Author : Zainab Idris Makawa Seenabu Category : Complete Novels
Kin sha maganin da aka bakine muryan yaua sadauki ne yake tambayana hakan.
Cak naja na tsaya na dan bata fuska nace ban sha .
Koma ki zauna kisha kafin ki kwanta yace min ba mussu na koma na zauna idan na
daga .
Maryam tace ga maganin bazaki sha milki din ba kafin kisha don bakici komai ba
ma.
Naman kaza da fresh milkin din takawo min kurba biyu nayi bakina ba dadi sai na
aje kwalin don bazan iya sha ba zakin shi naji ya kara bata min baki.
Still magana sukeyi da mahaifiyar shi amma hankalin shi yana a gareni ganin ban
ci komai ba yace maji kiwa yar ki magana ta ci tasha magani.
Fatima ko tea zakisha in baki iya shan wanan din don naga kaman yana da sanyine
ko ?
Nace ,a,a mama nasha ai na dan kara kurbawa kadan na aje kwalin nan nakoma saman
kujeran na zauna da kyau can kuma saina dunkule guri guda ashe barci ya dauke ni a
hakan ban sani ba.
Sai da mama tai magana sukaji shiru shine suka fahinci nayi barci ne.
Maji tace gaskiya banji dadin yadda kaiwa yarinyar nan ba kadaina wanan halin
karfin ku ba daya yake dasu ba.
Ko banza ita mace ce fa ysushe daga dan magana kadan zakai mata wanan horon
haka ?
Shiru yayi baiyi magana ba don koshi yadda yaga ina wahala sai baiji dadin
abinda yai min din ba.
Ga yanin yadda na kwanta yasa shicewa maryam ta da ita taje ta kwanta wanan
kwancin sai kafan ya kara ciwo ai.
Bai wani jima ba yamike zuwa dakin shi don ya kwanta sai dai bai shiga dakin ba
ya zauna daga waje gurin furanni kofan shi don ya sha iska.
Mamaki yayi dayaji har a lokacin jikin shi yana kamshin turare na na white musk
danake amfani dashi ajikin shi.
Take ya tuna da yadda yaji lokacin da nake kuka a jikin shi da likita ke ja min
kafa.
Tsukiyi dan ja daya tuna yadda likitan ya rike dan farin kafana wai yana shafa
min magani a kafan nawa.
Haushin da yasa shi mikewa ke nan yabar gurin da yake zaune ya fada dakin shi
cikin takaici.
To kai takaicin may kake ji da hakan yaba kan shi amsa a fili da oho, wanka
yashiga yafito kusa da rigan da ya cire yasa kan shi.
Kamshin ne ya kara bugo hancin shi abinda ya sashi dan lumshe idon shi ke nan
haka barci ya dauke shi.
****** ********* ******
Washegari kodana tashi na danji saukin kafan nawa sai dai yana da dan sauran
kunburi still.
Ban fito ba sai zuwa 9,30 nafito don na karya nai wanka na saka dogon riga baka
abuga farin mutum sai rigan ya haskani.
A falo yana zaune da abinci a gaban shi yana ci yana waya fitowa na ina dan dan
gyasawa yashi bina da ido.
Ina kwana nai mashi Amirah tace kin tashi ashe Bintu nace eh anty tace to yay
jikin naki ?
Da sauki anty na zauna yana kashe wayan yace zonan naga kafan nan ko yai sauki ?
Idan baiyi a koma a kara jamaki shi da safen nan da sauri nace a,a wallahi naji
sauki yaya.
Dariya suka saka min yace no ki bari akara ja maki for second time mana zaifi
sakewa.
Wallahi yai sauki sosai yaya abarshi kawai ki karya kisha maganin ki kada fever
ya dawo maki.
Na amsa da to nabar gurin shi zan shiga kitchen sai ga maryam dauke da wayana dake
ringing da sauri na dauka.
Bashar ne a layin yake min yajiki yace yanzu yace maryam tabadhi layina yakirani.
Na koma na zauna don ba zan iya tsawon tsayi a tsaye ba ina amsa wayan nashi.
Ya dain bani hakkuri nace wallahi ba komai nagode ai ina taka kafan yanzu nace ka
gaidasu mama.
Ina kashe wayan yana watso min wani irin mugun kallon dayasani shan jinin jikina
lokaci guda.
Sai na tuna ya saka min idon kancewa ina waya da maza a gaban kowa haka yasa
lokacin da marigayi Kabir keda rai na daina waya a falo gaban su.
Daga inda maryam take tsaye gaban tv tace yayanane yakira ki halan nace eh shine.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,,,,,
YA ALLAH DUK WACE TA TURA MIN NOVEL GA WANDA BAI BIYA BA ALLAH KA SAKA MIN AKAN MAI
SHI,,,,,
Zaune yake a falon fuskan shi a daure tun da ya shigo gidan yake hakanan mama ta
fahince shi amna sai batai mashi magana ba.
Yana nan zaune ya dafe kan shi yai shuru tare da lumshe idon shi Amirah tafito ta
gan shi zaune a gurin tace ,a,a yayana ashe ka dawo ne yace eh a takaice kawai.
Takara cewa yaya akawo abinci ko don mun san shi ke shigo dashi cikin gidan wani
lokaci.
No Amira barshi kawai wanan abinda nasha dazun is ok for me, ya mayar da idanuwan
shi ya lumshe su.
Can yace Amirah ta amsa da na,am yaya.
Ina wanan yarinyar take ne?
Tace wa ke nan yaya?
Yace Fatima.
Suna ciki ita da maryam ina ga kaman waya takeyi ma dana fito.
Yace kiramin ita please ?
Ta mike na fadin toh.
A tare muka fito mu uku a lokaci guda tanagaba ina bayan su .
Yadda muka samay shi yasa mu dan shan jinin jiki don babu fara,a tare dashi.
Nace a yar murya gani yaya ya dago jajjayen idanuwan shi da suka sauya zuwa ja
jajir sai da gabana ya fadi.
Yace ke a ina ki san wanan guy din dana gan ku tare a waje dashi ?
Shiru nayi na dukar da kaina kasa ya dago cikin hasala yace ba ke nake tambaya ba
ne ?
Nace a,anan garin yake.
Kin san ko shi waye da kike tsayawa dashi ne ?
Maryam tai tsagal tace yaya a banki yake aiki nan gari yake da zama ai kuma dan
ga,,,,
Ban tambayeki ba maryam ita nake son ta fada min abinda ta sani akan shi kawai.
A hankali nace ban san komai ba akan shi yadai zo yace yana so na ne.
To ki rabu dashi daga yau kada na kara ganin kazamin motar shi a kofan gidan nan
in ba haka ba sai na sa an kulle shi wallahi.
Kai wai yaya haka may yayi shi mutumin da zaka yanke masu wanan hukuncin haka ?
Maji ban yarda da shi bane don bai da record mai kyau, shine dalilina kawai.
Kallon shi mama tayi kamar zatai magana sai taji na ce nagode yaya na juya na bar
falon jikina yai matukar sanyi sosai.
Ina tunanen wani irin halin banza ne ga Usman da yaya ya yanke min wanan hukunci
a kan shi.
Sai kuma nace tau Allsh dai yai min zabi mafi alheri da kan shi.
Amma maganan yana ci min zuciya sosai ga Usman yana kirana amma sai naki daga
wayan har ya tsinke.
Haka yai ta kirana yana min text amma ban bashi amsa ba sai daga karshe yace
nagane wanan dan wullakancin yayan naki ne ya hanaki hurda ni.
Don dama tunda naga yadda yai min na fahinci shima yana kaunan ki don irin kallon
da yai mi tare da kin amsa gaisuwa na.
Wanan massage din yasa na dauki waya na kira Usman din nake ce mai tir da
maganan shi, don mai zai min wanan furcin ga dan uwana.
Fatima kada ki boye min nasan komai wallahi nasan shi ya hana ki kulani kada kice
zaki boye min ni ba yaro bane fa.
Haushi ya kara bani nace ashe da gaske baka da mutunci usman ni ka sani kawai don
matarka na lura tafi karfin ka shiyasa na daina kulla ka kawai amma kada ka kawo
min wani magana can na daban.
Sai na kashe wayan na fara tunanen zancen Usman may yasa wai duk masu sona suke
zargin hakane ga yaya sadauki.
Ni dai iya sani na babu wani abin soyayya daya taba hadani dashi banda hattara da
tsangwama da kina da yakeyi.
****** ********* ******
Sai bayan kwana bakawai da zuwan shi muka wayi gari da abin arziki don tsaraban
mota mama da Baba suka samu inda yai masu Umma kuma kyautan kudi masu yawa.
Ni dai ko tsinke bai bani ba dama tun ranan da yai min wanan magan muke zaman yar
tsama dashi bani yarda mu hadu dashi.
Kaman nasan bani da tsaraba, sai Allah ya rufa min asiri ban ma fito falon ba a
lokacin hayaniyan ihun su nake ji suna murna a falon.
Maryam ce ta shigo dakin inda nake tana nuna min sabon wayan ta mai matukar tsada
daya canza masu da sauran tarkacen daya kawo masu.
Nace kai anty amma kun gode yaya yayi kokari sosai wallahi Allah ya saka mai da
alheri.
Tace mama ta samu mota har da Baba kai ina son irin wanan tafiyan na yaya wallahi
don a jike yake dawo muna idan yayi nasara ga ball din shi.
Tace a,a na fa manta sai yanzu na tuna banga yaya ya baki, naki tsaran ba ko dai
abin yar sirice kuma?
Nace don Allah anty maryam daina wanan zancen kin san yaya mugu ne kada yaji
zamana a gidan nan yakare da mama.
Taso muje ki ga tsaraban mu don Allah kada ta tsanmani wani abu na sauko daga
gado muka fito tare da ita.
A zatona baya falon amma ina fitowa yana zaune sai dai kwana biyun da banganshi
na ya sake min sosai.
Gabana ya fadi don sai zuciya ta ta fara zargin ko dai yaya koma ruwa ne wai don
yanayi yau da na gani akwai magana gaskiya.
Ganin shi zaune yana waya muryan shi kaman mai jin barci ko kasala haka ya kara
tabbatar min da zargina akan shi.
Na nufi inda mama take zaune, cikin murmushi nace mama ashe alheri ya samay mune
haka yau ?
Eh amma ai bai gama ba don banga ya nuna min naki ba duk cikin tsaraban.
Nace kai haba mama kullun fa ana bani don yau kawai ai ba komai bane kila ya manta
da nine kawai.
Murmushin manya mama tayi tace ya manta dake Fatima, haba magana dai yana da
dalilin yin hakan da yayi kawai.
Ya dago still cikin irin muryan farko da yake waya ba ko darr a ran shi ya ce,
wai wanan yarinyar ban mata ba ban dai sayo mata bane ai na fada mata tun a cikin
waya ba zan sayo mata komai ba.
O ko gadarare ya mike tsaye tare da gyara wandon shi da ya dan takure don zama
yace eh maji.
Sai ya fice ko mama sai da tai mamakin wanan irin tsauri da yai mata yau ido da
ido haka don ba halin shi bane bata ansa a tsatsaye.
Yana fita dakin shi ya shiga dakin duk a hargitse haka ya kwanta rubb da ciki don
tun daren jiya yai mugun hadiye kwayoyi ko zai rags damuwan shi a ran shi.
Duk abinda nake hankalina yana ga yaya sadauki don haka nace wa mama zan shiga
gurin gwagona don tana gari tana fama da ciwon kafa.
Tafe nake ina tunane abinyi sai wata zuciya tace min gwada dai ki gani ko zargin
ki hakane ?
Ina tura kofan ga mamakina dakin da yake a rufe ko yaushe, sai na samau shi a
bude, kamar na koma don na hango shi a kwance rubb da ciki kamar yana barci.
A hankali nake bin dakin da kallo har na hango wani farin roba saman dan stoll
din dake dakin yana dagwara kaya akai,
Na jima gurin ina kallon roba don zargina ya zama gaskiya ko naga evidence da
idona.
Zan juya naji yace Fatima,
Jikina ya dauki rawa kamar na ruga a guje don tsoro, ya ce may ya kawo ki
dakina ?
Bance kallah ba nai shiru,
Yakara cewa uban wa yakawo ki dakina nace maki?
Ya dago daga kwancen dayake yana fuskan tana idon shi duk sunyi ja jajir dasu.
Bance kala ba sai karasa shigan danayi na taka har zuwa inda roban drugs din yake
na dauka nace ga abinda ya kawo ni dama kuma nagani.
Komawa yayi ta,kwanta,lamo kamar ya koma,barci nikuma ina tsaye na kasa daga
kafata nai bar mashi dakin shi.
Lokaci mai dan tsawo na zaci barci ya koma duk a tsorace nake a lokacin,
Nafara tafiya sai naji yai yar dariya da sauri naja na tsaya cikin tsoro da
sauraren shi.
Ga tsoro ya kamani ban san gulman da ya kawo dakin shi ba don gani kwam kuma a
part din samarin gidan gaba daya.
Hawaye ne na fara zubar wa daga idona a hankali ba tare da ya dago ba yace kuka
kuma again cikin magana kamar rada ya fadi hakan?
Don Allah yaya kayi hakkuri dama zargi nake tun dazun dana gan ka a haka ?
Murmushi yayi tare da mikewa zaune yace, ashe bayan gulma har kin zama C I D ban
sani ba ?
Haka kawai na tsinci kaina cikin karfin halin fadin gulman da nakeyi a inda ya
dace nayi nakeyin shi ba hakana kai tsaye bs ga abinda ba damuwa na ba.
Fuska a daure yace, lalaima yarinyar nan ta raina ni wallahi sosai, zaki gane
baki da wayo don gobe baki karawa wani bakin shishigin tsiya irin haka.
Wani irin naji cikina ya ansa kululu nace a raina yau ko na shiga uku nakawo
kaina da kaina.
Amma afili nace duk abinda zakai min nasan akan kauna mama kai min don irin
halarcin da take min a rayuwana komai zan iya yi akan farin cikin mama don bata
nuna min banbanci ba a cikin ku.
Shiru mukayi dagani har shi ba wanda yai magana don kukan da yaci karfina a
lokacin.
Ba tare da fargaba ba naci gaba da cewa why yaya why baka tausayin mahafiyan ka
why please ?
Kai kadaine da namiji da Allah ya bata a rayuwan ta kaine take tunanen samun
farin ciki a gurin ta.
Yan uwanka da ma mu dake a karkashin inuwan ku gare ka muke fatan samun budi a
rayuwan mu,
Amma kai yaya baka tausaya mata baka jin kan ta baka tuna irin gorin da ake mata
tsawon lokaci a gidan nan a kan ka why baka tausayawa kan ka da mahaifiyan ka ne
please?
Kafi son ko da yaushe ka zama abin kyama ga al,umma da kuma abin kwatance a gari
yaya kawai Allah kabar wanan harka ka dage da rokon Allah da bayar da sadaka akan
Allah ya rabaka da wanan halin kodon goben ka.
Ina kaiwa nan na fara tafiya zanbar dakin yace Fatima, naja na tsaya tsaye cak
guri guda.
Ido ya zuba min na dan lokaci yace wanan magana ta tsaya iya ni dake a nan.
Na girgiza kaina nace har abada bazan taba tona asirin dan uwana ba ga wani kai
dai kadai tsoron Allah idan wani baigani ba ko yaji ai Allah daya hanamu shan maye
yana kallon ka.
Murmushi yayi tare da mikewa tsaye daga zaunen daya ke ban tsan mani har ya kawo
gareni ba sai ganin shi nayi a gaba na ido da ido muke kallon juna dashi.
Banyi wata alaman ta razana ko kadan kada ya gane a razane nake lokacin dashi.
Ya nuna ni da yar yatsan shi yace ban san koke wata irin shu,umar yarinya bace da
baki da tsoro haka nima ina mamakin kaina da nake tausaya maki amma tafi babu komai
zamu kara haduwa wata rana.
Nace kadai tausayawa mahaifiyar ka da kan ka kafin har mukai ga kara haduwan.
Kuma bani fatan haduwan ya kasance irin wanan zargin a kan ka sai da ya zama wani
abin alheri can daban.
Roban kwayan na hannu na fita daga dakin tabi bayana da kallon mamakin irin
karfin halin dake gareni haka.
Sam banda tsoro ko shayin wani a idona yadda ya hango cikin kwayan idona gaskiya
ce sahihiyar ta na fada mashi kuma na fita.
Ina tafe ina sharan hawaye har nakai gidan gwagona sai da na samu gidan yana rufe
tafita ke nan .
Na juyo na dawo gida tareda boye roban kwayan a jikina har sai da na kai part din
mu ina shiga mama tace har kin dawo ne nace bata nan tafita.
Amma kuma ya fuskanki kamar kinyi kuka na dan yi yake nace kuka kuma mama?
Banyi kuka ba mama daga haka na shiga daga ciki sai kuma mama ta fara zargin ko
dai tsaraban da sadauki bai kawo min bane ya bata min rai har nai kuka?
Ina kwance daki saman gadon mu kaina sama kafana suna zufe daga kasan gadon, na
dan jingina jikina da kan gado.
Ban san shigowan ta dakin ba don nai zurfi ga tunanen da nakeyi a lokacin.
Fatima naji ta ambata abinda yasani saurin dago kaina ke nan ina kallon ta da
sauri ina kokari gyara zamana da kyau.
Itama dai zama tayi daga gefe na kadan tare da kura min ido kamar mai nazarin wani
abu a gare ni.
Abinda yaron nan yai maki ne yasa ki kuka ko?
Da sauri na girgiza kaina nace wallahi Allah ko daya mama ko kadan ban sa haka a
raina ba.
To may yasamay ki kai kuka da fitan ki yanzu, don ba haka kifita ba a gidan nan.
Dukar da kaina nayi kasa nace a hankali ba komai mama,.
Yanzu har takai lokacin da zaki iya boye min wani magana a cikin ranki.
Da sauri na kara dago kai nace wallahi mama ban boye maki ba sai nai shiru.
Bazaki fada min ba ke nan ko?
Maimakon nai magana sai na sake kuka shiru tayi tare da kura min ido har tsawon
lokaci can tace nace zancen tsaraban