Advertisements
Chapter 58 Reading A Lokacin Mu Ke by Zainab Idris Makawa Seenabu BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

A Lokacin Mu Ke by Zainab Idris Makawa Seenabu

Author :  Zainab Idris Makawa Seenabu Category :  Complete Novels

Chapter   58 / 92

171K to 174K   out of 275.8K words

baki masu zuwa daurin aure
sai kuma jiya gashi da safe kafin ku iso anzo da abinci da katifo wai daga
marikiyar taki ta aiko dashi.
Nace an gode Baba ya ce tau Fatima sai dai ban tsanmanin zamu kara samun lokaci
irin haka dake ba.
Abinda nake son ki sani shine shi zaman aure dan hakkuri ne don yanzu so ya kare
a tsakanin ku sai hakkuri.
Yi nayi bari na bari inji manya sai a zauna lafiya, kin dai san ance mijinki
mutum mutane ne gashi kuma dan gidan yawa.
Don haka ki zauna da kowa da halin ki duk da nasan ki amma ki kara da hakkuri
Fatima, shi hakkuri baya karewa fa musulmi.
Duk da a hasashe na ina fanin kaman wanan aure aure ne na hadin iyayye a tsakanin
ku dashi halinki shiya ha har suka kwaidaitu da son zaman ki da dan su.
Don haka ki kara wani saman wanda suka sanki dashi sai kiga akarshe ke ce da
riban hakkuri.
Take naji idona ya ciko da hawaye har na kasa control din su sai da suka zubo min
nan dai baba yaita min nasiha akan hakkuri da zamantakewan aure da kuma sabon
rayuwan da zan shiga ciki.
Mukai sallama dashi yana ta saka min albarka tare da fatan samun zuria dayyaba.
Yinin ranan haka nayi shi a kwace babu walwala tare da ni ga mutane sai masha,an
da sukeyi kawai.
Da dare gwagona mai masa tazo tace nazo mu tafi gidan su mahaifiya na don ko can
akwai yan uwa da suka zo buki.
Mun shiga gidan mutane sai jin dadin gani sukeyi suna ga amarya tazo gaida ku.
Nan muka shiga gaisawa da mutanen da na dade banga wasu ba sai ranan.
Sai wani lokaci na samu kebewa da mahaifiyana a wani daki dagani sai ita muka
zauna a dakin.
Tace tau yarinyar ga gashi dai Allah yayi zaki aure yanzu don Allah idan kin je
kiyi hakkuri da sabon rayuwan da zaki tsunta a sabon gidan ki.
Ance zo mu zauna zo mu saba ne sai dai mu mata da hakkuri aka san mu dan namu
yafi na maza don mune a kasa garesu.
Kina dai ganin irin rayuwan da nake ciki ba sai na fada maki ba kin san hakkuri
nake dashi don da ban hakkuri da tuni nabar gidan nan na,watsar da yaran nan.
Amma sai naga idan na fita na barsu dawa kuma zasu zauna har ya basu tarbiyan da
nake son su samu saboda kinga shi wanan ba irin naki mahaifin bane.
Ina jin haka sai wani irin kuka mai karfi yazo min don tausayin mama na dani
kaina.
Da kyat ta dan lalashe ni na sasauta cikin kuka nace mama ina ganin kusan rayuwa
guda Allah ya jefo muna na aure.
Don kinga shima din mashayi ne ne kaman baban su musa sai dai dan banbancin su
kadan ne don akwai wayewa a cikin nashi.
Mama bana son shi na tsane shi natsane shi a rayuwa na amma sai gashi magaifiyan
shi ta nemi alfarma a guri na akan na rufa mata asiri na aure shi.
Mama may zanyi da mutumin da bayaji tsoron sabawa Allah bai dauki sabawa Allah a
bakin komai ba.
Mama don mahaifiyan sadauki zanyi wanan auren don ba zan iya mussa mata fa
bukatan taba a gare ni.
Mama ta katse ni tace amma kin bani kunya wallahi yarinyar ga ina iliminki da
tarbiyan ki ya shiga da har kike ganin ba zaki iya taimakawa hajiya ba yau.
Tace da kikaga hjy ta zaboki a cikin dubu ta bukaci ki auri dan ta kina zaton don
kyau kine ko arzikin ki ko wani abu can.
Tayi hakane don tana hasashe watakila tagare ki zata samu nasaran raba dan ta da
waban halaiyar tashi.
Bafa don bata sonki ne tace ki auri dan ta ba suna da kudin da zasu aura mao duk
macen da yake so a duniyan nan.
Amma kikaga ta nace akan sai dai ke din take so ki zauna dashi, nasan kuma tai
hakane don tana ganin ke ce kila zaki iya kawo karshen wahalan nashi.
Shi fa hanyan sabon Allah shiga rai ke gare shi sosai, daga lokacin da akace
wanan abin baida kyau haramun ne, sai kiji zuciyar mutum na tura shi aikata shi a
ko wani lokaci.
Shiyasa akace an zagaye wuta da abin sha,awa wanda zuciya ke so, an kuma zagaye
aljanna da abubuwan ki wanda zuciya bata so.
Don hakane duk wanda ya kama hanyar aljanna zai ta haduwa da abubuwan da zuciya
bata so, haka kuma shi wanda ya kama hanyan wuta zai hadu da abubuwan da zuciya ke
so.
Shiyasa akace daga cikin hakkurin da ake son mutum yayi shine harda biyayya ga
Allah da manzon sa dama
magabatan mutum da kuma hakkurin gujewa sabon Allah.
Hana zuciya aika ta sabon da ya ginu a kanta farat daya abu ne mai wahala so sai
sai mai hakkuri.
Idan kana da hakkuri zaka iya jure jawo hankalin mai yawan sabon Allah sannu a
hankali ta yawan nasiha da lurar da mutum illar abinda take aikatawa.
Uwa uba kuma addu,a da nasiha ga mutum har Allah ya bada sa,a ya bari ko ya rage.
Yin fushi da mutum ko kaurace mashi baya hana mutum sabawa Allah sai dai ma ya
kara kangarewa kawai.
Amma jan mutum zuwa jikin ka shike sa mutum ya rage watarana har ya tuba ya
daina gaba daya.
Don haka ita hajiya taga cewa, kece kadai zaki iya taimaka mata gurin wanan
yakin.
Don haka yaki babba a gaban ki yar ba don hajiya ta dora maki nauyi mai girman
dauka gare ki.
Fushi zagi gori da kawar da kai ga abinda yake aikatawa yanzu ba naki bane yar
baba.
Don haka wani kawar da kan ki gare shi ko ki kyamace shi ba naki bane yanzu.
Don idan kinyi haka tankar kin kara tura shi ga halaiyar da yakeyi ne na kyamata
da uwarshi bata son ganin shi a ciki.
Hajiya ta wuce ki watsar mata da bukatan ta gare ki, sai dai ki kara runguma
kawai da hannu bibiyu.
Zata ci gaba da magana gwagona ta leko tana cewa fito mana Bintu, dare fa ta
soma kin san ba wuta garin.
Haka yasa nai sallama da mahaifiya na tana ta jero min addua irin da yadace duk
uwa taiwa yar ta da zata dakin auren ta.

****** ********* ******
Waagegari tun da safe wata mota ta iso da kujeru da rumfuna suka shiga hakawa sai
kuma fa mota da abinci ruwan sha na gora da leda sun iso.
Inna ta bawa ranan ta arare ta yafe itace kirjin buki arziki ya sauka mata a gida
sai yadda tayi zuwa tara da rabi sai dirin motoci ke tsayawa a kofan dan gidan mu.
Haba take guri ya kaure da yan ma,abba sai kirari sukeyi fa Alhaji wani ga Alhaji
wani yazo.
Zuwa can wani mai murya ke sanar da jama,a ta lasifikan shi Allah yayi lokaci
yayi yau an daura auren Umar faruq da Fatima Bintu akan sadaki naira dubu hamsin.
Sai wata matar babana ta rangada wani irin guda tana fadin yau Fatima Binta kin
gwada muna kin haihu a zariyan Ibrahim da maimunatu don kin jawo muna arzikin da
bamu taba sanin akwaishi na garin nan.
Allah yasawa auren ku albarka yakawo muna zuri,a dayyaba masu albarka arayuwa.
Bayan dan lokaci muka ji mata na fadin ance ku gyara ga angonne nan zasu shigo
gaida ku cikin gida.
Ina can boye kuryan dakin Inna tabawa naji matan tsakar gida na fadi wanan na
tsakiyan dogon ai shine angon lalai Bintu kan kin yi sa,an miji wallahi da ganin
shi ba karamin mutum bane.
A raina nace baku san komai ku kumbu a rufe ganin kyaun dan maciji kuke mashi
haka dahi nanan cikin shi.
Ba wani bata lokaci matan da aka zo dasu suka fara cewa wai a fito da kaya zamu
tafi take na saka wani sabon kuka mai tsuma zuciya.
Bashar ne ya dauko ni a motar shi sai kaunan mahaifiyata wata malaman arabiya ce
ita sai gwagona dana zo birni a wurin ta, kawa yena su biyu haka muka shigo mota
daya dasu.
Tun da muka fara hanya ina a dunkule sai kuka nake rusawa a hankali gwagona tana
min fada wai zan jawa kaina ciwon kai a banza kamar wace za aika gidan mugun abu.
A raina nace kyace haka mana tunda kin ja min mugun rayuwa a sanadinki duk na
fada cikin wanan rayuwan haka ai.
Bashar yace gwago kyale Fatima tai kuka yau don zata fada sabon rayuwa kuka ta
zama dole gare ta.
Magana ce yai mata a cikin magana wanda duk cikin motan nasan sai ita kadai ce
zata fahinci hakan kawai.
Gida ya cika yacika ya batse kamar may yan uwa da abokan arziki nisa da kusa
birni da kauyen an hadu.
Muna na isa aka fara futowa zuwa taron mu yan uwan mama da yan uwan mahaifin su
yan uwan umma da mama nasu suma ya ishe su ranan.
Ga Nafisa tayi halinta suyi party tayi tatil haka tashigo gida tana ta watsewan
ta gidan Amarya yaya Ahmad kuma suma suyi nasu bushewan sai tir da Allah waddai
akeyi masu ta ko ina.
Part din maji ne ba wani abin asha da akaji don bukin yaran ta neat akeyin shi
cikin mutunci da sanin ya kamata.
Ina rike da hannun kaunan mahaufiyata da yan uwan ubana don atare muka iso da
sauran yan kawo ni daga garin mu,
Wanan kauna mamana ta dan duko tace saka kafan ki na dama ki ja basmalah kafa
ashirin da daya tare da karanta, (fihizuma, wa huwa ala kulli shai in kadirr,,,,
kafa ukku)
Nan mukaja muka tsaya kaman muna wani abu na karanta tace kin gama nace eh tace
ubangiji Allah yasa ki shiga da kafar dama Fatima.
Mama tana jin mun shigo ta taso da kanta tazo ta tare mu ta rungumoni jikin ta
tana maraba da diyata sannun ku da zuwa.
Dakin mu na shige da kawaye na na samu su maryam dakin ya cika da kawaywn ta.
Suna ganina ta saka ihu tare da shekowa ta tareni da murnan ta nan muka zube na
hira ni dai ban da kuzarin bata amsa sosai a lokacin.
Zan iya cewa ni dai tunda aka fara shagalin bukin mu ban saka Amirah a idona ba
har naje na dawo din ban gan ta ba ga gida ya cika ya make da mutane.
Nace niko banga Anty Amirah ba fa tace wa tana can gidan yayan mu da wasu baki
ma, ana dai ince maki tana gidan ki can ta tare yau tun safe suke can da kawayen ta
wai suna wa bakin shi abinci.
Kin san ita yar ba ruwan mu ne daga cikin mu adole a bayan yaya take bata san
zatai kunya ba idan yaya ya shiga hannun wanan matashiyar matar tashi da nake gani.
Nace kai anty zaki fara ko tace wallahi Bintu bakiga yadda kika koma ba yau gaba
daya kamar wata yar kasan etopia can.
Kin san sune yakar kyayo acikin jin sin na yan adam.
Karfe daya da rabi a kaje daurin auren yaya Ahmad wai na yaya Imirana tun
bakawai na safe aka daura don su haka akeyi gidan matar shi.
Biyu da rabi aka daura auren su Anty maryam da Anty Nasmatu diyar mama, ita ba
ruwan ta da sha,anin kowa a gidan mu irin masu akidar ra,ayin rikau ne ita.
Muna nan akace wai za,ai dinner da karfe bakwai zuwa takwas na dare.
Haka yasa ana idar da sallah magariba mummy tace kowan mu ta fito dama muna cikin
shiri tun yamma kowa ta kimtsa tafiya gidan ta.
Nice farkon kaiwa don tare aka fita dani da maryam anty Nasmatu yan uwan uwar ta
suka kaita ita ma.
Jin an dakatar da mota yadan sani bude fuskana kadan gidan da nagani sai da
gabana ya fadi don zakace ba cikin garin sokoto kake ba a gidan.
Hankalina yai balain tashi ina yaya ya samu kudin da yai wanan gida haka ba dai a
ball kawai.
Ina jin Inna tabawa na fadin dankari ba fashi wanan gidan haka shine dai gidan
Bintu ko kuwa?
Ina makalle ga hannun kaunan mamana wacce dama ina ganin don haka yasa tazo daga
bangaren mamana.
Tace idan zaki saka kafan ki akasa ki karanto fatiha kafa uku, ko wani da
bissimillah.
Sai ki karanta Basmalah irin na dazun kafa ashirin da daya ki karanta falaki da
nas ki hada da ikilas uku uku Allah ya sawa aure albarka ya kare muna ke daga duk
wani abin ki na cikin aure.
Ina idarwa ta kama hannu na tare da rada min ki dinga karanta Hasbunallahu wani
imal wakeel har mu shiga ba adadi.
Muna tafe masu guda sunayi masu suraitai nayi niko ina saman bakina har abinda
batace ba idan yazo min janakeyi na neman tsarin daki.
Nan aka shiga bin gidan da kallo mun samu yan uwan mama acan sune suka tari
amarya.
Muna nan dai akace afito akai maryam nata gidan ba nisa sosai don unguwa daya
muke.
Wata kawar anty Amira mai makeup ce tashigo dakin bayan an watse tace amarya nazo
nai maki makeup na fita dinner ne.
A hankali na kware rufin da ke kaina sai naga tare da su Amira suke da kawayen ta
naji mai makeup din tana fadin masha Allahu friend wanan ce kike kira da yar kauye
haba waban aiko a fashion sai haka mana.
May kuma ake bukata ga mace ga kyau ga wayewa duk a gurin nan tsoki tayi tafita
daga dakin tace ma sauran su fita su bar mu.
Ta busu tarufo dakin tace na taso na saka kayan da suka shigo dashi a jikina
kallin kayan nayi da mamaki nace wanan kayan zan saka tace eh shine angi ya sayo na
dinner.
Ba yadda na iya dole na saka kayan hakana a jikina ba don naso ba sai da zan saka
nagane akwai wani daga ciki mai tare jikin mutum.
Tana min kwalliya tana min gulma wai may yasa Amira take ta faman kusheni ne haka
ita bata taba zatin haka zata ganni ba.
Don Allah kada na damu da duk abinda Amira da yan uwan ta zasuyi min hassadane
kawai take gani yana damun Amira.
Nace haba anty kin taba ganin mutum yai hassada da dan uwan shi nima fa kaunan
tane halinta dai ne baku sani ba amma haka take ita.
Tana min magan ganu akan rayuaan mazan yanzu abinda zakayi wanda zaka kama miji
da sauri a hannun ka ni dai umhumm kawai nake ce mata har muka gama komai da ita.
Ba matar ba ni kaina nasan na hadu haduwar da ban taba sani ina da shi ba irin
haka sai yau.
Sai tara da rabi akazo daukan mu zuwa gurin dinner wata irin haddan motace aka
bude min baya in shiga.
Duhu bai bari mutim ya gane ko mai a ciki sai da na shiga na zauna a zatona zamu
je daukan shi inda yake ne .
Sai da mota ta fara tafiya a hankali naji an matse min hannuna dana dauka kujeran
motan ce na dafa.
A hankali ya kare tankware hannun nawa yace welcome to ukuba house baby Fatima.
Wani irin faduwan gaba naji amma na dake yakara cewa da fatan dai kin shirya
danmaran taron abinda kika fada a shekaran jiya ko?
Nace shirye nake tsab da su don nasan cikin shi na shigo dama yace good baby
good.
Haske fitilon da ya haska gurin zakace rana ne a lokacin motoci kanan duk motan
dake garin aka kwaso ranan.
Zaka ji kida na tashi daga duk inda kake a farfajiyan gurin da kewayen shi.
Sai dan wani lokaci wasu mace da namiji suka zo inda muke dafa baya na gane
summaiyace kawata da mukaje kauye da ita sai wani da ban sani ba namiji.
Sadauki yadan rankafo daidai kunne na yana fadin idan kika bani kunya da halinku
na kauyawa wallahi nima sai na disga ki a taron nan kinji na fada maki.
Tare muka jera dasu zuwa wani dan karamin kofa shiga wani guri a hole din sai
ganin maryam da Bashar din ta nayi.
Mune a gaba shiga hole din suna bayan mu naji bashar na fadin Ubangiji Allah ya
sakawa maji da gidan aljanna da wanan hadin da tayi haka.
Muna shiga saida gabana ya fadi don irin taron da na gani a gurin mutane sai kace
ana wani taron addinine.
Nace hasbunallahu wani, imal wakeel a hankali.
Wani haske da kamshi da wasu abubuwa ake watso muna take guri ya dauki ihu up U F
kayi daidai wallahi.
Sai wani dan washe baki yake kamar da gaske yana so mun zauna aka fara event
yadda akeyi a ko wani buki na dinner.
Gurin yanka cake a tare mu duka hudu muka mike ko wani ango yana rike da hannun
amaryan shi,
Sai dai ni nawa angon rikon keta yai min don yatsuna duk sunyi ja saboda matsa da
yayi masu na kyata.
Shine ya fara yankawa yabani ba dan guntsura kadan aka hau tafe sai ni kuma na
yanko kato na kai mai a bakin shi mugun sai ya hada da hannuna ya tauna sai da nai
kara aka saka ihu.
An fitar da mu wai muyi rawa ni dai ina tsaye shine dai ya dan taka kadan sai
lokacin nasan wai yan kwallon su na kasa sunzo taya shi murnan aure ashe.
Nan suka zagaye mu suka fara ruwan dollars akan mu suna fada mashi wai yaya akayi
ya iya zaben mata haka gani kuma very young dani.
Duk wanda yazo zai mashi farin ciki akan ya iya zaben mace komai nashi a sa,a
yake shi.
Sai sha biyu da rabi nace nifa barci nake ji gaskiya zan je na kwanta ga photo da
muka sha har nagaji ranan.

58 / 92