Advertisements
Chapter 52 Reading A Lokacin Mu Ke by Zainab Idris Makawa Seenabu BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

A Lokacin Mu Ke by Zainab Idris Makawa Seenabu

Author :  Zainab Idris Makawa Seenabu Category :  Complete Novels

Chapter   52 / 92

153K to 156K   out of 275.8K words

kawai ba wani
ba,a fada masu ba ko anfada masu ma basu zuwa aini na dawo raka wa yan nan mutane
ko dan basu da imani.
Inkana binta nasu sai su kona mutum ga banza da wofi da jahilcin su wallahi.
Maji batai mai magana ba sai da yakai kaman kwana goma da dawowa tace tana magana
dashi.
Ya shigo suka danyi magana da Amirah mutumiyar shi ya shiga gurin maji don dama
idan zasuyi wani magana da yake serious daki suke shiga shi da ita.
Ya samay ta zaune a bakin gadon ta ya zauna asaman kujeran dake cikin dakin nata.
Yace maji yaya zancen su Amirah ne tace ai akan zancen ne nakira ka nan.
Tacs baka nan babanku ya tara mu kan zancen auren ku yace yana son gaba daya kuyi
aure lokaci guda nan da karshen sabon wata.
Yace ni maji dama akwai yarinyar da muka shirya da ita akan zamuyi aure sai dai
matsala daya shine ita ba musulma bace gaskiya.
Da sauri maji ta dago kai tace kafira ke nan ko may sadauki?
Yace eh maji Christian ce ita, yar kasar ghanace amma idan munyi aure nasan zata
musulunta ai.
Kai dakata ba cikin kayana ba wallahi.
Kada kasoma ka kara min zancen nan wallahi don zan bata maka rai sosai fiye da
tsanmanin ka.
Kai baka jin kunya ban gita cikin wani gorin ka ba zaka jefani wani idan su yaya
suka samu labatin nan ina kake son na jefa kaina.
Ban taba sanin rashin hankalinka yakai haka ba sai ysu din nan da har ka dubi
idona ba kunya kazo min wai da zancen auren kafira da bakin ka ko kunya bakaji ba.
Idan da kana da kani ko danka yace zaiyi wanan danyen aiki yaya zakaji a ranka.
Shiru yayi bai ce uffan ba sai ya dukar da kanshi kasa ya hada hannayen shi guri
guda yana dan jijiga kafan shi a hankali.
Itama mama shiru tayi don bacin ran da ya ziyarci zuciyar ta a lokaci guda bai
barin tayi magana.
Sai dai shi a zuciyar shi tunane yake ta hanya Baba zai gwada yagani ko da sa,a
don yasan ance Baba ne yai tsayewa Ahmad har zai auri wacce zai aura din.
Amma nashi dai akwai banvanci saboda zaman kafira bare kuma ba kabilar hausawa
ba.
Muryan maji yaji tajefo mashi tambayan da sai da ya girgiza mashi zuciyan shi
tana cewa.
May ke tsakanin ka da fatima ne ?
Da sauri ya dago ya kalle ta yace wata Fatima kuma maji ?
Fatima nawa ke gidan nan da kasani?
Maji badai Fatiman nan taki ba ko ?
Tace inba ita ba wata Fatiman nake nufi ?
Yace kai tsaye ni babu komai a tsakani na da ita maji?
Ance maki wani abu a tsakani na da ita halan ?
Maji tace sai an fada min ko tunda ni yarinyan ce?
Wallahi maji ni ba komai a tsakani na da ita Fatima ai a matsayin kaunata nake
daukan ta in ma,wanan ne shine kawai.
Shiru sukayi ba wanda ya kara magana daga cikin su ganin maji bata da niyan kara
mai magana yasa shi mikewa yana fadin shike nan maji tace tafi shike nan.
Har yakai kofa tace dakata wallahi sadauki duk ka sake har zancen arniyan nan
yafito a gidan nan sai na bata maka rai yadda ka bata min a gidan nan kagin kasa a
zageni acikin gidan nan dagari sai na fara yima tukun mara hankali kawai.
Yana fitowa fuskan shi ta canza kala yayin shi gaba daya ya canza a lokaci guda
kaman ba yanzu ya shigo da fara,an shi ba.
Amirah tana magana dashi amma ko kallon ta baiyi ba ya fice cikin bacin rai.
Duk muka bishi da kallon mamaki muna ko may yafaru dashi oho mashi.
Sai ga mama tafito dakin tana fada ita daya tana fadin ban taba sanin rashin
hankalinka yakai haka ba sai yau din nan?
Maji may kuma yayana yai maki yau kuma?
Sai da ta harari Amirah kamar da ita take fada tace bar mahankali da rashin
tunane kawai wai wata arniya yake fada min zai aura don ya gwada min shi dan
duniyan gaske ne.
Ashe ko dagaske yaya keyi da zancen wanan arniyan ya fada maki maji ?
Au dama kukun sani ne ke nan ko ?
Shi yanzu aka rasa wanda zai fada min a cikin tun baizo ba na tare shi mara
hankali kawai.
Maji ba yana son ta bane kuma shi zai zauna da ita abarshi mana yayi abinsh,,,
Bata karasa ba aiko maji tai cikin ta da fada sai da Amirah ta kwamce da bata
tanka ba gaskiya.
Maji tace ai dama zubin ku daya dashi baku san mutuncin kan ku ba balle kiji
zafin danaji.
Ranan kan naga fadan mama da bacin ran ta ance mai hakkuri bai iya fushi ba sai
ranan na tabbatar da hakan.

****** ********* ******
Da yamma da baba ya dawo maji taje gaishe shi tayi sa,a babu kowa agurin nan take
fada mashi Alhaji dama ina son in fada maka cewa.
Yaron nan fa yar gida yake son yi don da Fatima ce zasuyi aure ban dai fada maka
bane sai komai ya daidaita a tsakanin su dama.
Yanzun ko yazo angama magana itace kawai naga ta dace ya aura don yarinyar nada
natsuwa da hakkuri.
Cikin farin ciki Baba yace ikon Allah haka abin yake gaskiya nai farin ciki yau
dajin wanan labari don ni kaina na dade ina wanan tunanen a raina.
Sai gashi Allah ya karba min addua na a cikin sauki da dadin rai maganan tazo min
.
Zanga sadauki din in mashi murnan wanan babban albishir din da kikai min.
Tafita ta barshi da dadin rai sai murna yake har ya kasa boye farin cikin shi a
fili.
Washe gari Baba ya aika akira mashi sadauki anyi sa,a ya dawo daga exercises din
safe da yake fita da zaran sun fito daga sallah.
Rigan jikin shi ya sauya, ya nufi falon mahaifin shi don amsa kiran shi da
saurin shi don yasan ba kasafai Baba ke aikowa kiran shi ba.
Da sallama ya shiga falon ya samu Baba ya daga kofi zai kurba tea da yake sha.
Yana ganin dan nashi ya sauke kofin ya fasa kurbawa yana cewa sanda sadauki
sandagagare.
Zo nan zonan ka zauna yau in gwada maka farincikina dana kwana inayi jiya.
Mamakin may baba yaji akanshi yakeyi don rabon da yaji wanan kirarin da baba kan
mashi inyai abin jin dadi tun yana karamin yaron shi kafin ya fara shaye shayen su
bata.
Yace matso mana Babaatsonan kusa dani naji albishir din Alheri a gurin uwar ka
jiya da dare .
Tazo tana fada min kun shirya tsakanin ka da yarinyar nan Fatima zan iya cewa
nafi kowa farin cikin wanan hadin naku don na dade ina maka fatan haka a raina don
Fatima yarinyar arzikice a gareka duk wani namiji da yasan kan shi zai so ace ya
mallaki wanan yarinyar a matsayin uwar yayan shi nan gaba.
Duk bayanin da baba keyi sadauki ji yake kaman an watsa mashi ruwan zafi tun daga
saman shi har kan shi .
Yadaga kai ya fadawa Baba ba gaskiya bane wannan zancen, amma sai yaga farin
cikin da mahaifin shi ke ciki yafi karfin ya musulta shi a lokacin.
Ya san da zaran yace zai fada mashi gaskiyan zancen shi bai san komai ba akai
farin cikin rayuwan shi zai iya sayawa zuwa bacin rai ta zama mashi sana din tashin
ciwon shi.
Wanan dalilin yasa yaja bakin shi yai shiru, yana karba irin adduan fatan Alherin
da mahaufin nashi ke mashi akan zacen.
Sukai sallama ya mike gwiwan shi duk ya mutu da kyat yake iya daga kafan shi da
yake takawa a kasa dakin shi ya nufa cikin wani yanayi na susucewa a lokaci daya.
Yana shiga ya fada kan katifan gadon shi yayi yayi a lokacin ya samu ko dan kuka
yayi ko zai samu relief, amma abin ya faskara mai.
Wayan shi dake gefe ke ringing har yagaji ya katse don kan shi bai daga ba sai
kuma ga kiran ya kara shigo mashi lokaci guda ya daga daniyar zagin mai damun shi.
Bashar ne ya daga wayan yana tsaki yace yaya akayine wai Bashar din yace yana
kofan gida.
Yace shigo ina dakina yana shigo yanayin da yasamay shi a ciiki yabashi tsoro
sosai.
Lafiya may ya samay ka haka kuma ?
Ya watso maahi wani harara yace ban sani ba mugu ai kana daga cikin munafukan
dake son wargaza min rayuwana nasani ba yau ba.
Bashar na zama yace may kuma mukayi mi muna fukan da bamu son ganin farin cikin
ka?
Maimakon ya bashi amsa sai ya juyar da kan shi kawai gefe daya bai kalleshi ba.
Wai may ke faruwa ne wai ka koma haka lokaci guda kaman wani tababe yakara
tambayan shi mikewa yayi zaune daga kwanciyan da yake yana cewa.
Kana nufin baka san sherin da maji ta kulla min bane agidan nan wai ?
Innalillahi kana da hankali kuwa yau man ?
Maji ce kuma zata kulla ma sheri a rayuwanka ?
Wani kallo ya watsa mashi yace ba sheri banr may nene?
Murmushi Bashar din yayi yace don Allah may akayi ne wai ?
Yace kaaai wai maji ta fadawa Baba wai mun shirya tsakanina da wanan yarinyae mun
amince zamuyi aure.
Wata yarinya ke nan kake nufi wai?
Wata yarinya kake damuna akan ta gidan nan ?
Yace kana nufin wai Bintu?
Yace ita mana.
Alhamdullahi Alhamdullahi kai wani hikima sai manya wallahi tanan maji tafito muna
Allah mun gode ma.
Ya dago jajayen idon shi yana kallon Bashar dake ta kwada hamdalla haka cikin
mamaki.
Yace wanan abinda maji ta kulla min da may yakama Bassh?
Maji tarasa wace zata lakaka min auren ta sai wanan solaman yarinyar da
kwatakwata bata cikin tsarina.
O Lindan ce tsarin ka ke nan ko yar arniyan ka mai dan buje ko ?
Wani wawan nashi yakai ma bashar din ya kauce ma nashi ta hanyan ja baya.
Sadauki ya mike tsaye yace haba man may zanyi da wanan yarinyar ko maryam dina fa
batakai shekaru ba a duniya wai itace za,ace na aura ?.
Ita Fatima ba mace kake kallon ta ba ke nan ko ?
Wallahi zakasha mamaki kace na fada ma dan hakin daka rai shike tsone maka ido
watarana.
Kai may ya kawo kane ?
Yace manta yau zamu zamfara ne dakai ko kuwa?
Yace bazan tafi ba.
Dariya ya kama mashi yace kafara angwancin ke nan ko?
Zanci ubanka fa Bash wallahi idan ka kara bata min rai yanzu zan rufe daki dakai
nai maka tsinanen dukan tsiya.
Bashar yace sai dai yanzu kuma ka rufe daki da Fatima amma bani ba Bashar ba ya
juya yafara tafiya yace bari ma na shiga cikin nai ma maji godiyan wanan babban
albishir din da kai min.
Da sauri sadauki ya jawo shi ta baya yave kada ka farashi wallahi har ta zaci ko
nayi na,am ne da zancen har ina farin ciki da zancen ne.
Farin ciki kan ka kanayin shi komai dadewa zakace na fada maka ai.
Wallahi kada ka fara kaje gurin maji na fada maka, Bashar yace mai da yukan ka a
kube kamanta nima maji sarakuwa tave ina kunyan ta yanzu.
Kaima kuma ya kamata ka fara kunyan ta daga yau dan ta zama sarakuwar ka kaman ni
daga haka yafita dakin da sauri don yana iya shakoshi ta baya yadda yaga ya hasala.
Dan iska da ka tsaya kaga tsiya a dakin nan ya dade tsaye dafe da bango sai tsaki
yake shi daya a dakin.
Sai can yaji taahin motan Bashar daga gidan ya sauke ajiyan zuciya kawai



ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU

IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,,,


ALLAH DUK WACCE TA KARANTA BATA BIYA BA KAINE SHEDA INA BINTA BASHI,,,,,



Zaune take duk abin duniya ya damay ta a ranta ga shi yanzu daga ita har dan ta sun
zama abin magana a gari.
Ko a gaban ta zataji mutane suna bayar da labari yadda ma ba,ayi abin ba haka
za,a zake ana labarata shi.
Kowa da,kalar abinda yake fadi a bakin shi ba dama yaron ya fita sai yara abokan
wasan sbi su fara gudun shi kaman sunga dodo.
Haka zai dawo gida yana kuka yana fadin abinda yara yan uwan shi sukai mashi.
Abin duniya ya ishi mariya a ranta tai kuka har tagaji ta hakkura don kan ta
babu wanda zata kai kukan ta gare shi.
Gashi zaman gidan kawai takeyi tun lokacin da aka dawo da ita daga gidan su daya
tura ta manyan suka zo suka bashi hakkuri.
Ba don yaso ba ya hakkura da ita haka na amma zama takeyi ba abinda ke shiga
tsakanin su.
Koma cefane ne idan ya shigo dashi sai dai ya aje mata a kofan daki ba tare da
yai magana ba.
Idan kuma tana son wani abu sai dai ta tura yara su fada mashi abin da ake bukata
a gidan.
Ranan dai taga yana ta gyaran wani kangon dakin shi a zaton maria shine zai koma
ciki don ya bar masu dakin su sai bata kawo komai a ran ta ba.
Don dai tasan ba aure zaiyi ba mutumin da ko kudin cefane sai ya fita ya nemo
masu abinda zasu ci.
Ranan wani laraba ta zaune tana wanke wanke taji wasu mata su biyar sunyi mata
sallama.
Suka gaisa da ita sai suke fadin wani ne dakin da aka gyara daya daga cikin su
tace, tana ganin wancan ne da ke da sabon siminti.
Basu bi takanta ba suka nufi dakin suka shiga ciki suna dan dubawa anan suka
barta tsaye da mamaki.
Bata iya masu magana ba suka fita sai gasu da kaya suna shigowa dashi.
Kasa daurewa maria tayi tace wai bayin Allah daga ina haka bakuce min komai ba
kun kama shigo da kaya cikin gidan mutane.
Dayar matar tace a,a shi mai gidan bai fada maki yai aure bane yau matar zata
tare ma.
Ai mu amarya muka kawo yanzun haka munzo gyaran dakine ma kagin anjima mu kawo
ta.
Allah ne ya taimaka maria bata fasa ihu a gaban su ba amma sai ta fada dakin ta
can ta fasa abinta ita kadai tana fadin na,shiga uku yanzu da wani zanji halin da
nake ciki ko da zancen kishiya kuma?
Bata fito ba sai da taji fitan matan daga gidan mayagin ta ta dauko sai gidan su
ga girkin da ta dora a saman wuta nan tabarshi ta fita.
Da kuka ta samu uwar ta tana fada mata abinda ya samay ta nan uwar tashiga zagi
tana fadin amma Atiku ya cika tsohon macuci wallahi.
Yanzu da yake nan yana yawo kaman almajiri ashe har yana da kudin da zaiyi aure,
bamu sani .
Nan sukai ta kullawa ita da uwarta a tsakanin su har dare ya soma ta fito zuwa
gida.
Koda ta koma ta samu har girki ta ya kone wuta ya mutu don kan shi nan dai ta
kwashe shi haka na don bazata iya girka wani ba yadda take ji a lokacin.
Atiku na shigowa gida ta tare shi da masifa da jidali nan ya dakatar da ita yace.
Maria ki shiga hankalin ki wallahi kada na bata maki rai a gidan nan kin dai san
ina da haushin ki dama to ki iya kan ki dani wallahi ko ayita a akare a gidan nan
don dama kin kai min ko ina wallahi.
Nan ta shiga zage zage tana kiran shi macuci azzalumi dama ashe yana da kudi yake
ce masu baida shi yanzun ina ya samu kudin aure.
Yace wanan aure kikace dole na samo shi don naji dadin rayuwa na kuma duk mata ta
shigo gidan nan kikace zaki daga muna hankali wallahi sai dai ki koma gidan ku
kinji na fada maki mara mutun ci da tausayi kawai.
Ke abinda kikai min a duniyan nan har kina da bakin magana don zan kara aure.
Kuma ai dole na kara aure na samu wace zata kwantar min da hankali na wadda zanji
dadi da sanyin rai a gurin ta.
Ba irinki da kikai shekaru da shekaru kina gwada muna boni ni da diyana ba a
gidan nan.
Don tsaban iya cutan ki harda dan ciki kika zalunta dakanki da kanki kin mayar
damu abin zunde da kwantance a gari saboda tsaban kwadayin ki.
Yana fadin haka yai alwala ya fita, daga gidan ran shi a bace yana kutawa shi
kadai.
Bayan sallan magariba kaman masu jiran a idar da sallah sai ga yan kawo amarya
da gudan su sun shigo gidan.
A zaton maria za,a kawo mata amarya dakin ta irin na al,ada sai taga sabanin
haka.
Sai ma jin da tayi lokacin yaran ta suna cin abinci a,waje matan na gardama a
tsakanin su cewa.
Ko wanan ne akaiwa fyaden cikin su dayan tace karamin ne fa akace sai dayan tace
a,a fa ance babban ne mai sayar da pure water uban ma bai ko san tana aza mashi
tallah sai ranan da abin ya faru ya sani.
Kai amma wanan matar ta cika azzaluman mace ita tajawa dan ta wanan bakin sunan
haka har ya mutu ana kwatance dashi a gari.
Wani irin zafi da radadi maria taji a ranta take ji kaman ta fito ta basu amsa
amma kuma ita kadaice a gidan kada su taru su

52 / 92