Advertisements
Chapter 16 Reading A Lokacin Mu Ke by Zainab Idris Makawa Seenabu BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

A Lokacin Mu Ke by Zainab Idris Makawa Seenabu

Author :  Zainab Idris Makawa Seenabu Category :  Complete Novels

Chapter   16 / 92

45K to 48K   out of 275.8K words

har mai gidan yai mata warning din shiga harkokin mutananen gidan shi da
kan, shi.
Sai lokacin take mai jin zafin gwagonta hajiyan masa da tazo gidan mutane ta yar
da ita kamar wata wacce bata da uba ko gata.
Da uwarta da uban da ransu a duniya amma yau ta zama,marainiyar karfi da yaji a
duniya.
Ba don Maji mace ce mai halin alheri ba da bata san iya inda al,amarinta zai
tsaya,ba a,rayuwa.
Amma gashi Allah ya hada ta da mace tagari wace tasan ciwon kanta tasan zafin ta
a rayuwa.
Ta rike ta amana tankar itace ta haife ta ko kuma ince wata yar uwarta ta jini
can daban.
Yanzu Bintu ko falon maji bata son zama da yawa ko yause tana cikin dakin su a
kumshe.
Idan kuma aiki tafito yi zata yishi gudu gudu ta gaba ta kara komawa tashige daki
wai ita tana taka tsatsan da kanta.
A haka zancen tafiyan sadauki zuwa kwallon farko da zai fara fita ya buga yazo
masu.
Maji bata zauna ba sai faman karban taimako take akan dan nata akan shaye shaye
da kuma na tsarin jikin shi.
A cikin hakane maji tace wa yaranta su shirya sukaiwa kakan in su ziyara kafin
yatafi don kada sai yatafi su samu labari baza suji dadi ba.
Sadauki bai so wanan tafiyan ba amma ba yadda zaiyi ya zama dole yabi umurnin
iyayen shi.
Sai faman shiri suke amma Maji bataji duriyar Bintu ba don ko falo bata fito ba
don ba,a shiga makaranta ranan.
Da kanta tashiga dakin na yaran tun zuwan Bintu gidan ko yaushe zaka samu dakin
tsab dashi ba wani datti a cikin shi kaman baya can da dakin yake motsutsu kowa na
kyashin gyarawa .
Kwance ta samay ta ta kifa kanta a saman filon da ta ke akai.
A hankali maji takira sunan ta,da Fatima abinda ya dan sata firgita ke nan don
bata san da shigowan Maji dakin ba a lokacin.
Cikin dan firgita ta amsa da na,am mama tare da saurin kokarin mikewa zaune daga
kwanciyan da take.
Zama maji tayi daga gefen ta tare da dan kura mata ido tana cewa waiko lafiyan ki
kalau kuwa Fatima?
May ke damuwanki ne duk kwanakin nan kin koma,shiru kina kuma nisanta kanki da
kowan mu?
Dan murmushi Bintu ta kirkiro a fuskanta tana cewa ba komai mama kaina ne ke dan
ciwo shine nadan kwanta.
Tun yaushe kanki ke maki ciwo baki fada min ba fatima baki sha magani ba yaya
zaki ji sauki.
Shiru Bintu tayi tana fadin dama gashi zamuyi tafiya zuwa garin mu gobe tunda
safe gashi kuma baki da lafiya.
Don haka dole na barki nan har mu dawo don ba,a daukan ciwo akai kauye.
Da sauri Bintu ta daga kai ta kalli Maji, sai kuma ta dukar da kanta don bata iya
jure kallonta ido da ido haka.
Maji da ta fahinci may Bintu take nufi sai tace kada ki damu ba,a nan zanbarki ba
gurin hajiya kubura zan barki don kwana biyu zamuyi mu dawo insha Allahu.ko kuma
guda yadda dai tafiyan namu ya kasance don wanan mai tafiyan.
Bintu ta kara kallon Maji alaman ranta baizo hakan ba take cewa mama da abarni
ko anan din zan iya zama ai.
A,a haba Fatima yaya zanbarki karaman yarinya dake a daki ke kadai kuma gashi ko
lafiya,bai isheki ba ma.
Kada ki dmu nasan zata rike ki da kyau har mu dawo daga tafiyan, kamar Bintu tace
taji sauki zata tafi amma kuma sai take cewa tau mama.
Maji tamike tana cewa don haka saiki shirya kayanki wanda zaki dauka tun yau ki
koma can.
Bintu tanaji tana gani Maji da kanta ta dauki dan jakar kayan ta zuwa dakin
hajiya kubura.
Nan suka dan zauna suka taba hira a tsakanin inda tai mata sallama dacewa gobe
asubanci zasuyi zuwa tafiyan su.
Hakan akayi don koda gari ya waye har sun tafi ko don can ne kauyen Niger state
iyayyen ta suka koma da zama don noma.
Bintu bata farka,ba don maganin da tasha mai sa barci sai zuwa takwas na safe
lokacin har hajiya kubura ta shirya zuwa gurin aiki tana cikin uniform din ta.
Dakin da Bintu take ta leka tasamay ta zaune tana lazumi ta idar da sallah a
lokacin.
Kin tashi Binta ya jikin naki Bintu ta amsa a sanyaye da Alhamdullahi ga
breakfast din ki a falo idan kinyi wanka sai kici ni zan fita sai na,dawo.
Sai kindawo mummy ta bata amsa tare da kokarin mikewa da ga saman abin sallah da
take zaune akai.
Zuwa rana kadan ta dan samu sauki nan ta mike tafara gyaran part din sai da taima
ko ina tsab a part din sai bedroom din mummy ne kawai da ke a kulle bata gyara ba.
Tana gamawa tashiga tai wanka bayan tafito ne ta dan zauna sai kuma tai tunanen
kada su dawo da yaran ta basu samu abinci ba.
Kitchen din ta shiga inda ta samay shi sabanin na Maji don wanan komai na zamani
ne a cikin sa.
Ga kayan abinci na kala kala babu abinda babu cikin sa komai gashi kamar ba saye
akeyi ba.
Ta yanke shawaran tai masu tuwo don taga kullun yaran ta na zuwo rokon tuwo a
gurin maji don ita bata da time din tukawa ko yaushe busy take.
Nan ba bata lokaci ta girka tiemwon shinkafa da miyan agushi da manja tai amfani
da naman da tagani a fridge din.
Gashi ranan girkintane ta kwashe a wani kula da bai saurin sanyi takara hada masu
pepper surp din kayan cikin rago da drinks din hannu na kayan fruit din data gani a
kitchen din.
Takara gyara gurin ya koma tsab takoma daki ta kwanta sai yamma mummy tadawo da
yaran ta inda tun a,wajen part din ta soma ganin canjin yanayin shiyan nata.
Tana shiga dakin gaba daya taga duk ya canza mata sai ta tuna da lokacin da
take amarya a gidan komai nata tsab yake a lokacin.
Ba irin yanzu ba da,bata da lokacin tsayawa gyara komai kamar yadda ya dace mace
tana gida tayi.
Yaran suna shiga daki suka fara ihun da murnan ganin yadda komai nasu ya canza a
lokaci guda.
Dan karamin sune yafara maganan abinci Bintu dake fitowa daga dakin da take ciki
take cewa Anwar zo ga abinci can kazo kaci taja hannin yaron inda ta tsaya daga
kofa tanawa mummy sannu da dawowa.
Mummy tace Bintu ke da baki da lafiya kika sha wanan aiki haka sannu da fama
nagode.
Tana fitowa taga Anwar a hannun ta take cewa kaikuma may yafaru Bintu tace wai
abinci zaici.
Uwar tace kaida andawo kace zakaci abinci har yaushe muka dawo na girka maku
abinci.
Bintu tace a sanyaye mummy ai na yi girki tun dazun ma nagama bari na debo mai.
Da mamaki uwar tace kinyi girki Bintu bayan wanan uban aikin da kikasha haka.
Murmushi Bintu tayi ta juya rike da hannun yaron ta debo mashi abinci ta zauna
tafara bashi.
Saiga Mummy tafito daga daki idon ta ya sauka akan plate din da yaron ke cin
abinci take taga mai Bintu ta girka masu.
Wani irin dafi ne ya kumay ta tace kai amma wanan yarinyar Allah yai maki albarka.
Nan tashiga kitchen ta samu komai tsab kamar ko ina mamakine ya kama yadda
karamar yarinya kamar Bintu tai irin aiki haka mai yawa ita kadai.
Gashi kuma,ba lafiya ne take dashi ba ajikin ta take taji kwadayin zama da
yarinyar ya kamata don irin haka take son yaron ta dashi.
Ba,wani abinda aka taba mata ko aka lalata hatta sharan da tayi bata zubar ba ta
tara a wani roba har mummy din tazo tagani idan babu abinda take so daga ciki dai a
zubar dashi.
Haka mummy ta dinga jin dadin zama da Bintu kamar kada uwar rikon ta tadawo take
ji.
Suko matan gidan ai nan gulma ya fara tashi akan zaman Bintu gurin Hajiya kubura
na kwana biyu kafin maji ta dawo don ance babban gida ba,a raina dan magana
kadan,,,,,,,



ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU

IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,,,,,

A LOKACIN MU KE,,,,


Washe gari da safe sadauki yana dakin Maji saman dogon kujera ya dan nade hannayen
shi a saman kirjin shi idanuwan shi duk suna a lumshe, zakace barcin safe yau yake
a falon mahaifiyar tashi.
Duk zirga, zirgan da sisters din shi keyi yana jin su sai dai idanuwan shi a,rufe
suke still zakace barci yakeyi.
Maji ta,shigo dakin daga part din maigidan take, tana ganin Sadauki a falo tun
da farar safiya haka sai taja tai turus tana kallon shi cikin mamaki.
Ba tare da ya sauke hannun shi dake saman fuskan shi ba, ya ke cewa Maji barka da
asuba, jin haka,ya,sata sauke ajiyan zuciya takarasa gare shi cikin yanayin mamaki.
Yau kuma a,nan kazo ka,kwanta muna da,safe haka ko har yanzun kana kewar namu ne.
Murmushi kawai yayi wanda har yakai ga sauke hannun shi da ya kare fuskan shi
dashi da,farko.
Maji bana son Baba ya fita bamu gaisa da,shi ba shiyasa na zo nan nake jiran
ya,shirya sai na shiga gurin shi mu gaisa.
Maji ta,karaso cikin dakin tana fadin a to tin dai jiya naji ya fara tambayan ka
idan ka wuce yanzu za,a jiku dashi,
Yace cikin kara kwantar da kan shi bama za,a jimu ba insha Allahu maji,
Maryam ce ta katse su da fadin Maji tun dazun nake jira kizo sauran madaran da
ya,rage shine Bintu ta dauka wai tana hadawa yaya tea dashi .
Kai maryam baki da hakkuri wallahi jiyane fa kayan tean namu ya kare shine har
kin fara raki haka.
Sai a lokacin ya daga idanuwan shi da,sukai ja yake cewa No ni kubar shi bazan
sha tea ba,sauran tuwo nake son ci ni.
Yana kokarin tura hannun shi cikin aljihun wandon shi ya ciro kudi masu yawa
yace wa marya karbi jeki sayo maku kayan tea ku karya kafin na,fita.
Tana mika hannu zata karba ne, Maji ke fadi kai haba Sadauki na fada maka ka
daina wanan kashin kudin haka.
A hankali ya mike zaune da kyau yana fadin no maji ai wanan ba komai bane ki
barta kawai ta sayo masu abinda zasu karya su fita.
Anjima idan na fita zan sayo masu abinda ya dace a saya din yanzun dai tafi ki
samo wanda zaku karya dashi
Cikin mamaki yarinyar take cewa ai nan har dubu uku naga ka miko min yace baza su
isheku bane ko yaya.
Gaba daya suka mayar da hankalin su gare shi cikin mamakin yace a kashe dubu uku
a lokaci guda kan breakfast kawai.
Ke miko min kudin nan nan ki je ki sayo maku komai na dari biyu ki kawo canji
wannan bai san ciwon kan shi ba.
Ta juya gare shi yayin da take karban kudin hannun maryam tana fadin.
Jiya kaje ka yi barnan kudi kunyi yadda ranku ke so yai kuma shine zaka wani ce
wai su sayo kayan tea da wanan kudin haka masu yawa.
Murmushi ya dan sauke yana cewa No maji ki bata kada ki damu don wanan kawai don
Allah basu su sayo abinda suke son saya.
Sauran sai su hau Napep da shi zuwa makaranta ya mike yana cewa Baba din yafito
falo ne Maji tace yana falo na barshi yana karyawa ne.
Shi kadai ne zaune a falin nashi yana karyawa da,sauran tuwon da aka gyara mashi,
na,daren jiya,
Bawai rashi yasa ahi cin abincin ba a,a ra,ayi dai ne kawai yafi son yaci dumamay
da safe wai yafi rike mai cikin shi.
Falon na,Baban nasu yana da,dan tsarin shi xon tsari irin na,falon maza masu dan
abin hannun su irin na da can baya.
Duk da zamani ya,sauya bai sa Baba canza tsarin falon nashi ba a hake yakw zama
da abinshi duk da,akwai halin canzawan amma,bai canza ba.
Sadauki ya, shigo falin da,sallaman shi ya samu guri ya zauna tare da,gayar da
baban nasu cikin ladabi da,biyayya.
Baba ya amsa tare da fadada murshin dake fuskan shi na jin dadin hango tarin
natsuwa daga dan shi sadauki.
Baba,yace cikin yar tsokana haba dan kwallo kai kuma sai kawai ka bace wa mutane
daga dawowanka jiya.
Ga shi tun jiya ina zaune ina jiran kazo nasha labarin yadda kwallon ta kaya maku
a can don bamu da wani labari ko kunyi nasara ga tafiyan naku.
Cikin dan murmushi Sadauki yake cewa Baba munyi nasara da yardan Allah mun samu
shiga nida abokaina da mukaje, wanda basu samu shiga ba kadan ne kuma ba musulmai
bane su.
A to Alhamdullahi masha Allahu abu yai kyau gaskiya sosai haka muke son ji dama
ai tafiyan nasara.
Sadauki ya dan lumshe udon shi don jin yadda mahaifin shi yake farin ciki yau
da,samun nasaran shi a fili.
Shigowan su mama,Asiya da Umma da suka ga shigan sadauki gurin mahaifin shi shine
suka shigo don suji kwam.
Haka yasa fuskan Baba ya canza a lokaci guda daga fara,ar da suke shi da dan shi.
Don yasan shigowan su a tare haka da biyune suka shigo don basu shiri sai gurin
sheri.
Ganin shigowan su fuskan mahaifin shi ya canza ya fahinci mahaifinshi bai ji
dadin hakan ba,
Don haka ba,tare da,sun tattauna komai ba kamar yaddaa sukaso yi ya mike yana
fadin Baba ni zan fita adawo lafiya.
Har yakai kofa sai Umma take cewa kai baka iya gaisuwa bane ko may ne koko zuwa
kwallon kara zama dan iska ya mayar da kaine wai?
Haba Maimuna a kulun kalamin ki akan yaron nan babu dadi wallahi yanzu may yai
maki kuma kike kokarin yi mai wanan zagin haka.
Tau fa ai na manta dan Baba dan masu gida na ke wa fada don Allah ayi hakkuri
kada a zageni nima don na,zageshi.
Hmmm Alhajin yace cikin murmshi tare da,girgiza kai yace bana son ki,da,wanan
halin wallahi
yaya ke nan yanzun fa kin san dan kwallo ne ba,a wasa da al,amarin shi kuma
Umma ta lailayo wani ashar tace kwallon kaza kazan uba masu kwallo suna abin
arziki ai an san inda suke ba masu zuwa tafe ba,a bayan fage.
Daga Alhaji har sadauki dake kofa yana daura igiyar takalman shi a kafan shi sai
da ya,dan murmusa kadan.
Don jin abinda Umma tace mashi, Alhaji yace cikin murmushi a naku irin hasashen
kuke ganin bai koyo komai ba, Amma aini Alhamdullahi don naga haske ga wanan
tafiyan na sadauki a gidan nan jiyafa tare mukai sallah magariba dashi a massalaci.
Mama,Asiya ta cabe da cewa mu dai yadda akaje haka aka dawo muna don haka bamu ga
wani abin yiwa mutane rawan kai ba a nan.
Mu dai in muga yaro ya kara lalacewa wallahi dole a,dauki mataki a gidan nan don
ba,zamu zauna da irin mahaukata ba kullun hankalin mu a,tashe cikin gida.
Maji dake bayan su ta shigo kwashe kayan abincin da takawo wa baba tana jun komai
a kunnen ta.
Har ta dauki kayan tabar dakin batace masu kalla ba sai ma dan magana akan kudi
cefanen abinci ranan da zata girkawa Alhaji takeyi.
Inda sai a haka take dan samu canji ya rage ta danyi wasu lalurar ta dashi.
Anan tabar su suna wa Alhaji magana akan zuwan sadauki kwallo gari ya gari har
ghana amma bai tsinano uwar kowa ba a can.
A kofa shima ya hadu da hjy kubura dake bayan Maji gurin shiga part din mai
gidan nasu.
Hjy Kubura tana ganin shi sai ta fadada murmushin a,fuskan ta da dan fara,a takw
cewa a,a mayan yan kwallon mu, ke nan ya gajiyan hanya yace Alhamdullahi mummy.
Ta shige tana mashi wasa shikuma ya juya zuwa dakin mahaifiyan shi wanda bai
dade da shiga ba ita ma tashigo dakin dauke da kaya a hannun ta.
Koda Sadauki ya shigo falon mahaifiyan shi zama yayi tare da hade kai da gwiwa
cikin damuwa.
Bintu ce ta kai hankalinta gare shi ta karaso gare shi tana fadin yaya akawo ma
abincin ne yanzu.
Akwai kuma koko da kosai mai zafi an dama yanzun nan wa Baba sai a hado ma dashi.
No ki barshi kawai ya bada,amsa tace tau ko a debo maka kunun kasha kawai don
tasan kamar mahaifin shi yake gurin son koko da kosai da safe.
Cikin nuna gajiya da tambayan ta yake bata amsa da fadin ke ban son komai please
ki barshi nace ko.
Maji dake daga bayan su take cewa haba ina laifin ta, don taga su kafi damuwa
dasu shine take maka tayi mana.
A hankali ya dago yana kallon inda Maji take yake cewa bana jin ci ne fa shiyasa
kawai.
Ya sadauki kaifa kace zakaci saura yanzu shine nace Bintu ta gyara maka Amira
take fadin haka.
Yaya halan anyi ma wani abu a falon Baba ke nan ko maryam ce take mai wanan
tambayan.
A sanyaye yace ba ai min komai ba maryam kawai dai gajiya ce ke damuna kawai.
Yaya kun gaji da yawa kwallo ai ko na,wasa ne akwai gajiya balle irin naku na
kuke na kuke sai anci.
Yayi murmushi yace ai dama shi kwallo ba hutu bane motsa jikine kawai cikin shi.
Bayan fitan yan matan daga gidan kowa ta tafi makaranta, matan gidan kuma sun
futa aiki, ko haka yasa maji samun daman kebewa da dan ta don ta kara mashi nasiha
akan irin rayuwan da yake dake jawo mata magana da gori.
Sosai tai mashi nasiha mai ratsa jiki akan duk wani al,amarin dake gudana a gidan
takw ce mashi bata taba sa al,amarin gorin arzikin dasu yaya suke yawan yi min shi
ba,agidan nan a raina.
Nabar wa Allah al,amarina don shi da ya halicce ni yasan dalilin da ya yi

16 / 92