Advertisements
Chapter 87 Reading A Lokacin Mu Ke by Zainab Idris Makawa Seenabu BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

A Lokacin Mu Ke by Zainab Idris Makawa Seenabu

Author :  Zainab Idris Makawa Seenabu Category :  Complete Novels

Chapter   87 / 92

258K to 261K   out of 275.8K words

Baba Sani yaje gida duk da Baba baida lafiya amma haka yai ta yankar kauna da
tashin hankali yana zagin Nafisa da kawayen ta.
Ranan munsha zagi don har dani sai da Baba Sani ya hada ya zage a cikin fadan
shi da yakeyi.
Har yayi ya kare ba wani mataki da za,a dauka don ba,aga sadauki ba sai cikin
dare lokacin mutane sun rage ya shigo gidan ya wuce dakin shi ya kwanta bayan ya
fadawa masu gadi kada a bude wa kowa gidan.
Baba ya zo da wasu makwabtan shi amma masu gadi suka ki bude mai gida.
Haka ya hakkura ya koma da tarin takaici fam a zuciyar shi ba yadda zaiyi.
Asuban farko yazo gidan da masifa inda yake shiga ba nan yake fita ba yana fadin
don sadauki na ganin yana da dan hali shine har yake gani zai iya taka kowa ya
zauna lafiya.
Dama ba yau ba yasan cewa shi shedanin yaro ne shiyasa al,amarin shi bai mashi
ba.
Duk hayaniyar da yakeyi bai san yanayin gidan bai bari a sani ba a banza yake
ihun shi a,waje.
Na shirya a cikin wani dogon riga tare da daukan Amir a kafadana muka nufi dakin
shi mu gaida shi.
Na samay shi a tsaye yana saka aninin dogon rigar shirt da ya saka a jikin shi
jin shigowan mu yasa shi juyowa gare mu yana murmushi a fuskan shi.
Na karaso inda yake tsaye nace yaya na ina kwana yace maman Amir an tashi lafiya
ko yaya gajiyan jama,a dai ?
Jama,a sunyi dadi sai dai abinda ba,a,rasa ba kawai da kaje ya dawo na halin
taro.
Nace gaskiya yaya jiya banji dadi da kasa a rufe su Rahama ba kuma kai tafiyan ka
Baba har dare yana zuwa gidan nan neman ka ba,a ganka ba.
Yace ko yanzu yana a,waje ya tafi can gida jiya ance yaiwa baba tas da mutanen
gidan.
Amma kina nufin kinji dadin irin wullakancin da sukazo har cikin gida su sukai
min ko ?
Nace ayi hakkuri son kane ya rufe mata ido har ta aikata hakan ba wani abuba.
Kuma aiko banza Rahama yar uwar kace yaya sai hhakkuri kawai wallahi amma basu
kyauta ba gaskiya.
Nifa shigowan ta baidamuna sam don a tare na ganku gidan ku daya yar uwan kace
Rahama ta jini.
Hannun shi ya mika yana son karban yaron sai bai iya ba don bai kan dauki yaro shi
sam.
Zama yayi bakin gado yace min zoki gyara min shi please ban iya daukan yara ni.
Na zauna gap dashi ya tsurawa yaron dake barci nade a ciki a
showel a hannun shi.
Na zauna ina cewa ai yanzu naga zaka fara dauka tunda dai Amir din badani yai
kama ba.
Dawa yai kama ya tambayeni cikin dago kan shi yana mai kura min idon shi.
Ina dariya nace ai kaima kasani ni bai biyo ni ba,duk kaine ko yaya sagir ne ko
yaya Ahmed oho ?.
Da sauri yace Ahmed kuma Fatima please ki bar hada min yaro na da,wanan mara
mutuncin mutum wanda bai san Allah ba.
Nace hakkuri za,ayi yaya tunda ya riga da ya aikata yanzu baba ne abin tausayi
wallahi don na san har gobe koda yake haka abin yana damun zuciyar shi.
Yace ai Monday zamu shiga kotu dama zancen ne na suna ya hanani sukuni don naga
mutumin da yasai gidan baida mutunci ko kadan wallahi.
Yadda naso mu rabu dashi lafiya hakan baiyuyuwa sai anyi rashin mutunci dashi
za,a wanye lafiya.
Don kamar ma da gaiyya ya,sai gidan don Sagir yace min wai yaji yana fadin zai
saka a rushe gidan yayi maikatan shimkafa ne a gurin don idon gari gidan yake.
Nace ikon Allah kada Allah ya bashi ikon yin haka a,rayuaan shi da ya barwa
mutane abin gori har tarihi.
Nace amma yaya yanzu mama Asiya tayi matukar sanyi sosai sai neman shiri takeyi
da mutane.
Ko dana haihuma tare da ita fa muke kwana a,asibiti har aka sallamay ni.
Yace wanan dadin bakin sai tai maku kuda bakusan halinta ba ai kaikayine ya koma
kan mashekiya.
Don ni suka so na lalace na aikata hakan uwana tashiga balai Allah ya karw ni.

Ya mike yana fadin barin fita zuwa wajen wa yancan marasa mutuncin inji yaya zamu
kare da su.
Nace suwa ke nan fa ?
Yace Rahama da kungiyar ta na yan iska mana da tazo min da fitina gida.
Nace sai anyi hakkuri suma basu zaci cewa al,amarin zai kai haka ba ai, sunzo ne
suyi son ransu suyi muna iskanci su tafi.
Sai Allah yafisu suka samu wa yanda suka fisu balai a gidan suka jamay dasu.
Wai ki fada min gaskiyan yadda abin ya faru don in san abin fadi a can.
Tsaba na mayar mashi da komai yadda akayi akai fadan yace ai bari zanyi maganin
su don zan masu kashedin shigo min gida watarana ne wallahi.
Nace amaryan naka zakaiwa wanan furucin haka kasan fa itama nan gidan ta ne tana
da ikon da zata shigo ko ina take so a gidan.
Harara ya watso min yace a,a kila dai kece zata aura bani ba dai kan don ni
wallahi har gobe na tsani mutanen nan marasa mutunci.
Jiya wata matace ra rufe ido take fada min abindaya faru ne haka naso nagane ta
amma ban gane taba.
Nace ai matar Atiku mai wanki ne mana matar da kullun take godiya kan taimakon da
kaiwa dan ta a baya Aliyu mana.
Yace Allah sarki itace wallahi gar gobe ina son in taimaki yaron ya zama wani
abu idan ya girma don na wanke mai wanan bakin tabon a rayuwan shi.
Allah ya nufa nace mashi yace sai ya dawo nai mashi Allah ys tsare yafice daga
gidan.

Yana fita ya samu mutane cinjim a kofan gidan shi iyayen yaran da Rahama ta,
gaiyyato su rako ta nan suka shiga bashi hakkuri akan ya jaye maganan don yan sanda
sunce wai kotu za,a kaisu.
Sai ga Baba sani da motar shi ko kashe motar baiyi ba da kyau yafito cike da
masifa babban riga yana jan kasa.
Yace ashe baka da mutunci haka sadauki ban sani ba kai har ka isa kasaka a kule
muna yara su kwana a caji office.
Sadauki yai murmushi yace amma Baba kaji irin rashin mutuncin da,suka zo gidana
sukayi ko?
Kai har ina gidan yake da kakewa mutane wanan wulakancin haka kan shi akan wanan
yar matsiyantar matar taka kake son wullakanta muna yara kamar wata mai asalin
kwarai can.
Baba maganan ya tsaya iya ni daku kada ka hada da yar mutane please ?
Ko nima zaka saka a kulleni ne idan na zageta din ?
Bai mai magana ba don yasan dalili yake nema kawai ya shiga motar shi ya nufi
police station din inda ya samu su Rahama sun ji jiki sosai dan kwana dayan da
sukayi a rufe.
Nan yasaka akai masu warning akan kada su kara shiga mai gida gaba dayan su idan
ba haka ba zai yi karan su again a kulle su kuma.



ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU

IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,,,,


IDAN KIN BIYA KIKA,TURAWA WANDA BAI BIYA BA DAKE DA ALLAH,,,

Munyi arbain yaro yayi matukar kyau dashi gashi sai kara murjewa yakeyi yana kara
haske da kiba sosai.
Ga sadauki yanzu sai ahari,a akan gidan su sukeyi da dan masani wanda yaja sosai
a kan zancen.
Anyi nasaran kama yaya Ahmed an kulle shi a cewar Baba ma kada a sake shi a rufe
shi don matsayin shi daya da barawo a gare shi.
Tunda gidan shi ya shigo mai ta dakin shi ta baya ya fasa ya shiga ya kwashe mai
duk wani abin kwarai nashi a lokacin.
Don haka sata yazo yai mai a gida kuma ya kwashe mai takardu da ga baya yazo ya
kwace mai gida.
Hankalin mama Asiya yai matukar tashi sosai jin irin hukuncin da baba yace a
yankewa yaya Ahamed.
Sai gata a gidan mu tunda farar safiya ta sallama muna lokacin na gama shiri na
tsab nayi kwalliya Iyya tayi wa Amir wanka takawo shi ya sha nono.
Don shan nono kawai ke kawo Amir gurina da ya gama kuma zata goya shi sai idan
ya falka ko tana daki su kwanta tare.
Haka nake fita na barsu zuwa school don ina semester karshe yanzu ga karatuna.
Sallaman mama yasa mu fitowa daga dakina ina rike da yaro a hannu ina bashi nono
muka fito falon.
Mama Asiya ce zaune saman kujera ta rafka uban tagumi cikin damuwa take.
Nace a,a mama sannu da zuwa ashe kece mama shine kika zauna a falo baki shigo ba.
Tace Fatima ba zama nazo ba mijinki na zo gani Allah dai yasa yana gida bai fita
ba ?
Nace yana nan mama tace yi min magana dashi don Allah Fatima kice gurin shi nazo.
Na nufi dakin tabini da kallon yadda na koma wata fresh dani sosai kamar ba Bintu
ba can.
Yana kwance ya kifa ciki yana barci na,shigo dakin na samay shi a hakan .
Sai da na zauna bakin gado na dan fara taba shi a hankali ya bude idon shi ya
dago kai yana kallo na.
Ina zaune ina kallon shi ina gyara yaron a nono nace ina kwana ina dare da fatan
an tashi lafiya ?
Ya dan goga kan shi a filo ya gyara mirginowa yana kallon mu yace my friend har
ja tashi kai wanka ni ina kwance ko ?
Nace tuni mukai wanka kaima ka tashi kai wanka sai ka karya sai dai mama tana
falo tana jiran ka.
Yace mama tare da kallon agogon bangon dakin shi da ido yace wata maman ke nan ke
jira na kuma ?
Nace mama Asiya ce mana Asiya kuma may kuma ya kawo ta nan gidan ko dama takanzo
ne wai ?
Nace gaskiya bata taba zuwa haka ba babu wani dalili sai yau kawai tazo ya ja
tsaki ya mike zaune da kyau sai da ya shiga bandaki yai brush yafito daga dakin.
Ya karbi Amir a hannu na ya fice da shi ina bayan ta jin motsin fitowar mu daga
dakin ta dan gyara zama da kyau tana cewa kafitu Sadauki ga mamakin shi sai yaga
yau itace ma mai gaisheshi kafin ya gaida ita.
Yace lafiya dai mama naganki da sasafe hakan ga ko wani abu kuma ya faru ne a
gida.
Maimakon mama tayi magana sai kawai ta fashe da kuka mai tsuma rai sosai.
Yace haba mama may yafaru ne ban son wanan kukan da kikeyi ni fa dan ki ne mama
don Allah may ke faruwa ne please.
Mama ta dan tsagaita kukan ta tace sadauki nazo gurin ka ne neman taimako akan
dan uwanka da ke a tsare.
Don Allah sadauki ka saka baki wa baban ku ya dan sasauta kalamin da yayi akan
wai a daure Yaron nan da yace.
Yace mama amma dai kin san Ahmed bai kyauta wa Baba bai kuma kyautawa mu yan uwan
shi ba.
Babu abin kunyan da yafi ace wai dan uwanka yasayar da gidan ku na gado ga kuma
mahaifin ku da rai.
Tace na sani sadauki yaron nan bai kyauta ba ba ku kadai yaiwa tozarci ba har ma
dani mahaifiyar shi tunda ina a cikin gidan yanzu.
Tace kaiwa Allah ka taimaka a tsare shi a lalabeshi ina sauran kudin suke aji
idan yaso idan zai biya sauran da gabaya ne sai muji yadda za,ayi.
Sadauki ya gyara rikon yaron dake a hannun shi yana cewa mama ai antambaye shi
babu kudin a hannun shi yanzu yace yayi sayayan kayan part da yake sayarwa saura
kuma matar shi ta sai abubuwan bukatan ta.
Tace da karfi dama na,sani aidama nasan wanan shegiyar matar tashi yarinyar banza
itace ta saka shi a,wanan halin.
Sadauki yarinyar nan tun farko na fadawa yaron nan ba matar auren shi bace ita
yarinyar da ta san kaduna tasan lagos itace zata zauna zaman aure agidan wani.
Ko fa,abinci bata iya yi mashi gashi nan kullun cikin yawon zuwa saye ko yazo
gurina yaci sai Alhaji yai mai fada yanzu ya bari.
Idan dai tace ga abin da take so duk inda zai shiga ya samo shi sai ya shiga ya
samo mata shi ake zaunawa lafiya in ba haka ba ko ba,su da zaman lafiya ita dashi
ke nan.
Yace kai amma gaskiya bata kyauta ba wanan aiba so bane kamar ba auren soyayya
sukayi a tsakanin su.
Mama tace soyayyan may can kuma dama aiba son shi takeyi ba karya yai mata shi
mai kudi ne kuma dan mai kudi.
Kakaga ko akwai karya acikin wanan yanayi koba gaskiya ba .
Yace Allah ya kyauta mama tace amin cikin damuwa tare da nisawa takara fadin
yanzu don Allah jika kaida Fatima gwanin ban sha,awa da ku ga zuria Allah ya fara
baku a tsakanin ku.
Kowa yaga yadda zaman ku yake sai yai maku sha,awa sosai don ga yi nayi bari na
bari ba irin wancan mai bakin auren tsiya ba da duk ta halakamai rayuwan shi ko.
Mama yanzu ki koma gida naji bukatan ki insha Allahu zan san abinda akayi abin
yazo da sauki ai Ahmed dan uwana ne najini ba zan so naga ya,wullakanta ba nima.
Godiya sosai mama tai mashi har da saka mai albarka da fatan gamawa da duniya
lafiya (kudi ke nan)
Nan dai ya mike itama ta mike yai mata rakiya har kofan gida ta,shiga motar ta
wanda ya fara jin jiki yanzu sosai.
Sai da yaga fitan ta daga gidan ya sauke ajiyan zuciya ya tsaya suna gaisawa da
su maigadi har suna tambayan lafiyan Amir dake a hannun shi.

****** ********* ******
Mama tana komawa gida dakin maji ta shiga ta samay ta,a zaune tana karyawa ganin
ta a,shiri kamar fita zatayi yasa take kallon ta da mamaki.
Sai da ta samu guri ta zauna take cewa daga gidan sadauki nake yanzun haka.
Gidan saudauki maji ta tambaya tace eh na tafi na samay shi ne kafin ya fita akan
zancen yaron nan.
Don ya taimaka Alhaji ya jaye zancen daurin da yace sai anyi mashi nasan yayi
laifi mai muni amma sai ina ganin daurin da yace aimashi kamar zai iya kara jefa
shi a cikin fitina kuma ya kara hinjirewa yafi haka.
Don Allah idan sadauki ya shigo ki ka taimako na hjy maijidda kiyi mai magana duk
da dai yai min alkawari akan na kwantar da hankalina zai duba al,amarin da idon
basira in Allah ya yarda.
Maji tace ai tunda kin mashi magana zai duba din da ke dani ai duk daya muke a
gare shi don duk uwanshi muke Ahmed kuma ai dan uwan shi ne.
Tace amma zan kara mashi magana nima akan magana don ya duba al,amarin.
Tace nagode tare da mikewa tana fadin barin tafi na duba yaran nan na barsu basu
ko tashi ba na fita daga gidan.
Allah ya sauwaka mama tace mata tace Amin tana tsaye take cewa aini godiya na ga
Allah shine sadauki yana da abin hannun shi da zai iya taimakawa dashi.
Hakane inji maji tace da yanzu ai duk munsan inda muka nufa tunda mai gida yace
yana bukatan gidan shi da,wuri haka.
Sai da ya gama abinda yake ya shirya ya fita daga gidan ya nufi gidan su ganin
iyayyen shi.
Ya samu mama a dakin ta suka gaisa nan take cewa dashi sai ga hjy Asiya kun gani
da sassafe haka yace eh tazo dazun itace ma ta tayar dani daga barci ai yau din
nan.
Nan yake fada mata yadda suka kwashe da mama din tace tunda taje har ta ganka sai
kasan yadda zakayi da shi yanzu.
Kayi kokari ka taushi mahaifin ku yayi hakkuri akan maganan da yayi yace ai babu
damuwa maji.
Ya nufi gurin mahaifin su don ya gaidashi ya samay shi zaune a keken dake taimaka
mashi ga tafiya wanda shi sadaukin ne ya kashe kudi masu yawa ya saye shi don baba
din ga shawaran da likita ya bashi a can.
A mutunce ya durkusa ya gaida baba din sanan ya tambayi lafiyan jikin shi ?
Baba yace Alhamdullahi can baban yace yaya zancen kotun naku yakaya ne cikin
maganan shi da ba fita yake sosai ba.
Kan shi ya dago yace Baba ai mun yi magana ta fahinta da mutumin yace a jaye
karan idan har zan biyashi kudin shi na,kara mai riba a sama.
Baza,a kara mai ba inji baba aiko shi mai laifi ne don ba gaskiya bane yasan ina
a raye ya sai mingida ga hannun dana.
Sadauki yace hakane baba ai yanzu shi lauyan tanan ya bullo mai shine yasa
hankalin shi ai ya tashi sosai.
Don da da farko yana ganin zaici riba ga maganan amma yanzu jikin shi ya fara
sanyi kan case din.
Ance halinshi ke nan ko mutuwa akayi sai ya kwace gidan marayu ya,saye a araha ya
cuce su.
Baba yace shine ni bai jira na mutu ba yazo cin nawa ko?
Kayi hakkuri baba kaddarane duk haka ba kyau ma gana tuna aanan zancen a zuciyar
ka don kara tayar ma da hankali kawai maganan zaiyi.
Insha Allahu gidan ka har yanzu yana a matsayin naka illa iyaka mubashi kudin shi
daya,bashi Ahmed din shike nan a zauna lafiya.
Shiko Ahmed din ku kulle dan banza can yayi iya rayuwan shi a gidan yari don
banga amfanin haihuwan shi ba ni.
Hakkuri dai za,ayi baba ai yanzu shima a cikin tashin hankali yake ko yaushe.
Wanan yarinyar da ya,aurace ke kaishi ga halaka akace don ba yarinyar kirki bace
wallahi.
Bashi ya aurota ba inji baba sadauki yai dariya yace baba kaine fa ka,yarde mai
bayan mama ta hana abin .
Shiru baba yayi yana daya sani a,ranshi don

87 / 92