Advertisements
Chapter 59 Reading A Lokacin Mu Ke by Zainab Idris Makawa Seenabu BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

A Lokacin Mu Ke by Zainab Idris Makawa Seenabu

Author :  Zainab Idris Makawa Seenabu Category :  Complete Novels

Chapter   59 / 92

174K to 177K   out of 275.8K words

Hakan yace wa Bashar akai mu gida naji bashar na fafin kaifa yace yaya zan tafi
nabar abokaina ka kuma san ina da bakuwa sai na lalabata fa yace kadaiji tsoron
Allah wallahi.
In banji tsoron Allah ba bashat tsoron ka zanji kafasan yanzu wallahi surukin ka
nake ka tuna.
Bashar yace nima ai surukin ka ne tunda kaunata kake aure kaga munyi one one ke
nan ai.



ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU

IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,,,


IDAN KIN BIYA KIKA TURAWA WANI MUN BARKI DA ALLAH,,,,


A LOKACIN MUKE,,,,


Maria ta rasa may ke ma rayuwan ta dadi yanzu don gaba daya hankalin Atiku na gurin
sabuwar amaryan shi da tashigo mashi da sauyin yanayin rayuwa.
Duk wani ladabi da biyayya na aure amaryan maria ta iya shi haka yasa take ta
sace zuciyan Atiku don dama haka maza ke so .
Gashi da ita da dan ta abinda ya faru dashi na kaddara yaki gogewa gare su.
Kusan kullun sai yaron da akaiwa fyade ya dawo mata gida da kuka wani yai mashi
gorin abinda ya samay shi.
Itama dai din idan gidan buki ta tafi ko unguwa haka mata zasu dinga cewa Allah
sarki ashe itace abin ya faru da dan ta.
Abin kunya harda yan uwan ta na jini sai su dinga fadar maganan yadda hankalinta
zai kara tashi taji kaman a ranan abin ya faru da Aliyu.
Ga maigidan ta da yake yawan musguna mata a gida duk abin da tayi bata iya ba
yanzun gareshi.
Saboda tabon abin da ta aikatawa dan shi ya matukar tsaya mashi a zuciyar shi
sosai.
Ta ramay tai baki sosai gashi sanyi ne yanzu bata cinikin ruwa ko kadan kuma ko
banza bata da mai mata talla yanzu.
Wanan bakin cikin da take ciki da yai mata yawa yasa ta tafi gurin mahaifiyan ta
cikin tashin hankali.
Nan uwar take ce mata ai sai ki zauna ki ta hadiyan bakin ciki, in kina fidda
kudi, kije ai maki aiki ki samu kan mijin ki ki fitar idan kuma kin boye su sai dai
ki zauna kina hadiyan bakin cikin da namiji kina kallo zai zama mijin ta ita kadai.
Hakalin maria yai mugun tashi da maganan mahaifiyan ta nan dai ta bata shawaran
ta dawo akwai inda zata kaita don mutumin aikin shi kaman yankan yukane saboda
gwanancewan shi da iya aikin shi.
Take maria taji kamar an cire mata damuwan ta don sai take gani kamar har tayi
nasara ma ko a lokacin.
Ta dawo gida da farincikin ta ta samu har amaryan ta ta gyara gida sai
kyali ,gidan keyi don ko yaushe a cikin gyara yake yanzu.
Tai ma Maria sannu da dawowa ta amsa mata a tatsune ta fada dakin ta don ko
sallah batayi ba a lokacin.

****** ********* ******
Ina idar da sallah na fito na fara gyaran gidan kafin wani lokaci gidan ya dauki
kamshi gaba daya, nan na fada kitchen for the first time don na fara girka abinci
da akaina.
Kayan aikine na electronic gasu nan kala kala a kitchen din na fara tunanen wani
simple abinci zan yi a lokacin.
Ina bude store din kitchen din naga kayan abinci da na,shaye, shayen, kwali da
sauran duk abinci da sha tap a store din.
Na dan dade tsaye ina bin kayan da kallon mamaki don abin yayi yawa sosai a store
din.
Dankalin iris na debo tare da kayan miya nai tunanen yin dan fate mai ruwa na sa
naman koda dake cikin fridge din na dan yi amfani da danyen attarudu.
Sai ruwan shayin dana dafa yaji kanunfari kamshi na tashi daga cikin shi.
Ina tsaye a dining ina gyara kayan abinci naji ya shigo gidan cikin kayan motsa
jiki yake.
Ban san baya gidan ba sai da naga dawowan shi daga inda nake tsaye nace mai ina
kwana.
Lafiya kawai ya amsa dashi ya shige part din shi kai tsaye inda ya shiga wanka.
Nima wanka na shiga na gyara jikina ina tsaye bakin wardrobe dina da hijjab dina
don sai da nai sallah walha, zan dauki kaya naji an shigo dakin.
Na juyo a firgice ina ganin shine nace cikin daure fuska don may za,a shigo min
daki haka ko sallama babu kuma.
Kallon mamaki yai min tare da daure fuskan shi sai kuma naga ya dan dara yace
dakin ki fa kikace yarinya?
Nace au nan din dakinkane ko kaga ni nashiga naka dakin ne da zaka ce nan din ma
nakane?
Yace lalai yarinya kina da karfin hali wallahi ni da gidana kuma yau ake son kafa
min doka akai.
Yace to bari na tunatar dake in har kin fara shagala kin samu gidan zama.
Ki sani duk wani abinda ke cikin gidan nan gaba daya har ke mallakana ne don baki
san yadda na samay su ba.
Saboda haka ina son ki shiga hankalin ki daga yau don kada ki wani mike kafa wai
ke ga maigida tunda kinga banza ko ?
Ashe shiyasa jiya nida gidana da kayana har kika sawa daki key wai ke ga mai daki
ko?
Nace saukin abin dai nima ba kasuwa aka dauko ni ba dai yace towa kuma yasani sai
anbincika wanan.
Raina yai balain baci nace kamar yadda kaima akwai alaman bincike akan ka dole.
Sadauki yai murmushi saboda yaba ma karfin halina yace yarinya idan zamuci gaba
da haka zanfi kowa farin ciki da hakan a gidan nan.
Yace ai duk macen da zatayi abinda mijin ta ke so ana kyautata zaton samun
sakamako mai kyau a gurin ta.
Don haka mu zuba dake a haka a gidan nan aga wanda zai sha wahala.
Ya fara tafiya yake cewa sai ki fito muci abinci don ban yarda dake ba kada ki
kashe ma uwana ni.
Nace bazanci ba idan kaci sai ka mutu don kai ke tsoron mutuwa yanzu kuma ma na
kashe ka nakai tarin zunubin ka ina ?
Yai murmushi yace ban dai yarda ba na fada maki ina jiranki a falo don nasan
halin yan kauye da son banza don a gajewa uwata da yan uwana dan abinda aka gani.
Ya sa kai ya fice daga dakin yana dariyan keta raina yai balain baci haka na
karasa shiryawa ina mitan maganan shi a raina.
Kaman bazan fita ba amma kuma sai tsoro ya kamani kada yazo wani abu ya samay shi
ace nice nafito tare da dan saka takalmin na tare da daura dankwalin rigana ga
kaina sai karamin hijjib na saka iya kafada na.
Saye nake a cikin redmaid din dogon rigan abaya maroon color nafito nima sai
kamshi ke tashi a jikina.
Yana zaune yana waya yana jin motsin fitowana ya kura min ido da sauri naga ya
kawar da kan shi gareni.
Ashe gaban shi ne yai wani mugun faduwa ganin yadda na sake mai a lokaci guda.
Naja kuran dake gefe zan zauna yace kaji min yar kauye yana kashe waya yake
kallona yace wancan kujera zaki dinga zama mai fuskantar wanan don kada wani ya
shigo ya samay ki cikin zaman kauyawa ace yar kauye na kwaso gida na.
Ban zauna ba sai jawo plate din da nayi na fara zuba mashi abinci komai da ya
dace na dan zuba mai yadda muka saba zuba mai a gida.
Na koma na zauna a inda ya umurce ni yana daukan spoon yace one warning again
daga yau idan ina gidan nan bana son ganin wanan takunkumin hijjabin naki kamar
zaki cin kasuwan kauye dake.
Nace ai ni ba don ka na saka ba don Allah nake saka abina dama.
Yace kin makaro da wanan dakin zauna gidan ku sai kita faman saka abinki amma ba
gidan Umar ba kan.
Haushi ya kamani ganin ya kura min ido yana jiran na cire hijjab din dake wuyana.
Dole na dan sa hannu na zare hijjab din daga wuya na gaba daya surana yafito a
fili.
Sai lokacin naga ya fara cin abinci nikan na kasa sai naji yace may kike nufi ko
dai da gaske kinyi barbaden ne a ciki wai?
Nace banda gadon wanan amma ban sani ko ku kunayi a gidan ku shiyasa kake ganin
duk mata haka suke.
Dago kai yayi ya kalleni yace dakata kada wautanki ya kaiki ga zagin gidan mu
yanzu na koya maki wayyo a gurin nan.
Shiru nayi don nasan zai iya idan na kara magana na fara shan dan faten da na
zuba a plate a hankali.
Banyi ko rabi ba naji na koshi sai na fara juya cibin kawai ina wasa dashi a
plate din a hankali.
Yana kallon abinda nakeyi bai min magana ba har yagama ci na mike zan fara kwashe
kayan.
Yace shiyasa baki kiba oya maza ki cinye abincin nan kafin nazo na sure ki dashi
yanzun nan.
Don bakin barna kinga banza yasa kika dafa da yawa kin san baki ci?
Na turo baki gaba nace nifa gaskiya na koshi don ban jin yunwa saboda ba abinda
na hade balle yunwa ya damay ni.
Tsawa ya daka min yana fadin will you finish it my friend ?
Dole na dan fara turawa kamar zanyi amai ga nauyi da kunya da suka cikani lokaci
guda.
Ganin saura kadan ya mike ya bar gurin na zaci fita zaiyi amma sai naga ya koma
saman kujera three seater ya kwanta tare da dora kafan shi daya saman kan kujeran.
Kitchen na shiga na wanke kayan da muka bata na kara gyara gurin da mukaci abinci
na juya zan shiga daki naji yace.
Waye dan gadin gidan ki kina daki ina falon ina maki gadin gida maza ki dawo nan
ki zauna mara kunya kawai.
Nace ikon Allah nifa ba boya bace don naga kana son mayar dani kamar wata wacce
ka sayo.
Yace amma ke yarinya ce karama ba,a fada maki cewa sadaki na biya bane lakadan ba
bashi ba kikazo gidan nan ne ba wai.
Don haka ina da right din da sai abinda nake son za,ai min a cikin gidana idan
kuma kince ba haka ba sai na kira maman naki da taci kudin sadakin nawa tazo nan
tabani abina yanzu.
Don ba zan biya kudina ba don bukata na kuma a kun tata min a banza yadda nace
dole shi za,ayi a gidan nan kinji na fada maki daga yau.
Haka na dawo falin na zauna ina jiran wani sabon cin mutunci daga bakin shi kuma.
Bai min magana ba sai wayan da yake ta bugawa ana kuma bugo mashi wanda akasari
murna ake mashi kan auren da yayi.
Sanyin A C da yai yawa a falon yasa na dan takure a guri guda har barci ya
daukeni a zaune ban sani ba.
Jin kaman nai barci a inda nake zaune yasa shi juyowa yaga ina barcin kuwa.
Ido ya kura min har tsawon wani lokaci yana bin ko ina na jikina da kallo har
tatsun hannu na da kafa sai da ya kare masu kallo lokaci mai tsawo.
Nikan sai barcina nake hankali kwance jin kaman an tabani yasa ni farkawa
furgigit idon shi a kaina.
Na turo baki tare da gyara wuyana da yai min tsami nace ni dai in mutum yana
maita ne ko shan jini wallahi kurwa na kur akan shi.
Dariya yayi yace yar kauye kona kara maki karfin A C din ne don naga kinji dadin
hakan har da sake min baki kina barci.
Nace inda bamu dashi ne a dakin uwata sai kai min gori dafin abin kafin kayi
kudin ka kaganta dashi.
Yace ai nasan shi ya jawo ki yanzu tunda can kauye babu shi anzo an samu na banza
ana sha nan.
Nace dakata wallahi gida gidane haka uba ubane kada ka kara zagan min gidan
iyayye na nima.
Yace idan an zaga may zakiyi nace na rama aiko yayo kaina cikin tako daya duk
yunkurin mikewan da nayi nagudu sai da ya cin min gurin.
Nan ya matse ni saman kujeran muna shakan nunfashin juna yace ki rama din ina
sauraren ki.
Shiru nayi ina fadin ka sake ni kawai mugu sai kara matseni a kirjin shi da yayi
bai sake ni ba.
Wani irin bugawa naji kirjin na yi fal, fal gashi kuma bai sake ni daga jikin shi
ba.
Nace cikin karfin hali mugu kawai ka sake ni wallahi ko na fadawa mama cin amanan
da kake min yanzun kuwa.
Yace go ahead kirata yanzu tunda baki da kunya ki fada mata na matse ki ko ?
Sai da ya gaji don kan shi ya sakeni daga jikin shi na tashi da sauri nai daki
ina fadin mugu kawai ni bari ma na cire kayan nan don sun haramta gare ni daga yau.
Yace wallahi duk kika cire kayan nan sai na tube ki zindir a gidan nan naga
tsiya.
Ke har wata mace ce can da kike ganin kamar kina da wani ajine wai?
Daki na koma na zauna a bakin gado idanuwana suka ciko da hawaye don takaici.
Nace a raina may kullun yake nufi da fafin wani har mace ce da za,a gani aji
sha,awan ta ko may ?
Muryan shi naji daga falo suna gaisawa da wasu haka yasa da sauri na saita kaina
nasan baki mukayi a gidan.
Ashe yan uwan mamane suka zo gaida mu da kuma yi muna sallama washe gari zasu
koma gida.
Shi ya shigo yana fada min zuwan su tare da jamin kunne na saita kaina in har na
bari suka fahinci wani abu har naja sukai mashi fada sai na yabawa aya zaki.
Nafito ina murmushin dole nace lah mama kune ashe sannun ku da zuwa.
Maimakon na zauna saman kujera sai na zube kasa ina gaida su a cikin girmamawa.
Masha Allahu Baba kaikan wallahi kayi dacen mata a rayuwan ka yarinya haka da
ladabi, yaushe yaran yanzu masu rawan kai zasu tsaya yiwa sarakai wanan gurmamawan
haka.
Baba don girman Allah ka rike matar da daraja ku mutunta junan ku, ku rufawa kan
ku asiri a tsakanin ku.
Darajan miji shine na mata yadda ka mutunta matar ka haka duniya zasu mutunta
maka ita.
Ke kuma Fatima don Allah basai mun fada maki ba don yaran yanzu boko yasa kun san
komai na rayuwa zaman takewan aure sai dai idan kun ki amfani dashi kawai.
Don haka kin dai ga yadda uwar ku take rayuwan ta a gidan ku idan kinyi koyi da
halin yayan mu da kika zauna da ita babu wani rayuwan da zai gagareki hakkuri a
duniyan nan.
Don haka yi nayi bari na bari abinda duk mijinki bai so kin sani, don kun zauna
guri guda gwargwado kin san halin shi yasa naki.
Gaba dayan ku idan kuka ba da kunya uwar ku kuka tozarta ita da taga dacewan
hakan ta hada ku.
Komai yaya bata boye muna ba na hadin da tai a tsakanin ku kuma ku yanzu bazaku
taba fahintar manufan ta ba sai nan gaba.
Don haka ku taru kuba mara da kunya ku kashe ku bisa a tsakanin ku ba komai ne ma
ita yayan sai taji shi ba tsakanin ku duk abinda zakuyi ku boye sirin auren ku
tsakanin ku don gujewa shigan ta wani hali.
Kai kuma Baba don Allah duk wani abin kurciya da akayi sai abarshi a matsayin
kurciya ne yanzo kakai ga tara iyali nan zuwa badi war haka in Allah ya kawo rabo
sai kuga mun dawo taron suna gidan nan kuma.
Nan dai sukai muna nasiha ma ratsa jiki suka zauna nan tare dani sai dare suka
koma gidan mukai sallama cewa bazasu dawo ba kuma.
Har kofa na raka su suka tafi suna muna fatan alheri da samun zuria ta gari.
Suna wucewa na koma ciki wanka nayi tare da sallah ishai na zauna ina zikiri naji
dawowan shi gida tare da rufe kofan gidan.
Hakan yasani sani bazai fita ba ko ina ke nan again ganin shi nayi tsaye da farar
leda a hannun shi, na dago kai na dube shi ban san yaya akayi ba naji bakina yana
mashi sannu da zuwa a lokacin.
Ledan ya miko min yace na dafa mashi liptop din dake cikin ledan naman kuma na
kai mai falo saman dining zai fito yaci.
Inda ya aje min saida na shafa namike zuwa yin abinda ya sani na fara dafa ruwan
liptop din batare da na tsaya karan ta kona maye ba.
Na fito na aje mai naman da zafin shi a table tare da ruwa da drinks mai sanyi.
Ina kitchen naji fitowan shi, falon ya zauna ya fara cin naman da na aje mashi.
Sai da na juye ruwan ga wani dan karamin flask na hado da cup na nufo falon yana
zaune yana cin naman shi hankali kwance nace ga shayin na dafa.
Ya dago kai yace injin baki zuba sugar ba a ciki nace mai a,a hakana na dafa don
ban san ko na may ye ba.
Da hannu ya nuna min na aje anan ina ajewa na juya zan shige yake cewa ke
bazakici naman bane ?
Na koshi na bashi amsa a taikace yace may kikace ban fa son shegen gardaman nan
naki kinji na fada maki.
Nace naci abinci a dasu mama na koshi dazun kafin su wuce don sai da nai masu
girki sukaci da yamma.
Baice min komai ba na juya na shige na zaci daya gama zai shigane amma sai naji
ya kunna TV dake falon ko da ban fita ba wasan kwallo akeyi a tv nace bissimillahi
Allah nazo gidan masu yi.
Ni dai har barci ya kwashe ni ban san lokacin da ya shige ba sai tsakar dare na
falka naji shiru na kara jan bargona na gyara rufe jikina da kyau.

****** ********* ******
Haka mukaci gaba da rayuwa a gidan zaman doya da manja ba wani abinda ke shiga
tsakanin mu sai in yana bukatan

59 / 92