkan da za,a ba
mutum.
Zuwa yamma Nafisa suka shigo gidan da mutanen ta nan kallo ya koma kan su kuma
sai gulma ke tashi a kan su.
Kuryan daki suka kutso anan muka zauna dasu wanda hakan yai masu dadi sosai don
ni bani nuna masu kyama ko kadan.
Don nasan Allah ne ya jarabce su da yin hakan kuma muna rokon Allah ya yaye masu
hakan a rayuwan su.
Basu dade da shigowa ba sai ga tawagan Rahama da kayen ta sun kai su goma suma
dai sai a hankali wallahi.
Su ko suna ganin burgewa ne hakan suna jaye da troler har kuryan dakina inda nake
suka kutso kai.
Sai dai suna shigowa ganin tawagar Nafisa tab a dakin yasa jikin su yai sanyi
akan wulkancin da suka kullo suzo suyi a gidan.
Don sun san gaba da gaban ta wa yan nan yan daban da suka gani sun cuna masu gurin
iskanci sau milayan albarka .
Don su basu tsoron ta kwana balle ta bare masu ko kadan sun saba da casa juna a
daba ko.
Daya daga cikin su tace ga kayan yaron Rahama nan takawo mai aita saka mai har
kala ashirin ba dai.
Daga cikin yan daban Nafisa daya ta cabe da cewa kai amma kuma ta makara don
tasamu har uwar yaro da uban yaro sun saya mai kaya na kasan waje masu tsada ba yar
sokoto central ba.
Sai ta koma da abinta ko ta samu cikin dangi a basu su suka don shi wanan yaro ko
ta sunan shi mai tsadane balle suturan shi.
Ke kuma a suwa gayyan na anya waya gaiyato ki nan yar daba mai arna dubu.
Tace yanzu dani dake aga wanda aka gaiyato wanda ke tsaye ko wanda ke zaune kafin
ai haka ashe Nafisa ta mike sai ji mukayi kawai ta kwashe Rahama dake gefe tsaye da
mari kayau.
Abin nema ya samu kafin haka su Raiha da Nuriya har sun mike tare da sauran su
sai ko daki ya rude da danbe in bakaci bani guri na sudade na bar dakin ina haki
nagudu dakin dasu gwago suke zaune.
Take gida ya cika harda maza sunyiwa su Rahama kaca kaca da suturun su duk
anyayaga masu shi.
Sadauki yana site din shi mummy takirashi a waya sai gasu gidan yazo a hasale
tsawa daya yai masu kowa yaja ya tsaya.
Yace maynene haka wai please may kuke min haka a gidana ne wai wata mata tace
muna aha,anin mu na lafiya wai ko yan kungiyar Rahama sukazo muna da fitana duka da
zagi da habaici wai gida nasu ne sunzo ne kuma ba,wanda ya usa ya kore su a gidan.
Idon shi ya runtse yana maijin takaici yace ma Sagir dake bayan shi ya kira mai
mobil police yace kuma a rufe gida ba inda zasu.
Take tan sanda suka shigo aka kwashe su sai police station aka rufe su kan
tuhumar sunkai mai fada a gidan shi sun tayarwa mutane da hankali.
Baba Sani ranan kamar zaiyi hauka gashi ya kira wayan sadauki yafi a kirga amma
wayan a kashe take wayoyin shi duk ya kashe su.
Yaje police station ance baza,a bada bellin su ba sai sadauki yazo da kan shi.
Har dare ba wanda yasan inda yake ashe yana can sabon gidan shi da yake ginawa
gaba kadan da inda muke duk dai a unguwa daya ne da inda muke yanzu.