Advertisements
Chapter 6 Reading A Lokacin Mu Ke by Zainab Idris Makawa Seenabu BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

A Lokacin Mu Ke by Zainab Idris Makawa Seenabu

Author :  Zainab Idris Makawa Seenabu Category :  Complete Novels

Chapter   6 / 92

15K to 18K   out of 275.8K words

ya shiga hali na
maye sosai.

Fatima don Allah zoki sayo min magani kafin duhu ya kara yi don yanzu dana aiki
su Amira Alhaji yagan su fada zai min sosai.
Kiyai sauri ki dawo da wuri kinji Fatima kada ki dade kinji Fatima dare ya soma
sosai.
Don takwas saura yanzu, ban son fitan dare ga diya mace haka koshi dole yasa zan
aike ki don kaina ya matsa min da ciwo sosai wallahi.
Bintu ta dauko hijjab dinta ta,saka ta fito ta karbi kudin maji tafada mata
kalar maganin da take son a,sayo mata.
Tana zuwa aka bata maganin ta juyo zuwa gida gap da zata shiga gidan ne taga
mutum a kwance bakin get.
Sai faman nasari yake harta dan raba shi zata wuce don tagane wanene a kwance
gurin.
Da,sauri ta dawo ta dan duka a kan shi a hankali tana fadin.
Yaya sadauki ka tashi ka,shiga daga ciki kada wani ya gan ka anan haka.
Da kyat ya bude idanuwan shi ya kalleta cikin maye ya nunata da hannu ya bude
baki da kyat yana fadin, tare da nunata.
"Ke zan _ci uban,ki idan baki ban guri ba walla_hi sai ya mayar da kan shi kasa.
Innalillahi Bintu ta furta a fili ta mike tsaye kamar zata wuce sai kuma taji
bazata iya ba don idan har wani ya gan shi a haka yashe a kasa cikin maye, yau
bakwanciyan hankalin ga Maji dama gashi kanta tun safe take yana mata ciwo.
Komawa tayi iya karfin ta ta dago shi daga kwancen da yake ta na cewa tashi yaya
ka koma dakinka don Allah.
Shegiya idan baki barni ba zan maki dukan tsiya wallahi, yafadi a cikin muryan
dan maye.
Bintu bata bi ta nashi ba sai kokarin mikar dashi take shiko sai ashar yake jefa
mata.
Cikin ikon Allah ta samu ta daga shi daga inda yake kwance ta kaishi daidai
kafadan ta duk da yai mata nauyi amma haka ta daure ta ja shi zuwa dakin shi.
Da kyat ta lalabo key daga jikinbshi cikin wandon shi na baya ta bude dakin
tana,shiga wani wari ya daki hancinta, haka ta daure ta kaishi bakin katifan shi.
Sai barci yake a kafadan ta cikin maye, tana son kifar dashi don duk tagaji saura
kiris su zube tare sai ya kwararo mata amai da fitsari a lokaci guda duk ya bata
mata jiki dashi.
Haka ta daure ga,warin amai yana damun ta ta kifar dashi akan katifan dakin.
Kallon hijjab din ta da ya lalace da amai da fitsari tayi tare da girgiza kanta
tana Allah ya kyauta tajowo mai kofan dakin tare da dunkule hijjab dinta daya
lalace da aman shi.
Gap da zata shiga gida taji karan motar Alhaji habu dake dawowa daga kasuwa, shi
da sauran yaran shi dake bin shi shago.
Da,sauri ta karasa kada suga fitowan ta part din samarin gidan kuma dakin sadauki
su fassara mata zance.
A can cikin gida kuma Maji hankalinta ya tashi sosai ganin Bintu ta dade sai
gata saidai a hargitse take don hankalinta ya tashi.
Amira data kalleta yadda ta shigo gidan take cewa, ke lafiya kika dawo wata kala
haka dake ji yadda jikin ki ya lalace.
Saida Binta ta kalli jikin ta take cewa cikin sauri faduwa nayi gurin kwata
da,wata mota tabiyo gefena.
To amma ai ba kwata bane kamar amaine jikin ki tace gurin masu saida abincine
gurin.
Ta mikawa Maji maganin ta,shige ciki don duk a tsawale take da aman dake jikin
ta dama.
Saida tai wanka ta gyara jikinta tsab tafito falon inda suke ta zauna tana
kallon shirin da ake a sokoto tv.
Maji dai bata ce masu kalla ba don kanta da yake damunta da ciwo a lokacin.
Sai da ta dauki lokaci bayan tasha magani sannan kan ya fara lafa mata don ranan
bata ko fita zuwa yiwa maigidan su sannu da,dawowa ba.
Wai ko yau yayan ku yadawo kuwa don banga ya shigo ba daukan abincin shi.
Amira tace, waya sanan mashi kila yana can gurin yawon banzan shi sai baba yasan
bai gidan yazo yaitawa mutane masifa akai.
Bintu tace da zan shigo nagan shi zai shigo da leda da,ya,sayo doya soyayya
gurin mai sayar wa nagan shi da zan wuce yana saye.
Oho ashe shiyasa banga yashigo ba ya samu abinda zaici ke nan .
Ai da yana jin yuwa da yanzu yashigo ya cinyewa mutane abincin su ko inji
maryam.
In baici abinci ba nan a ina kuke son yaje yaci ne maryam, ni dai idan zai shigo
yaci a nan din ai zaifi min komai dadi.
Bintu taji tausayin Maji ya kamata a zuciyar ta take cewa kai uwa uwace dai.
Da yau maji zata san halin da dan ta yake ciki tasan da yanzu suna cikin tashin
hankali da balai a rayuwan su a shiyar su.
Amma dai yau Allah ya rufa wanan asirin an wuce gurin in ba,wani ikon Allah ba
kuma.
Tana jin su suna hiran su amma bata saka masu baki ba sai faman tunane take a
ran ta.
Shigowan baba a part din ya katse mata tunanen ta suka fara gaida shi suna mashi
sannu da,dawowa.
Bintu ce tafara mikewa tashige daga ciki sai Alhaji yabi su Amira da harara dole
suka mike simi simi suka shige bayan Bintu.
Yace marasa kunya kawai wai har bakuwa tafisu hankalin sanin ya kamata.
Har yanzu gwagon yarinyar nan bata dawo bane ko kuwa dai?
Bata dawo ba Maji taba shi amsa a takaice, takara da cewa ni ban ma son rabuwa
da yarinyan don halinta na kirki yai min.
Hmmm ki dai ji da na kanki kafinki kara jajibowa kanki sabon matsala ya bata
amsa.
Ai Fatima ba matsala bace zan ma iya cewa zaman ta ya zama min alheri don kaga
yaran nan suna samu karuwa sosai a gurin ta ga ta yar karama amma akwai addini
sosai a kanta.
Ta godewa Allah da,ya bata wanan baiwan har takai ga samun yabo haka na alheri
Allah muma ya shirya muna yaran mu.
Ban ganki ba ne yasa nabiyo nagani ko lafiya don nasan ba halinki bane rashin
zuwa yi min sannu da kasuwa.
Maji ta dan ya mutsa fuskanta tana cewa wallahi tun safe nake fama da ciwon kai
yanzun ma aka sayo min magani na,dan sha shine naji yadan fada min.
Naso naje gaishe ka amma sai nai tunanen ko ka shige ne ko ai.
Ki daina shan magani haka batare da likita ya baki umurni ba idan kinji kan ya
matsa maki aida kin kirani nazo mun tafi asibiti ko .
Naga ciwon kaine kawai shiyasa ban dauke shi wani babban ciwo da zani asibiti
ba.
Haka dai kikace a lokacin da ya karasa takon shi inda take zaune yana kai hannun
shi akan wuyan ta don taba jikin ta yaji lafiyan ta.
Kai haba Alhaji ai na samu sauki dana sha maganin nan yanzu, ki dai bar wasa da
ciwo don ciwon da ka raina shike zama babba yanzu.
Allah dai ya sauwaka inji maji tafada cikin dan sauke ajiyan zuciya.
Ki dai bar tunane akan wanan yaro ki kai kukan ki ga Allah shine zai bamu mafita
akan shi,insha Allahu.
Allah yada inji Maji ta fadi voice din so soft don zancen Sadauki yana tayar
mata da hankalinta sosai.
Daga haka yai mata saida safe yabar part din nata cikin tausaya mata halinda
take ciki yanzu kan lalurar dan ta wanda duk ta tayar da hankalin ta.

Washegari sun tashi kowa na batun fita zuwa makaran ta sai Bintu ce a gida don
ita yau basu zuwa makaranta suna hutu.
Part din nasu yai shiru bakajin motsin kowa duk lokacin kowa yafita zuwa nashi
tsabgan gaban shi don ci gaban rayuwan su.
Wani irin yunwa ne ya farkan dashi daga nauyayen barcin da ya yi mai tsawo bai
san inda yake ba.
A hankali ya bude idon shi inda ya kurawa silin din dakin nashi ido, can yakai
kallon shi ga agogon dakin a hankali yaga har tara da rabi na,safe.
Da kyat ya iya mikewa zaune ya samu har yakai tsaye don yunwan da yake ji yai mai
yawa sosai a lokacin.
Wanka yashiga yana wankan ne abinda yafaru jiya da dare ya dan fara dawo mashi
a,rai.
Kai aiko na,shige su tunda wanan bakuwar yarinyar ta san da wanan zancen don
yanzu nasan ta fadawa Maji halin da,ta ganni a ciki daren jiya.
Aiko idan har ta fadi sai yai mata dukan da sai an kwantar da ita asibiti sai da
ya shirya tsab yafito tare da kulle dakin shi ya nufi cikin gida don ya gaida Maji
ya kuma karya saidai gaban shi na faduwa badon yana son cin abinci ba da bai shiga
gidan ba a lokacin.
Da sallama a bakin shi ya shiga part din nasu duk da ya hadu da mama a kofa
amma bai mata magana ba ya shige abinshi tabishi da harara tana fadin mara kunyan
yaro kawai tabbatacce.
Maji dake zaune saman salaya tana lazumi ta karba mai sallaman shi tana cewa sai
yanzu katashine babana kowa a gidan manya da yara sun kama gaban su ko.
Yace cikin dan shafan kan shi wallahi Maji barci ne ya kara daukeni bayan mun
dawo daga sallah.
Ai jiya da,dare muna ta jiran kazo kaci abinci baka shigo ba har ana batun rufe
gida sai Fatima ce ke fada muna cewa.
Gaban shi yai wani faduwa ras ras kafin yaji ma yarinyar tafada wa maji din.
Maji tace take ce muna ta gan ka,,, lokacin Bintu tafito daga cikin daki tana
cewa Mama a canza zanin gado ne.
Wani uwar harara ya,watsa mata saida ta kasa fadin maganan da zata kara fadi.
Maji tace ashe jiya doya kaci ka kwata gata itace ke ce muna tagan ka kana,sayen
doya da kwai da dare dana aike ta.
Wani wawan numfashi ya sauke tare da dan sake fuskan shi yace eh wallahi maji shi
nake son ci shiyasa na saya ai.
Fatima dauko wa yayan ku abinci shi ya karya yafita shima don ban son zaman gidan
nan kamar mace.
Bintu ta juya inda yake tana cewa ina kwana yaya can kasan harshen shi ya amsa
mata da lafiya kalau,
Ta juya zuwa cikin kitchen ta dauko mai abin karin shi takawo mai gaban shi ta
duka don ta aje mai ya faki idon Maji yana cewa kin kuru baki fadiba dana karyaki
yau wallahi.
Da sauri Bintu ta mike tabar falon don kada ya kara ce mata wani abin kuma don ko
yanzu ta tsorace dashi don mashayi ba abinda bai iyayi shi.
Sunaci suna hira da mahaifiyar nashi tana dan mashi hira maikama da nasiha sai
cin abincin shi yake hankali a kwance abin shi.
Daidai Bintu na shigowa taji yana cewa ni dai Maji don girman Allah ki yardan
min natafi wanan wasa kiyi hakkuri ki gwadani ki gani idan ban canza ba kada ki
kara bari na tafi don Allah maji.
Daka ta sadauki na riga na fada maka cewa bazan yarda da zancen tafiyan ka
ba,wani kasa can da babu kowa na gida a tare da kai, nan ma da kake a gaban mu yaya
muka kwashe da kai?
Bintu batasan yadda akayi ba tace mama yace don girman Allah ki barshi yaje
insha Allahu zakiga canji a gare shi da yardan Allah ke dai adduan ki yake nema da
yardan ki.
Da har zai bude baki yace ke wayasa bakin ki zan balballaki yanzun nan, amma sai
yaji maji tace .
Fatima bar shi kawai ni nasan halin abina ke yarinya ce baki gane may nake nufi
da zance na yanzu amma ba zancen tafiya a guri .
Tafiyan ma fa wai na wasan kwallo haba sai kace uwar banza da batasan ciwon kan
ta ba.
Maji komai zamuyi saida adduan ku don haka kamara yayi kisawa zancen albarka ki
mara mashi baya yakai ga kudirin shi.
Don ba,a san mai gobe zai iya yi ba shiru maji tayi tace kai Bintu badai iya
magana ba dai kam.
Shiko Umar shiru yayi yana mamakin wanan yarinyar yadda ta iya magana haka kamar
wata tsohuwa can.
Fatima naji zancen ki sainai shawara ya dan dakance ni kawai nagama nazari
nagani ,
Daga haka ya mike tare da cewa cikin murya ba dadi zan fita sai nadawo Allah ya
tsare tace sai kadawo.
Haka fita jiki ba karfi yabar dakin sai dai yaji dadin yadda wanan yarinya ta
saka baki har Maji ta dan yi taushi sosai yagani ai.
Tun lokacin da sukai wanan magana hankalin maji bai kwanta ba sai sakawa take
ta walwalewa a ran ta daga karshe dai ta watsar da zancen ma kawai.
A na cikin haka gwagon Bintu ta dawo daga kawai ta zo gidan bayan ta huta don
ganin Bintun ta.
Nan suka tare ta da murna sai bin Bintu take da kallon yadda gaba daya ta canza
mata a fuskan ta ta kara haske da kiba, taiwani irin kyau da ita.
Nan ta shiga yi wa Maji godiya da karamcin da tai mata akan rike mata yarta yar
dan uwan ta da take hannun ta.
Maji tace haba hajiyan masa ai Fatima mutun ce yarinya ce mai dadin zama da sanin
ya kamata sosai.
Naji matukar dadin zama da ita a gidan nan don ta taimaka min da abubuwa da dama
a gidan nan
Hakane ma yasa nace ko kin dawo bazan barta takoma gurin ki ba sai dai mu zauna
nan da ita tunda danan da can guri ki ai duk dayane kuma a shiya daya muke dake.
In dai har hakan bawai zan takura maki bane gwago tai godiya da karamcin Maji
tana cewa nagode Hajiya dama ba zama nadawo nayi ba don jinya nake a can na yayata
da bata da lafiya.
Shine naga na barta a nan da suna sati biyu gashi har nai sati hudu a can baku da
labarina, kada hankali ku ya tasbi na rashin jina da bakuyi ba na tsawon lokaci.
Ai babu komai nasan tunda najiki shiru lafiya ne ai tunda kin san inda aka barta
ai.
Nan suka dan taba hira gwago tana bata labarin rashin lafiyar yar uwarta da take
jinya a kauyen su.
Da zata wuce ne ta bukaci da Bintu ta rakata ta dan gyara gida don kuran da yayi
na rashin mutum a cikin shi na wani dan lokaci.
Aiki sosai Bintu tayi a gidan harda girki saida tai masu don suci tanayi tana
tambayan gwagon ta labarin mutanen gida.
Sai da suka natsune Bintu takw fada mata irin rayuwan kawai cin data samu a
gurin Maji da kuma irin matsalar da take ciki akan dan ta da baijin magana da
bukatar shi a gurin mahaifiyar shi na son tafiya wani gari buga kwallo da yake son
zuwa yi.
Gwago tace kai amma ko hajiya da ta barshi don bata san ko shine mafitan ta ba
arayuwa tunda har yai mata alkawarin canzawa idan ya dawo.
Gwago tana fada irin ta manya tana fadin ai gara ta barshi ya tafi don batasan
abinda Allah ya shirya ba a kan yaron.
Suna ta zancen ita da gwagon ta har dai dare yayi don haka ranan a na gidan su
Bintu ta kwana da,gwagon ta suna kewan junan su.
Sai washegari da yamma ta shigo gidan cikin jin kunyan Maji da yaran ta, sai
faman yi matasheri sukeyi taga gwago ta gudu masu.
Maji tace yanzu Fatima haka zamuyi dake ni da nake fadin anan zaki zauna shine
kina gani gwagon ki kika gudu gurin ta ko?
Ko dama bakijin dadin zama damune dai kika boye muna hakan ?
Da sauri Bintu takai kasa tana cewa ,a,a mama ba hakana bane kawai dai na tsaya
ne na kara shirya mata kayan ta.
Jeki ga abinci can a kitchen ki diba kici inji Maji tana mata magana cikin
kallon fuskan yarinyar.
Mama na koshi gwago tai muna gwaben ganye mun ci dazun mun koshi sosai ban jin
yunwa yanzu. Sai dai anjima in Allah ya kaimu.
Daga nan ta samu guri ta zauna tana kallon maryan dake dakilar wayan ta tana
dariya ita kadai.
Sun kai wani lokaci falon yana tsit kowa yana tsabgan gaban shi sai Bintu dake
ta tunane kala kala cikin ranta yadda zata zauna a gidan nan dake cike da tarin
matsaloli.
Fada sukaji tsakanin mama Asiya da uwargida ya kaure sai cacan baki suke a kan
yaran su.
Maji bata fita ba tana zaune a falon ta har sukaci suka sude ko magana batayi
ba, sai ma Amira da tace su daici kan su munafukan banza kawai kanku ake ji.
Sai lokacin Maji tai magana dacewa Amira ban son rashin kunya fa iyayyen naki
kike zagi da munafukai kuma.
Kada na kara jin wanan kalamin a bakin ki ko kin manta cewa ke ma watarana uwace
a wani gidan.
Shiru Amira tayi don tasan in ta kara furta,wani abu yanzu Maji zatai cikin ta da
masifa sosai.
Har masu fadan suka kare cacan bakin su da tonon asiri ba,wanda yai magana a
dakin daga dakin mummy Amarya ma ba tafito ba haka ma yaran ta.
Don ita dama,yar i don't care attitude ce a,gidan harkan kowa bata shiga sai in
abu yakai mata karo.
Sai da yamma sosai gwago ta shigo gidan gurin Maji inda ta aika mata da abincin
dare tace kada

6 / 92