Advertisements
Chapter 18 Reading A Lokacin Mu Ke by Zainab Idris Makawa Seenabu BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

A Lokacin Mu Ke by Zainab Idris Makawa Seenabu

Author :  Zainab Idris Makawa Seenabu Category :  Complete Novels

Chapter   18 / 92

51K to 54K   out of 275.8K words

Maji ta fadi a fili tareda mikewa don tabar dakin don tasan
idan takai wani lokaci a ciki yana iya zama masu matsala da maigirkin ranan watau
mama Asiya.
Ta koma dakin ta ta samu yaran ta kowa da waya a hannun shi suna dakala.
Sai Bintu ce da bata da waya ta ke zaune tana karatun littafin islamiyan ta da
take bita.
Shigowan ta yasa su dan dogo kai suna kallon ta don sun saba idan ta je gaida
Baban su tadawo suna kallon yanayin ta idan bada bacin rai ta,shigo ba don gudun
ace yayan su ya aikata wani abin asha kuma.
Sai dai sunga tsatson farin ciki a fuskan ta inda kafin su tambaya take ce masu
Amirah ance gobe insha Allahu yayan ku zai dawo garin nan yau sun sauka lagos gobe
zai karaso gida da yardan Allah.
Gaba dayan su dadin wannan labarin sukaji don sun san tun da har yakai warhaka
kuma ance sun dawo komai ya tafi normal insha Allahu .
Ba kamar yadda suke daridari ba da farko don gudin kada yaje yai shaye shayen shi
a koro masu shi.
Washe gari tun da safe suka fara dan gyaran wuri da kuma yi mashi abinci na
musan man dan taron shi.
Maryam ce da Bintu suka gyara mashi dakin shi tsab don komai sada suka fitar suka
share suka goge mai sabon zanin gado maji tabayar suka shimfida mashi.
Wanda karfin aikin ma duk Bintu ce tayi shi ita kadai maryam sai karatun ta take
a cikin wayan ta kawai.
Ganin suna aikin yasa yan sa idon fahintar kila mai dakin zai dawo ke nan.
Mama Asiya ce ta fara samun Umma da zancen cewa yau naga mutanen ki sai wani jin
dadi sukeyi harda gyaran wuri.
Nafisa tace da zan shigo dazun naga suna,gyara dakin yaya sadauki ai.
Muga atsiyar da ya tsinano masu a can ai sai rawan kafa suke wai yatafi ya dawo.
Wanan dan shaye shaye may kike zaton zai ita tsinano masu a can, ai yadda yaje
haka zai dawo tsula dashi dan ganye kawai.
Ranan sai kawai aka kafa dandali a tsakar gida don gulma katuwar tabarma suka
shimfida wa kan su nan aka baje ana ciye ciye ana hira wai.
Maryam ce tashigo gidan tana cewa yau kan gulma yakai gulma a gidan nan bakiga
har tabarma,aka baza ba manya da yaran su a tsakar gida don kawai aga may yaya zai
dawo dashi.
Ni dai Allah ya kawo min shi gida lafiya yasa wanan tafiyan ta zama mai silar
shiryuwan shi.
Suka amsa mata da Ameen maji.
Sun zage sai faman goge gogen falon su da babu komai sukeyi don dai ya haske
kawai.
Sun gama dan har wanka sunyi lokacin suna zaune falo suna dan hira jefi jefi
tsakanin su.
Suka jiyo muryan shi ya shigo gida da sallama a bakin shi, kamar muryan yaya
sadauki naji a,waje Amira take fadin haka.
Hamdala Maji tayi a fili tana fadin shine ba kama ba ai taji dadi don ko ba komai
ta tsinkayo canji ga yanayin shi sosai don gashi ya shigo gida har da sallama a
bakin shi yau.
,Nan sukayo waje don taron shi da saurin su hae suna karo da junan su.
Kamar yadda ya tafi
daga shi sai yar jakar shi wanan karon ma haka yadawo masu sai yar karaman jakar
daya goya a bayan shi.
Daga inda matan gidan suke zaune da yaran su suna shan rake suka tsura mai ido
kawai.
Shine yake ce masu sannun ku da gida mama daga haka bai karasa ba ya juya zuwa
part din mahaifiyar shi.
May na fada maki Asiya na fada maki tsula ya tafi tsula zai dawo muna rabu da dan
matsiyaciya kawai masu gadon tsiya ta ko ina.
Dariya suka sa dasu da yaran su a lokaci guda wanda sai da ran sadauki ya dan
sosu don yasan dariyar a kan shi ne.
Sai dai ya dake ya rugumi kannen shi da suka sheko suka rugumay shi suna mashi
sannu da zuwa.
Banda Bintu wace take tsaye daga gefe sai dai da murna a fuskan tana cewa,
Sannu da zuwa yaya cikin yar muryan ta ko bai jita bane yadai ja kannen shi suka
shige kawai abin su ciki.
Bayan su tabi suku suku da ita tana dan dariyar yake a fuskan ta.
Inda MMaji take zaune ya isa cikin farin cikin shi ya zauna kasa tare da sa kan
shi saman cinyarta yana cewa Maji yaya na samay ku?
Murmushi maji tayi tace anya Baba na kwallo kaje kuwa kaga yadda duk ka canza
min a lokaci guda.
Murmushi yayi yace kai haba dai maji kwallo ko naje wallahi ban ramay bane?
Sai tai dan murmushi wanda rabon haka a tsakanin su ya matan lokacin shi.
Maji ta,waiga inda Bintu take rakube tana cewa, Fatima kawo wa yayanki ruwa ko
yasha Amirah tace da abinci ko gaba daya.
Nan suka shiga kitchen din tare wanda Bintu ta fara dauko abin shan da suka
shirya mashi takawo mashi.
Ta duka ta aje zata juya yake cewa ke wata irin bakauya ce kinga mutum ya dawo
baki iya gaishe shi ne.
Amira dake aje tire din abinci take cewa aiko ta gaida kai yaya sai dai in bakaji
bane.
Maji tace kadawo ke nan ko hutawa bakayi ba zaka fara takura min yarinya ko.
Ya juya inda suka aje mai kayan abinci a gaban shi yana fadin kai kai kai Amira
duk ni kadai wanan abinci haka mai yawa.
Ga,wacce tayi su nan ai da yawa tana nuna mashi Bintu dake can gefe kujera a
zaune kasan ties a dakin.
Amira tace ta ba bako yake ba yau ai batai laifi ba ko don ance bakon ka annabin
ka.
Sosai yaji dadin wanan karamawan da kannen shi da mahaifiyar shi sukai mashi
haka wai duk shi sadauki keda wanan taron.
Shigowan hjy Kubura dakin shi ya katse hiran jin dadin ganin shi da suke yi a
lokacin
Tashigo da fara,a a fuskan ta tana cewa yanzu su Anwar ke fada min wai bakon
ghana ya dawo ina shigowa.
Murmushi yayi yana cewa mummy mun samay ku lafiya ko?
Lafiya kalau sadauki yaya hanya yaya can kuma I hope komai normal.dai ko ?
Inda dane Maji zatace tsakani da Allah tazo taron shi amma yanzu data rage ta,
sai take kallon makirci ne ya kawo ta kawai.
Nan ta kare kitihin ta ta fita daga dakin daga inda Bintu take zaune tabi da
kallon makira kawai ita da maji da suka san komai.
Maji bayan yaran sun kaure da hira tadan fito tsakar gida tun daga inda su mama
suke zaune aka jefo ta da hausa.
Tsula ke nan wai tafiyan sundundun madundun yadda aka tafi haka aka dawo zaban
kunya.
Dan nagada ai bai iya gado ba dama taya za,ace kagaji abu kuma ka ketare shi.
Maryam dake bayan Maji bata san tafito waje zubar da bawan lemun da suka,sha ba,
sai jin muryan ta maji tayi daga bayan ta tana cewa.
Mu dai mun gode ma Allah ai yaje lafiya ya dawo lafiya yan bakin ciki da suka so
kada ya dawo sai su mutu.
Da sauri Maji ta juyo kanta tana cewa ke maryam ban son rashin kunya fa da suke
zancen su sun ambaci sunan wani ne.
Sadauki da suke daki suna jin amsar da maryam ta bayar sun san akwai magana a
waje sai sukai shiru daga ita har sadauki din lokaci guda.
Maryam ta shigo tana turo baki gaba tana cewa yan bakin ciki kawai dama nasan
sheri da ganin kwam ya,zaunar da su ai a gurin kuma sun gani.
Maji ta shigo dakin don haka maryam din tai shiru don tasan in taji tana
mita,yanzu zata balballeta ne da fada.
Sai da maji ta zauna ta dube su a nutse take cewa abinda nake so daku maryam
shine.
Duk wacce taji a na,sake magana a gidan nan inda ba sunan mu suka ambata ba kada
wacce ta kara tankawa kowan su.
Amirah tace Maji su wasu irin mutane ne da son fitina daga dawowan mutum zasu
fara sakewa mutane magana kamar suna jirace da shi.
Maji tace suna jirace mana ba hassada bane kawai rudin shedan ai komai mutum zai
iya yi don jan fitina.
Fitana,suke so don sunga yadda yaje haka ya dawo masu shine abin dariyar su ai
tunda dan matsiyaciya ce shi.
Murmushi kawai Sadauki yadan yi yace su suna nan da halin nasu har yanzu wai.
May zasu fasa tunda kullun mugin nufi suke sakawa akan mutane inji Amirah tana
mikewa take fadi hakan.
Haka fa jiya naji Nafisa tana zagin Bintu wai yar ci rani ba bu ranan komawa gida
anga wuri.
Maji tace sai dai su mutu kuwa,don ko babu ranan komawan Fatima gida a gidan nan.
Bintu tadan ji kunya ta,sunkuyar da kanta kasa tana wasa da yatsun ta.
Maji tace gani sukayi yar ci rani tafi su mutunci da sanin ya kamata shine
hassadan su, don babu wanda zaice tai mashi laifi a gidan nan tunda bata shiga
harkan kowa.
Ta juya inda Bintu take zaune tana cewa don haka Fatima ki saki jikin kawai ki
dainawa kowa dari dari tunda ba wanda ya isa ya koreki cikin su.
Wama ya isa inji Amirah bakin ciki ne kawai da hassada don ko ranan naji yaya
Imirana yana cewa, wai ina aka samu yar kwara ne haka wai.
Sai naji Umma tana mashi fada wai ina kwara din take yarinya haka da fari kamar
zabaya.
Duk kan su dariya suka sa Maji tace cikin dariya kai bakin ciki ho ina Fatima tai
irin farin zabaya kuma in ba,sheri ba.
A fakaice ya dan saci kallon farin Bintu da ake magana shi dai baice masu uffan
ba a cikin zuciyar shi kawai yake magana shi kadai kan al,amarin kishiyoyin
mahaifiyar su.
Tun suna yara yake jin suna kirawa Maji kalman tsiya har su kan su din diyan ta.
Mikewa yayi a lokaci guda yana fadin zan je dakina maji ina key dina yake ne
wai ?
Yana fita daga dakin daga gurin da Bintu take zaune bata san lokacin da ta sake
ajiyan zuciya ba a fili.
Duk suka juyo suna mata dariya Amira tace dodon ki ya fita ke nan ko , don naga
idan yaya yana guri zakiga Bintu a,takure kamar wace za,a yanka.
Ba dole ba yana son firgita min yarinya da mugun halin shi ki saki jikin ki
Fatima haka halin shi yake baudade ne shi ko yaushe.
Murmushi kawai Bintu tayi batare da tace masu uffan ba,sai mikewa tayi tafara
kwashe kayan da suke a tsakar falin nasu.

****** ********* ******
Yaron yana tsaye tana loda mashi ruwa a,sabon roban da ta,sayo mashi wanda yafi
na farko da yake fita dashi girma.
Don yanzu ya dan fara sabawa da,tallan ya iya,ba kamar farko da yake dawo mata
dashi ba idan ya fita.
Tana gamawa ta juya inda yake tsaye tana fadin na jakka da hamsin ne na saka maka
kai sauri ka,sayar kadawo kafin mafadacin ubanku ya dawo gidan.
Ya dauki ruwan da,kyat yai mata,sallama ya fita, hat ya yi nufin zuwa inda ya
saba kaiwa gurin masu wasan ball sai kuma ya fasa yace bari yakai wani guri da yaga
ana aikin gina.
Yana,tafe yana fadin a,saya,ruwa mai sanyi ruwa dai, mai sanyi,
Sai yaji ance daga wani gefe pure water da sauri ya juya zuwa gurin har yana,dan
tuntube.
A bakin wani shago wasu matasa ne zaune su hudu suna hira sukackira shi.
Yun bai karaso ba dayan yake cewa kai amma yaron ga gaskiya yana da kyau gashi
dan tallakawa yana,talla amma tsab tsab dashi wallahi.
Ai kasan wasu iyayye suna da kokarin gyara yaran su kafin su fito yafi kazo
sayen abu gun yaro kazanta ya hanaka iya,saya.
Ysron na karasowa gurin su dayan yace sauke mana dama tin da,zun nake nema ruwa
masu sanyi wallahi don layin mu jiya babu wuta wallahi.
Nan suka fara zukan ruwan sai da kowa yasha leda biyu biyu dan sanyin da,ruwan
yayi sosai ga dama ana,dan karen zafi a garin.
Ganin da Aliyu yayi yanzu yanzu yayi cinki yasa shi dan samun guri dan nisa
kadan dasu ya zauna kafin su sallamay shi su bashi kudin shi ya tafi dama ya gaji
nauyin ruwan yai mashi yawa.
Da haka mutanen dake wucewa suka zo suna saye har ruwan ya,saura kadan a roban.
Sai ga,wata mai abinci tazo ta zauna daga gefen shi take ruwan ya kare ya karbi
kudin shi ya juya gida da sauri ya,karo wani.
Wasa wasa,sai yagane gurin ana,samun ciniki fiye da inda yake zuwa da,farko don
haka ya mayar da,wurin gurin kai tallan ruwan shi ko yaushe.
Yana mayawa kusan biyar a rana kafin ya koma gida don zuwa makaran ta da,sukeyi
da yamma.
Watarana kuma in yan tsiyan sunackan maria sai tace mai idan sun tashi cin
breakfast ya gudo yazo ya fita mata da ruwan ta.
Da sannu yan gurin suka fara sabawa da yaron har suka yarda dashi suka,fara dan
aiken shi sayen taba abinci da sauran su.
Yakai yanzu inva ruwan shiba basu sayen ruwan kowa do shi ko yaushe ruwan shi
zaka samay shi da sanyi sosai koda ba,wuta don freeze maria yana aiki sosai duk
yadda aka kawo wuta zaiyi saurin daukan raba yai sanyi.
Tun maigidan yana zargin tabarbarewan karatun dan shi yana fada har yagaji
ya,saka,mai ido do uwar bata bari ya,fadi tinda tasan abinda take shukawa a bayan
shi.
Sosai maria take jin dadin yadda danta yake mata,talla haka tana cewa Allah
ya,bashi kan ciniki sisai tayi sa,an haihuwa ita.
Tan godewa Uwarta data,bata wanan shawaran da badon haka ba da yanzu tana,nan
tana,wahalan neman dan talla bata samu ba.
Kulun bankin ta,sai bunkasa yake don yana samun canji suna shiga mashi yadda ya
dace.
Yanzu ji take koma mijin ta yasani baida yadda zaiyi da ita don bazata iya hanawa
dan ta wanan tallan ba.
Shiko maigidan mutane da dama sun shatare shi suce sunga Aliyu yana tallan ruwa
da yazo yai magana bai gand komai gareta.
Don haka yaja,bakin shi yai shiru har ranan da zai kamasu da hannun shi ranan yai
alkawarin zai dauki mataki a kanta, sai ta rena kanta ga hakan.

****** ********* ******
Tunda sadauki ya fita zuwa dakin shi bai fito ba ya,samu guri ya kwanta,tare
da,karewa,dakin da yasha gyara kallon mamaki.
Don yasan ba aikin su Amirah bane wanan wa yan nan malalata yaushe
ma,suka,iya,gyarawa Maji guri yai kyau balle na,wani.
Da,sauri zuciyar shi da,tafara tunane tabashi amsa,da,fadin ba,aikin kowa,bane
sai wanan yar kauyen ta Maji.
Bakowa zai iya wanan aikin haka,ba,sai ita wata irin yarinyace bata jin ciwon
jikin ta ita aiki bai isanta ko yaushe a,tsaye take ita.
Nan dai har barci ya dauke shi inda bai farka,ba,sai da yamma lis don gajiyan
da,ya,debo.
A,tare ya hada,sallah dake kan shi yayi ya,zauna gurin har lokacin da,aka,fara
kiran sallah magariba,ya,wuce masallaci akai jam,i dashi.
Yaushe rabon shi da,yin haka,mutumin da komai nashi a,tsabare yake abinshi bai
shiga mutane kamar mugu yake ko yaushe, sai yawan nisanta kanshi da mutane yakeyi.
Tun a masallaci suka hadu da mahaifin shi ba karamin dadi yaji ba na ganin
Sadauki a jam,i tashin farko da,dawowan shi.
Sama sama suka gaisa da mahaifin nashi don akwai mutane da yawa lokacin.
Yai matukar manakin yadda mutane ke kokarin gaisawa dashi yau sabanin da can baya
da mutum zai wuce ya,wuce abinshi ba mai gaida wani cikin su.
Shi girman kai mutane kuma suna kyamar dabian shi da ya tsira acikin al,umma.
Ana idar da,sallah direct cikin gida ya,shiga gurin mahaifiyar shi don bai gaji
da jin dadin ganin ta,da,yayi don dan,kwana biyun da,sukayi basu tare a lokacin
yasan dadin Maji sosai gare shi.
Ashe ma yawan fadan dayake ganin tana mashi wani babban gata ne gareshi.
Don zaman ta kusa dashi yafi rashin ta a kusa dashi ko yaushe.
Yana shiga falin duk suna zaune ga dan busashen falon nasu kamar kullun suna
hira.
Sannu da dawowa suke mashi gaba dayan su a cikin murna kamar su lashe shi don jin
shi da,suke ajiki ranan.
Cikin harshen turanci yake ce masu daidai lokacin da yake zama kai I miss you
people fa.
Ina yawan tuna ku ina can ko wani lokaci wallahi,
Yace ina Maji take ?
Tana part din Baba tana hada mashi abinci yace ok yau itace da duty ke nan ?
Maryam ta bashi amsa da eh,
Zaunawa yayi dakyau yace Amirah may aka dafa ne da,daren nan ?
Amirah ta bashi amsa da tuwon semo da miyar kubewa danya.
Jeki kawo min na dan ci na fita,na,samo maku dan wani abin sha kafin dare yayi.
Maryam mai kwadai tasa ihun kai canji yaya wallahi har naji dadi har cikin raina,
Yace common see yo mai kwadan tsiya kawai tace ba haka na,bane bakaji har gori
ake muna wai mu saidai abamu abamu kullun.
Wallahi wanan abin ya dade yana,bata min rai bafa rokon su muke ba kuma,da kudin
mahaifin mu ake saye amma,don diyan sune a,kasuwa shine ake wa Maji gori da mu.
Bintu da,taga basu da niyar bashi abinci ta mike taje ta hado mashi takawo
mashi don dama zaune take gefe tana sauraren su.
Ga abincin yana kallo ya tasa a gaban shi amma maganan da maryam tayi ya hana,shi
cin abincin.
Yasan daga shi har yan kannen shi biyu ba karamin hakkuri sukayi ba agidan nasu.
Don sun taso suna ganin kalubali rayuwan iri, irin tun suna yara har yanzu
da,suka mallaki hankalin su.

18 / 92