Advertisements
Chapter 2 Reading A Lokacin Mu Ke by Zainab Idris Makawa Seenabu BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

A Lokacin Mu Ke by Zainab Idris Makawa Seenabu

Author :  Zainab Idris Makawa Seenabu Category :  Complete Novels

Chapter   2 / 92

3K to 6K   out of 275.8K words

kasuwa sai dai yana daki shi yana rage
kayan jikin shi.
Hakane ya bata daman shigewa ciki batare da yasan dawowan ta ba gidan.
Ganin ta kawai mahaifiyar ta tayi don haka hankalinta ya kwanta don tasan da
zaran mahaifinta ya ji bata gidan matsala ya faru ke nan.
Tafito daga dakin mahaifiyar ta,a,daidai lokacin da mahaifinta yake kokarin zama
a,saman tabarma a kofan dakin shi tana cewa baba sannu da,dawowa kawai ta,sa kai ta
shige abinta,
Ashe tana gidan ai yanzu nake batun nace wai tana ina ne banji motsin ta ba
uwar tace tana ciki ai tundazun, (Uwa ke nan,)
Nan ya zauna yana cin abinci suna hira da mahaiyar Raiha cikin so da kauna a
tsakanin su,

****** ********* ******
Yaro ne daga kofan gida yake kwada,sallama yana cewa abani ruwan pure water, na
naira goma.
Da sauri Hanne tafito daga dakin ta tana cewa shigo ka karba kaji ta bude dan
fridge din ta ta dauko mai ruwa leda biyu ta bashi ta karbi kudin zuwa dakin ta,
Ba,ajima ba wata yarinya tashigo itma ta saye haka mutane suka gane cewa tana
sayar da,ruwa ana dan shigowa gida ana,saye.
Nan tai shawaran ta fara dan kayan sanyi irin zobo da kunun ayya tana hadawa
dashi ko zata kara cabawa ga samu,
Kudin ta bayar aka,sato mata kayan zobo da na kunun ayya ta hada.
Ba bata lokaci aka ganeta mutane suna shigowa,saye tun dai da,zafin ranan da,ke
yawa a garin don ko baiyi sanyi sosai ba ana saye hakana.
Ance rai da kwadai don haka Hanne tafara shawaran canza fridge din ta zuwa wanda
yafi wanda ke gare ta girma don ta kara bun kasa sana,an ta dashi.
Da maigidan ta yadawo ta fada mai ahawaran da tayi shiru yayi don baida na fadi,
don baida na fadi saboda yasan cewa shi kan shi yana amfana da wanan sana,an data
samu tana dan yi yanzu.
Saboda yana tare masu gurare da dama na yau da kullun a gidan har ma,da wanda
bai zata ba don yan zu a lokaci ne muke inda mata suke bada nasu gudun mawa a gida
fiye ma da yadda ba, zata ba a rayuwa




ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,,,,,,
A LOKACIN MU KE,,,,,


MAJI ce kwance a,saman dogon kujeran dake cikin falon dakin ta, ziciyar ta a
cacushe yake mata da bakin da bacin rai ga radadi da zugin da yake mata.
Bakomai ke damun zuciyar Maji ba sai irin halin rayuwan da Allah ya jarabi dan
ta dashi.
Wanda a da can baya ba haka rayuwan shi take ba sai yanzu da girma ya fara shigan
shi ne bakon al,amarin ya fara shigan shi haka.
Hayaniyar da take ji yana tashi daga cikin gida yasa ta sauri mikewa zaune da
sauri, don ta saurara idan dai ba saudakine ya ja mata wani sabin maganan ba kuma a
gidan.
Aikuwa jitayi mama tana fada tana cewa wanan yaro ya dai zama muna masifa a
gidan nan yanzu.
Yaro guda ya zama alkakai acikin yan uwa wai mai saudauki ke son mayar da mutane
ne haka wai, duk yaro abu ba abu ba ya kai mai duka bugu haka har na tsiya.
Sai muryan dayar kushiyarta da take biwa tana cewa ni wallahi karan shi zanyi
akan takalman banza zakaiwa yaro mugun duka haka har ka fasa mai baki.
Anty watau amaryan su tace a,a kada ki karan shi kijira har shi mahaifin nashi
da ya bata shi ya dawo ki fada mai muji ko muga abinda zai yi,
Basu suja batashi ba da so sun dauki son duniya sun dora akan shi yanzu ai ga
abinda so ya jawo masu sun gani.
Maji dake daga daki takai zaune a hankali saman kujeran da ta tashi a kanshi
tana maijin zafin maganganun su a ranta don dai ita tasan a iya yinta ba wani gatan
da ta gwadawa dan ta, a baya fiye da sauran yan uwan shi.
Amma babu yadda zatayi don ance dan kuka mai jawa uwar shi jifa don da bai shiga
harkan yaran su kamar yadda ta hore shi da zafin zuciyar shi akan ya rage da bai ja
mata yawan magana na habaici ba ga kishiyoyin ta.
Wasu irin hawaye ne masu dumi suka fito daga idanuwan ta a hankali, a daidai
lokacin Amira dake cikin daki kwance tafito falon nasu.
Ganin yanayin uwar,su yasata karasawa kusa da ita ta zauna tanavmai kura mata
ido tace yaya sadauki ne ko maji.
Don Allah maji ki fita zancen su ki daina zubar mashi da hawaye malamin mu fa na
islamiya yace muna ba kyau uwa tai kuka akan dan ta musan ma ma da namiji don
Aljannar shi yana ga hannun ki mama don Allah ki yi hakkuri ai ya kamata ace kin
saba da halin shi yanzu ki daina bata ranki a kan zancen shi hakana.
Suma ai daukan magana ne mai yakai su ga kayan shi tunda sun san bai son raini
shi.
Baki maji ta bude da nufin tai magana sai kuma bacin rai ya hana ta iya furta
komai sai taja bakin ta tai shiru, amma duk AmiraA yarinyace karama zancen ta ya
shiga ran ta sosai don haka tai shiru kawai amma a zucuyar ta ba dadi sam wani
kunci take ji sosai.
Har dare sadauki bai shigo gidan ba don yasan abinda yaiwa kanin shi yana can
ana jiran shi dashi cikin gida.
Shi ko yanzu daidai yake jin shi dakowa don ya fahinci daga mahaifiyar su har su
duyan ta ba mai kaunan su a gidan gaba dayan su.
Sai yamma kamar kullun malam Habu yadawo gida ko hutawa ba,a bari yayi ba aka
tare shi da zancen sadauki akan yaiwa Abdul mugun duka wai don kawai yasa mashi
takalman shi na kwallo yafita dashi gurin wasa.
Kai kawai malam habu ya kada yace wanan yaron wanan yaron ya kai min ko ina a
rayuwana wallahi.
Daidai lokacin Maji ta shigo dakin saye da hijjab din ta mai ruwa light green.
Tana mashi sannu da dawowa amma bai karba mata ba,sai cewan da yayi Maijidda
wallahi danki ya zama min masifa a rayuwana .
Kullun har zullumin dawo gida nake daga kasuwa don nasan da zaran nadawo da,wuya
ba,a tareni da zancen shi wanda zai bata min rai ba.
Shiru maji tayi tana,sauraren kalamin maigidan nasu a gaban sauran kishiyoyin ta
yana cewa ki fada mashi wallahi zanyi maganin shi don na lura kamar ma ya fara
shaye shaye ne a rayuwan shi.
Niko bari kiji in har hasashe na ya zama
gaskiya to wallahi ba zan barshi a gidana ba ya bata min sauran yara na na kirki.
Allah ya tsare ya kare Maji ta furta a fili aidama haka kawai zaki iya cewa
bayan shi baki da,wani abin fadi ai,
Bata ce komai ba,sai hadiyan bacin ran da tayi tare da juyawa tana fadin Allah
ya kyauta.
Malam Habu yace ai zai zo ya samay ni zan mu hadu dashi don ba zan yarda
ya,sabauta min yara ba ga banza.
Maji dai fita tayi daga dakin don tasan ko ta,tsaya,babu abin da,zataji banda
bacin rai kawai.
Din haka taiwa kanta kiyamallaini tabar dakin don bazata iya jure sauraren
kalaman mijin nasu ba akan ita da dan ta.
Tafiya take zancen mijin nasu gareta yana ci mata rai don zancen sadauki shi ne
zance mafi muni dake hada ta,da maigidan nasu.
Duk irin kwaram din da,aka,sha a,baya baya akan kishiyoyinta da ita a baya, baya
tayar mata da hankali kamar zancen sadauki da ya taso mata a yanzu,
Yanzu saboda shi tana ji tana gani duk wanda ya kwaso zancen shi akan tane zai
yaba mata don halin dan ta kawai,
A kulun kalaman maigidan ta ga dan ta yanzu yana kona mata zuciyar ta da jikin
ta ba ma zuciyar ta kadai ba,
Ita a,zaton ta ai wanan abin abinda ya shafe su ne baki dayan su bawai ita kadai
za,a dorawa laifin ba don itace mahaifiyar shi ne kawai kowa ke ganin laifin ta ita
kadai.
Abin da ya kamata su taru su nuna bacin ransu a kai su tayata bakin ciki amma sai
gashi kowa ya,zamay yabarta da laifi ita daya.
Amma babu komai ta furta a,ranta tare da hade yawun bakin ciki a cikin ta, tana
mai sauke ajiyan, zuciya kawai.
Bata ankara ba,sai hawaye kawai taji yana biyo mata a idon ta.
Gaskiya zancen Sadauki yana tayar mata da hankali sosai ta rasa wanda zata kai
kukan ta gare shi ya tayata bata shawara a cikin gidan.
Don duk yanzu suna matukar nuna mata kyama akan zancen shi gabadayan su gidan har
shi maigidan kan shi.
Shin may nayiwa Allah da yai min wanan mumunan jerabawan haka akan dan tilon da
daya da Allah yabani namiji a duniya ?
Ni dai nasan harga Allah ban cuci dan kowa ba a rayuwana da wanan jerabawan
yafado a kaina.
Duk da ni marainiya ce na riki maraici na ban kai kaina inda Allah bai kaini ba,
ina zama a matsayina na mara galihu har a gidan aure na.
A hankali ta kara lumshe idanuwan ta tana tuno rayuwanta na baya da kuma irin
kokatin ba yaran ta tarbiyan da takeyi.
Ba komai take kara tunawa ba,sai irin dafin bakin da maigidan su yake mata
a,baya,
Da yakan ce maijidda duk da ba komai ke gare ki ba,a,duniya ni ina sonki a yadda
kike.
Don kina da komai da nake bukata sabida ke ta daban ce acikin matana, ba zan iya
jure rashin mace irin kiba .
Kallo daya in nai maki yana wanke duk kan wata matsalar rayuwana don haka nake
kwadayin samun zuri,a dake don nai alfahari dasu koda bayan rayuwana ne.
Murmushi gami da hawaye ne yazo mata a lokaci guda ta furta namiji kanin ajali.

****** ********* ******
Akwana a tashi yau Bintu satin ta hudu gurin gwago Asmau a garin sokoto.
Kullun sauraren take raji gwago na mata zancen zuwa gida amma shiru kake ji ba
zancen, har ranan ta gaji tai wa gwagonta zancen komawan ta gida amma sai gwago
take ce mata.
Haba Bintu yanzu ke har kina sha,awan komawa gida gurin wanan bakar matan uban
naki mai mugun nufi a kanki ko yaushe.
Nifa da mahaifinki mun yanke shawaran kiyi zaman ki a nan don yace hankalinshi
yafi kwanciya idan kina a guri na ko kiyi ni sa dasu kadan.
Don haka ki kwantar da hankalinki kiyi zamanki a nan ba zancen komawa gida don
hankalin mahaifinki ya kwanta.
Badon Bintu taso ba dole ta yarda da zancen gwago din don tasan haka zancen
yake.
Kullun adduan mahaifinte ke nan akan Bintu Allah ya kawo lokacin da zaki bar
gidan nan zuwa wani guri ke ma ki huta hakana wa rayuwan ki.
Tunda mahaifiyarki ta barki bata damu da damuwar ki ba ko wani hali kike bata
sani ba.
Gaki yarinya natsatsiya duk halarcin da kikewa matar nan da diyan ta kina bauta
masu dare da rana ba gani take ba.
Amma kiyi hakkuri da irin rayuwan da kika tsinci kanki a ciki haka Allah ya
kaddara maki taki rayuwan zai kasance a gidan uban ki.
Hawayen da ya silalo mata ne ta dan sa gefen hannun ta ta share a hankali.
Duk lokacin gwagon tana kallon ta a cikin muryan kuka ta dan dago kanta a hankali
tace to gwago zancen karatuna fa ?
Wanan ba matsala bane ai Bintu zan yi magana a,samo maki makaran tar jeka kadawo
dake can kasan layin mu ta gwaunati sai kici gaba da zuwa ko?
A hankali Bintu ta,daga kai alaman taji ta juya jiki ba karfi zuwa cikin dakin
kwanan su don ta gyara masu saboda yamma yayi kuma,su basu sharan dare saboda ance
baida kyau, yana kawo tsiya a gida.
A kwana a tashi ba,wuya a,wurin Allah Bintu tafara zuwa makaranta kamar yadda
gwago tai mata alkawari a baya.
Da yake Bintu yarinya ce mai hazaka baiwanta daga Allah ne, sai bata sha wani
wuya ba sosai a cikin karatun ta komai tana ganewa yadda ya dace.
Yawan aiken da take mata gidan malam Habu yadan sa tasaba da Maji da yaran ta
don a gurin su kawai take dan samun fuska a gidan ko su ba wani can sosai ba.
Sai dai idan Maji ta aiko sayen masa in har Bintu ce a kan tandar suyan waina
sai ta cika masu kula fam tace akaiwa maman ta.
Haka yasa watarana Maji tasa su Amira su dan yi kwalemar kayan su su ba Bintu
don taga tana da bukatan haka saboda rashin wadatan da basu dashi ita,da,gwagon
nata.
Gwago Asmau batai sanyi a kafa ba gurin shiga gidan don taiwa maji godiya ita da
yaran ta, da suka ba yar ta kyautan kaya.
Ta shiga gidan bayan sallah azahar lokacin Bintu ta dawo daga makaranta ke nan.
Tare suka shiga ita da Bintu din, inda suka samu maji zaune a falon ta kasan tias
din dakin nata tana gyara wani ganye da,alamar magani take hadawa dashi.
Sallaman su yasa ta dan gyara tana mai ansa masu sallaman su da fara,a a fuskan
ta.
Sun gaisa da,gwago inda tafara zabga masu godiya tana mata fatan alheri akan
alherin da sukai wa yarta, Bintu.
Cikin murmushi Maji take cewa ai Bintu yarinyar kirki ce halin alherinta ne yasa
sukai mata haka.
Sun dan fara hira tsakanin gwago da Maji inda gwago ke cewa wallahi nakan so
shigowa mu gaisa da ke, amma kuma yanayin gidan naku ne baida dadin shigowa don
kowa idan ka,shigo sai ya,dinga ma kallon munafuki.
Maji tace haba dai hajiyan masa ai ba yau muke dake ba koma sun zarge ki da
hakan ai su ma mutanen arzikin su suna shigowa gidan nan amma ban damu dasu ba ni.
Gwago tace ai babu komai insha Allahu zan dan dinga shigowa idan na,samu lokaci.
Suka mike suna,wa junan su sallama nan gwago ke cewa ina Sadauki ya yashiga
kwana biyu bana ganin shi dai.
Murmushi Maji tayi tana cewa yana nan baidai zamane suna batun rubuta jerabawan
su na karshe ne shi yasa ba,a ganin shi yanzu.
Allah sarki inji gwago Allah ya taimaka Allah ya bada sa,a Allah ya tsare muna su
daga duk wani abinki dana sheri a rayuwan su.
Amin inji maji inda taji dadi sosai da addu,an mai masa da,taiwa sadauki wanda ta
dade rabon da taji wani mahaluki yai mashi wanan adduan.
Har,zasu fita Maji tace su dan tsaya tazo inda tashiga daki ta dauko masu dan
sabulun wanki da clean cikin irin wanda mijin su yake kawo masu duk sati don wankin
tufafin su.
Gwago tana ta godiya da fatan alheri ga maji suka fito, a tsakar gidan nan suka
hadu da amaryan su tana shigowa gwago na gaishe ta wani kallo ta,watsa mata na ke
wacece ?
Gap da zasu fita daga get din gidan suka hadu da sadauki yadawo ko kallon arziki
basu ishe shi ba sai ma gwago ke ce mai Umar sanda mazan fama andawo daga bokon ke
nan ?
Ya wani sha toka fuska babu walwala ya ansa ciki ciki Maji dake tsaye daga bayan
su data rako su take ce mai bakajin hajiyan masa tana gaida kai ne sadauki
Yace cikin wani murya ai na amsa mata mana ya shigewan shi part din su na,samarin
gidan.
Allah ya shirya ka inji maji ta furta a fili sai gwago tai dan murmushi tace amin
ke dai ai yaran yanzu sai addua kawai.
Ke dai kibi abinki da,addu,a Allah yasa halin iya kurciya ne kawai .
To Amin hajiyan masa halin wanan yaron sai shi wallahi haba bari fafin haka mana
inji gwago ke zaki kara jan abinki ga jiki kina lurar dashi dasannu zai bari ai
wanan kurciya ne Allah yasa takara fadi tai masu sallama ta tafi.
Bayan sun tafi maji taga yadace tabishi dakin shi suyi magana tunda Allah yasa
yashigo a gaban idon ta.
Yana duke yana hada wayan tv tashigo dakin abinda yasa shi saurin dagowa ke nan
daga inda yake duke.
A hankali take bin dakin dake hargitse da kallo sai warin dakin irin na,samari ke
tashi daga dakin.
Cikin ya mutse fuska take ce mashi, yanzu kaiko inda kake kwana baka iya gyarawa
babana ace dakin dan musulmi ne haka inda ake ibada?
Wai may ke damun kane haka babana na zaci kaine mutim na,farko da za,ayi koyi da
halin shi nagari a gidan nan sai dai kasshh ban samu hakan daga gareka ba sadauki.
Naga alamar abinka ba mai yankewa bane, sai a lokacin yadago kai yadan kalli
mahaifiyar tashi yana fadin may kuma nayi yanzu maji?
Yanzu fa na dawo daga makaranta tun safe da nafita gidan nan .
To babana shine baka iya,gyara muhalin ka haka dubi fa kagani ai wanan wani abin
cutarwa ma yana iya shigo maka baka,sani ba.
Zan gyara ya bata ansa a takaice don yasan duk lokacin da tai amfani da kalaman
babana a,gars shi maganace ta kwantar da hankali da fahinta take nufi a gare shi.
Don ba ko yaushe take amfani da kalman babana a gare shi ba tafi kiran shi
da,Sadaukin da kowa a gidan yake kiran shi kamar yadda mahaifin shi yake kiran shi
dashi tun yana karamin shi dashi.
Ta,dan dade a,tsaye tana kallin shi a cikin tausayawa dan nata ga,irin rayuwan
shi

2 / 92