Advertisements
Chapter 8 Reading A Lokacin Mu Ke by Zainab Idris Makawa Seenabu BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

A Lokacin Mu Ke by Zainab Idris Makawa Seenabu

Author :  Zainab Idris Makawa Seenabu Category :  Complete Novels

Chapter   8 / 92

21K to 24K   out of 275.8K words

kawai suke samun fuska a
gidan nan har nadawo na,samu sunci abinci hankalin su a kwance.
Don may yau zanga naki cikin wani hali na kasa nuna bakin cikina akan hakan abin
baiyi dadi ba gaskiya amma ayi hakkuri don Allah.
Hawaye ne suka zubo wa Maji daga idon ta take cewa hajiya, kubura ban san yaya
zanyi da,wanan yaron ba a,rayuwa ta duk yadda ake ba yaro tarbiya nasan ina ba
sadauki shi a,rayuwa amma a karshe duk ya,watsar dasu ya zabi wanan harkan
na,shashan ci.
Hmm abin fa yanzu sai addua don ya fara zama ruwan dare ga matasa sai dai wanda
Allah ya kare kawai shine ya tsira.
Na san zafin wanan tun a gida don ina da kani mai irin wanan rayuwan amma cikin
ikon Allah yanzu ya daina ya koma normal mutum din shi kamar kowa.
Wani abinda baki sani bama shine abin fa ba mazane kawai ba harda ma mata wallahi
mata ma ba,wai yara ba manyan mata hamshakai wallahi.
Ke dai kawai Allah ya gyara muna amma a lokacin muke da in kana da da namiji ko
mace baka huta ba kowa da tashi irin matsalar.
Ki dai yi hakkuri kada ki sa zancen a ranki harki jawa kan ki matsala babba yazo
yai maki illa a,rayuwanki.
Maji tai mata godiya inda hajiya Kubura ke cewa don Allah a dake da addua da
rokon Allah kuma ki toshe kunnnen ki ga duk wani magana ko gorin da wani zai maki
don ba wanda ya wuce hakan ai.
Maji takara cewa nagode Hjy Kubura nagode kwarai Allah ya saka da alheri tabar
dakin tana masu sai da safe.
Ta kawo daidai tagan hjy Asiya taji tana cewa yaran ta wallahi kuyi hankalin da
mashayin nan na gidan nan kunga ya fara haukacewa don haka duk wanda ya shiga
tsabgan shi kun dai san ba,a shari,a da mahaukaci sai dai ace kuyi hakkuri an cuce
ku.
Shigewa tayi part din ta tana jin kamar ta hade ranta yadda zancen yake mata kuna
a rai.
Ikon Allah yau Sadauki dan cikina ake kirawa hauka da raina ikon Allah Allah ka
taimakeni ka,shirya min wanan yaron ya Allah na rokeka.

Hajiyan masa bata zaina ba da dare ma sai gata ta dawo gidan ta kara ba Maji
hakkuri inda suka kara tattaunawa akan al,amarin tai mata alkawarin shiga da fita
don suga ya daina wanan harkan.
A nan tabar Bintun ta don dama ba yazo don ta,bane sai dai duk shiyan nasu ranan
haka suka kwana cikin bacin rai babu maidadin rai daga cikin su.
Washe gari ma haka suka tashi sukuku duk ran su ba dadi saida safe ne Alhaji
yakira su gaba dayan su ya tarasu a falon shi.
Inda ya kira sadauki da sauran yan uwan shi suka zauna don tattauna matsalar
da,ya fada ciki.
Bayan gurin ya natsune maigidan yafara magana kamar haka.
Dama nataru kune nan don kowa yasan akan dalilin dana kiraku nan, batare da dogon
magana ba ina son kowan ku yasani Umar gashi nan a gaba na daga yau na yafe shi
daga cikin diya na.
Don ba zan zauna da dan da zai jawo min abin kunya ba a gidana, na,wuce ana
nunani ga mahaifin mashayin nan can.
Kuma ka sani daga yau kada ka kara shigo min gida don kada ka bata min sauran
yarana kimtsatu.
Uwargidan su tace gaskiya wanan matakin yayi daidai wallahi don gaskiya nima tun
jiya nake wanan tunanen don barin shi cikin mu gamu da yawa a gida yana iya sa wani
yaron yai koyi da halin shi na banza.
Mama Asiya itama ta tare zancen dacewa nima wallahi hakan yai min daidai don
gaskiya barin shi a cikin mu babban hatsari ne don kada wata rana ya zo ya shawo ya
kama mu da bugu.
Wani irin zafi da dacin zuciya Maji take ji shiko sadauki kan shi yana duke don
kunyan mahaifiyar shima yake ji ba nasu ba don yasan shine ya jawo mata wanan sukan
da ake mata mai kama da an daba mata wuka a zuciyar ta.
Assha Alhaji wanan maganan da kayi wallahi ba girman ka bane.
Ka taba ganin inda hannun mutum ya rube ya yanke ya yar dashi, don Allah ya
jarabi wanan yaron da wanan lalurar shine zaka yanke wanan danyen hukuncin haka
akan shi.
Wallahi baka kyauta masu ba ko kadan in kai masu haka daga shi har uwar shi.
Idan bamu jashi a jiki muka nuna mashi illan abinda yakeyi ba kyau ba, watau ya
tafi ke nan yafi nan lalacewa ko?
Gidan kowa yanzu akwai matsala in hat gida babban gida ne amma kowa hakkuri yake
yana boye abin shi yana jan kayan shi a jiki.
Amma ya daina shigo maka gida dakace ita uwar shi a ina zata gan shi har tasan
halin da yake ciki ta tsawata ma abinta.
Da dai ka haife shi kuma jerabawa ya fado kan shi sai ayi hakkuri anema mashi
shiryuwa ga Allah shine daidai.
Kai ji hajiya kubura wallahi ni ban son al,amari da munafunci uwar ahi in tana
son ganin dan ta taje gidan mashaya ta,samay shi mana inda yazabi zama.
Umm,umm hajiya Asiya wallahi daji bai gama cin wuta ba ba aiwa kututure barka,
kema fa uwace kamar hajiya maijidda don haka kii iya bakin ki.
Tuff tuf wallahi bakin ki ya sari danyen kashi wallahi nikan ba,a cikin kayana ba
wallahi, watau baki kike min akan diyana ko ?
Ni ba baki nai maki ba gani nayi ko ita uuwar shi bataso dan ta da hakan ba,
jerabawa ne dai daga Allah ya fada kan shi.
Kaidon Allah ni ya,ishe ni ban kira ku nan ba don kuzo kuna min cacan baki kiran
ku nayi don ku ji shawarana.
To gaskiya Alhaji shawaran ka bai yi ba gara ka canza wani, wani irin huci
Alhaji yayi yafitar da iska daga bakin shi.
Yace naji amma idan ya ganin ni wallahi ya kama kan shi inba haka ba zamu sa
kafan wando daya dashi a gidan nan kaji na fada maka yaron banza yaron wofi kawai.
Tashi ka bani guri mara mutunci kawai mun sakafan wondo daya dakai a gidan nan
wallahi ko.
Allah dai ya,shirya muna shi kawai za,ace amma wanan fadan ai bayi ba,wallahi
tana fadin haka tamike tabar dakin cikin bacin rai, sauran suka bita da kallon ke
asuwa munafuka mun san sallon kishin ki ai.
Ita ma Maji mikewa tayi tabar dakin tabarsu nan tafada dakin ta tana kukan bakin
ciki da takaici.
Yau dan ta yaja mata wullakanci ga kowa agidan saboda shi anzaunar da ita ana
fada mata magana son ran mutum.
Shiko Alhaji ya mutuwan son hajiya kubura badon yaso ba ya yarda da,shawaran ta
don kawai kada su sami sabanine a gidan.

****** ********* ******
Tun da akai wanan case din sadauki bai kara,shigowa gidan ba yau kusan sati daya
ke nan haka ranan abin da da mahaifi maji tatura maryam ta duba mata shi idan yana
nan takira matashi don tana son suyi magana dashi.
Itama hajiya kubura ko yaushe tana tambaya idan yadawo ko ya shigo sai maji tace
mata bai shigo ba ai.
Maryam ta samay shi a kwance dakin shi ya yi kwanciyar rigingine yana kallon
saman dakin ta tsaya daga kofa tagaida,shi tafada mai sakon mahaifiyar su.
Yace taje tace gashi nan zuwa, ta dawo ta fadawa maji abinda yace mata bayan
kamar minti goma sha ya,shigo gidan sai dai bai shigo ba kamar yadda ya saba ya dan
tsaya daga waje kadan ya tura wani dan kannin shi ya kira mai maji dakin ta.
Yaron yashigo yana cewa yaya sadauki ne yace na kiraki yana daga waje wai.
Amira tace bazai shigo ba ke nan bari naje na shigo dashi, maji tace ai kunya
marin da ne .
Amira na zuwa tace yaya Maji tace nace kashigo daga ciki mana ka tsaya nan .
Yace look Amira ki fada mata bazan shigo ba gani nan dai tazo ina jiran ta,
tausayin dan uwan ta ya kamata ta juya rai a bace takoma ta fadawa uwar nasu abinda
yace mata.
Maza jeki kice mashi nace bani son diban albarka shi da yai laifi ba,ai fushi
dashi ba dai shine zai wa mutane zuciyan banza.
Amira na fada mai sako sai gasu a tare sun shigo gidan da ita.
Yana saye da farin shadda a jikin andanyiwa shaddan kwalliyan dan bakin kyalle a
gaban rigar da fari.
Ya shigo da,sallama ya koma kaman wani kamili dashi ya ramay yai dan dogon wuya
sai dan bakin da yayi.
Maji ina wuni kamar bazata amsa mashi ba tai shiru ya samu guri ya zauna a saman
kujeran dakin.
Tausayin mahaifiyar shi ne ya kama shi don ita ma ta,ramay ta,fada sosai da ka
kalleta kasan tana cikin rashin kwanciyar hankali sosai.
Yaya ina wuni muryan Bintu da ke mikewa zata shiga daga ciki ne ya katse mai
tunanen shi a lokacin.
Lafiya kawai ya amsa mata,dashi sai kuma dan abinda ya,faru ranan yafado mai a
rai din ya dan iya tuna lokacin da ta bude mai baki kan shi yana samancinyan ta ta
tura mai manja a ciki.
Wani irin kunyane ya kama shi da nauyin yarinyar don yasan ta taimaka mai har sau
biyu a rayuwan shi.
Maji tace kai ba,ai fushi dakai ba shine kai zakiyi da mutane ko, da kai fushi
kaki shigowa may kake nufi da yin haka.
Maji ba,wai hakana bane kinji abinda baba ya fada ai shiya sa ni kuma naga gara
kawai nabar shigo mashi gida kada na ja maki matsala.
Matsala kuma na yaushe sadauki akwai maysalar da kuma yafi wanan din da ka jawo
min ne a cikin gidan nan.
Maji don Allah kiyi hakkuei wallahi kaddarace amma ban taba shan kwaya ba sai
ranan koshi bacin raine na rashin barina nabi abokai na gurin kwallon da akayi
yakaini ga hakan.
Insha Allahu bazan sake hakan ba da yardan Allah don Allah dai kiyi hakkuri maji
ya fadi cikin kwantar da muryan shi.
Yanzu Baba na kana ga inin irin hanyan da ka daukar wa kanka shine daidai gareka
gare mu ma.
Kaiwa kanka fada,wallahi ka dibs ka gani saboda kai aka zaunar da ni kowa na
fada min irin abinda yaga dama a lokacin.
Inda ka gyara halinka duk gidan nan wa ya isa yai muna haka babu shi wallahi don
ni ba ruwana da harkan kowan su.
Amma sanadiyar abinda ka aikata ji irin yadda kowa ya takamu son rashin ana fada
muna abinda aka ga dama.
Maji kiyi hakkuri don Allah insha Allahu ba,zan sake ba da yardan Allah hakan
ba,zai sake faruwa ba.
Nan dai taita mashi nasiha tana cewa yanzu ashe badama su Amira su yi laifi na
kawo maka karan su a matsayin ka na babba a cikin su.
Ni hajiya kubura wallahi tai min komai don ta nuna min ita uwace a gareka kuma
tasan ciwon kan ta ba kamar sauran iyayyen naka ba.
Don haka wallahi kaiwa kanka fada kaceci kanka kace ceni ni uwarka da yan uwanka
kafitar damu daga zagi mutanen duniya.
Sun kai wani lokaci tace ya tasgi ya tafi take ce mai kuma daga yau ya tabbatar
da ya dinga zuwa gida yana cin abinci bata son yana ci a waje inda batasan ko ina
bane.
Yai mata godiya ya mike yabar gurin tare da kara bata hakkuri yabada baya take
cewa jika don Allah kamar wani mutumin kirki can ashe mutimin kawai.
Murmushi yayi yace kiyi hakkuri maji don Allah bazan sake ba insha Allahu.
Yana fita ta sauke ajiyan zuciya tare da cewa a filo Allah ka,shiyar mun da wanan
yaron dama sauran yara masu halin shi na,wanan lokacin,,,,


ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU

IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,,,,


Baby yaya zamuyi ne ina son ki rakani zuwa lagos don ina da seminar da zamuyi a
can, kuma dake nakeson zuwa.
Shiru Raiha tayi tana nazarin zancen shi a cikin ran ta don tasa abu mai wahala
ya dauko mata.
Yaya zatayi da uyayyen ta a gida may zata fada masu ina zata ce masu zata tafi.
Muryan shi ne ya katse mata tunanen ta yana cewa naji kin yi shiru mana ko baki
san rakani ne wai?
Hmm ba,wai hakana bane kasan in da hali koma ina ne zan iya raka ka amma ban san
yaya zanyi da iyayyena ba may zance a gida.
Haba baby sai kace wata local can dan karya kawai zaki shirya masu mana kice
zaki gurin wani dan uwan ki koda kauye ne kinga indan munje mun dawo sai na kai ki
garin ko kwana daya kiyi sai ki dawo ko?
Nan ma,Raiha shiru tayi tana tunanen akan zancen shi don tasan abune mai wuya
abarta zuwa wani guri ita kadai.
Gashi kuma tana son bin shi sosai a ranta don batajin yanzu zata iya rabuwa dashi
ko na dan lokaci kadan ne.
Sai cewa tayi zan yi shawara don nasan abinda zan yi akan tafiyan.
Huci yayi don jin dadin yasamu yadda yake so daga gurin ta nan ya shiga yi mata
abinda yasan tafi bukata daga gare shi har suka kai ga,watsewar su a hotel din da
ya kaita.
Da zasu rabu ne yake jadfa mata cewa next week ne fa sunday tafiyan su kuma da
jirgi zasuyi tafiyan, don haka yana son yasan idan zata tafi ya sai tickets din su
shida ita.
Ba matsala tabashi amsa zansan yadda zanyi mu tafi din tare insha Allahu.
Wani shu,umin murmushi ya,sauke tare da,shafan dogon fuskan shi ya na cewa dat
is my baby shiyasa nake kara,son ki.
Tun dawowan ta gida take ta faman sake sake a ranta sai kullawa take tana
warwarewa ita kadai a ranta.
Can wani dabara ya fado mata a rai tai wani murmushi daidai uwarta ta zo shigewa
take cewa, mama ina fa son zuwa kamba gurin su kaka na dubo su.
Kamba Raiha kedawa zaki tafi har kamba ? Raiha tace haba mama sai kace wata
karamar yarinya ni ko makka ai ina iya zuwa ni kadai yanzu.
Kai Raiha wai may kike daukan kanki ne yanzu har nawa kike da zakice zaki iya
kai kanki makka.
Yanzu dai mama da na shiga mota daga nan sokoto ba sai jega ba daga jega ga
motocin zuwa garin kamba nan sai na,shiga kawai.
Eh lalai ashe ko zaki iya aiko kin kyauta bari malam ya dawo na fada mai Allah
yasa ya barki dai ki tafi din .
Raiha cikin marairai cewa take cewa don Allah mama ki tayani rokon shi ya barni
ba dadewa zanyi ba sati daya zanyi nadawo kawai.
To shike nan bari yadawo din muji yadda za,ayi idan zai yarda sai ki shirya ki
tafi aini wallahi kin kyauta min nasha kulla tafiya na dubo su amma sai abin bai
yuyuwa.
Yanzu kinga ai inkije sai ki taimaka min nasan halin da,suke ciki a can din.
Sai da,dare bayan mahaifinta ya dawo ne take sheda mashi bukatar yarsu na,son
zuwan ta kauyen zu garin kamba wanda ko anje kambadi sai an shiga mota ko mashin
zuwa can.
Haba nana yanzu kamar Raiha ne zamu saka a mota daga nan har kamba ita kadai
a,wanan zamanin da muke ciki.
Malam insha Allahu zata iya ai yanzu tasan hanya zata iya kai kanta ita kadai
bada wani ba.
Nan dai suka kama inyafito nan tafito mai nan abin mata da miji har ya yarda da
zasu tafi ya bata kudi tayi sayayya da kudin mota wanda zai kaita.
Sosai Raiha taji dadi a ranta nan take ta kira Nasir take sheda mashi halin da
take ciki.
Yai murna yaji dadin samun nasaran da sukayi don haka washe gari yaje yai saya
masu ticket din tafiyan su.
Bayan kwana biyu suka shirya sai air port inda suka tashi zuwa garin lagos ita
da shi.
A wani katafaren hotel ya sauke su ita dashi inda tun ranan ya fara nuna mata
wane shi, don dama can ashe a sannu yake binta.
Bata da hutu a gurin Nasir don kusan a kanta yake kwana har gari ya,waye.
Tun tana iya jurewa halin Nasir har Raiha tafara raina kan ta da kanta don yanzu
yakai bar ta baya yake ne manta.
Da farko takiya amma da tasha duka a gurin shi dole ta yarde mashi yana yadda
yake so da ita.
Idan sun gama kuma ya dauko kayan maye ya dirka mata sai ta futa hankalin ta .
Sati dayan da sukayi Raiha tagan shi kamar shekara daya ne na,wahala da ukubar
zugubar namiji a gare ta.
Sam babu tausaya tsakanin ta da nasir ko kadan kamar ba soyayya ce ta hada su ba
don yi yake kamar ya samu boya.
Saura kwana uku ta dawo ya shiga da ita gari shida wani abokin shi suka je zaga
garin da ita.
Yai mata sayayya sosai na abinda duk tagani tana so a fitan nasu taci kayan ciye
ciye masu kyau sosai da tsada.
Bayan sun dawo sai taga wanan dayan abokin nashi baida niyar tafiya kamar yadda
tai zaton tafiyan shi.
Ashe bata sani ba aun hada plain a tare shida Nasir zasuyi amfani da ita gashi
shi ba ko musulmi bane dan uwan ta.
Nan suka samay ta da ihu da komai suka kwana a kanta suna juyata yadda suke so.
Tai kuka har tagaji tahakkura ta kyale su suka gama don kan su ka barta, abokin
nashi yata yaba ma dadin ta har yana rokon Nasir da ya bar mashi ita for ever amma
nasir din yaki yarda da hakan.
Yake cewa Michael ai ba,addinin su daya ba don haka ba,zai yarda ya zauna da ita
ba.
Bai san bayan sunyi barci Michael ya dauki

8 / 92