Advertisements
Chapter 3 Reading A Lokacin Mu Ke by Zainab Idris Makawa Seenabu BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

A Lokacin Mu Ke by Zainab Idris Makawa Seenabu

Author :  Zainab Idris Makawa Seenabu Category :  Complete Novels

Chapter   3 / 92

6K to 9K   out of 275.8K words

ta bahagon halin da ya,fada ciki.
Hawaye ne ya,gangaro mata a,daidai lokacin da ya,dan dago kan shi ya kalleta don
jin da yayi tayi shiru a,tsaye bata fita ba daga dakin.
Shiru yayi yana kallon ta sai ya dan dukar da kan shi gareta, tace babana ban
son ganin rayuwan ka haka .
Wanan rayuwan da kake yi ba,shine irin rayuwan da na,soka dashi ba a,rayuwan ka.
Don Allah babana ka canza rayuwanka a gidan nan ka koma kamar ko wani yaro na
gidan nan.
Ina son naga ka canza ka koma normal life din ka kamar kowa a gidan nan wanan
halaiyar dakakeyi ba,rayuwan alheri bace a gare ka damu ma kan mu da muke naka.
Katai maki rayuwanka saudauki ka canza halinka don Allah kazamo min abin alfahari
a,duniya, gama kowa dake tare damu.
Zan so ace na zamo uwa abin alfahiri ga duniya na nasamu da dan albarka
a,rayuwana, kamar yadda sauran uwaye suke alfahari danasu diyan.
Zan so ka,sasauta halaiyar ka akan wanda kake a yanzu don samun natsuwar
hankalina dana mahaifin ka.
A hankali maji ta fashe da kuka,wanda kuka ya sa ta kasa karasa maganan da take
son ta fada mashi.
Maji ya ce cikin sanyin murya nifa ban san wani hali da nake yi ba,wanda har
zaisa ki zubar da hawayenki haka akaina.
Kallon shi maji tayi a cikin mamaki don watau shi bai fahinci ma yana,da nakasu
ba ke nan tare dashi.
Tace kako san har mutanen gidan nan sun fara zargin wai kana shaye shaye ne,
Ya,dago kai da,sauri ya,dan kalle ta sai kuma ya dukar da kan shi yace maji nifa
wa yan nan mutanen sun fara isa ta,sun fara saka min ido har da bina da,sheri haka?
Ni dai ka gyara halinka shine bukatana a,gare ka idan ka gyara babu wanda zai
dora ma,sheri ai.
Ta juya tana cewa Allah ya kyauta kaji bukatana gareka don naga yanzu guduna ma
kakeyi baka son shigowa nasan lafiyan ka kamar yadda kasaba yi a baya.
Bin bayan mahaifiyar shi yayi yana mamakin mutumin da,yafara gano likin shi a
gidan don haka ya zama dole ya canza takon shi tun mahaifan shi basu tabbatar
da,zargin su ba akan shi.
Don yasan in hakan ya tabbata ba karamin tashin hankali mahaifiyar shi zata shiga
ba har ma mahaufin shi din dake nuna yanzu babu ruwan shi da shi yanzu.

****** ******* ******
Zaune take ta tula kudi a gaban ta,sai faman kidayawa take a hankali don gudin
tai kure.
Sai da ta kirga su cif tajera a,faban ta tana kallo sannan ta,sauke ajiyan
zuciyar ta.
Yanzu abin da ya rage min na hada kudin fridge din nan saura dubu goma don haka
bari na kara kaimi naga sun hadu na,samu kafin azumi na dauko babban fridge wanda
zai isheni sana,a yadda nake so.
Tashi tayi da sauri ta mayar da kudin inda ta ciro su ta boye, don gudun kada
wani ya gani yasan inda ta,aje don tasan da,zaran maigidan ta ya kyala ido yaga
kudin nan sunan ta sorry don yanzu zai mata dadin baki sai ya karbe su gaba daya su
huta.
Abinda bata sani ba shine shi maigidan nata sam hankalin shi bai ga,abin hannun
ta ko kadan don asali ma,shi bai bukatan wanan sana,an wahalan da yaga tana saka
rayuwan ta a ciki yanzu.
Don da,ace yana,da,hali da iyalin shi sunji dadin rayuwa a gurin shi.
Amma ina talauci kamar ya yanke saka ne a kan shi don kullun bida yake amma
kamar ba,ayi yake sai dai Allah bai hanashi dan abinda zasuci ba agidan daidai
gwargwadon hali.
Mikewa tayi ta gyara dakin har zuwa tsakar gidan su don akwaita da,tsabta ko
yaushe duk da,talaucin su zaka,samu gidan su tsab tsab dashi.
Yaran tane suka fara dawowa daga islamiya inda tun a,waje tasan da zuwan su din
saboda hayaniyar su da taji tun daga waje.
Sannu da gida Umma suke cewa sai faman ce masu take kun dawo sannun ku da,dawowa
,
Yar karamar yar ta,take cewa mama yau a makaranta malam yai muna alwala mungani
nima zan iya yadda yai muna nagani.
Nanyaran suka shiga bata labarin yadda malamin su ya koya musu yadda ake alwala
har lokacin da mahaifin su yadawo daga kasuwa suka juya gurin shi yana,alwala suna
bashi labari n abinda yafaru a islamiyar su yau.




ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU

IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,,,,

A LOKACIN MU KE,,,


Waya take sai ko mama dake kusa da ita bata iya jin may take fadi a,wayan , saboda
matukar tausa muryan ta da tayi ga wayan.
Sai yar dariyar da tayine yasa mama dake zaune saman kujera yar tsugunno dago kai
tana mata kallon mahaukaciya.
Ta dan dauki lokaci tana wayan cikin jin dadin abinda ake fada mata ga,wayan
wanda babu maijin ta balle a san abinda su ke fadi.
Mikewa,tayi zuwa cikin dakin su inda ta kwanta saman dan gadon katakon dake
dakin mahaifiyar nata.
Nan ta shige cikin katon hijjab ta rufe kanta sai dai hannunta na akan gaban ta
zuwa kirjin ta a hankali take dan shafa,su don kada a gane may take a lokacin.
Nan taci gaba da,wayan ta na tsawon lokaci mai tsawo sannan tai wani mike barci
ya dauke ta.
Haka mahaifiyar ta ta shigo dakin daga gurin girkin da take yi ta samay ta
kwance tana barci,
A fili ta furta kai amma,anyi malalaciyar yarinya gurin nan yanzu barci kikayi
ashe ni ina jiranki ki min shara a,tsakar gida.
Nan dai uwar dole itace ta karasa aikin ta,da kan ta inda Raiha bata farka ba
sai bayan sallah azahar ko shi sai da kyat uwar ta,tayar da ita don tai sallah.
Bayan ta gama cin abinci a lokacin har uwarta na zance dora girkin dare don
yamma tayi sai ga Raihanatu tafito a cikin shiga na fita da katon hijjab din ta har
kasa.
Sai dai kassh da mutum zaiga mai ta sa a kasan ta da yayi tir da Allah waddai da
irin shigar ta haka.
A,a Raihatu ina kuma zaki a wanan lokacin bayan yamma ya riga da yayi ko?
Mama dan wani guri ne zan tafi ba,wai dadewa zanyi ba yanzun zan dawo mama.
Tana fita bata tsaya ba sai shagon sayen kayan mayen su wand kamar kullun gurin
ya zama majalissan matasa yan maye kala kala.
Duk da jami,an tsaro suna kawo masu samay akoda yaushe suna zuwa kama mata a
gurin masu dabian shaye shaye.
Can ta kutsa tashige daga ciki gudun kada wani yagan ta a gurin don gudun ganin
idon sani.
Brosha na ganin ta a lokacin yana mikawa Umar kayan harkan shi Umar wanda yake
tsaye da bakaken kaya fuskan shi a murtuke.
Burosha yana ganin ta ya fara washe bakin shi cikin farin ciki da ganin ta yana
cewa
A,a yau mutumiyar an shigo ke nan kayan aiki sun kare ke nan dai ko don ba,a
ganin ku sai rana,tai zafi.
Ya dauko canji zai mikawa Umar yake ce ko yau din ma,za,a barmata canjin ne dan
wancan katon ma naga kai ka biya mata.
Wani kallo Umar ya watsa wa Raiha yace cikin dakiya don Allah ka,sallamay ni don
kasan ban son ina dadewa a gurin nan naku,
Raiha cikin yatsune fuska tace aikowa ma,sauri yake don ba wanda yazo don ya
tsaya .
Kamar Umar ya bata amsa har ya dan bude baki da zuman yai magana sai kuma yaja
bakin shi yai shiru .
Borasha ya mika mai canjin shi yai gaba bai tsaya bin ta kan raiha ba balle ya
kulata ma.
Bin shi Raiha tayi da kallo tana fadin ji shi kamar wani mutumin kirki wai sauri
yake bai son a gan shi.
Brosha yace to ke nan fa wanan zubulelen hijjab da kika,sa wa zai dauka ba
islamiya zaki a haka ba .
Dallah gafara malam nagafa kafara saka min ido don tsokanarka ya fara yi min
yawa fa.
Dan sa ido kawai ina ruwan ka da shigata wanan nayi ne kawai don batar da sau
amma a ciki ai shigar manya ne nayi sai ta dan daga mashi hijjab din ta inda ya
hago wani matsatsen rigar da ta,sa duk nonuwan ta sun dan bultso a gaba sai dan
guntun buje na zuwa part dakd saye a kunkurun ta iya cinya kawai.
Kai brosha ya daga tare da fadin kai amma Raiha kin kai shu,uma irin wanan shigar
haka sai ina?
Don dai nasan da,akwai inda kike nufi zuwa da wanan shigar haka da kika boye
cikin wanan katon hijjab din naki.
Tai wani har da idanuwan ta tana cewa ashe ka gane ke nan mazan, yau casu gare
mu har dare shiyasa na dauki kayan aikina don ya taimaka min a can,
Tirka sa ki ce yau akwai babban harka ke nan raiha don nasan mutanen mu zasu hadu
a gurin,
Tace hakane amma ba,wai irin wa yan nan ba wanan gayu ne masu harka da kwalabe da
manyan wa yan nan,
Nima hanya akai min don naje naba idona abinci ko zanyi cafka a can don kasan
ala,amarin sai da kwaskwarima ciki wanan lokacin don gamu nan birjit ko ina kowa na
rabon ido yasamu mai cafkan shi.
Gaskiyan ki Raiha nima nasan sai da haka al,amarin don abin ba,a cewa komai.
Aje lafiya a dawo lafiya a yo muna kamu babban giwa mu sha shagalin mu muma
ga,aljihun shi.
Ta,wuce tana tafiya a cikin rangaji da layi irin nasu na mashaya da suka goge a
fagen boyon kan su, don batar da kaman nin su ga mutane.

****** ********* ******
Guri ne mai kyau da,shuke, shuke ko ina bakajin komai sai sautin kidan dake tashi
na turan ci na mawakan Afrika.
Tana fita daga cikin napep din da ya kawo ta ta samu dan nesa kadan ta cire
hijjab din dake a jikin ta tare da dan kara gyara tufafin dake jikin ta.
A hankali take takon ta zuwa inda mutane sukai dan dazo akasarin maza da matan
gurin zakace ko ba diyan gari bane.
Don irin shigar su da kuma aakin kan su sai mutum ya rantse cewa ai a wata kasar
arna ya ke ba cikin garin sokoto ba ma gari shehu usman dan fodio.
Mutumin da yai gwagwalmaya akan addini a kasa da,watsa su har sauran kasashen
duniya don amfanin al,umma.
Amma,yau sai gashi a,kasan shi garin shi duniya da lokaci yasa matasan kasar
kwaso akidar yahudawa suna yadawa da cusa shi ga,sauran masu tasowa na baya.
Wanda ba,a sokoto ba kawai yanzu ko ina a kasashen hausaw a na samun wanan akido
jin na koyan akidar wasu da,al,adun su.
Allah ka tausaya muna ka,shirya muna al,umman mu yaran mu kan,nen da ma,sauran
yan uwa musulmai baki daya,
Da farkon shigan Raiha a guein ta dan sha jinin jikin ta don tana ganin abinda
yafi karfin idanuwan ta.
Sai da ta hadu da,wasu kawayen ta biyu haka yadan sata sake jiki dama can sune
suka gaiyato ta gurin.
Daga inda take a zaune tana bin mutanen gurin da,kallo a fakaice tana kallon
irin shigar da mata da mazan gurin sukayi abin sai shukaran kawai.
Don nata shiga ai mai sauki ne bisa ga na wasu yan matan yadda suka saka dan
mitsitsin abu a jikin su abin ba dadin gani
Raiha sai tarena kanta a guri don taga iyakar wayewa a gurin yan duniyan da suka
fita iya duniyan ci sosai.
Taro yai tsit saboda fara gabatar da bukin da,aka,soma wanda suka ce sunyi shi
ne don tunawa da kafa gungiyar su mai shekara biyar da,kafuwa yanzu.
Inda,wasun su sin mutu wasu kuma,sun dain harka suna wani kasar haka dai
maigabatar wa yai ta bayane na,shirmay a guri a na ihu da,sowa irin na yan iskan
matasan zamanin nan.
Sai kuma aka fara rawa da da,zagaye duk wanda aka jefa a bu ya fada a kan shi
dole ya fito yai rawa ko a ci mai shi taran kudi.
Irin wanan jifan ne koda aka jefo sai abin yafada akan jikin Raiha wace ke can
ta juya tana magana da kawar ta.
Jin an sa ihu yasata juyawa don ganin may akewa ihu haka,sai jin kyalen rawan
tayi a kan ta inda,zasuyi rawa da,wani sauri dan dogo fari dashi.
Dole badon Raiha ta so ba ta mike tafita filin don bata da kudin biyan tara har
dubu biyar idan bazakai rawan show ba.
Fitowan ta yasa mutane da,dama gurin suka,san da,zuwan ta a,filin, inda aka sa
masu kidan tausi watau cool music,
Rawa na ban mamaki sukayi da saurayin a filin inda,suka bada show yaron ya,dinga
juyata yadda ake rawan kidan na ai nahi.
Wanan abin ne ya haska Raiha,a idon mutane don dama Raiha yarinya ce mai kiran
mata duk wani abinda ake so gajikin mace ta mallake shi ko.
Wani matashi wanda tun fara,event din ya kafa hular shi a gaban goshi kamar baya
kallon abinda ke faruwa a gurin ya mayar da hankalin shi a kan raiha,sosai.
Yarinyar ta,tafi da imanin shi don haka ya yanke shawara a,ran shi cewa dole ne
ya nemay ta don ya gana da ita,yadda yake so.

****** ********* ******
Yanzu abubuwan sun dan yi sanyi wa Maji akan Sadauki don tun ranan da tai mafada
sai ta dan samu sauki daga gare shi.
Don haka shawaran hajiyan masa yai mata rana a gurin ta sosai maimakon fada na
fitan arziki ga yaron yanzu nasiha da ban baki yafi komai sauki ga yaron yau.
Don yanzu sam ba ruwan shi da kowa gidan kwata kwata yafita batun yaran su amma
fa idan ka,shiga shirgin shi duk da haka bai ragawa mutum.
Safiya ce matan gidan kowa sai harkan gaban ta takeyi ba,ruwan wata da wata a
gidan kowa tasa tafisshe ta haka zaman su yake.
Sallaman Bintu ya,dakatar da Maji daga aikin da takeyi daga cikin uwar dakin ta.
Tafito suna gaisawa da maji a cikin mutunci da ladabi da tsintsiya a hannun ta
Bintu sai take mika mata ledan da,gwagon ta, ta bata ta kawo wa maji din.
Tare kuma da karban tsintsiyar dake hannun Maji Bintu ta karba duk da Maji ta so
hanata amma yadda ta marairaice yasa Maji mika mata tsintsiyan sharan.
Nan ta kara yabawa da hankali da tarbiyan yarinyar tana dama ace nice da haihuwar
wanan yarinyar ma hankali da sanin ya kamata haka.
Tas ranan Bintu taiwa dakin tare da kawar da komatsan dake a fili ta,shige mata
dasu daga ciki don yanzu dama duk Maji ta sukurkuce bata da,wani kuzari a jikin ta
saboda dafin bakin cikin dan ta ya fara tabata sosai.
Bayan Bintu ta gama da gyara waje ta kofan part din Maji ne ta shigo dakin
tana,saye da dan hijjab din ta mairuwan cingan .
Tana cewa Mama na rarage ni zan tafi gida kada gwago taga na dade ban dawo ba.
Nagode Fatima Bintu Allah yai maki albarka Allah ya albarkaci ruwan ki, Bintu
ta amsa cikin yar muryan ta, da Ameen mama nagode.
Ta fita daga gidan matan gidan sai binta da kallo suke da take aikin suna mamaki
don dai su sun san yaran su basu iya wanan aiki da yar karamar yarinya tayi haka.
Duk wanda ya,shigo ya,samu yadda Bintu ta gyarawa Maji guri sai yai maga suce
kai Maji amma yau kan kun sha aiki sosai maji waban gyaran guri haka.
Tace wa Ameera bani fa nayi shi ba yar gidan hajiyar masa ce ta gyara min shi
haka ta shigo ta samu ina shara sai ta karba shine tai min wanan aikin haka,
Yarinya yar albarka da ita da mutunci ga sanin ya kamata a yar karamar yarinya da
ita haka.
Amira tace ni dai yarinyar tana bani shawa wallahi don tasan girmama na gaban
ta sosai.
Har maigidan sai da yaiwa Maji magana dacewa yau shiyan nan naki yai min kyau ga
kamshi na tashi sosai.
Murmushi maji tayi tana cewa ya ta yar albarka tazo tai min wannan aikin yar
gidan hajiyar masa na makwabtar mu
A,a tayi kokari su wayan nan katar banzan may sukeyi ne da,bazasu iya gyara guri
ba,sai wata tazo ta gyara masu.
Maji tace halin yaran nan ai sai su don ko sunyi basuyin yadda wanan karamar
yatinyar tayi.
Tun wanan rana kwana bibiyu sai Bintu ta shigo gidan gurin maji ta dan yi mata
aikin da ya kamata tai mata sai ta koma gida.
Sannu sannu har Bintu tafara fahintar cewa Maji tana fuskantar matsala a gurin
mutanen gidan don basu kaunarta sam.
Ga fitinar dan ta da koyaushe ya shigo gidan tana jin yadda yake uwar ke fama da
shi akan wasu matsalolin da bata fahinci aini cin yawan laifin da yakeyi ba ako da
yaushe don maman nashi bata fitowa fili tafadi sai dai taganji tana cewa.
Baba kaiwa Allah ka rufa min asiri ka,daina halin nan naka don girman Allah.
Sai ya kan katse uwar da wani irin magana a gala baice da cewa ni mama mai nayi
ne wai kullun ace wai mutum yai laifi.
Sai yafita a kasalance yabar dakin zuwa waje maji kan bishi da kallo har yabar
dakin ta sauke ajiyan zuciya tace Allah ya kyauta.
Yawan ganin da Sadauki yakewa Bintu a gurin mama bai sa ya,sake da ita ba
asalima dai shi yarinyar haushin ta yake matukar ji a,ran shi sosai.
Don tafaye yin abu kamar muna fuka idan ta ganshi ta kama dan noke noke ke nan
kamar taga dodo ko mugu bata jimawa zata bar dakin ta ce

3 / 92