Author : Zainab Idris Makawa Seenabu Category : Complete Novels
min bakina da hannun shi daya.
Bakina yana matse nake ce mashi mamace tace nazo na dubaka wai tana magana da kai
.
Saboda hannun shi daya ya taushe min baki bai bari yaji abinda nake fadi ba.
Birkito dani yayi daidai fuskan shi muna kallon junan mu face to face ni dashi a
hankali yace may yakawo ki dakina muna fuka ?
Ya dan sauke hannun shi daga bakina nace mama ce tace nazo na,,, sai ya kara
matse bakin iya karfin shi.
Mamaki da tonon asiri sai jin saukan hannin shi nayi zuwa kirjina yana fadin
abinda kikazo nema ke nan bakar jarababiya kawai.
Na girgiza kai idona a rustse nace da karfi wallahi mamace ta aiko ni gurin ka.
Bai sake ni ba kuma bai fasa abinda yakeyi min ba a lokacin, wasu hawaye naji sun
fara dan silalo min daga idanuwana.
Bin jikina yake a hankali da shafa yayin da nake jin saukan numshin shi a kunnuwa
na cikin wani bakon yanayi.
Cizo nakai ma hannun shi nace da karfi wallahi Allah ba gulma nazo ba mama tace
nazo na kiraka wai .
Daidai kirjina ya tsaya ya dakata da abinda yake min nace don Allah yaya ka sake
ni in tafi wallahi mama ta aiko ni na kiraka .
A hankali yakai hanniwan shi saman kirjina yadan shafo su cikin hikima irin ta
maza da sauri na dan sulale nai kasa don abinda naji a lokacin.
Kara dago ni yayi daga dan dukawan da nayi ya dago fuska na tare da hada shi da
nashi ban aune ba yakai bakin shi ga nawa ya dan fara tsotso a hakali.
Nan na shiga ture shi daga jikina kaman dutse nake turawa don ko motsi baiyi ba
kuma bai fasa abinda yake min ba.
Can naji ya turani da baya da karfi tare da dafa bango yace yar iska gobe ki dawo
min daki kadan kika gani yau.
A hankali na dafa bango tare da dan bugewa cikin kuka nake fadin har nakai kofa
wallahi ban yafe mugu mazinaci kawau aiko ta biyoni a guje ban tsata ba sai falon
mu.
Yaya haka kuma da sauri mama ke tambayana tare da son jin bayani daga gurina tana
kallona.
Nace cikin kuka ba yaya bane ya kai min nashi wai may yakawo ni dakin shi.
Sai gashi ashe yana bayana a lokacin sai kamshi yakeyi kamar bashi ba.
Tace kai kuma daga na aika yarinya ta kiraka sai ka kai mata nashi kai dai
wallahi sadauki katon banza ne wai dadin may kake ji gurin zaluntar yarinyar nan?
Yace haka tace maki nashin ta nayi ?
Ai duk ni na ja mata hankan tana zaune zaman ta ta tashi na aike ta kiran ka na
manta kai mugune gareta.
Inda nake zaune ya dan kalla sai faman zubar da miyau nake ina tofarwa tare da
goge bakina da dan kwalun dana cire akaina.
Gashina daya sha gyara yana kwance hat gadon bayana yasha gyara sai walkiya
yakeyi.
Murmushin ke ta ya sakar min tare da dan kashe min idon shi guda daya.
Mama tace mai dama zancen abinda zakaba iyayyen kane maza masu buki, don banji
kace min komaiba har yanzu kan zancen.
Yace ni maji may zan basu kuma ?
Sadauki iyayyen naka kuma suna buki zakace may zaka basu bayan kowa yanzu yasan
kana dashi.
Murmushi yayi kamar wanda yake a cikin nishadi yace OK maji sai ki fadi abin da
za,a basu din ai ina ganin is OK.
Nasan aljihun kane Baba na balke na shatama ko nawa zaka iya ba iyayyen ka yace,
maji ki fadi kawai ba matsala ai tace hamsim hamsin yayi ko yace kai haba haba mji
adai basu koda dari biyu biyu ne ai ina ganin is ok for them,
Kai yaya har dubu dari biyu biyu baiyi yawa ba yace baiyi yawa ba Amirah bari a
basu kawai.
Yana fadin haka yace maji abari har da safe sai na ciro masu na kawo maki kiba
Baba ko ?
Har lokacin ina zaune sai hawaye nake zubarwa ina bakin cikin abinda sadauki yai
min yau ashe dan iska ne haka ban sani ba shi da yake ikirarin cewa bai taba zina
ba ashe tsohon mazinacine haka ban sani ba.
Nai zurfi a cikin tunane na nake jin muryam maryam da karfi tana fadi, da gaske
yayan mu yace saka hannun shi ga aljihu yace kowa tazo ta karbi nata key din gashi
sai lokacin na dan dago ina kallon su.
Keys ne ya ciro daga aljihun shi yana mika masu nakai ido ina kallon keys din .
Yace kowacen ku wanda ta zaba dazun shine nata juyawan da zasu gurina sai ganin
ina kuka sukeyi.
Lah Bintu badai har yanzu kukan dan nashin da yayayai maki ki ke tayi kamar wani
nashi can.
Ya dago tare da kallo yace au wai kuka takeyi bafa wani nashi sosai nai mata,ba
dama nasan kukan shagwaba da jin dadi zaki tsaya yiwa mutane haka.
Ya kare maganan shi cikin lashe bakin shi kamar wani maye can nace a fili mugu
azzalumu kawai na mike na shige daki cikin kuka.
Dan murmushi yayi tare da lumshe lumsarsu idanuwan shi da da tun shigowan shi
falo suke mashi haka.
Ko may ya tuna sai yai murmushi tare da bude idanuwan shi caraf acikin na maji
tace Baba na wai wani irin keta kaiwa yarinyan nan yau haka har kasa ta kuka.
Yace bata fada maki ba maji dan kai mata nashine fa nayi kuma ban ma samay ta
sisai ba fa.
Wallahi kadai ji tsoron Allah gashi don tsaban ket kasa yar mutane kuka haka idan
bata ji zafin abinda kai mata bata bacin ka haka yau.
Ai ba yau kafara mata kyeta ba amma bata taba fada haka ba ido da ido sai yau ?
Wallahi maji bata jin magana ne tafaye shegen gulman tsiya kungan ta nan.
Mi dai bata taba muna gulma ba don muke zama da ita sai dai ke da ka saka mata
ido don kiyayya kake ganin haka gare ta.
Kiyayya kuma maji aiko yayana bai ma Bintu haka kawai dai ke ke ganin hakan
wallahi amma ita,ai Bintu ba baya ba itama kingan ta shegen tsokanane da ita.
Anty Amirah Anty Amirah wallahi ki iya bakinki akan Bintu da yayan mu, inba haka
ba watarana zakiji kunya sosai wallahi.
****** ********* ******
Kwance ya ke saman gadon dakin shi rigingine ya saka hannun shi yai crossing
dashi idon shi biyu amma yanayin kwanciyan shi sai kace yana barci ne.
Saboda idanuwan shi da suke a lumshe a lokacin a hankali yake tariyo abinda ya
faru a tsakanin shi da Fatima.
Hannun shi da ya sauke akan kirjin tane ya fado mashi a rai yana tunanen may ya
hanashi ya cire hannun shi a jikinta a lokacin.
Murmushi yayi da yadda ya samu sa,an bakin ta ya tsose su yadda yake so son ran
shi.
Wani murmushi yayi naketa yace gobe ki kara yar iskan yarinya kawai gaba abinda
zan maki idan na kama ki sai yafi wanda nai maki yau.
Dariya ya kwashe yadda maji ke fadan wai ya nashi yar mutane ba gaira ba dalili
don cin amana.
Yasan da yau maji tasan abinda yai wa yar nata da ya shiga uku a gurin maji da
masifa sai yabar garin ba shiri.
Yakwashe da wani irin dariyan keta shi kadai yadda ya ga na koma gefe ina kuka a
falo dazun da ya shiga.
Yace a fili may be this is her time to have romance with somebody ?
Ina daki barci ya gagati indona nayi brush yafi a kirga kafin na kwanta don ina
ganin ya zuba min abin mayen shi ga bakina kila ga kazantan da nake ji a raina.
Har anty maryam tafara zargin may wainake ta wanke ma bakine tun daxu nace mata
ina jin bakina badadi ne yau.
Tace aike ne dan abu kadan idan yaya yai maki sai ki ta faman mashi kuka shiyasa
yake jin dadin yi maki kyata ai.
Kema ki zage kai ki dinga ramawa idan yai maki bawai ki zauna kina kuka ba tunda
naku sallon takon ke nan a haka.
Hararan ta nayi nace don Allah anty barni kada ki kara min bakin ciki naja bargo
na rufe jikina don sanyin da akafara a lokacin.
Washegari ban fito da wuri ba ina gudun in fito na hadu dashi a falon sai
guraren shadayan rana nafito falon .
Ban dade da zama ba sai gashi ya shigo falon da sallaman shi nan suka shiga
gaidashi ban dani da nai kaman ban gan shi ba.
Nan ya dora idon shi a kaina ko kyaftawa bai yi yace ke baki iya gaisuwa bane
halan yar kauye?
Da sauri na mike tsaye zanbar falon yace kina tako daya daga gurin nan yanzu sai
nai maki abinda kike so.
Cak naja na tsaya guri guda ban motsa ba daga inda nake yace look at her kamar
wata takwarai can nan ko shedaniya ce ta karshe.
Na juya nace ni wallahi ba shedaniya bace sai dai in kaine shedan,,,,,,,,aiko ina
ganin ya taso na ruga ciki da guda na kargamay kofan daki ina mai da haki.
Yace ashe ke karamar yar iskane ai daki bari na samay ki gurin yanzu na
wujujugaki wallahi.
Daga cikin daki nace anki a tsaya din mugu kawai macuci yace ai kama ki zanyi sai
kin fada min waye mugu a gidan nan.
Ban fito ba sai da na tabbatar da yafita daga gidan ina fitowa suka kwashe min
da dariya Amira tace kai Bintu ga tsoro gajan magana ai shine maganin ki wallahi.
A raina nace baku san komai ba da bakuce min haka ba kuma da kun raina shi
wallahi.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,,,,
IDAN KIN KARANTA KO KIN TURAWA WANDA BAI BIYA BA ALLAH NE SHEDAN MUNA BINKI
BASHI,,,,
ALOKACIN MU KE,,,,
Mun kama hanya sai hiran su suke shi da Bashar niko ina bayan mota zaune a takure
cikin damuwa.
Bashar ne daga inda yake zaune ya dan juyo yace min Bintu gaki kinyi shiru mana.
Nai dan murmushi yake kawai nace ba komai yace ko kina son a sai wani abune?
Kai kawai na girgiza mai nace idan mun kai wani kauye zan sai dan tsaraban da zan
kai wasu mama kada naje masu hannu sake.
Sai faman gudu yake shararawa da mu har sai da naji tsoron gudun da yake da mu
nace komai nashi dai na muggai ne ko kashe mu yake son yi ne wai ?
Kafin wani lokaci sai gashi mun fara hangen garin sokoto daga nisa mun da kara
gaba nani ya taka burkin motan da karfi sai dana nan dan firgita bani ba har Bashar
dake gaban mota sai da ya kalleshi.
Muna nan zaune shiru ya bude mota yafita zuwa gefen da nake zaune ya bude marfin
mota fuska a daure yace nafito ina fitowa ya mayar da marfin motan ya rufe .
Ina tsaye jikin mota ya daro hannau shi guda saman kan mota dayan kuma ya sashi
daga gefen kunkuruna sai dai mota ya dafa.
Take naji cikina ya kada min fuskan shi a daure tamau yace ke dakata kiji kada
kikaga nazo na dauko ki naji wanan zancen a gida ran ki zai baci sosai wallahi duk
kika bari maji taji cewa nine nazo na dauko ki sai na bata maki fiye da tsanmanin
ki.
Nace baka son asani may yasa kazo ka dauke da ka barni mana har lokacin da na
tashi dawow,,,
Bakina ya murde dakarfi yace ke baki da kunya ko ina magana kina magana who is
the master?
Jin zafi a bakina yasa na dan zille na duka sai ya komane sai saman kirjin shi na
fada.
Da sauri na kara dagowa hakan yasa muka tsaya muna facing din juna face to face.
Ya dan dade yana kallona sai ya kuta ya juya ya shiga mota yana fadin kinji
warning din da nai maki wallahi duk naji zancen nan sai ranki ya baci dani wallahi.
Na shiga mota idona yai ja kaman zanyi kuka ina cewa ni wallahi wanan cin zalin
ya isheni don anfika karfi sai a dinga cuta maka kawai.
May kike fadi yace sai lokacin Bashar dake muna dariya yace haba ka barta hakana
mana please?
Ya tayar da mota muka ci gaba da tafiya, bai tsaya ba sai wani guri da ake sayar
da kayan irin na kauye na ciye ciye.
Nan suka fita sai gasu da sayayan kayan tsaraba mai yawa irin na kauye ana lodawa
a buth din motan.
Muka bar gurin nidai ban san may damay suka sayo ba a lokacin muna shiga gari a
play over ya samu guri ya tsaya.
Can ya tare wani mai Napep yake cewa, ya kaini gida tare da mai kwatancen inda
zai kaini, yabiya shi kudin shi nan mutumin ya loda kayana a cikin motan shi.
Su mama suna zaune sai ganina kawai sukayi a bazata kawai nan suka shiga cewa la
Bintu ashe kina hanya ?
Yaran da suka shigo min da kaya na diban masu rake gyada dafafa na basu suna ta
jin dadi suka fita.
Naje gurin mama na rusunna na gaida ita cikin jin dadi da gani tace Fatima shike
nan kinje kin samu guri kin share ai har ina batun binki ne da banga kin dawo satin
nan ba.
Nai murmushi nace mama ai zan dawo tunda an koma makaranta, tace yayasu wajen
mamaki suna lafiya ko nace duk lafiya kalau mama suna gaida ku.
Ta kalli tsaraban da nazo dashi tace Fatima wanga tsaraba haka mai yawa fa dariya
kawai nayi a raina nace aikin mahaukaci ne.
Nan muka shiga hira dasu anty suna min sheri wai naje naga mama na kasa dawowa.
Sadauki bai shigo ba sai da yamma lokacin ina cikin daki maryam ke fada mai Bintu
fa ta dawo yaya.
Yace taga daman dawowa ke nan ta samu kauye ta zauna kaman wani birni can.
Tasa min kira na fito sai ganin shi nayi a zaune nace yaya ina wuni ?
Ya amsa a kasalance da lafiya?
Kinga daman dawowa ke nan ko ?
Murmushi kawai nayi mashi na karasa gurin maryam nace gani anty tace dama yaya na
kiraki ku gaisa ta fadi tana dariya.
Na juya kawai na koma ciki, ina gyara kayana ban fito ba sai bayan magariba don
nasan lokacin bai nan.
Ina cin abinci kawai sai gashi ya fado falon saudaya na daga kai na kalle shi ban
kara ba.
Maryam ce take ce mai yaya adebo ma tsaran Bintu na kauye yace kai maryam kayan
kauye ai sai yan kauye.
Daga inda nake zaune nace, muko dashi mukafi wayau kayan kauyen don yafi bada
lafiya ai.
Yace ke yanzu lafiya kike ke nan a haka kamar a karya ki?
Kafin nai magana maryam tace a,a yaya aiko yanzu Bintu ta yi kiba in kuma tafi
haka ai bata kyau.
Ni wallahi duk da mace ce amma nafi son mace haka silynder da ita sharp din mutum
duk dress din da yayi sai yai ma mutum kyau.
Ga Bintu kuma dagowa ce ga wanan uban farin nata kamar yar larabawa da ita.
Kai maryam don Allah ya isa haka kada kisa kan Bintu ya fashe wanan dadin haka
inji Amirah?
Maryam tace wallahi anty da har haushi nake ji idan mun fita da Bintu yadda
matane ke yabata amma yanzu nima nasan gaskiya suke fadi.
Watarana fa muna alwala a makaranta wata na ganin gashin Bintu ta yanka salati
wai ikon Allah yanzun ke kina da wanan gashin haka kike faman boyon shi ga hijjab
kullun ?
Sai lokacin yaya yai magana yace, shiyasa ta bude ai don su gani su yi magana.
Nace kai haba yaya haka kawai zan bude kaina wa nake son ya gani kuma?
Ke kika sani dai tunda an gani an yaba din ai yadda kike son agani din.
Shiru nayi wani takaici ya kumay ni a raina nace ni wallahi wanan ai zargine
kawai?
Yace nakara jin kin bude wani part dinki a jikin ki sai na bata maki rai gidan
nan.
Dan Allah yaya ji yadda maryam ma take wani zuzuta fatima wallahi sai kace wata
sarauniyar kyau can.
Su dai suka sani shedanun yara ne wallahi kin gan su nan shiya sa duk suka fita
sai maza sun biyo su don suke kiran su.
Wanan sheri da may yai kama saboda Allah haba dai yaya kana biyewa Anty Amirah
tana zuga ka kawai yaya.
Ni dai wani haushi da takaici bai bari na ko iya dago kaina ba a lokacin don irin
takaicin da nakeji.
Amirah tace maza kan na zuwa har ana masu yanga da kuri kafin a dauki wayan su
tafadi cikin dariya.
Kai haba anty ai wanan sheri ne kawai kike kulla muna gar wasu maza muke kulawa
mu don Allah,
Baiyi magana sai shirun da yayi can ya dan bude abincin da aka aje mai agaban shi
ya fara ci nikan na mike na shige dakin mu.
Amirah tace kibar gudu ai don kada a ci gaba da zancen zaki shige ko?
Shima bai bi ta kaina ba yaci abincin shi ya tafi abin shi kawai.
Ban san yaya akayi Bashar ya fadawa Anty maryam su suka daukoni daga kauye ba
ranan da na dawo.
Amirah na falo ta dunkule saman kujera tana chatting maryam na zaune tana gyaran
farcen ta.
Maji na zaune tana gyaran wayan ta da ke hannun ta ruwa ya dan zubo mashi da take
sha.
Nafito da plate a hannu na da abinci zanci na zauna na fara ci ban dade ba sai ji
nayi maryam tace.
A humm wai