Advertisements
Chapter 34 Reading A Lokacin Mu Ke by Zainab Idris Makawa Seenabu BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

A Lokacin Mu Ke by Zainab Idris Makawa Seenabu

Author :  Zainab Idris Makawa Seenabu Category :  Complete Novels

Chapter   34 / 92

99K to 102K   out of 275.8K words

har muka je dakin da yake kwance.
Baba na yana kwance sharkaf dashi sai nishi yake guda guda suna mashi sannu kafin
ma nai magana mama tabawa tace kai Bintu akwai ki da,shiririta wallahi.
Tun dazun ga mutumi yana wahala kin tai kinyi zaman ki baki dawo ba nace mama
wanda zai kawo min kudin ne baizo ba har yanzu.
Tace ba Kabir din yace ya basuwa ba shiko mi tsaidashi hakana wai ?
Muryan yaya sadauki dake kallon dakin cikin kyankyami yake cewa wai may sukace
yana damun shi ne?
Sai lokacin nace mama ga mamana nabirni da nake wurin ta ta sun zo da yaranta.
Tace ayyo Allah sarki kuna sannun ku da zuwa to a,a hanya yaya sauran jama,an
gurin ku,
lafiya suke inji maji, ta amsa mata akaice.
Kara tambaya yayi tare da matsawa gurin Baba ya kura mai ido a ran shi yace ashe
agun shi wanan yarinyar ta,kwaso fari haka.
Ga mutun cikin wahala amma farin shi yana nan bai gushe mashi ba natural skin ke
nan
Yace wa Babana may ke damun ka ne Baba?
A hankali Baba na ya nuna maran shi da hannun shi da kyat.
Yace shit kun aje mutun haka a kazamin guri haka yana ra wahala ciwo daban magani
daban .
Ina likitan yake naji may sukai mai anan don musan inda za,a dora akai.
Yajuya zuwa gurin likitan muka taka mai baya ni da maryam har zuwa,dan dakin da
likitan ke zama ko shi a kazance yake gurin.
Yana ganin mu zai fito yafara,washe bakin shi duk goro yasa shi yana fadin ,a,a
malam Bintu yau baki mu kayi ne ?
Sun zo duba jikin Baba na ko ?
Yaya sadauki da haushin yadda dattijo kamar wanan ke wasan baki wai yaga yan mata
yace don Allah likita muke nema?
Yace mallam ai ni incharge din gurin ka wani kallo yaya,ya,watsa mai yace ina,son
in san may ke damuwan bawan Allah nan mahaifin yarinyar nan ya nuna ni sai malamin
asibitin yace Fatima Bintu yar ma,aiki.
To gaskiya dai munan in munce ma ga ciwon daka damun shi munyi karya abu gudana
dai mun bashi taimako don ya dan samu karfin jikinai kawai.
To idan babu damuwa zamu tafi dashi birni yau aje aga may ke damun shi a can yace
gaskiya na hakan yana da kyau sosai walleh.
Ko ina zamu iya samun motan da zata dauke shi ya tambayi likitan yace in anyi
sa,a za,a iya samun mota bakin yar kasuwa inda motoci suka tsayi.
Bai tsaya jin komai ko gidiya ba yajuya muka bi bayan ahi sai likitan ke
cewa ,a,a Fatima Bintu yau tafiya za,ayi abar mu.
Daga inda yake munajin tsukin shi mudai bamuce komai ba muka bishi maryam ta
shiga gaba ina baya sai inda motoci ke tsayawa a kauyen namu .
Munyi sa,a kuwa don mun samu mota daya a layi zasu tsaya dogon jinga dashi yace
ko nawane zai biyasu azo a tafi kawai.
Muna zuwa ba adauki lokaci ba muka kama hanya sai sokoto da Baba dake kugin ciwo
ba barci kwana da kwanaki gareshi dama mu masu jinyan shi.
Direct asibiti muka nufa dashi yashiga ya fita nan da nan likitoci suka taru kan
babana suka,fara binciken matsalar shi.
Sun fara bashi taimakon gagawa tare da,wasu allurai da suke ganin ya dace dashi
sai gashi ya samu barci cikin dan lokaci kadan.
Muna nan har dare yana barci sai ga yaya da,wasu samari biyu yan uguwar mu yaran
shi ne don nakanga suna mashi abu yace muna mu tashi muje gida jinyan namiji sai
maza.
Komai ya,sayo ya masu na bukatan su da ma wanda zasuci jiki ba karfi na mike
nabisu muka tafi har da mama ta bawa mukazo gida da ita.




ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU

IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,,,,

IN KIN TURA MA WASU DA BASU BIYA BA DON KIN BIYA , ALLAH YA ISAR MUNA AKAN KI,,,,


A LOKACIN MU KE,,,,,



Tun da safe na farka na shirya abin karyawa, da za a kai asibiti na tayar da mama
tabawa,ta shirya don mu tafi tare.
Dakin mama na leka har lokacin zaune take saman salayan ta ta azzakar a gurin.
Na fara gaida ita nake cewa mama zamu tafi asibiti mu dubo Baba na kuma shirya
abin karyawan su.
Kai ta,gyada min tare da daga min hannu alaman a dawo lafiya ta nuna min post in
dauki kudin mota a ciki.
Mun fito lokacin duk su Amirah suna barci abinsu hankalin su a kwance sukan.
Ban san ya akayi ba ko yaga fitowan mu ne, muna tsaye daidai inda zamu samu abin
hawa sai ji nayi ana horn daga,bayan mu, ban so juyawa ba amma jin horn din yai
yawa yasa ni dan waigawa.
Sadauki ne zaune cikin haddadan motar shi yana saye da kayan wasa farare sai dai
wadon dogo ne har kasa haka ma rigan maidogon hannu sai jan da,aka,sa,daga gefen
kafada zuwa hannun rigan layi biyu.
Fuskan shi a,daure tamau dashi kaman bai taba dariya,ba ganin ya,tsaya,a gaban mu
kuma baiyi magana ba na gane may yake nufi.
Bude motar nayi nace wa mama ta bawa ta fara shiga, ta sa kai tana fadin
bissimillahi rahamanin rahim, ina kwana Alhaji ?
Bai amsa mata ba don baiyi tsan manin da shi take ba, sai da ta gyara zama da
kyau nima na shiga bayan na zauna tare da rufe marfin kofan mota,
Wani kyatci naji yayi tare da,furzo, iska daga baki irin na jin takaicin wani din
nan.
Ya wani fisgi mota da karfi yan mintina sai gamu bakin UDUTH asibitin koyar
da,kwararun likitoci na wanan nahiyar.
Na bude wa mama tabawa ta fara fita daga cikin motan nazo zan fita tare da daukan
basket din da muka zubo abinci a cikin shi yake cewa.
Yarinya,baki sanni ba har yanzu zaki rena min wayo bakauyar banza kawai ni driver
gidan ku ne.
Naji zafi zagin da yai min amma sai na,share don dan ni ya,taimaka muna nakuma zo
abin kunya ana jin harshe na sama tare dashi bai yi ba.
Amma badon taimaka wa mahaifina da yakeyi ba da yau ba abin da zai hanani rama
zagin da yai min harda cewa gidan mu.
Gidan mi koda muke tallakawa ai muna da mutunci a idon duniya don bamu da abin da
za,ai muna fade, a kanshi sai talauci halittan Allah kawai.
Mu, muka fara shiga dakin da babana yake kwance aciki muka samu mata san suna
mashi wanka dole muka dan zauna daga waje har agama mashi wankan.
Muna nan zaune shi bai karaso inda muke ba sai zuwa can na hango shi tafe da
leda a hannun shi ya nufo dakin.
Bai muna magana,ba ya zo ya,shige kamar nace kada ya shiga a gyara baba ne ashe
yasan an gama,shirya shi, shine yazo kai tsaye ya shige dakin.
Can dayan matashin ya leko yana fadin ance ku shigo angama muka mike sai cikin
dakin baba yana zaune Sadauki yana gaban shi yana mika mashi abinci a plate.
Mamaki nayi dana samu ya na tsaye a gaban gadon yana shayar da babana abin
karyawa da kan shi.
mamaki ya rufe ni a cikin raina yadda sadauki mai daukan kai, mai izzan tsiya,
mai fadin rai kamar wani mugu can akoda yaushe ba alaman rahama a fuskan shi ko
kadan.
Amma kuma wai shine tsaye yake shayar da babana mutumin kauye tallaka mai jiran
Allah ya kawo aci.
Tun daga kofa mama tabawa cikin muryan yan kauye ana magana a na daga murya take
fadin a,a malam kan jiki yai kyau wallahi kaga ikon Allah.
Nan muka shiga gaishe su tare da,matasan nan biyu da suka kwana da Baba na a
daren jiya sai lokacin na fahinci cewa wata kila hayan su akayi don suyi wanan
aiki, a biyasu kudin su.
Lokaci ne, komai mairai yana gani a wanan zaman da muke a cikin sa haka.
Da kudin sai ka zama sarkin dole saboda yanayin lokaci mai kudi yafi basarake
daraja a idon al,umma.
Suma kansu sarakunan suna zubar da kimar su don kwadayi ga tallaka bawan su don
kawai kwadayin kudi .
Sai da,Baba na ya,shanye tea,din tas sadauki ya,barshi yana,mashi sannu nan yake
cewa matasan nan zasu iya,tafiya,gida su dawo .
A tare suka,fita,dashi ya nufi gurin likita inda ya samu bayanin matsalar dake
damun Baba na dole sai an mashi, theater.
Bai muna bayani ba kada hankalin mu ya,tashi don haka yaja bakin shi yai shiru sai
da gwago mai masa,tazo yai mata bayani abinda za,ayi kuma a gobe za ai mashi aikin,
Da farko gwago taso ta,rude amma yana daga,mata hannu yace dakata mai masa ban
son abin tashin hankali shiyasa na kiraki don na,fada maki saboda zaki fi su
kwanaciyan hankali ke.
Tace tau sadauki yanzu may ake ciki yace zamu tafi tare dakw ne ki saka hannu a
matsayinki na yar uwar shi.
Tare suka tafi gwago na ta,saka hannu akan aikin da za,aiwa babana gobe da dare.
Washe gari naga shiga da ficen da yaya sadauki yake a kan Baba na yai yawa amma
sai na dauka don halinshi ne taimakon yasa yake hakan.
Washegari ranan aikin ina sauri na tafi asibiti mama take ce min dakata, Fatima.
Sai gabana ya fadi ras,ras tace bari nazo mu tafi tare kuma ban son abin tayar da
hankali idan mun tafi ki natsuna sosai banda shirmay.
Nace tau, tau,mama gaba na sai faduwa,yake ina ganin kaman wani abu ya samu
babana boye min kawai akeyi.
Itako mama ta bawa sai hira take cikin daga murya ba abinda ya samay ta kamar
wagara.
Mun samu har anyi mai theater an fito dashi ko sadauki da,yaran nan suna zaune a
gaban shi cirko cirko.
Wani kallo cikin tashin hankali muke yiwa Baba dake kwance sharkaf saman gado
kamar baida rai.
Da,sauri na isa gurin shi ina cewa baba may ya samu baba ina kokarin fasa kuka a
lokaci guda.
Hannu ya daga min cikin daka,min tsawa yake cewa ke shout up please kada ki muna
kuka anan please.
Aiki, akai mashi baya son damuwa Fatima mama take fada min haka daga gefena da
take tsaye tana,kallon yadda yake sauke numfashin shi a hankali kamar zai shude,
Ranan a haka muka wuni cirko cirko tsaye cikin tashin hankali don ance irin aiki
da akai mashi is hard aiki matsala,sosai ake samu idan ba,ayi a hankali ba don a
marayan maza akai mashi aikin.
Gaskiya wanan jiyan banda abinda zance wa mutanen gidan mu (gidan maji) don ba
karamin kokari sukai min ba kan ciwon dake damun babana ko aikin shi tsada gare shi
sosai.
Kwana uku da yin aikin ya,samu sauki sosai don yanzu har zama yake yadan dauki
lokaci a zaune.
Sai dai ya,wani irin ramaywa yai baki sosai sai ya koma,wani dogo dashi.
Da,sallama na,shigo dakin da,yake ban zaci cewa yaya sadauki yana dakin
ba,a,wanan lokacin don bai faye shigowa da,rana haka ba.
Jin sallama yasa su juyowa su na kallo na har da baba na dake zaune ya dago kan
shi da sauri ya dan saki murmushi yace Bintu ke tashi?
Na tambayi maman ki tace min ke kwanta kin samu barci.
Nace baba na dan kwanta barci ya dauke ni kaina ke ciwo shine na dan kwanta
kadan.
Yaya dake zaune kusa da babana a bak8n gado ya bashi gassashen kifi yaji hadi
yana ci a hankali .
Baba na Yace tai zuwa ki nemi paracetamol ki sha keji, kada ya kaiki kwance.
Nace tau baba yace ki tai gida ai na gode wallahi Alhaji karami yai min komai
duniya da lahira, wadda sunkai min suma Allah yai masu.
Mutum baka hada komai dashi ba zanan mutunci dai yai maka haka aiko ankai Allah
dai ya kara daukaka da darajja.
Duk wanda ke gurin aka amsa da Ameen mamatabawa tace ai halin yarka na yya jja
muna wanan alherin haka.
Shidai mikewa,yayi yafita,daga dakin har yakai kofa ya tsaya,batare da,ya juyo ba
yake cewa make sure kin bashi maganin shi ida uku tayi.
Ya sa kai yafita can sai ga wani leburan asibiti ya turo kofa yace ga magani ance
nakawo wa Fatima wai natane ta duba yadda aka,rubuta tasha.
Mamakin wanan sauyin rayuwa na yaya,sadauki ba ni kadai ba kowa na,mamaki ya koma
wani salihi rashin yawan maganan shi ya karu mai.
Sai yana yawan aikin alheri sosai ga alumma mabukata da,rabon su ya ratsa
ta,gurin shi ni dai zan iya cewa gaskiya alhamdullahi don rabon mu ya,ratsa aljihun
shi tunda,mahaifina ya samu lafiya,a sanadin shi.
Don da akauye yakw sai yadda Allah yayi dashi kawai a can don ance mutum bai
mutuwa,sai kwanan shi sunkare.
Sosai babana ya samu sauki gashi daga Alhaji har maji da yaranta zuwa mutanen
gidan su sunzo duba ma mahaifina.
Wasu dai gulmane wasu kuma tsakani da Allah ne ya kawo su.
Kabir yazo nan asibiti ya samu baba tadan jima gurin tsaye shi bai zauna ba don
girmamawa,
Yana batun wucewa,ne yaya,sadauki ya shigo dakin yana saye da, sworth farare masu
kyau da tsada a jikin shi farare zakace ba dan hausawa bane kan shi yaji oil sai
sheki yakeyi mai, kafan shi cikin bakaken cover shoes masu tsadan gaske ga agogon
da,ya,daura mai matukar tsadan gaske.
Hannun shi yana,rike da dan key din motar shi yana juyawa a,hankali, yana shiga
dakin yaga Kabir a zaune ya,sheda shi sosai ya gane shi.
Su mama tabawa aka,shi gaida Sadauki da yi mai barka da zuwa yana,wani amsawa
cikin basarwa,yadda halinshi mai kama da kyankyami yake.
Kabir daga inda yake tsaye ya kurawa babana ido yana barci yajuyo gurin miskilin
yana mai mika mai hannu don suyi musaba,a irin ta addinin musulunci.
Yace mai sallamu alaikum cikin mika mai hannun shi kamar mai jin kyamar hannu ya
wa i basar tukun ga hannun kabir a mike can cikin sham kamshi ya dan mika mai hannu
tare da,basar wa suka gaisa.
Duk da abin baiwa Kabir dadi ba ama sai ya shaye ya,dakw yana cewa sannun ku da
kokari fa Allah ya,saka maku da,alherin sa.
Kamar bai jiba ya juya yana cewa ni zan tafi idan ya tashi ku kira likita yace a
kirashi akwai abinda za,aimashi.
Daga haka ya fice dakin ni ina daga waje ban ma san yadda suka kwasa ba a cikin
dakin.
An dan jima kadan Kabir yafito daga dakin nan na mike nazo ti mashi rakiya zuwa
inda motar shi take.
Mun dan fara,tafiya,yana cewa,gaskiya jikin yai kyau don da,Alaman aikin anyi
sa,a sosai gare shi.
Nace sai dai Baba ya ji jiki sosai wallahi ya dai samu gatane shine har yai
saurin murmurewa haka.
Sunana naji yakira, murya a sanyaye yace Fatimatu don Allah may ke tsakanin ki
da,wanan yayan naki na nan garin wanda ya shigo dazun ina ciki.
Nace wa ke nan don ban kula da,wanda ya shigo dakin ba ina can baya ni.
Yace wanan da,muka,taba gaisawa dashi acan gidan ku mana wani farin guy haka, mai
dan tsawo kadan, mai karfi haka.
Nace,wai duk wanan kwatancen haka yaya sadauki ne mana dan mamana na,garin nan
shi kadai ne danta namiji a duniya.
Kuma dan kwallo kila ma kana jin sunan shi don har kasan waje yake fita wasan
kwallo sosai.
Nace ummumm wama suke kiran shi ne da,guy name din yan kwallo sai can na tuna
nace U F sukekiranshi.
Yace au shine dama UF dan kwallon jahar nan tamu lalai ina jin sunan shi ko sosai
wallahi a lailai guy din dollars sun zauna don yana kawo wuta sosai ga kasan nan
anaji dashi.
Nace lalai ma ni ban damu da harkan kwallo ba balle nasan wani abu acikin sa
sosai.
Sai tambayan da ya jefo min ta bazata na a kunnuwa na yana fadin to may ke
tsakanin ki da shi Fatima.
Da,sauri na juyo tare da,dakatawa,da,tafiyan da nakeyi nai may tambayan hausawa
tambaya cikin tambaya.
Nace washi yaya sadauki din yace sunan shi kuma ke nan ko nace eh UMAR FARUQ yake
shine ma,anan UF din ai yace ok.
Nace sai ban fahinci tambayan da kai min ba nacewa may ke tsakani na dashi nace
yayana ne mana, dakin mu guda dashi ai dan fa mamane na fada maka tun farko.
Yace nasani kin fada min, shima yaja ya tsaya wuri daya tare da fuskanta na
da,kyau.
Fuskan shi ta nuna min damuwa acikin ta karara nace ba wani abu a tsakani da shi
sai yan uwan taka kawai, amatsayin yaya yake gare ni.
Sai naga yai murmushi mai ma,ana da magana can ya nisa yace badon na fadi wani
magana ai fushi dani ba dana fadi abinda nagani a zuciyar shi.
Nace kaga yana matukar jin haushi na ko wallahi haka yake mugu ne tun da nazo
gidan su zama yani gaba da hattara da tsangwama.
Shi kullun yar kauye da munafuka yakw ce min don kawai yaga mama tana so na.
Fatima nace na,am sai yayai shiru can yadan harde hannayen shi gaban kirjin shi
tare da kallo na ido da ido yace .
Wanan yayan naki sadauki yana son ki na hango kishin ki karara a kwayar idon shi
wanda ba kowa ne zai fahinci hakan ba sai wanda ya kwantar da hankalin shi sosai
zai gane hakan.
Wani kallo nai mashi na amma baka san komai ba nace, haba yaya kabir har may ya
rufe maka ido yasa ka fada min wanan magana haka.
Mutumin da ko kashe ni yana iya yi don haushi da takaici na da yake ji zakace wai
yana so na.
Ni may ma zanyi da wanan may bakar zuciyar kamar arnakun farko.
Wai tsaya ko don kaga ya taimakawa mahaifina ne yasa ka fadi wanan maganan?
Nasan ba,shi yai niyar hakan ba uwarshi ce ta sakashi yai taimaka muna don tasan
yana taimakon mara shi a gari.
Yace to is OK tunda baki yarda ba amma watarana zakice nace nidai don Allah ki
rike min amanan kanki don wallahi ina tsoro don zantafi zuciyana

34 / 92