Author : Zainab Idris Makawa Seenabu Category : Complete Novels
ta girka komai ta dinga bari akai mata daga nan gidan su.
Shine gwago tashigo yin godiya gurin Maji din da,wanan irin halarcin da take
gwada masu haka.
Maji tace haba dai mai masa ai yiwa kaine ina laifi duk cikin shiyan nan baki
aminta,da kibar yar ki a gurin kowa ba sai gurina, kika yaba da ni ai wanan ma wani
mutuncine babba.
Murmushi gwago tayi tana cewa Allah dai yabar daukaka da girma Allah kuma ya
kara shirya muna yaran mu.
Ameen inji Maji tare da sauke ajiyan zuciya a fili tace bari mai masa ba boyo a
tsakanin nidake yanzu.
Jin haka yasa Bintu tai saurin mikewa,zuwa ciki tabar su gurin ganin ta,shige
yasa maji hararan su Amira dake zaund suma din mikewa sukayi suka shige suna
zunburo baki gaba.
Maji ta kara kwantar da muryan ta kasa, tana cewa hajiyan masa ina cikin
matsala da,wanan yaron na,waje na.
Yayan su Amira ke nan inji gwago maji tace shifa,wallahi sai tace cikin kariyan
murya mai masa yaron nan yana son kashe ni wallahi.
Maganar safe daban ta rana,daban ya zama wa kowa kaya a gidan nan balle ko banza
kin san irin zaman da muke a gidan nan.
Yanzu msi masa nifa har na fara,zargin ko yana shaye shaye ne don abinda yake
abin ma bana kai sake bane.
Subbahanallahi i ji gwago Allah ya tsare ya kare hajiya amma kada ki mashi
mumunan zargi haka don Allah.
Koma maye dai dole ke uwa hakkuri zakiyi kikara jan danki a jikin ki kina nusar
dashi hanyan alheri har ya gane.
Mai masa ni yanzu har abin yana son yafi karfina wallahi don kinga sam yaki
zancen shago kamar kowa shi kuma ba,wani sana,a yaje zuwa yi ba yadda kowa keyi.
Ina gani a gidan nan ko wani da yana kawo wa uwar n shi abin arziki daga shago
amma ban dani sai ma shi Alhanin ne wani lokaci yakan ji tausayina ya dan taimaka
min ko shi da kwankwami da komai yake min.
Tunda kinga ba karfine gareni ba don ni banyi karatu mai zurfi kamar sauran matan
gidan ba.
Amma mai mas wanan yaron duk da haka bai zama min da ba wallahi takare da sake
kuka wi, wi,wi a lokaci guda.
Ba kuka zakiyi ba hajiya kamata yayi ki kara jajirce kina mashi addua da fatan
alheri, kin fasan bakin uwa taki ga "yayan ta.
Mai masa wallahi inayi sai dai kawai na kara akan wanda nakeyi don banda lokacin
kai na ko yaushe sai na yarana tun bai zama haka ba ma, balle yanzu da al,amarin
shi yai kamari sosai cikin gida.
Yanzu ke hajiya baki fahinci ko akwai wani buri wanda yafison yayi abin ba akan
kasuwan ci din.
Saida Maji ta share hawayen da ke fuskanta take cewa, mai masa waifa shi ba komai
bane gurin shi sai sha shanci wai kwallo.
Kwallo yake da ra,ayin yi maigidan mu yayi fada har yagaji yanzu ya saka mashi
ido yabarshi da kwallon.
To hajiya wa ya,sani ko anan alherin shi yake ga wasan kwallon.
Wasan kwallo kuma mai masa za,a samu wa i alheri a cikin sa ?
To ba haka naji ana fadi ba wai suna samu ga harkan sosai kinga sai muyi mashi
addua mugani ko anan arzikin nashi yake.
Hmmm mai masa ni wanan ai abin kunyane a gareni ace wai cikin gidan nan da na
yafita zakka wai bai kasuwanci sai kwallon kafa kawai.
May zai samu a cikin wasan kwallon kafa kuma banda shashanci irin na sadauki
kawai.
A,a hajiya ban son ki na fadi haka fa kin daiga ki godewa Allah idan har zaiyi
wasan ya jawo mai alheri da kintsuwa ai gara a arshi ya,tafi yayi abinshi
kinga,zaki rage taahin hankali don kin san inda yake.
Ni kuma nai maki alkawari insha Allahu zan taimaka maki akwai gurin malamin dazan
tafi maki can kauyen mu sai yai muna istihara akan matsalarshi don muga may ke
damun shi ne wai.
Don kingafa gidan ku babban gidane gaki da kishiyoyi marasa imani da tsoron
Allah.
Don haka abu na farko shine mu fara,sani may ye nasabar wanan matsalar tashi ne
wai ?
Shin daga Allah ne ko kuwa,saka mashi hannu akayi din a danbala makishi yakoma
haka.
Hmmm mai masa ba,wanda ya saka mashi hannu shashancine kawai irin na yaran yanzu
.
Ya hadu da miyagun abokai sun sauya mashi tarbiyan dana bashi tun farko don
rashin tausayi irin na dan yau.
Kin taba zuwa akai maki istihara akanzancen ne ko kuwa dai haka kike gani ke ?
Gaskiya ban taba zuwa ba mai masa ina dai hasashen hakan ne kawai a raina.
Hajiya yanzu duniya tai nisa wallahi kibar mutum inda kika barshi kai kana
kwana,wasu na maka hansari ne,
Balle yanzu ba,a zama kan yara ko nawane gareka dole katashi masu tsaye gurin
nema masu tsari da kuma addua.
Gaskiya ni mai masa ban taba yin komai akan yaran nan ba gaskiya nidai nasan ina
masu addua sosai wallahi.
Hajiya wanan zamani ai ya,wuce ko gurin mutane don zamani ya lalata mutane da son
kai, don A LOKACIN MUKE,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,,,,,
A gurin da suke zaune suna magana suke jin hayaniya daga cikin gida, shiru sukayi
suna saurarawa.
Labulen dakin tane ya,daga ko sallama babu ya fado masu dakin duk jikin shi yai
futu, futu da kasa ga wandon shi kamar yai fitsari a ciki.
Kara shigowa yayi daga cikin dakin ya fadi kasan ties din falon jagwab dashi sai
kuma ya fara nasarin barci.
Innalillahi Baba na may ke faruwa ne haka, may ya samay ka, may akai maka, wa
yai maka wanan abin haka.
Sai ta,sake wani irin kuka cikin wani murya mai ban tausayi da tsuma zuciyan mai
sauraren ta.
Innallilahi wa,inna alaihim rajium Baba kada dai ace da gaske shaye shaye kake
yi haka.
Cikin kuka take magana da tashin hankali, mai masa kin ga yaron nan yau yadda ya
koma ikon Allah.
Allah kataimake ni ya Allah wanan yaron yau may zangani haka da idona.
Nashiga uku na lalace a rayuwata Sadauki may ka koma haka yaushe ne kafara wannan
bakar rayuwan haka.
Takara daga murya tana cewa Baba na badai shaye shaye kakeyi ba cikin gigicewa
take maganan.
MAJI bafa,,, abinda ya,samay ni just ,,,, relax ,, relax Maji,,, kawai,kawai
dai ,,,, dan joy neeee,,,,,
Sai ya mayar da kan shi kasa yaci gaba,da barcin shi, nashiga uku mai masa yau
dan nan ya, jawo min magana babba a cikin kishiyoyi da al,umma.
Baba da nasan wanan rayuwan zakayi a duniya da na barar da cikin ka na huta da
ganin wanan bakar ranan da nagani yau a,rayuwa na.
Haba haji ki daina fadin hak don Allah yanzun dai musan abin yi kafin abin yai
mashi illa haka.
Mai masa ai gara ace ya mutu da na zauna ina ganin shi a gabana haka.
Umm,umm hajiya don girman Allah ki daina fadan haka wa dan ki Ai babu abinda ya
gagari Allah ko?
Kuka mai tsuma rai Maji takara sakawa cikin tashin hankali tana fadin da daya ke
nan tilo namiji da Allah ya bani mai masa yau ga abinda ya zama min a duniya.
Ba u komai Allah ya shirya muna shi dashi da ma sauran diyan musulmai masu wanan
halin.
Daga waje kofa tsakar gida kuma kishiyoyin maji a tsatsaye suna fadin ikon Allah
yaukan mun ga abin mamaki a cikin gidan mu wanan bakar masifan ya,fado muna.
Hmmm lalau akwai magana da,sake don dole a,dauki mataki ga hakan kafin a lalata
muna yaran mu.
Dayar kuma sai cewa tayi kai gurin bakar jaraba har an kwaso muna jikokin yan
maye a gida yau ga abinda bakar jaraba ya jawo a gidan nan.
Ace wai cikin gidan nan yadda muke da mutunci a cikin shiya an samu dan maye irin
haka.
Allah kai muna tsari da wanan bakar masifan ka kare muna yaran mu dama karshen so
ke nan ga yaron da ba,a kwabo ai.
Haba dai ai wanan ba daga nan ba inji amaryan su kowa dai yabi nashi da addua
amma ai ita Maji ba itace ta turashi zama haka ba kudai kowa ya iya kan sa don
wanan masifan ta shafi kowan mi a gidan nan, ba ita kadai ba.
Ke don Allah ni ban son munafumcin banza ina ko ke bai bari ba indai sadauki ne a
gidan nan.
Haka sukai ta cacan bakin su daga kofan dakin Maji da suke daga ciki suna jin
cacan bakin su.
Mai masa kinji abinda nake fada maki ta fadi cikin kuka da tashin hankali.
Ai basu kamar Allah ba don ba wanda ya wuce jerabawan ubangi daga cikin su.
Ke dai kibi dan ki da adduan neman ashiryuwan daga Allah dan yanzu ke ce da
matsala basu ba.
Kara jajircewa ki koma haikan gurin ubangiji tare da nemar taimako, kina bashi
koda baya so ki bashi ya shanye a gaban ki ba bayan ki ba.
Insha Allahu nima zanyi kokari naga na taimaka da dan abinda zan iya gurin
al,amarin.
Don kinga shi aikin shedan shiga rai ke gare shi sai mutum yai kamar zai bari
sai kuma shedan ya rude ka ka koma.
Don haka yanzu ki yawaita jan shi a jiki ki kada ki biyewa maganan mutane kina
nuna mai kyama ko hattara ,a,a ki jawo danki zuwa jikin ki don ki san damuwar shi.
Shigowan Bintu dauke da dan wani kwanon glass na tangaran da cibi a cikin sa yasa
sukai shiru baki dayan su.
Su Amira duk suna tsa tsaye cirko cirko sai faman kuka sukeyi da tashin hankali.
Gurin da yake kwankwance sharkaf dashi ta nufa inda ta durkusa tare da dora kan
shi a cinyar ta suko duk ido suka saka mata.
Amira na ganin haka ta fahinci may Bintu ke shirin yi masa don haka itama ta
karaso tare da karban kwanon daga hannun Bintu.
Haka maryam itama ta guso inda suke da taimakon su ta samu ta bude mai baki da
kyat suka dura mai manja da girshirin da ta hada har kusan cibi uku,
Sai ya fara wani irin tari ya bude idon shi da kyat tare da dan kara yunkurawa
sai kuma bintu ta mayar da bakin shi da karfi ta rufe gam sai ko yai wani zabura
tace ku danne min shi dan Allah.
Maji dake gefe tana kallon su ta kara sakewa da wani sabon kuka sosai cikin
tashin hankali.
Yan mintina kadan saiko wani irin amai ya taso mai nan ya fara sharara amai
kamar zai amaye kayan cikin shi a lokacin.
Amai sosai Umar yayi a lokacin sai kuma ya koma barci dan gefen su kadan.
Bintu ce ta kwashe amai don su sauran sai faman kuka suke tayi cikin tashin
hankali.
Dawowa tayi falon ta zauna a cikin damuwa da tashin hankali,
Maji ce ta taso inda yake takai mai wani irin mari da duka mai gigita mutum
abinda yasa shi bude idanuwan shi ke nan yana kallon ta.
Yace cikin muryan maye Maji may nayi kike duka na haka?
Uwar ka kayi dan banzan yaro mara mutunci kawai wallahi sadauki sai Allah ya,,,,
Haba mama kiyi hakkuri dan Allah kada ki furta mai mugun kalami yafi kuma nan
lalace maki don Allah dai kiyi hakkuri mama takarasa cikin kuka da tashin hankali.
Mai masa tace haba hajiya watau baki dai ji abinda nake fada maki ba ke nan ko?
Wallahi idan ma yafi nan ba tsira zakiyi daga zagin duniya ba don haka ki dawo
da hankalin ki guri daya kiyi nazarin magana ta.
Hannun ta ta cusa cikin aljihun shi don jin karar ledan da takeji daga cikin
aljihun nashi.
Fito da ledan tayi daga aljihun nashi sai wasu kwayoyi suka zubo daga ciki da
yawa haka.
Salati suka saka ita da mai masa a lokaci guda take cewa kinga abinda ya sha
yafitar mai da hankali ko.
Koma ki zauna saman kujera kada ki fadi kinji hajiya akwai Allah shine zai muna
maganin abin.
Ba,a san ko wacece daga cikin matan ta bugawa maigidan waya ba, sai kawai gashi
yazo a sukwane gidan cikin tashin hankali shi da sauran yayyen sadauki.
Dakin maji da akace masu ya na ciki suka shiga anan suka samay shi kwance sharkaf
kasa yana barci.
Nan suka samay shi da duka mai shuri na shuri mai mari yana mari saida ya farka
daga barcin da yakeyi.
Suna ganin ya tashi suka jashi zuwa waje kiiii sukaci gaba da dukan shi cikin
tashin hankali.
Ganin zasu halaka shine hajiyan masa ta isa gurin ta fada saman jikin shi tana
tare dukan tana fadin haba Alhaji ai duka baya yi sai dai addua tunda abin yai muni
ko?
Cikin takaici da bacin rai Alhajin yace mai masa bari kawai mu kashe dan banza
may zanyi dashi cikin zuria ta mara mutunci kawai.
A dai yi hakkuri dan Allah abi al,amatin sannu tunda ya riga da ya aikata sai a
san hanyan bi da shi kawai yafi.
Amma duka ai kara hinjira shi kawai zakuyi ba wai gyara abin ba .
Duk mutanen gidan suna tsaye tsakar gida cirko cirko sai amaryan su ce itama ta
tako gurin ta kama mashi hannu zuwa part din ta duk da Alhajin yana ce mata wallahi
ki barshi ya fito min gida ba dana bane wanan dan banzan yaron kawai.
Bataji ba,sai kulle kofan part din ta da tayi dashi a ciki ta,zaunar dashi nan ta
shiga lalashin shi da bashi magana tana mashi nasiha.
A kan ya daina wanan muguwar akidar da ya sawa kan shi ko dan martaban iyayyen
shi,
Tace ka tausayawa mahaifiyar ka Sadauki yau ka san irin halin da uwarka zata
kwana aciki ai babu abi mafi muni ace yau cikin dubu nakane lalattace.
Dukar da kai UMAR yayi kasa tare da,wa i irin nadama ya,ziyarce shi a lokaci guda
yake cewa mummy kuyi hakkuri insha Allahu zan daina bazan kara ba.
Tace da ka kyautawa kanka,wallahi da ka cece mahaifiyar ka daga tashin hankali da
masifa.
Kuma kaje in komai ya lafa kabata hakkuri kai mata alkawarin baka sake shaye
shaye har ma da mahaifinka.
Shiru sukayi ya,sadar da kan shi a kasa can takara cewa, yanzun kai ko don irin
zaman da ake a,wanan gidan kowa ya tunkaho dan shi wani abu ne bai saka kai zuciya
ka zama wa uwarka dan kwarai abin musali ga sauran dangi.
Maza tashi jeka kai wanka ka,tsabtace jikin ka don naji kamar sun fita daga
gidan.
A lokacin su Maji suna daki hajiyan masa na kara bata hakkuri da magana mai
kwantar mata da hankali, har ta dan sauko tana daukan nasihan mai masa.
Mai masa take cewa yanzu dai yana gurin kishiyar ki ta,saka shi a dakin ta ta
rufe dashi nasan nasiha take mashi a can.
Wa mummy Amarya ko wa ina ganin itace dai mai daki can kusa dake karshe.
Itace maji ta fada a hankali don in ba itaba nasan indon su yayane sai dai a
kashe shi ai.
Sadauki yafito daga part mummy yana tafiya cikin dan gyasawa a hankali don dukan
da yasha ya taba mai kafa har da baya duk jikin shi ya farfashe sosai don dukan da
yasha gurin mahaaifin shi da yayyen shi.
Wa yanda ke tsakar gida a zaune suka bishi da ido da bakar magana8 suna fadin
andaiyi hasaran haihuwa wallahi.
Yadago kai ya,watsa masu harara sai dai bai tanka masu ba ya shige yafice daga
gidan kawai.
Ranan Maji tayi kuka kamar ranta zaifita da,kyat mai masa ta samu tai shiru,
tare da bata magana.
Gwago mai masa ta sa Maji taje taiwa Amaryan su godiya kan halarcin da ta nuna
mata kan dan ta.
Maji ta shiga part din tana saye da hijjab mairuwan toka har kasa a jikin ta sai
dai duk idon ta ya kumbura don kukan da ta yini yi ranan.
Da sallama a bakinta tashiga dakin inda ta dan tsaya daga kofa tana sallama
daga waje.
Akai mata da iso da amsa sallaman da tayi hakan yasa ta daga labulen ta shiga
daga cikin dakin.
Bayan ba,tasan dakin ta tsaru kamar na yan boko dama don komai akwai cikin dakin
nata.
Amma da take ita ba ruwanta da bin dakin kishiyoyin ta,sai bata iya kaiyade abin
dake cikin part din gaba daya.
A,a hajiya maijjida kece tafe yanzun fa nake son nagama da wanan dan rigiman
naje gurin ki sai kuma gaki cewa karamin yaron ta da ta yaye amma ya dan tasa
yagirma.
Ta kai kallonta ga yaron tace Amir kaine wai dan rigima aiko ba ruwan shi dai
nagani.
Cafdi baki san komai ba ke na wanan ai fitinanne na karshe wallahi.
Yanzu fa nake zancen zuwa gurinki na kara baki hakkuri akan abinda yafaru dazun
don abin ba dadi gaskiya saidai hakkuri da addua kawai Allah ya shirya muna su baki
daya.
Maji tace nazo ne nai maki godiya kan irin halarcin da kikai nuna dazun din.
Nagode Allah ya saka da,alheri Allah ya kara bamu hakkurin zama da junan mu yasa
wa zuria albarka.
Habba hajiya maijidda ai shi da na kowa ne danki fa da nane kamar yadda nawa suke
naki.
Ke fa mutum ce mai kokari da sanin ya kamata duk irin halarcin dakike min kan
nawa yaran aina sani.
Don ko dawowa sukayi ban dawo ba,daga school gurin ki ne