Author : Zainab Idris Makawa Seenabu Category : Complete Novels
Shikan shi ada can baya kafin ya fara dan shaye shaye yana kokarin dan dauke
masu wanan nauyi.
Amma tunda yafara shaye shaye komai ya,dagule mashi a lokaci guda.
Shi kan shi ba zai iya cewa ga dalilin da yasa ya tsiri yin shaye shaye ba,a
rayuwan shi.
Haka kawai ya,wayii gari yaji yana,da ra,ayin yin haka a,ran shi.
Tunanen shi ya katse ne don jin muryan maji da yayi a gaban shi tana cewa may
kuma ya faru ka,tasa tuwo a gaba kana tunane,
Ko baka iya cin abincin mune yanzu ka koyo cin dankunun mutanen kasar ghana.
Murmushi ya dan sake a gefen fuskan shi wanda sai ka kula zaka gane murmushine
yayi haka.
Maji takara tanbayan shi komay yasa may shi taga yana tunane haka karo na biyu,
duk yan uwan dake surutu basu kula da,damuwar da ya shiga ba.
Yace wallahi ba komai Maji gajiya ce kawai danayi yasani yin shiru haka.
Ya jawo kwanon abincin a gaban shi yafara diba a hankali a cikin plate din dake
gaban shi.
Kadan yadan tsakula ya ture plate din yana fadin ya koshi da abincin.
Maji tace amma sai ina ganin kamar ba gajiya yasa kaki cin abincin ba dai, ai
gajiya bai hana cin abinci tunda har naga kayi wanka ko?
Ya mike a lokaci daya bayan ya wanke hannu yana cewa bari na,dan fita na,dawo
yanzu.
Da,sauri maryam tace tau yaya adawo lafiya cikin gidimi.
Maji tace dakata ina zaka bakaje ka gaisa da mahaifin ku ba daya dawo duk da yace
min kun hadu a massalaci dazun.
Yace Maji da nace saida safe kafin yafita naje mu gaisa da shi da kyau nai mashi
bayanin komai.
Daga inda maryam take tace shine daidai Maji bari ya fita yadawo din kawai
da,safe suga juna da,Baba din.
Akwai dai abinda kuka,kulla nake gani kukuka,sani koma may ye ai ta juya zuwa
cikin dakin ta.
Bayan wani dan tsawon lokaci ya,dawo da ledoji irin na super market manya har
guda uku a hannin shi.
Da murna suka tare shi suna karban ledejin maji dake fitowa daga daki tana fadin
Fatima don Allah kada ki gaji kinji dauko min abinci naci nima.
Zataci gaba da magana sai ganin abinda ke wakana falon nata tayi, takai idon ta ga
ledojin da su Amira ke budewa.
Drinks ne snacks, su apple da nama gudan mai yawa na rago da kaza gassashe.
Take kamshi ya,gahraye falon nata a lokaci guda sai faman binsu da kallon mamaki
takeyi daya bayan daya.
Bintu da ta riga tamike take cewa a hankali Mama na debo maki abincin ne?
Yace ke bar abincin nan dauko mata plate kawai ki zuba mata wanan taci tasha
drinks din.
Cikin mamaki maji takai zaunr a saman dayan kujeran ta tana cewa haba Sadauki
kai da ya kamata kai tanadi shine zaka biyewa wa yan nan makwadaitan ka,fara
almubazaranci da kudi haka.
Murmushi kawai yayi azuciyar shi yace mamana bakiga komai ba ma tukun ai.
Amma a fili cewa yayi ai maji wanan bai hana ai tanadi don su wa naje wasan badon
ku ba aci kawai bai sa ya kare ai.
To amma sadauki kana dai jin har an fara min gori yaddackaje fa haka ka dawo wa
mutane tsula dakai.
Maji kada ki damu da zancen su wanan magana da sukeyi takine a gare mu yanzu.
Bintu tana kawo plate din tamikawa Amira dake ta faman bude kayan, inda Amira ta
dago kai tama cewa maji may zan yago makine daga ciki?
Dakuwa Maji tamika mata tana fadin ungo naki nan ta juya inda Sadauki yake zaune
tana fadin kada ka biyewa wayan nan yan kwaden don basu san ciwon kasu ba,su ba
abindake ran su sai kwadayi.
Kai tanadi ga dan abinda kake samu don gaba nada yawa don kaine muke gani wani
gin shikin mu gidan nan.
Maji kada kiji komai kuci kawai ai don hakane na,sayo maku din don naga kunci kun
sha daga gareni nima.
Komai da ya,sayo saida Amirata sawa Maji inda shima sadauki ta zuba mai a cikin
dayan plate din.
Ta juya inda Bintu take makure tana cewa bisimillah mana zo muci ko,?
Maryam data fara kaiwa abaki tace ,a,a bazataci ba kin san ita akwaita da
filanci ai.
Shigowan yaron Asiya da,aka turo don yafa may suke a dakin saboda dariyan su da
akeji,
Amma sai ya fake da yazo gayar da yayan sune da dawowa.
Maji tace Amira ta diban mashi inda ta yaga mai rabin kaza guda da yan sauran
tarkace tabashi yafita.
Maryam tace munafuki gulma dama tazo yi ba duk gaisuwa yakawo shi ba fa.
Kai ke kan maryam wallahi ki rafe yawan zargi ina laifin shi yadawo yahi dan uwa
yadawo yazo ya gaidashi.
Kila ba inji Amira maji tace ku dai kuka sani don bakujin magana.
Bintu dai na gefe tun da ta dauka saudaya,sai faman taunan shi take ta kasa
hadewa duka.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,,,,,
A LOKACIN MU KE,,,,
Bai yarda ya,fita daga gida sai yai wanka ya gyara jikin shi kamar yadda yaji ana
yabon shi da tsabta ko yaushe,
Yanzu yana ciniki fiye da farko a baya don ko bai sayar ba mutanen gurin zasu
saye na karshe suce zasuyi amfani dashi da dare dashi, don da dare ana wuyan samun
pure water.
Haka yasa yaron ya kara kwantar da hankalin shi da mutanen gurin da yake zaman
don yanzu duk sun saba dashi ko sosai sun kuma yarda dashi yaron nada kirki yana
da,wayo,
Don duk inda suka aike shi da gudu zai tafi kuma bai bata ranshi.
Ya kai yanzu taban da ake aiken shi saye ya canza sallo don dai shi bai san wani
irin taba bane shidai a ganin shi ai duk taba tabane.
Amma sai dai yasan wanan yafi wanda yake sayo masu don sai anyi warning din shi
akan ya boye idan an bashi kuma idan ya sayo kada ya,basu infront of mitune yai
hiding din shi.
Haka ko yake ko wani irin sako zai bayar in secret zai ba mutum abin shi.
Duk hiran da matasan zasuyi a kan idon shi ne cikin kunnen shi yake shiga.
Akwai wani wanda idan ya sai ruwan shi ko nawa ne canji zaice ya bashi kawai bai
karban canji gurin yaron.
Haka yasa Aliyu har Allah Allah yake yafita tallah koda lokacin fitan nashi baiyi
ba.
Suma gurin da ya tun karo zaka ji suna smally ya iso ke nan yaro kana wanka,fa.
Shiko yarinta sai yaji kan shi ya,fashe yana mai jin dadi yana kokarin yin wasa
da su don sun saba dashi ko.
Nan za,a fara smally sayo min sigari zo ka sayo min abinci tsalaken titi da dai
sauran su.
Irin haka,watarana yazo sayen sigari sai ga wani abokin mahaifin shi yace ,a,a
Aliyu wa ya aiko sayen sigari kuma?
Yace wani mutum ne a van tsalaken titi ya aiko ni aka mika mai yatafi, sai
mutumin yake fadin kai amma gaskiya haka bai dace ba a aiko karamin yaro sayen irin
wanan abin baidace ba da karamin yaro.
Mai shagon yace aiko kullun sai yazo ya,saye kashi da kashi ake aiko shi ni
nazata ma ko mahaifin shine ke aiko shi saya.
Ina mahaifin shi ai bawan Allah ne, ina mutumin nan mai dako a bakin kasuwa mai
wuce wa tunda safe yana fitowa kwanan can na malam sale.
Mai shago yace nagane shi dan shine ashe yace wallahi dan shine kai wanan mutumin
ai ba ruwan shi wallahi.
Mut8m ya hadu da mijin maria yake fada mai abinda yagani da idon shi a kan yaron
shi.
Bai ji dadin zancen ba, nan ya koma gida da fada anyi sa,a ya samu Aliyu a gida
nan ya haushi da fada harda dukan shi sai da yayi ranan kuma yai mai fada daga
ranan duk wanda ya tareshi ya aikeshi sayen taba yace Baban shi ya hanashi zuwa.
Washe gari da,aka ake shi yake fada masu cewa, an fadawa Baban shi yana zuwa
sayen taba harda dukan shi akayi kan hakan.
Kai mutane dai wallahi muna fukai ne yanzu har mahaifin ka,saida ya,samu wanan
dan labarin kamar wani abin sheri can.
Nan suka,bada shawaran ya canza shago kawai inda baza,a sani ba yana zuwa.
****** ********* ******
Tun dawowan su ka fara karo da kwalayen da akai amfani dasu a dakin Maji na kayan
da aka haka, duk da an kwashe anzubar da saura ga kuma shirgin kayan da aka fitar a
inda suka barsu dazun.
Yaran su ne suke fada masu cewa yau basu nan an sha aiki a dakin Maji don an
gyara mata dakin ta kamar na amarya.
Mama Asiya bata yarda ba saida ta shiga hardakin don ganewa idon ta abinda yaran
ke fada masu.
Tun daga labulen falon tafara shock don bata ma taba ganin su ba da idon ta gidan
kowa ba.
Kujerin da tai tozali dazune suka saka gaban ta wani irin faduwa, don tasan bana
kasar nan bane da ganin su.
Juyawa tayi don babu kowa a falon bata tsaya ba sai dakin Umma wadda itama
shigowan ta gidan ke nan a lokacin.
Yaya waiko kinga abinda idona yau yaganan min may kuma kika gani zaune takai
tafara lissafawa Umma abinda tagani da idon ta.
Amma sai Umma bata dauki abin da muhinmanci ba ta zaci kawai idon Asiya ya rufe
ne har take dada abinda akasa don ina zasu samu kudin irin abinda take fadin tagani
a dakin Maijidda.
Maji da ta idar da adduoin ta da mika godiyan ta da neman tsari a gurin Allah
tafito don yi masu sannu da zuwa.
Don kullun suka dawo dama sai tai masu sannu da dawowa bata gajiya duk da
gwatsaleta da watarana sukeyi.
Har ta juya sai kuma ta tsaya tana cewa yaya baku nan fa abin arziki yau ya
samay ni don dan ki ya sayo min kayan daki da kudin da ya samu.
Wani dan nawa Umma ta tambaya a gwatsale cikin basar wa maji tai murmushi tace
dan ki sadauki mana.
Umm,uummm, dakin dai Maijidda tunda gashi uwarshi ya sani inda danane ai da ni
zaiwa.
Tace idan kin huta sai kije ki gani ki samin albarka a ciki, ta juya ta fita zuaa
gaida mama Asiya .
Itama ta fada mata yau abin arziki ya samay ta daga dan ta tazo tagani don Allah.
Nani kawai tace ba wani adfuan alheri akan wanda yayi din dama ita da tasamu din.
Hjy kubura dai dama sai yamma lis take shigowa gidan kullun koda kuwa sun tashi
daga gurin aiki ne bata dawowa sai ta gama gantalin ta take shigowa gidan da yaran
ta a gala baice da yunwa.
Maji tana shiga daki tafara cirewa kowa tsaraban shi kamar yadda suka tsara ita
da diyan ta.
Matan gidan dai sun samu turamay yan ghana masu kyau da tsada turmi biyu, biyu
sai yaran su maza bandir din shadda kowan su koda kuwa yaro karamine,
Yan matan kuma dogayen riguna da turamay suma aka basu, masu kyau sosai.
Nan gida ya kaure da surutu kowa da abinda yake fadi inda babu wanda yazo godiya
cikin su sai yaran ne duk wanda akabawa zai zo yayi godiya da jin dadi masu bakin
hali irin na uwayen sune basu shigo ba.
Hjy kubura da aka kai mata sakon cikin mamaki tace sadauki fa ya kawo muna wanan
haka don harda kwallon da danta yaba da soko saida aka sayo mashi
Bata san da zancen gyaran dakin ba saida ta shiga taga ikon Allah dare daya Allah
ya kai su gaba haka.
Tace may nake gani haka hjy maijidda kice min ci gaba yazo ke nan nan ta shiga
sauran dakunan tana kallo tana kada kan ta cikin mamaki don bata taba zaton haka
ba.
Falo ta dawo tana fadin kai Maijidda kin ko tambayi yaron nan akan kwallo ne ya
samu wanan kudin haka?
An fa kashe kudi yakai miliyan biyu a nan ma kawai fa tanayi tana kara latsa
kujerun don jin kwalitin su.
Tace ina dan nawa yake sarki yan kwallo ke nan ace mutum shigan farko ya dawo da
haka.
Sai bayan ta mike take cewa ja iri yako tafi da dabun da nai mashi na tafiyan
kuwa.
Maji tace ai yace yaji dadin danbun sosai shi uake ci ma a can yasha ruwa kawai
don bai saba da irin abincin su ba sosai ,a lai kan naga alama.ai.
Tafita tana tunanen hitan su da yan office din su dazu da safe da suke cewa ashe
dan kwallon gidan ku yadawo tace cikin tabe baki yadawa yadda yatafi shiririce
mana.
Wanan dan iska wani tsiya dama zai tsinanowa mutane a can ban da tambadan daya
saba nasan ya tafi yana shaye shayen shi sun koro shi.
Sai dayan dake rubutu take cewa ,a,a nifa naji kanina na fadin shine ma yazo na
farko don ya samo kudi sosai wallahi.
Ba gaskiya bane wallahi yadda yaje haka ya dawo tsiya tsiya dashi wallahi don ina
ga baiko maganin sisi ma.
Don ya samu wani abu da naji ko gurin Alhaji ne ko inga suna facaka ko ba abinda
ya tsinano.
Sai daya tace balle ma mashayi kafin fa suyi sai an bincike su agani idan kana
shaye shaye basu yarda ka buga kwallo yanzu.
Balle ma bai samo komai ba suna dai ganin hakane tunda ya tafi har wani kasa yin
wasa.
Sai gashi ta dawo gida ta samu zancen abokiyar aikin ta ashe gaskiya ne ke nan
boyon kurwa yai masu dama.
Maji dai ta rakata da harara tana fadin muguwa aniyar ki tabiki dakin ki munafuka
yar sheri, Allah ya shirye ki kawai.
Maji tace wa Amira gobe ina son a kwashe tsofin kayan nan akai wa mai masa gidan
ta ita ma,ta canza.
Nan Bintu tafara murna tana godiya kafin hjy masa tazo tayi mai karfi da bakin
ta.
Sai da yamma da Alhaji yadawo ya samu wanan labarin gurin mama Asiya da ta fara
tsegunta mashi ciki tsigar gulma.
Yace masha Allahu kai amma ko naiwa maijidda murna haihuwa ta fara rana ke nan
yau Allah ya amsa mata adduan ta .
Sai ga maji da nashi tsaraban shaddoji da su turare masu tsada ta zube mashi su
a gefen kujeran da yake zaune.
Ya kalleta cikin murmushi yana fadin yanzu Asiya take fada min abin arzikin da ya
samay ki ashe sadauki ya fara fitar da uwarshi.
Maji tai murmushi tace kai haba Alhaji kai kuma da kanka zakai min sheri kuma.
Suna cikin magana sai ga hjy Bintu dauke da tsaraban ta dana yaran ta tana ta
faman washe baki tana fadin ga abin arzikin da mutanen ghana suka kawo muna.
Yace mata nima kinga ga nawa nan yanzu aka kawo min shi ko dubawa ban gama ba.
Mama Asiya mai girki tashigo ganin kayan hjy Kubura dana yaran ta yasa take kallo
don taga sun fi yawa ga idon ta.
Nan take cewa hmm muma fa anbamu har yaran nan gaba dayan mu gidan.
Masha Allahu inji Alhajin ya fadi yana mai kai ruwa a bakin shi yace haka ake son
samu idan ka samu kowa ma yasan kasamu cikin yan uwan ka.
Yana gama cin abinci ya nufi dakin Maji don yaga abinda ake ta faman zuzutawa,
Yako gani kuma yai murna da farin ciki sosai sai faman sawa dan shi albarka
yakeyi.
Bayan fitan su Amira tace ikon Allah yau Baba ne da kan shi kewa yaya sadauki
wanan adduan haka.
Amma da can an zuga shi a kan shi sai faman cin mutunci da tonon asiri yakewa
mutane a tsakar gida.
Maji take ce mata wanan ai haka yake duk uwa mai haihuwa sai ta samu bacin ran
mahaifi akan dan ta watarana.
Don duk abinda yayi mara kyau laifin uwa ne maikyaune na uba ni dai na godewa
Allah daya takaita min wanan bakin cikin da wuri.
Maryam dake kunna tv take cewa amma ai basu daina kiran shi da sunan mashayi ko?
Don ko dazun naji Umma tana fadin wai tsaraban yan shaye shaye suka samu take
fadawa yaya Imirana da ya shigo.
Ba sai ta dawo dashi ba tunda bata son kayan mashayi da aka bata maganan banza
kawai.
Maji dai shiru tayi batace masu uffan ba har suka gaji sukai shiru.
Da safe ne sadauki yaba mahaifin shi check din kudi yace yana so ya fara noma
dashi ko za,a samu anan ma din
Bayan Alhaji ya karbi kudin yaga yawan su yake cewa sadauki duk wanan kudin haka
akan kwallone kawai ka samay su.
Ya dan dukar da kan shi a kasa yace Baba a nan na samay su don ma ban yarda bane
da,har wasu club sun so su sayeni amma,nace masu a,a subarni cikin club dina kawai
har gaba.
Ikon Allah ashe Alhaji Sani gaskiya yake fada min cewa idan nai hakkuri Allah
yasa maka hannu watarana sai na dara akan kwallon ka.
Murmushi kawai sadauki yayi ba cewa mahaifin nashi komai ba yana fita hjy kubura
tana shigowa suka gaisa dashi ya fita.
Alhaji ke ce mata kingani ikon Allah kudi sadauki ya kawo min wai na fara noma
dashi.
Maimakon yaji tayi murna yadda ya zata sai ji yayi tace Alhji adai binciki a gani
wanan harkan amma abin yai yawa wallahi.
Ya juyo cikin mamaki yana kallonta yake cewa ban gane hausan ki ba fa kubura.
Tace ni gani nayi kamar wanan kudin sunyi yawa ace duk a saboda kwallo aka samo
su haka gaskiya abincika dai aji.
Yace to kina ganin kamar da