Advertisements
Chapter 61 Reading A Lokacin Mu Ke by Zainab Idris Makawa Seenabu BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

A Lokacin Mu Ke by Zainab Idris Makawa Seenabu

Author :  Zainab Idris Makawa Seenabu Category :  Complete Novels

Chapter   61 / 92

180K to 183K   out of 275.8K words

ciki na kai mashi.
Ban fito ba sai da,na kara gyara dakin tsab nafito don na samu kayan da yacire
a,watse inda yake ajewa na feshe dakin da airfreshiner.
Dakina na koma don nagaji gani na san tunda yana gari gobe dole akwai aiki gare
ni.
Sallah nayi tare da dauko rigan barci na na saka har zan kwanta sai na tuna ban
sallami MUSA ba .
Nafito a cikin yare nai mashi magana cewa idan ya gama kada ya dade yaje ya
kwanta yace min to Allah ya bamu alheri.
Duk da zani ne saman rigan ya san shirin da nayi alokacin na kwanciya ne.
Daki na koma ban dade da kwanciya ba naji barci ya fara dauka na gashi ban sawa
kofa key ba yadda na saba sawa nufi idan na falka zanyi sallah sai na rufe kofan.
Can cikin barci naji kamar ana tsaye a kaina duk da rufe nake a cikin bargo bai
hanani jin nauyin mutum aikana ba.
Da sauri na bude bargon dake rufe har kaina yana tsaye ya harde hanbayen shi biyu
a saman kirjin shi ya dan jingina jikin shi da bangon daki haka ma kafan shi a
harde suke mai.
Ganin shi a dakin yasa nai saurin mikewa zaune cikin dan rudewa nake cewa wani
abu zan makane kuma?
Ke dakata yace min cikin daure fuskan shi tambayan ki nake son yi .
Wani muna funci kike kokarin kulla min a gidan nan kuma ?
Cikin mamaki na dago kaina tare da dan kallon shi ganin ni yake kallo ido da ido
yasani dukar dakaina a kasa.
Yace tambayan ki nayi may kike kullawa akaina don ban fahinci wanan bakin ladabin
shegun da naga kinayi ba tunda na dawo gidan nan.
Murmushi nayi kawai tare da kokarin mikewa zaune da kyau banyi magana ba sai da
na mike tsaye da kyau tare da manta yar rigar barcin dake a jikina.
Sai da naga wani mayen kallon da yai min nai saurin koma da sauri na zauna tare da
jawo zanin da ke saman gado na kara dan rufe jikina dashi.
Idanuwan shi na a lumshe yake ce min ke nake saurare zakiyi magana ko sai na saba
maki yanzun nan.
Nace laifi ne kuma idan mata ta kyautatawa mijin ta ashe nace kada ka manta
nauyin ka yanzu a kaina yake.
Duk wani nauyi da nasan naka yana a kaina shi nake kokarin ganin a matsayina ta
matar gidan nan na sauke shi a kaina ko kuma hakan shima sabawa ne ga Allah.
Bai yi magana ba bai kuma fita daga dakin ba sai lumshe idanuwan shi kawai da
yayi a lokacin.
Can naji ya furzo iska daga bakin shi yana fadin idan kika kuskura kika kulla min
wani makirci har na fahinci haka wallahi sai na mugun saba maki kinji na fada maki.
Daga haka naga ya juya yafita daga dakin hakan yasa na mike nabi bayan shi na
sakawa dakina key kawai.
Amirah da taga shigan shi guri na shiru shiru taga bai fito ba ta mike cikin
bacin rai ta shige dakin ta sai sauke ajiyan zuciya takeyi kawai.
Tana cewa a ranta may yaya sadauki ke nufi da wanan yarinyar badai yana nufin har
ya mika kan shi gareta bane mai zai gane gurin wanan bakauyan yarinyar da maji ta
nace a kanta.
Tace kai yayana ban taba zaton haka ba daga gareka gaskiya kai mai tsadane kai
mai daraja ne sai yar manyan mutane ta dace da irinka.
Bintu bazan taba bari ki samu farinciki ba a zuciyar yayana har abada sai dai ki
zauna zaman gadin gidan nan kawai

****** ********* ******
Washe gari kafin kowa ya tashi na gama hada komai na gyara ko ina na gidan sai
kamshi ke tashi na koma ciki na gyara jikina tare da saka kaya wani dogon riga Afr
abaya mai simple design.
Ina zaune gaban mirror wayana yai kara na dauka ina mamakin mai kira na da
safiya haka.
Anty maryam ce ina dagawa tace amarya kina kamshi fa, yaya labari.
Dan tsuki nayi nace kai anty maryam ni dan Allah ki rabani da wanan zancen kinji.
Tace cikin daga murya may kike nufi wai wallahi Bintu kiji tsoron Allah duk wanan
nasihan da nai maki kina nufin baki dauka ba ko may ?
Nace haba Anty yaya kike son nayi da mutumin da baidamu dani ba zargina mafa yake
wai bai yarda da sauyin da yagani gare ni ba.
Dariya naji tayi tace bashi bane ya fara kamuwa ke nan kedai kawai yi yadda na
fada maki shi da kan shi zai kawo kan shi gare ki sai dai in ba mace ta haife shi
ba.
Amirah ta koma ne nace tana nan what wani gulma ya tsayar da ita kuma a gidan ku
amma dai Anty bata da kunya wallahi.
Yanzu zan sa maji ta aiko a dauke ta tunda ita bata san ya kamata ba don may zata
zauna maku gida ta haku walawa.
Shi musa nasan namiji ne ba zai tsaya saka maku ido ba namaji yayana na fadin
makarantan kwana yake so ya sama mashi nagari ya kai shi.
Wani mugun dadi naji a raina nace da gaske Anty tace wallahi jiya naji yana
magana cewa yana nan yana mai process don baya son ya koma kauyen nan kuma don
yaron nada kirki.
Nace wai ban ma san urin godiyan da zan ma yaya Bashar ba wallahi na dade ina
tunanen mafita akan kannne na anty don haka suke zaune ba karatu wallahi.
Tace a sannu duk sai ai masu mafita yanzun dai mu samu kan wanan baudaden mijin
naki tukun shine mafitan komai.
Nace nifa anty ba wai ya damay ni bane kawai ko hakan ma da muke is ok ai.
Tace kina da hankali kuwa Bintu mace baliga kamar ki zaki zauna danamiji sai kallo
ni na fada maki sa ido kiyi kallon yadda zamu kamashi wallahi.
Mun dan kai wani lokaci muna waya da ita tana kara fada min abinda zanyi, mukai
sallama da ita.
Muna gama waya ta kira mama tana cewa bayan sun gaisa ko anty Amira na kusa na
kira wayan ta bai shiga ba tace ba tana gidan yayan ku ba ko kin manta ne ?
Tace bata dawo gida bane mai takeyi a gidan kuma bayan maigidan ya dawo ?
Yaushe ya dawo inji mama tace jiya da yamma mana ya shigo gari haba dai ita ko
gidan amare mijin mutum ya dawo may zata kuma zauna yi masu a gida?
Maji tace ai yanzu zan tura Abdul ya dauko min ita bata da kunyane da bata zauna
a tsakanin su ba ai.
Bayan sun gama waya da Maryam mama ta kira wayan yaya tana cewa ashe ka dawo ne
Baba na?
Kunya yaji da ta fadi haka yace cikin dan kamay kamay wallahi yanzun nake shirin
nai wanka nazo gida ai.
Tace babu komai ka huta abinka har zuwa yamma ka shigo ai wanda ke da iyali kuma
ina zaka da dawowanka.
Sai dai ka fadawa kaunan ka ga Abdul nan zuwa yanzu ya dauke ta maza ta dawo
gida.
Ban san may ta tsaya yi maku gida ba kuma bayan tasan kana bukatan hutawa da
iyalinka.
Murmushi yayi kai haba maji jiyane fa na dawo ai ba komai takeyi ba zata dawo
anjima idan zan zo .
A,a maza yanzu ga Abdul nan zuwa zai dauko ta dawo gida haka na ladan ya isa
kuma.
Suna gama waya da mama ya shiga wanka sai da ya shirya tsab cikin kanan kaya
kamar yadda ya saba shiryawa, ya fito daga dakin shi sai annuri da kamshi ketashi
gare shi.
Amira ce zaune a falo nan ya zube gurinta suna gaisawa da ita sai wani shan
kamshi take wai tana fushi ya shiga guri na amma shi bai ma fahinci may take nufi
ba da hakan.
Yace maji tace ki shirya ga Abdul tafe yanzu zai tafi dake wai.
Bata so batace tunda safen nan kamar abin kora kuma ?
Yana zaune idon shi na akan kofana amma babu alaman fitowa na a lokacin.
Mikewa yayi tsab ya nufi dakin nawa tsaye nake ina shirin fitowa ke nan Allah ya
ingizo shi dakin.
Ina ganin shi na zube kasa ina fadin ina kwana yaya?
Yace ba tare da ya amsa ba Amira zata koma gashi kayana basu iso ba har yanzu.
Nace ko zata tsaya har su iso ne juyawa yayi yana fadin umurni ne daga maji.
Ki fito ki bamu abinci kafin Abdul ya iso daukan ta mun samu bata falon a lokacin
haka yasa na bita dakin ta.
Da sallama na shiga amma bata karba min ba nake cewa anty ashe yau zaki koma yanzu
yaya yake fada min haka.
Tace eh zan koma nabarki kiyi yadda ranki ke so ai nasan kece da aanan kullin don
na tare maki guri jarababban yarinyar kawai.
Haba anty may kika tare min aiko kina nan ba,a fasa abinda za,ayi kinga ashe
zaman ki bai hana komai.
Bintu kada fa ki kawo min rashin kunya wai ke adole ga wace ta san dadin namiji ko
?
Dariya nayi nace anty aure ne fa kema idan kikayi zaki gane haka ba wai jaraba
bane dadin aure ne kawai.
Lalai yau Bintu har nikikewa gorin aure har wani aure ne kikayi har kika san
dadin shi ke.
Kai haba anty kema aikin gani gashi kuwa kamar har ya damay ki kullun kina magana
a kan shi.
Da ki baro idan kayan yaya yazo ki karbi tsaraban ki zaifi ki koma hakana don
kada mutanen gida suga kin dawo empty.
Dama sjine gurin ku ai ku mamaye komai nashi ya zama naki ke da yan uwanki kawai.
Ba abinda zaki taba sai nazo gidan nan don nasan halin yayana dole nice mai raba
mashi kayan shi.
Nace da ke nan kuma anty yanzun kan ai akwai mairabo tsakanin ku ina fadin haka
na fito daga dakin na barta tana yabo min magana.
Mun karya duk da a takure nake amma ban yarda Amira ta fahinci komai ba akan
zaman mu dashi a gida.
Munan cikin karyawa Abdul ya shigo gidan nan suka shiga gaisawa da yayan shi ina
gefe nace yaya Abdul ina kwana ya juyo gareni yace sarautan mata yaya kike?
Nace mai na zubo ma, abinci ko yace kaman kin san bar karya ba nace nasani mana
yaya tunda gauro kake.
Bintu yaushe mijinki yai aure da zaki fara kira min gauro saurana fa kusan
shekara bakwai ko takwas.
Kai yaya wallahi kada kaiwa kanka baki nasan komai fa ina Nadiya take da zakace
haka?
Yana zaune yanajin hiran mu da yaya Abdul inda ya juya kan Amira yace kin shirya
ne ku tafi ?
Yaya ko kaima kora na kakeyi ne kaman wanan mara kunyan yar kauyen dake fanin ta
samu guri.
A,a Nafisa yaushe kuma kuka fara haka da Bintu ina Bintu tai kama da yar kauye ko
ada can balle yanzu da ta zama wata princess can da ita.
Nace yaya Abdul fada mata dai ko zata bude idon ta tagani ni dai nasan akwai
wata a kasa tsakanina da Anty kawai amma ni nasan nawaye ai yanzu.
Dariya magana ta tabashi yadda nai magana waina waye Amira tace kaiyya haka kike
gani ashe ke don kinga yanzun kina rayuwa a cikin wanan gidan .
Abar rayuwan kauye ko nace kai anty ho ke manta ni diyar mamace tun yaushe mama
ta mayar dani yar gatan ta.
Dama ai shine gurin ku ashigo a mamaye komai ai aleale sai yadda akayi da dangin
miji ko?
Kai Amira tashi ku tafi please bani son irin maganan nan for god sake kaunan kice
fa kubar wanan irin maganan mana ?
Yaya Bintu ce kaunata ko wa shiru yayi yadda na fahinci baiji dadin kalaman ta ba
a gare ni.
Kallon mamaki take mashi tamike tare da shiga dakin da ta mayar nata ganin tafito
da jakar tasa namike zan karba.
Tace kada ki soma taba min jakkana munafuka zamu zuba ni dake don babu gurin zama
agidan nan gurin ki.
Ido muka hada yai min wani shu,umin murshi na mugunta tafita batare da tace dashi
uffan ba.
Mikewa yayi yabi bayan su ina mata agaida mutanen gida.
Gurin da mukaci abinci na gyara muna tare da kawar da duk wani abinda ya dace a
gidan .
Daki na koma ina zaune ban san barci ya dauke ni ba a gurin can yadawo suna falo
da musa ya mike zai fita yace ina zaka tafi ustaz yace akwai inda nake fita gurin
mai shago muna hira ko dasu maigadi.
Yaron nafita yaji zaman falon ya ishe shi don haka ya mike zuwa waje jin dayayi
shuri ban fito ba yashiga dakin.
Dakina ya shiga ina kwance na dunkule saman gado kamar wata yar jaririya dani.
Kallon yadda na dunkule kamar mai jin tsoro yayi ya dade a kaina saida na dan
gyara kwanciya tare da kara dunkulewa yabar dakin.
Ikon Allah sai gashi nai mafalki da Kabi yanace min Fatima yau ina iliminki
da,wayon ki suka shiga.
Kina kokari kasa cin jerabawan ki zaki halaka kanki kin kuwa san irin dumbin
masifan da zaman dakika zaba da mijin ki yake haifa maki?
Ubangiji babu ruwanshi da halin shi rayuwan biyayya da zaman takewan ku zai duba
abinda yakeyi tsakanin shi da Allah shi ne.
Muddin baki bi mijinki ba Allah zai kamaki da laifin haka, kuma makomar ki shine
wuta.
Fatima kibi mijin ki kinji sauda kafa don Aljananki yana karkashin kafan shi ki
faranta mashi ko yaushe kinji kaunata kad ki halaka kanki.
Sai nafara kuka murmushi naga yai min kawai yajuya yafara tafiya kaman cikin wasu
duhun itatuwa ya bace abinshi.
Zubur na mike tare da salati sai zufan da yafara karyo min a goshi na kawai duk
da A C dake aiki a dakin.
Kabir na furta a fili wasu irin hawaye naji suna zubi min nace Allah ya jikan ka
bawan Allah kila sadaka yake so nai mashi.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU

IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,,,


IDAN KIN BIYA KIN TURAWA WANDA BAI BIYA BA MUN BARKI GA ALLAH,,,


A LOKACI MUKE


Washegari kamar yadda na saba tashi na kamala muna abin karyawa ina yi ina duban
kofan dakin da Anty Amirah take ciki har na gama bata bude kofa ba.
Wanka nayi na gyara jikina duk da ba wani kwaliya nayi ba amma nayi kyau zani da
riga ne na atamfan super the most classic one na daura.
Falo na fito na fara karyawa sai da na kusan gamawa ne, na ji ta bude kofan ta
tafito daga dakin.
Cikin murmushi nake gaishe ta, inda ta amsa min cikin ko in kulla tare da zuwa
tafara bude abinda na girka muna.
Sai can bayan ta zauna take cewa yanzun duk wanan abinda kika dafa haka wa zai ci
su ne wai?
Nace dani dake ne fa anty sai masu gadi da zan dibanwa nakai masu.
Humm,ummm lalai dan tallaka bai iya samun guri ba wallahi, Bintu tun ba,a je ko
ina ba kin fara wanan nan irin barna haka ?
Nace haba anty ina kuma barna haka ni dana tashi gurin mama ne kuma zan ce na yi
barna.
Masu gadi fa har mutum uku ne gidan nan kuma shi da kanshi yace na dinga basu
abinci suna ci.
Dakata Bintu may yakawo zancen yaya a nan magana ce iya ni dake mukeyin ta ko?
Kada ki soma kice zaki raba muna zumuncin mu da dan uwan mu don tare kika gan mu
ke haye kawai kikai muna daga sama.
Kodan maji ta cuce shi ta mashi wanan cushe na auren ki har kike ganin kamar ke
wata tsiyace yanzu.
Bari kiji koda ace auren so kukayi da yayana wallahi ke Bintu kinyi kadan ki
rabani da dan uwana ana magana kin wani kawo zancen yaya kin saka a ciki mafari ki
samu wani sheri ki kulla kice nace kada kiyi abinda yace kuma.
Kallon mamaki nake mata nace haba Anty may nai maki ne haka wai yanzu kike nuna
min irin wanan rayuwan a tsakanin mu nifa kaunar kice anty.
Koshi yaya din bai gwada min irin wanan kiyayyan da kika dauko gwada min .
Yar uwar wa ai dake yar uwatace da killa zan dan raga maki ta wani guri amma ina
hadin kifi da kaska kuma.
Sanan shi yaya ina yaga gurin nuna maki wani abu kisa uwarshi ta tsine mashi yana
zaman zaman shi akan wata banza can.
Anty nice banza kuma yau ?
Kila da hafsatu nake magana .
Cewa mahaifiya ta data haife ni wai da ita take magana na dago cikin mama idanuwa
sun kawo kwalla nace nagode Anty.
Kada ma ki gode din don wallahi ki sani Bintu nifa na tsane ki a rayuwana tunda
kika sa maji taiwa yayana haka.
Murmushi nayi tare da mikewa ina kokarin daukan kulolin abinci na juye wa su
maigadi nake cewa nagode babu komai.
Ina juyawa naji tana fadin mace a haka ba gaba ba wani fasali na mata kamar
solama dake.
Mamaki nake ina tafiya yadda cikin dan lokaci ta sake akaina gaba daya duk ta
manta da rayuwan mu a baya don kawai wanan auren na dan uwan ta da aka sakaniyi
bada son raina ba.
Naji tana fadin wallahi duk wani muna funcin ki ke da gwagon ki tun farko na
fahince ku kwadai ne kawai yakawo ku dama cikin rayuwan mu.
Allah ne shedan hakan kuma nace mata batare da na juyo ba tace ko kina so ko baki
so sai wata tashigo gidan nan yar arziki taci

61 / 92