Advertisements
Chapter 90 Reading A Lokacin Mu Ke by Zainab Idris Makawa Seenabu BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

A Lokacin Mu Ke by Zainab Idris Makawa Seenabu

Author :  Zainab Idris Makawa Seenabu Category :  Complete Novels

Chapter   90 / 92

267K to 270K   out of 275.8K words

,
IDAN KIN BIYA KIKA TURAWA WANDA BAI BIYA BA MUN BARKI GA ALLAH, , , ,


A hankali na sako kafana waje wanda don samun daula yai wani lub lub dashi fari
fatte gwanin ban sha, awa.
Yan uwane da abokan arziki birijit a gidan ba masaka tsinke a ko ina na gidan sai
motoci xa suka haraban gidan da wajen gidan.
A hankali ya zagayo inda nake a tsaye ban yi aune ba sai ganin yan jonarlist nayi
a gaba da kayan aikin su.
Nan suka fara jero min tambaya ina rike ga hannun sadauki daya makale ni.
Sun fara da tambayana suna na da alkata dashi na fara da sallama irin ta addinin
musulunci wanda ni ban san ma wai hausa ya canza salo ba inji mutanen dake gurin.
Nace sunana Fatima Abdullahi mata a gidan Umar faruq da ake kira da UF dan wasan
kwallon kafa na international.
Sukace hajiya wani irin farin ciki zaki nunawa mutane a wanan tafiyan da duniya
ke ganin kunyi da maigidanki mai tarin nasarori a cikin sa.
Nace to Alhamdullahi don gaskiya bazan iya nuna farin ciki da dadin da naji ba a
cikin wanan yanayi da muka samu kan mu a cikin sa ba.
Sai dai kawai nace nagodewa Allah ubangiji da yakai mijina a cikin wanan matsayin
tare da kara godewa Iyayyen maigidan nawa wanda da taimakon adduan da iyayye ke
muna muka kai ga wanan matsayin da muke ciki a yau.
Nace ina matukar alfahari da godewa Allah da kasancewa mijina a cikin wanan
matsayin da ubangiji ya nufe shi da zama a yau.
Ina ma kowa fatan alheri a rayuwan shi da fatan kara samun nasara ga duk wani
abin alheri da wani ke bukatan yi a rayuwan shi.
Mutanen da suka zo taron mu kuma ina mika godiya na a gare su akan lokacin su da
suka bayar gurin nuna muna farincikin su a gare mu Allah ya mayar da kowa gidan shi
lafiya.
Nan suka juya zuwa gare shi suna tambayan shi nashi farin cikin da zai nuna
shima.
Mai interview din yace Umar faruq Abubakar kayi namijin kokari sosai gurin haska
muna kasan mu ga idanuwan duniya a matsatin ka na babban da wasan duniya da ake ji
dashi a wanan lokaci tare da kuma jawo wa kasan mu nasarori gurin harkan ci gaban
ta.
Wanda a yanzu babu abin da zamu ce sai mu maka godiya don wanan halakar nasarorin
da kajawo wa kasa zata kawo ragewan zauna gari banza ga matasan da suka gama karatu
babu aikin yi a tare dasu.
Yace insha Allahu haka nake fata don wanan kamfanonin da za, a bude zai bukaci
ma, aikata kimani dubu ashirin da biyar a ko ina na sassan kasan nan maza da mata
indan har mutum yana da takardun da muke bukata a gare shi.
Dama wanda baiyi zurfin ilimi ba za, a samu daidai dashi asaka shi a inda ya
dace.
Mai tambayan yace masha Allahu mujin dadin jin wanan dibin nasaran da kasan mu ta
samu ta dalilin ka wanda muke fatan samun haka ga sauran matasan kasan nan masu
kishin zuci kamar ka nan gaba.
Sai dai baza mu barka haka ba ko zaka iya fadawa duniya da masu sauraren mu ko
shekaran ka nawa a yanzu.
Sai da yai dan murmushi tare dan jawoni a jikin shi kadan yace yanzu shekarana
talatin da daya cif insha Allahu.
Yace yayan ka nawa matan ka nawa ?
Yai dariya tukun yace matata daya gata nan a kusa dani kana ganin ta sai yaro na
daya Amir wanda yaci sunan mahaifina watau Abubakar.
Yace itace matarka ta farko ko akwai wata a gaban ta?
Yayi murmushi yace itace mata ta tafarko kuma ta karshe .
Don yar uwata ce aure mukayi na zumunci da ita wanda ta zama muna aure na soyayya
daga baya.
Hakan yasa mutanen dake tsaye suna kallon interview din wasu suka numfasa daga
gefe don jin abinda yace .
Mai tambayan yace daga karshe wani irin godiya zaka mika ga mutanen da suka taru
a nan saboda kai.
Ya dan murmushi tare da daga kanshi ya kalli inda mutane suka taru don shi yace ni
Umar banda abinda zance wa tan uwa da abokan arzikin da suka taru a nan don ni
kawai da iyalina.
Sai dai nace inawa kowa fatan alheri a rayuwan shi kamar yadda suma suka taru
anan don ni da iyalina.
Ina ma kowa fatan alheri shima mutumin yace na gode da lokacin ka da ka bamu
shima yace ya gode.
Nan suka jaye kayan aikin su suka bamu guri inda muka shiga gaisawa da mutane
dake jiran mu a haraban.
Can na hango anty Amira da wani dogon mutum a tsaye daga gefe daya na zare
hannuna daga rikon da sadauki yai min na nufi gurin ta.
Da dan sauri na na rugumota a jikina itama dai ba laifi ta riko ni din tana dan
murmushin yake a fuskan ta.
Nace anty nayi missing din ku mun samay ku lafiya tace mun dai yi missing din dan
uwan mu kawai Bintu.
Nasan magana ta fada min don tana fadan haka bata tsaya ba ta wuce zuwa gurin
sadauki mutumin yabi bayan ta tabar ni a tsaye nan.
Naji an dafa kafada na ina juyawa anty maryamce tace kada ki damu don ko kin saba
da halinta yanzu ai.
Shigowan su Nafisa ya katse muna zancen mu nan suka rugumoni da farin ciki suna
fadin kai matar yaya kin bamu kewa wallahi sosai.
Barin Nafisa da mutumin da take tare dashi wanda ta gabatar mai a matsayin wanda
zata aura wai.
Yayi ya nufo inda nake tare dasu nafisa nan suma suka shiga gaidashi tare da mashi
sannu da zuwa suna mai taya shi murna samun karuwan da yayi.
Hannuna ya kama zuwa kofan shiga gidan namu wanda yake a rufe a lokacin don za,
abude shi da addua don shiga ciki.
Malaman da aka gaiyato ne suka bude gidan da addua tare da fatan gamawa da duniya
lafiya.
Mun shiga gidan da farinciki gaba daya mutane sai yaba kyau da tsarin gidan suke
yi.
Abincin da aka girka don taron mu aka shiga ci kowa sai da ya wadata yaci ya
koshi zuwa yamma mutane suka dinga watsewa daya bayan daya kowa a cikin farin ciki.
Ganin an dan rage yawa sai yan gida tsiraru suka rage ba yawa yasa na juya gurin
anty maryam nace zan dan shiga ciki anty .
Tare da ita muka shiga dakin da yake a matsayin mallakina wanda yasha kayan alatu
sosai na zamani don komai daga waje aka shigo dashi a gidan.
Yana zaune tare da Amira da Bashar dasu yaya sagir da yaya Abdul suna hira.
Muna mikewa ya bini da wani irin kallo na so da kauna yana cewa maryam ki barta
ta huta please koma may ye ai zata labarts maki idan kun natsu.
Don nasan bakunan nan naku tab yake da gulman da kowan ku ya tara ya tsiyayawa
dan uwa.
Nace kai haba dai yaya kana iya raba anta da jini ni da anty maryam sai Allah fa.
Yace ai na gani na kuma sani don gashi ta haki zaki barni a nan ni kadai.
Kai kade kuma yaya inji Amira yace kin san na saba da matata yanzu bamu raba
second a tare.
Amma wanan da kike gani naga yau tana son nisanta ta dani idan ban yi niya ba.
Amira ta kawar da kai gefe daya don ta fahinci i yanzu ba karamin ji dani yaya
sadauki yake yi ba har bai iya boye feeling din shi a gaban kowa.
Ga wani irin kyau da haske dana kara tare dani ga wani annuri da take gani yana
fita tare dani.
Lalai kam Bintu tayi sa, a da dace a rayuwan ta na jajircewa da tayi ta mallaki
zuciyan sadauki da ma ruhin shi a baki daya.
Lalaikam shima din yayi dace samun Bintu a matsayin matar aure a gare shi don
mace mai kyau da addini rahama ce ga namijin daya samay ta.
Kalli yadda ta koma yana wani ji da ita da dan shi wanda ko dan kukan yaron bai
son ji komai nasu gwanin burgewa.
Gaskiya yayi sa, an samun mace mai kyau a rayuwan shi da Rahama ce ai bazai wani
jin dadin nunata haka ba a duniya.
Ba Amira ba kowa ya kalle mu zancen zuci yake a kan mu don ko mun dace da junan
mu sosai.
Don sadauki za, ace mutum ne mai sa, a a rayuwan shi ga dukiya mai tarin yawa
Allah ya daukaka shi dashi.
Ga mace ya samu mai kyau da tarin addini tare da ita ta gyara mai rayuwan shi don
duk wanda ya ganshi yasan ya watsar da halaiyar shi ta da can baya.
Hassada dangin shedan tuni Amira ta mike tana fadin ita zata tafi gida sai
anjima kuma.
Sadauki yace haba Amira tun yanzu ki tsaya mana har ayi sallah sai ki tafi gida
tunda ba koranki ake ba?
Tace no bari kawai na tafi don naga kamar kana son hutawa ne da iyalin ka tafice
tana cika tana batsewa a ranta.
Ya gurgiza kan shi yabita da kallo don yasan abinda take nufi akan Fatiman shi ne
take wanan cikar haka tana batsewa ita kadai.
Sun dan jima suna hira akai kiran sallah suka mike zuwa sallah nikan muna dakina
mun baje da maryam muna hiran yaushe rabo da ita.

****** ********* ******
Bamu samu jan mu ba sai bayan karfe tara kowa ya watse yarage daga mu sai iyya a
gidan da take ta faman gyaran guri.
Ya fito daga dakin shi a cikin jallabiya baka mai gajeren hanni yace haba iyya
wanan aikin yai maki yawa fa gaskiya.
Nace a nemo muna wasu masu taimaka wa agidan mutum biyu aikin ki kawai ke yanzu
shine kula da Matar gidan da yara ba ruwan ki da wanan aikin kuma haka.
Tace haba Alhajina har ina aikin yake a nan ai ba sai an nemo wasu ba zan iya ko
ni kadai.
Yace a, a iya na gama magana ko gobe ne insha Allahu masu aikin zasu fara zuwa
sai ki gwada masu komai daya dace suyi.
A lokacin na fito ina saye da wani dogon riga dinkin shi simple ne irin na zama
gida mai launin jikin kura, kaina da hula dana daure gashina a cikin sa.
Nan nake cewa , a, a iyya baki huta ba hakana har yanzu don Allah ki huta kibar
aikin nan haka har da samay ga Amir kuma goye a bayan ta tare dashi take aikin.
Tace wai na dan rage kayan nan kafin safe kada gurin ya kwana haka da kazanta.
Badai tsabta ba kan Iyya don mace da bata haihuwa dama ance tsabta gare ta sosai
haka ne ya kasance ga iyya din don yar ta daya a duniya.
Kima tayi aure sai dai ba wani dadi a gidan auren don wahala take sosai sunan ta
suwaiba.
Yatana da yara uku ga mijin bai wani aiki sai dan buga bugan da yakeyi kawai iyya
tasha min magana akan wanan zaman na Suwaiba haka nan.
Haka yasa na sa a raina zan wa yaya magana akan wanan matsalan don ya kamata a
taimaka ma rayuwan su don Iyya gaskiya ba laifi mace ce mai rikon gaskiya da amana.
Fruit muka zauna muka dan sha muna hira yaso fita da daren zuwa gida don yaga
iyayyen shi sai dai yana tare da gajiya.
Waya naji sunyi yana ba baba hakkuri sai da safe zai shigo ya duba su insha
Allahu.
Bamu jima ba muka shige ciki muka kwanta iyya ta bukaci na bar Amir a gurin ta
wanda naji dadin hakan.
Don ko banza an kunsa yaye shi ma a lokacin don haka yana bukatan dan jayewa daga
gare mu.
Don ya manta da nono da sauri a cikin sauki batare da ya wahala ko ni na wahala
ba.
Washegari ma masu zuwa muna sannu da zuwa sun kara cika muna gida ba wani hutu
sosaia lokacin don jama, a kada su ce ina masu fadin rai
Kowa haba haba nake da zuwan shi don duk abu daya ne ya kawo su da mai kudi da
tallaka sunzo ne don nuna farin cikin su gare mu.
Na fahinci mutane mu suna a cikin wani hali na haula, i don wahalan da ya ishi
mutane haka yasa duk wanda yazo naga yana da dan rauni nake taimaka mai wasu zan
basu sabulai da kudi wasu kuma sun fi karfin karban kudi a gurina sai dai na basu
tsaraban abinda ya dace dasu wanda ankawo min abubuwan da zan rabawa mutane dake
shigowa taron mu.
Sai bayan kwana biyu da dawowan mune na fahinci an canza muna ma, aikatan mu dana
saba dasu abaya.
Ma, ana anbarsu a tsohon gidan mu da muka taso haka yasa banji dadi ba nai magana
da yaya yace zai duba al, amarin.
Da yamma kuwa sai ga Atiku da iyalin shi sun zo taron mu na tare su da farin ciki
nake tambayan su yaran su sukace suna lafiya.
Tare ma suke da maigidan su yana waje nace a, a shine zai tsaya a waje ku shigo
dashi mu gaisa mana.
Amaryan shi ta fita ta shigo dashi nan muka gaisa nake tambayan shi mai yasa bai
dawo nan inda muka dawo ba.
Yace hajiya ance nan kayan aikin ku duk yanzu na naura ne bazan iya aiki dashi ba
nace haba haba basai a koya maka ba.
Gaskiya daga gobe gaba dayan ku har su baba musa duk a nan zaku dawo da aikin ku
sabbin a kai su wancan gidan.
Nan ya shiga min godiya nake tambayan shi Aliyu fa suke ce min yana nan gida
kudin makaranta yai tsaye tunda maigida baya nan.
Banji dadin jin haka ba nace gobe yazo da yaron za, a san abinda za, ayi akai
insha Allahu.
Nakawo tsaraba da kudi na basu shi kuma mijin na bashi kudi ga sayi shinkafa
dashi.
Nan ya dukar da kai sai hawaye ya fara zubo mai yana cewa hajiya ban san irin
godiyan da zan maki ba keda maigidan ki akan irin taimakon da kuke muna a rayuwan
mu ba.
Ga yaron nan Aliyu maigidan ki ya taimake mu a baya an mashi aiki ance da ba, ai
aikin ba haka zai koma dan luwadi shima don abin zai ta damun shi idan bai yi ba.
Yanzun ko kinga zancen ya koma tarihi a sanadinku ke da maigidan ki da kuka
taimakawa rayuwan mu.
Nace haba malam atiku babu komai ai duk yiwa kaine may ye amfanin kana tare da
mutum baka taimaka mashi ba.
Munyi sallama dasu zasu tafi sai ga maigidan ya dawo nan suka tsaya suna gaisawa
dashi.
Yace malam Atiku hajiya tace sai a dawo daku gidan nan ko nai magana da Bashar
yace duk zaku dawo nan da aiki daga gobe insha Allahu.
Nan ya shiga godiya nace ai na manta maman Aliyu don Allah ina son kuyi min wani
taimako keda abokiyar zaman ki.
Sai gaba daya hankalin kowa ya dawo a kaina nace ina son don Allah duk safe a
dinga dama muna koko da kosai ana kaiwa makaran tan dake da almajirai sadaka da
yamma kuma ina son duk ranan jumma, a a dinga dafa shimkafa da wake buhu daya ana
kaiwa sadaka a wanan makarantan.
Don haka sai kuyi min lissafin abinda kuke bukata daga kayan aiki da kulan da za,
a dinga zubawa sai naji na aiko maku da kudin.
Kara zubewa sukayi a gurin suna min godiya cikin jin dadin wanan ci gaban da suka
samu na rayuwa.
Tunda dama manejin rayuwa ne sukeyi ba wani sana, an da sukeyi yanzu zaune kawai
suke a gida dan abinda mijin su ya samo ake amfani dashi.
Munyi sallama dasu akan zanji sako daga gurin maigidan su idan ya zo gobe aiki.
Suna fita sadauki ya juyo inda nake zaune yana sauke ajiyan zuciya yace wanan
sabon hikimar kuma ta maynene queen ?
Nace godiya da neman kariya ga ubangijin mu yaya na kasan duk wanda Allah yai ma
baiwa ya kamata ya gode masa.
Sai nake ganin yaran almajirai masu bara a titi zamu taimaka da dan abinda zasu
ci suji dadi a ransu muma muji daga ni, imar su.
Yace haka yana da kyau sai kuma may kike gani ya dace ayi don kudin kwallon da na
samu wanan karon ina son inyi amfani dashine a sadakatuljari,a
Nace akwai magidanta mabukata yaya da abinda zasu ci da iyalinsu yake masu wuya
akwai kuma marayuwa da ke neman taimako don Allah ya kamata ayi awani abu akai yace
insha Allahu angama queen.
Na kuma gode da wanan shawaran taki zan duba nasan abinda za, ayi na taimako ga
alumma daya dace ayi.
Sai da mukai kwana uku na shirya na tafi gaida su mama don lokacin mutane sun
dan tsagaita shigowa muna sosai gaida mu.
Wanda wasu gulma ne kawai ke kawo su gidan don suga yadda gidan namu yake ne.
Shiga nayi na alfarma dagani har Amir da Iyya muka tafi gidan namu sadauki ne ya
jamu a mota.
Mun samu su lafiya sai dai gaskiya duk akwai sauyin canji a tare dasu mama ce
kawai zaka kalla kasan bata da wani matsala a tare da ita.
Amma sauran gaba daya duk sun wani jemay kamar basu ba Umma duk kiban nan nata
yanzu ya tafi tsufa ya taso mata sosai tare da ita.
Ga furfuran dole daya bata masu kansu ita da mama Asiya yanzu kana ganin su kasan
suna cikin wani bakon yanayin da basu saba ba a baya.
Mama tai matukar farin ciki sosai da ganin mu ta shiga haba haba damu a gidan.
Kaunata dake gurin ta ta murje tayi kyau da ita sosai harda tsayi naga ta kara

90 / 92