Author : Zainab Idris Makawa Seenabu Category : Complete Novels
fada mashi ba yakara complain
kan cewa ban damu dashi badaine tasa hakan.
A hankali nace na tuba sake ba insha Allahu, abin mamaki sai naji ya kwashe
da,dariya tana is alright hakan ma yafi min don yanzu zan dinga samun ki available,
Uhhm kawai nace cikin murmushi.
Ina dago ido mukai arba da yaya sadauki da ya maka min wata uban harara na kawar
da kaina tare da ci gaba da waya na.
Kabir yace min yanzu yana hanya zai tafi wani gurin aiki ne amma idan ya,dawo zai
kirani.
Nace tau Allah yakaika lafiya Allah ya,tsare min kai.
Ina kara dago ido muka kara arba dashi dole nace mashi cikin yar murya sannu da
zuwa yaya ya hanya.
A daure ya amsa min kamar wanda akasa shi amsawa dole.
Nikan namike zuwa daki sai Maji take cewa ina kuma zaki ba,aci abinci ba nace sai
anjima zanci mama.
Kai Fatima kina dai wasa da cin abinci har yanzu mutum haka bai damu da cin
abinci ba.
Nikan na shige abina daki ban tsaya ta kansuba don wanan mai mugun halin dake
zaune a falon.
Ban dade da shiga ba naji ruwa yakara tsinkewa kamar da bakin kwarya.
A hankali na mike don na rufe window din dakin mu dake bude don feshin ruwan
dake shigowa.
Karan mota naji za,a fita daga gidan mamaki ya kamani wake da karfin halin fita
daga gida a,wanan lokacin da ake tsula ruwa haka masu yawa.
Mantawa nayi ina,son nasha ruwa sai na koma falin na dauka nan nasamu Maji na
magana cikin takaici.
Tana cewa yanzu fita yayi cikin wanan ruwan haka ba ko ina zai tafi ba sai gurin
shegen shaye shayen su.
A duke nake gaban fridge ban san lokacin da na dago ba nace mama yaya ya koma
shane kuma ?
Cikin takaici tace min Fatima bari ke dai, Allah dai ya kawo min saukin wanan
al,amarin kawai.
Abu sai yayi kamar ya sauki sai kiga yaron nan ya kuma koma ma halinshi lokaci
guda.
Nace anya mama wanan abin ba ci gaba ake da tufka ana,wal,wala ba kuwa?
Amirah tace nima dai hakanace daki na koma hankalina a tashe da zancen danaji
mara dadi.
Sai yanzu nagane abinda ya jawa maji ciwon zuciyan da akace yana barazanan kama
ta.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,,,,,
A LOKANCIN MU KE,,,,,
Da, tuna ne na kwanta barci bai dauke ni ba har tsawon wani lokaci ga ruwan da
akeyi ba a dauke ba har cikin dare sai tsula ruwa ake kamar da bakin kwaraya.
Hasken wutan mota ce ta haska dakin da muke0 kwana a ciki nida Anty maryam don
gyaran da akayi dan yi a gidan yanzu.
Part din Maji ne farkon shiga gidan don sauran suna daga ciki suna ganin sun
shiga ciki kusa da part din maigidan.
A hankali na mike zaune na juya inda maryam ke ta barci ta yarda wayanta sai
massage ke ta shigowa mata.
Window dakin na dan leka naga, mai shigowa a lokacin yaya sadauki na hango yana
kokarin rufe motar shi.
Tafiya take a cikin rangaji irin nasu na yan maye kamar zai fadi ya dan dade a
tsaye kafin ya bude kofan dakin shi ya shige.
Na koma bakin gado na zauna zuciyana naji ba dadi ko kadan tausayin Maji ne ya
rufe min zuciya na.
Ina nan zaune naji motsinta hakan yasani sanin cewa batai barci ba idon ta biyu
ke nan tana dakon dawowan dan ta tilo daya da masifa ta haushi na shaye shaye.
Haka na kwana ina matukar jin tausayin ta a raina har garin Allah ya waye muna.
Ranan bamu shiga school duk muna gida gaba dayan mu bayan na gama muna,abin
karyawa don yanzu Maji ta raba muna aiki kowa da ranan girkin ta.
Na fito saye da wani buje da riga dinkin yan Niger, da hjy kubura ta sayo muna
da suka je da Baba ta sayowa duk yan matan gidan hardani na samu shiga.
Ina zama nake cewa mama ina key din dakin yaya mu gyara mai, da sauri maryam take
cewa nikan ba zan iya ba nagaji gaskiya yau hutu nake son yi.
Ina ganin ai yana ciki don banga ya shigo ba Amira tace naga fitan shi da safe da
kayan wasa a jikin shi.
Mikewa, nayi tsam na dauki kayan gyaran wuri na fice daga part din mu nasa key
din hannuna dakin ya bude.
Bin dakin nake da kallo duk da dan sauyi da dakin ya samu an saka mai kayan
zamani a cikin sa.
Kafin na fara gyara na fara aiwatar da nufina da yakaini dakin, daga nan daga can
ina bude wani kwali dana gani saida naja baya da sauri don tsoron da naji.
Kwayoyi ne ciki irin masu tsada da,akai muna lecture a kasan makil a cikin
kwalaye.
Gaba daya na kwashe su da,sauri nakai toilet din dakin na watsa ciki nai flushing
din su suka wuce,
Haka nauwa sauran syrup din da nagani kai duk wani magani sai da na turashi a
toilet din ya wuce.
San nan na,gyara mashi dakin tsab nafito da sauri kafin ya,dawo ina fitowa nazo
na zauna ina jiran yadda zamu kwashe dashi.
Bayan wani lokaci muna zaune sai hira muke kwasa tsakanin mu ya fado dakin
idanuwan shi sun kade sunyi ja dasu.
Yan uwan shi ke mashi sannu da zuwa amma ni ko kallo bai isheni ba don nama raina
da,al,amarin shi gaba daya.
Magana suke mashi amma,bai iya,basu cikaken amsa sai cewa yayi Maji wa ya gyara
min daki na.
Wani kallo ta,watsa mai kamar na tsana tace wakasan yake da,kokarin haka,ba
Fatima ba.
Inda nake zaune da,waya ina game ya,kalla kamar zaiyi magana sai ya kuta kawai
mikewa yayi har yakai kofa yace tare da kallon inda nake zaune.
Ke kawon min abin karyawa na daki zan watsa ruwa ne yanzu.
Maji tace bana son suna shiga dakin ku idan kuna gida bari mana ta mika mai maji
Amira ta fadi hakan a lokacin har na mike ko tsaye don na,shiga kitchen.
Ance abu ga manya ashe uwar ta dan fahinci da,akwai wani abu don haka ta kyale
mu.
Saida na dauki kayan zuwa dakin ta saka hijjab din ta tabiyo bayana batare da
sanin kowa ba.
Ina shiga ban san yana tsaye daga kofa ba sai ji nayi an kai min shaka da karfi
yana fadin Uban wa ya baki izinin shigowa dakina ki kwashe min kaya.
Ina kikai min pills dina yar iskan yarinya kawai mara mutunci.
Idanuwa na,sun futo sunyi ja don matsan da nasha jinake kamar zan shude.
Yakara cewa uban wa ya,aikoki ki kwashe min kayana?
Muryan maji mukaji daga bayan mu tana cewa, ubanka ya turo ta ta,kwashe mara
mutunci kawai sake min yarinya kaji.
Ya sake ni da sauri sai da naji wani iska mai sanyi ya ratsani lokaci guda, ta
juya tana kallona take cewa ina abinda kika kwashe mai din?
A hankali nace mata na,yi flushing din su a toilet sun wuce, tace kwayan ke nan
ko nai shiru ban bata amsa ba.
Ta nuna min hanya tace zoki wuce kinji rabuda dan iska mara mutunci kawai,
da,sauri na,fita zuwa part din mu a hirgice dani.
Azuciya ta ina cewa anya zan iya kuwa wanan irin shaka haka kamar zan shude
lokaci guda.
Na zauna jiki ba karfi sai mazurai nake da idona can sai ga maji tashigo na zaci
zatai min magana amma sai naji tayi shiru batace min uffan ba.
Ina nan zaune sai gashi ya shigo dakin cikin shigan shi na mutunci zaka dauka
wani mutumin kirkine can idan ka gan shi a lokacin.
Magana yake wa Maji babu wanda yaji may yace mata sai dai mukaji tace Allah ya
tsare kawai.
Ba irin yadda ta saba mai addua ba idan yace zai tafi wani gurin.
A,a yayana tafiya kuma zakayi yau bayan jiya kadawo?.
Yace ba dadewa zanyi ba kaduna zan tafi akwai wasan da zamuyi ancan yau da yamman
nan gobe zan dawo.
Har kofa suka,rakashi cikin jin dadi a ran su suna tayi mashi adawo lafiya yana
daga masu hannun shi.
Maji batai min magana ba sai da rana na idar da sallah ta kwala min kira nazo da
sauri ina fadin gani mama.
Samu wuri ki zauna tace min ida na na kai zaune a kasan ties din dakin nata.
Fatima fada min komai kada ki boye min don naga ke kina da hankali kinfi sauran
tunane.
Nafara magana,saiga Amira tashigo hakan bai hanani fasa maganan da zan fada mata
ba.
Nace tun fitan shi cikin dare jiya ana ruwa nagan shi ta,window dakin mu har ya
dawo a cikin maye banyi barci ba.
Naga kuma yashigo da leda yana tangadi haka yasani sanin cewa da kayan mayen ne
ya dawo a hannun shi.
Shiyasa da,safe nace zan gyara dakin nashiga ba fara neman su sai gasu na gani
nan na nuna mata hoton su dana dauka a,wayana dakuma yadda nai flushing din su.
Allah yai maki albarka Fatima, da yanzu duk wanan abin shaye su zaiyi a cikin shi
tayaya wanan bazai wa mutum illa ba wai.
Nan take fadawa Amira tun da yazo rai a bace yana tambayan wa ya gyara mai daki
nasan akwai magana shiya da yace takai mai abinci don ban taba jin yace haka ba
nasan akwai wata a,kasa.
Bin su nayi na,samu ya shaketa wai sai tafito mashi da kayan shi sai gani.
Amira tajuyo inda nake race kai Bintu akwaiki da karfin hali wallahi ai danice
sai kawai na,suma.
Nace niko muddi ina gidan nan anty naga yayi abin shan sa na dauki alkawari sai
nai mai magana.
Baki, gani zai kashe muna uwa da bakin cikin shine anty?
Murmushi Maji tayi sai ta kara jin Bintu ta,shiga mata a,rai sosai fiye dama baya
yanzun saboda ita tai wanan kasadan haka.
Amma a fili cewa Maji tayi kiyi a hankali Bintu kin san karfin ku ba daya,ba
dashi badon Allah ya kawoni ba da Allah kadai yasan irin dukan da zai maki kan
kayan mayen shi.
****** ********* ******
Tuki yake amma zuciyar shi sai faman tukuki takw mai yana kitayatta idan ya samu
sa,an Bintu irin dukan da zai mata watarana.
Haka ya isa ya kira maji tana kallon kiran shi amma taki daukan wayan nan ya gane
har yanzu fushi take dashi ke nan.
Da yamma ma bayan sun gama,ball yakira sai Bintu dake falon ta dauki wayan tasan
shine amma sai cewa tayi mai wayan bata kusa ta kashe wayan kit.
Haushi da takaicin yarinyar suka rufe shi a lokaci guda yace a fili, I will deal
with dis girl.
Bari na dawo zata sha mamakina don naga akwai raini a kanta.
Ance kowani mahaluki danasa irin baiwan sai dai wanda ya,rena nasa kawai amma
kowa da irin wanda,Allah yai mai.
Hakane ga,sadauki don yanzu yana cikin matasan da kasa ke alfahari dasu a fagen
kwallon kafa.
Don idan yana a cikin kwallo Allah na bashi sa,an jefa kwallo ga raga, yaci duk
tsananin wasa idan ya kama sai yakai gola.
Suna gama wasa washe gari ya kamo hanyan sokoto bai iso garin ba sai zuwa yamma
sosai ya iso gida.
A lokacin muna,gyaran falon Maji duk da,ba aikina,bane amma ina tsaye ina,taya
anty maryam mofing din kasa.
Sallaman shi yasa gaba daya suka juyo kan shi suna,mashi sannu da zuwa.
Amma banda ni da na zage ina,aikina hankali a,kwance.
Sadauki ya samu kujera ya zauna akan daya daga cikin kujerun falon nan suke ta
tambayan shi ya hanya ya wasan su na can.
Naso na share shi don ina cike da takaicin makuran da yai min jiya kafin ya tafi
tafiyan dayayi.
Sai nai tunanen bari dai nagaida shi kodon mahaifiyar su dake zaune din bata,rage
ni da komai ba na rayuwa.
Don yan magana,sunce ko lahira wani tana cin albarkacin wani, na dan waiga gurin
da yake zaune ya wani lumshe idanuwan shi nace.
Sannu da dawowa ?
Tankar a mafarki ya tsinkayi zakkakan muryan na ina,gaidashi.
Da sauri ya,wani bude idanuwan shi, yana kallo na na zaci ba zai karba sai naji
yace yauwa.
Ban kara bin ta kan shi ba naci gaba da,abinda nakeyi a lokacin, ganin da nayi bai
bar cikin falon ba yasa na aje mopan ina cewa anty maryam ki karasa sauran zan
shiga ciki.
Dakin mu na nufa duk da magariba ne amma sai na,fada kan gado in tunanen ashe
kuwa zan iya taimakawa Maji kuwa.
Shigowan Anty maryam din daki yasa ni dakatar da,shawaran da nakeyi a lokacin.
Tace lalai ma Bintu watau gudowa kikayi kikaki karasa,min aikin ko?
To tashi yaya yace ince ki hado mai abin sha yasha kafin ya tafi sallah.
Nace anty ke mai zai hana ki hada mashi nifa ban iya masifan shi wallahi.
Mutum ko yaushe a murtuke kamar mugu sai faman bakin rai da hararan mutane.
To naki yake so ai yana ganina,baice na,hado mashi ba,sai ke, yake son
ya,wahalal.
Ta fadi hakan cikin yanayin zolaya tare da yin dariyar keta a fili tana ta
darawa.
Nace wallahi anty badon mama ta haife shi ba,sai nace yayi gadon mugun ta,sosai.
Maryam ta juya tana fadin lalala haka,kikace mashi bari naje na,fadawa Maji kince
yayi gadon mugun ta a,gurin ta don haka,baki hado mashi.
Da sauri na mike na,sha gaban ta ina cewa don Allah anty yi hakkuri kada ki
hadani da mama barin fito na kawo mashi.
Dariya tasa min tace koke fa aikw ce da shegen rashin ji kike taba mai kayan shi.
Na,jera ruwa a jug da,cup cikin dan tiren su na,roba nafito mashi dashi falon .
Yana zaune a,falon har wanan lokacin ya,dauki kafan shi daya,ya,dora,a,dayan
yana,kallon news din da ake a,tashan NTA.
Na kai turen gaban shi na aje da zuman na bar gurin.
Yace waye zai zuba ruwan da kika girke kamar wata,bakauya haka dake sai shegen sa
ido.
A ya,tsine nace ai dama yar kauye ce ni.
Yace ke baki da kunya fa don naga kina,son raina ni a gidan nan don kin samu
guri.
Nace a hankali badai a,guri ka,na,samu gurin ba ai, da hanzari na,mike na,shige
ciki kafin ya,furta,wani abu.
Nan na barshi baki bude yana mamakin da,alajabina sai ya kuta,
Yana kutawa daidai Maji tana,fitowa da,alwalan ta,do ita,saidai ta jira kiran
sallah kullun haka dabian ta yake.
Ta bishi da harara tana cewa kada ka,soma taba min yarinya wallahi za,ajimu dakai
a gidan nan.
Da,dare muna,zaune abinci kowa ke ci sai gashi ya shigo falon wanan karon ya
canza kayan jikin shi zuwa wasu kanan kaya masu matukar kyau na maza.
Ya zauna ba,wanda tai azancin mikewa ta bashi abinci nima da nake taimakon shi
ina,bashi sai na,share shi kawai don yanzu ban ganin kimar shi kaman da can baya.
Waya na dake gefe yai kara don haka nakai hannuna da sauri na dauka don ganin
kowaye mai kira,na.
Kabir ne, yake kirana da,sauri na dauka don kada kiran ya tsunke a lokacin.
Da murmushi a,fuskana nake cewa Assalamu alaikum sahibi rayuwa,
Ya,amsa da cewa haba Fatima kishin ruwan rashin jinki da,ganin ki yana,son
illantani amma,ke ko a jikin ki baki damu daki kirani ba.
Na dan langabe kaina kamar yana,kusa dani nace, cikin yanayin tausayawa.
Nace wayyo Muhammad Kabir dina,wallahi ba,haka,na,bane kasan yanayin karatun
dana,fara ne ba hutu yanzu, amma nima na damu da na gan ka ai.
Ya ce hummm saika ce dagaske Fatima keda har yanzu baki iya,sakewa dani idan ina
kusa dake.
Ni dai yanzu ina,rokon ki rage wanan masifan kunyar taki haka,na adan bani gurbi
nima.
A hankali na,dan saki wata,yar dariya mara sauti nace yadda kake jin rashi na a
kusa dakai hakana nima yanzu nake jin naka ai.
Yace aiko danafi kowa sa,a a duniya zukekiyar yarinya kamar ki tana jin kewan
tsoho kamana haka.
Maganan shi ta,sani yar dariyar da ban tashi yi ba tare da langabe kaina a
hankali saman kujeran da nake kusa dashi.
Wani irin tsaki mukaji ya,sake tare da,mikewa tsaye yana fadin maji ni zan dan
shiga gari sai da,safe.
Tace abincin fa,bazakaci bane yace No abarshi kawai tea zan sha idan nadawo.
Ya fita maji na fadi zaka gurin mugun halin naka ko don nasan dai can ka nufa.
Baice uffan ba sai yar guntuwar murmushin da yayi iya yake.
Yana fita daga falon maryam tace Bintu yanzu gaba,daya kin canza daga Bintu kin
koma wata mara kunya,can dake.
Wayan ma,a,gaban mutane kike ba,kunya,ba tsoron kowa, Amira tace barta sai
watarana yaya ya,fasa wayan nan din karamar aikin shine hakan tambayi maryam kisha
labari.
Nace aiko da,ya,biya ni koda yake inma ya,fasa,aishi ya,saya,min dama shikw nan
yayi amai ya lashe ke nan.
Nan suka,sani gaba suna min sheri wai suna son gani Kabir din nan daya sace min
zuciya haka,ya,mayar dani wata,mara kunya haka.
Nace anty Amira,bafa yaro bane matan shi biyu da yara,biyar.
Kafin nakara,furta wani abu sukace a lokaci guda mata,biyu da yara,Bintu ?
Shine har kike wani rawan kai haka akan mai mata da,yara baki tsoron kishiya ne
ke?
Nan na,basu labarin irin takakan da matarshi takawo min hargidan mu a,kauyen mu.
Cabdijam wallahi kin fara,gani ke nan may ke cikin auren mai mata yanzu
banda,tarin rashin kwanciyan hankali.
Nace cikin yar murya,to anty wanda ya samu badashi za,ayi ba idan hakane yafi min
zama,alheri arayuwana Allah ya,tabbatar min.
Amira,tace wallahi kina,da karfin hali ashe haka Bintu nikan danice da tun zuwan
matarshi gidan mu mun rabu dashi wallahi din alama,ya nuna ko a gida,akwai
matsala,ke nan.
Kafin nai magana,sai mukaji maji tana cewa, ke kada ku zugata Alkah ya,hana,auren
mai mata,ne halan.
Idan ku bakuyi ita da,tasan ciwon