Advertisements
Chapter 73 Reading A Lokacin Mu Ke by Zainab Idris Makawa Seenabu BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

A Lokacin Mu Ke by Zainab Idris Makawa Seenabu

Author :  Zainab Idris Makawa Seenabu Category :  Complete Novels

Chapter   73 / 92

216K to 219K   out of 275.8K words

ko?
Nace mai Alhamdullahi dan hira,muka taba sama sama ya kashe wayan yana min sai da
safe.
Har barci ya kwashe ni a gurin inda nake a kwance sai faman tunanen shi nakeyi
ina matukar mamakin wanan sauyin nashi nace Allah ke nan mai iko yau wai ni Fatima
ce yaya sadauki ke wa wanan kulawan haka yanzu.
Washe gari bayan nayi sallah na fara aikin gyaran gida da ta ko ina duk da gidan
ba wani dauda ke gare shi ba sosai amma,sai kyalli gidan ke yi kawai.
Haka kawai nace bari nai girkin abinci rana mai kyau da haduwa ,sosai na zauna
na girka ..
Sai da ga abincin na gama amma kuma na kasa cin komai daga ciki sai kallon shi
nakeyi a gabana kawai.
Abin mamaki sai gani ina kewan ganin yaya sadauki don ina bukatan ace yanan yaci
wanan girkin dana hada.
Ban kai ga karshen tunane na ba naji bell din gidan yana ringin a kasalance na
mike zuwa duba wanda dake sallama a kofan gidan.
Yana tsaye rataye da coth din shi a kafadan shi sai yar jakar kayan shi dake
sabale a hannun shi.
Na kasa boye farin ciki na dana gan shi a lokacin na ji kamar na fada mai a jikin
shi na rungumay shi amma kuma bazan iya yin hakan ba.
Kamar wanda ya karanci zuciya ta a lokacin sai naga ya ware min hannayen shi da
sauri ba bata lokaci na fada tsakiyan hannayen shi.
Ya mayar ya rufe ni dasu ina jin yadda yake sauke ajiyan zuciya a hankali kamar
yadda nima ajiyan zuciyar na sauke ina cewa sannu da zuwa yayana.
Dago kai yayi tare da dan ture ni baya kadan nai mamakin hakan sai ji nayi yace
niba tsoho bane da zaki dinga kirana wani yaya can na fada maki kuma sai kin biya
bashin hakan da kika fasa min tunda na fada maki bana so.
Da sauri nace iam sorry my life ai min afuwan please bazan kara ba da yardan
Allah.
Murmushi naji yayi tare da cewa yana tafiya ina tafe a bayan shi tare da jakar
dana ansa a hannun shi.
Zubewa yayi saman kujera yana lumshe idanuwan shi a hankali dakin shi na wuce na
kai jakar na dawo na dauko drink hade da cup na nufo shi.
Idanun shi suna a lumshe hannun shi na saman wuyan shi yana kokarin cire nicktie
din da ya daura a wuyan shi.
Na tsiyaya mai ruwan lemo a cup tare da dago cup din ina cewa uhmm, yaya love ga
ruwa kajika makoshin ka dashi ko.
Sai a lokacin ne ya dan bude daradaran idanuwan shi ya sauke idanuwan shi a
kaina.
Sai ce min yayi bissimilah ko tare da gyara zaman shi yana nufin na bashi.
Gaban shi na dawo na tsugun na kadan tare da mika cup din a bakin shi a hankali
yake kurbawa ina yi ina cire cup din daga bakin shi a hankali har ya sha fiye da
rabin wanda na zuba mai a cup din ya daga min hannun shi yana cewa thanks.
Haka yasa nagane cewa ya koshi ke nan na aje cup din daga gefe dayan saman table
din.
Nace mai abinci fa my love?
Zan so idan na samu amma bari na watsa ruwa na sauke gajiyana tukun .
Shigan da nayi yai matukar burge shi sosai don kayan sun min matukar kyau sosai
english wear ne a jikina wando da riga yar rigan daga baya ne ya dan sauka min
kadan amma daga gaba bude yake yana yauki sosai idan mutum ya motsa da jikin shi.
Yana matukar bukatan matar shi a lokacin amna sanin cewa tana cikin period yasa
shi daurewa tare da jan guntun tsuki kawai yana kokarin mikewa tsaye.
Dakin shi muka nufa da taimakona ya shiga wanka ni kuma na kwashe kayan zuwa
kaiwa mai wanki ya wanke su.
Tsab na shirya dining din na jera mai komai yadda ya dace na aje shi tare da
komawa dakin nashi don nagani ko yafito daga wankan.
Na samay shi a tsaye gaban wardrobe din shi yana ciro kayan da zai saka a lokacin
da sauri na kara tare da taimakon shi.
Na fitar mai da wasu masu saukin sakawa a jiki na mika mashi sai da ya shirya
muka fito daga dakin a tare da shi.
Sosai yaji dadin girkin yafara ci cikin jin dadi da kwanciyan hankali sai dai
yana mamakin yadda ya samu nai girki haka kaman nasan da zuwan shi garin ranan.
Sallama mukaji a tare muke kallon mai shigowa gidan yaya Bashar ne sai su
maigadi dake shigo mai da katan shi har dining din yaya Bashar ya karaso yana fadin
kai mutumina dama dai an san da zuwanka ke nan wanan girkin haka ?
Yai murmushi yace nima dai shine nake mamakin hakan kunyan maganan yaya bashar
naji nai dan murmushi kawai.
Gyaran jikin da akaimin jiya yasa nai wani irin balain kyau sosai kurciyana ya
kara fitowa fili sosai a lokacin.
Yaya bashar zama yayi sukaci abincin a tare suna hiran bayan robo a tsakanin su
ganin lokacin sallah azahar yayi na sulale zuwa dakina nai sallah.
Ko da na fito na samu sun fita hakane yasani sanin sun fita zuwa sallah ne.
Bayan sun dawo a falo suka zube ranan a tare suka wuni a gidan can bashar yace
kai bari na tafi gida nima gashi na hanaku walawa kaida yar kaunata.
Dan tsuki yaja yana fadin kai wani angwancewa tun tafiyana fa take zuban jini wai
har yau bai tsaya ba wanan ai yazama matsala ke nan ko?
Haba wani matsala kuma kai mutumina badai har ka fara damuwa da rashin mace ba ke
nan tare da kai.
Yace I dont know gaskiya amma kila hakan ne kasan ina under training din ka ne ai
dole ne na ji hakan .
Kai ban son sheri kaji kai dai kawai kazo hannu ka shiga gari kawai amma ni
yaushe na taba baka wani training can.
Wanda kulkun kana cikin jajayen mata da bakake kuna kallon ko wace kala har gida
ake kawo maku tayi fa nasan a raha don fatin jinin ku kawai.
No no no kada kai min sheri wallahi bash ni idan ba a kan matana ba tunda nake
ban taba aikata haka ba wallahi iyakata kiss kawai da mace ko shi ba wai wani can
ba mai yawa.
To yanzun kan kaunata ta cira tutan ta akan haka ta kawar da wanan rantsuwan ai a
zuciyar ka ko?
Ban sani ba yacd je gata can daki ka tambaye ta ina ganin zakafi samun amsanka a
gurin ta.
Yace wani don Allah rufa min asiri kaji kada kasa ana daukana da daraja na koma
shasha .
Sadauki yace dama may kake dan iska ita daine da bata san halinka ba take daukan
ka wani kamili can.
Nafito daga daki na samay su sai kwasan dariya suke tayi sai dai wanan karon
akwai hijjab a jikina kasan cewan yaya Bashar yana a gidan haka yasani rufe jikina
don shi tunda ba muharamina bane shi.
Da hannu yaya sadauki ya yafuto ni lokacin zan shiga kitchen ke na hakan yasani
na juyo garin su nuna Bashar yayi da hannun shi yace ga mai magana dake nan dama.
Kallon yaya bashar din nayi wanda kunya ya rufeshi sosai yace Fatima kyale shi
kin ji sherin shi ne kawai na juya kawai da murmushi na bar gurin su.
Kayan tsaraba ne sosai yazo muna dasu na nan gida Nigeria daga doya manja mai
kyai na kwarai irishi har buhu guda aka sayo.
Na juya naji muryan shi yake cewa cire mashi kayan su yatafi yabar mutum ya huta
cikin iyalin shi.
Ni dai nabar gurin inda aka tara tsaraban na kalla gasu birjit dasu komai na
girki an sayo bayan muna dashi.
Na debo wa yaya bashar da yawa nakai mashi na koma tare da hado wasu masu yawa
zan fita dashi yake cewa nawaye wanan din kuma ?
Nace wai da su maigadi zanba don su suka shigo dashi gida yace yana da kyau
hakan.
Murna sosai masu gadi sukayi suna ta zuka min albarka tare da godiya kamar nice
na,sayo kayan.
Ban tsaya ba nafitar da namu dan kadan sauran na,shirya su na don za a kai can
cikin gida gurin su mama.
Haka muka kwana bai tabani ba sai faman juyi da tsuki yakeyi shikadai a inda
yake kwance.
Sai washe gari na barshi yana ta faman rankon barcin da bai samu ba daren jiya.
Haka muka wuni ya fita zuwa gida ya gaida su mama da sauran mutanen gida.
Bai dawo gidan ba sai da yamma lis bai bata lokaci ba yafita sallah
Na idar da sallah magariba ina addua ban san da shigowan shi dakin ba sai jin shi
nayi yace uh,umm, haba Fatima kin fara sallah shine baki fada min ba ko yaune kika
fara sallah dai.
Girgiza kai nayi yace what Fatima tun yaushe kikai wankan tsarki nace kwana biyu
da ya wuce ke nan.
Wani irin kallon mamaki kaman take kuma fuskan shi ya sauya a lokaci guda sai naga
ya juta ya bar dakin .


ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU

IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,,,,


A LOKACIN MU KE,,,,


Gaba daya na daina kwaliya a gidan na daina fitowa falo yadda na saba na zauna a
tare dashi, gashi wasa wasa mun fi sati daya haka sai zaman yar tsama mukeyi a
tsakanin mu.
Shi kan shi har bashar ya fanhici yana da yar matsala a tare dashi sai dai bai
san daga ina matsalar take mai ba.
Tunda zurfin ciki irin nashi bai bari ya fadawa kowa halin da yake ciki balle a
bashi shawaran da ya dace dashi.
Zaune suke ga system ya aje a gaban shi amma ya kasa sauraren bayanin da bashar
yake mashi a lokacin.
Shiru bashar yayi yana kallon shi can yake cewa wai may ke faruwa ne sadauki naga
fa duk kwanan kana cikin dan damuwa.
Guntun tsuki yaja yace may ga nine wai lafiya kalau nake bashar ya hade hannayen
shi biyu guri guda ya tagumi dasu ta kasan gemun shi yana kallon abokin nashi na
tsawon dan lokaci.
Can yace tabbas akwai matsala a tare da dakai wanda nake gani kamar daga gida ne
ko gurin kaunata Fatima?
Nace maka babu komai murmushi bashar yayi yace wallahi akwai komai kan don ni
nagani kafada min may ye matsala please ?
Don nima shawarana da matsala bata wuce ka akan may kai zaka dinga boye min
damuwan ka wanda a gaskiya banjin dadin hakan wallahi ko.
Kallon bashar yayi yasan abinda yafadi gaskitane har cikin ran shi ya dan ja
tsuki ya mike tsaye tare da saka hannin shi a cikin aljihun shi ya nisa gurin
window office din ya nufa yana kallon waje can ya nisa kadan ya juyo inda bashar
yake zaune yace.
Bashar wallahi Fatima tana son jefani a cikin wani hali saboda dan dalilin ta
mara amfani.
Ai tasan yadda nake ta amince ta aure ni amma kuma may zai sa yanzun sai da na
yarda da ita zata bijiro min da,wasu akida nata na daban can.
Bashar ya ce tare da mikewa ya dan tako zuwa inda sadauki yake a tsaye yace ban
fahinci tasan halinka ba ta yarda ta aure ka haka nan ?
Yace kai tsaye kwarai eh ai tasan koni waye tasan ina sha aiko ?
Bashar ya rintse idanuwan shi don takaici yace haba haba man kaida bakin ka har
kake ikirari da sabon Allah haka why why please.
Lokaci yayi fa da zakaiwa kan fada kafin ai maka yau tun kuna kubiyu kaida Fatima
inaga sai yaran sunzo an fara masu gori a makaranta akan shan ka.
Idon shi ya rutse yace kaga abinda yasa ban sha,awan auren ba hausa tun farko
amma maji tanace akan wanan yarinyar sai nayi.
Ita Fatima har ta isa ta hanani abinda nakeyi ko nai niyar yi kamar ta who is she
bad way ?
Itace ko wani abu don gashi saboda ita ka shiga bakon yanayi kana gani Fatima ba
wata haske bace a rayuwan ka halan.
Ya dago ya kalli bashar ido da ido yace haske haske fa kace yace to haske may
Fatima take a gare ni kuma?
Bashar yai yar dariya tare da dan buga kafadan sadauki yace ko wani irin haske nw
a yanzu kafi ni sani wallahi.
Halan ka shawo har ta fahinta da hakan ko yace wai shine takewa fushi kwata kwata
yanzu ta daina kulani har yar kwaliyan nan ma ta daina yin shi kullun tana daki a
kumshe tana hadiyan bakin ciki.
Bashar yace da sauri kagani kagani zaka kashe yar mutane saboda mugun halin ka ko
?
Yace oh nima ma zan kasheta ba itace zata kashe ni ba ita da takasa bani hakkina
dake a kanta.
Wallahi ta shiga hankalin ta don tasan idan yau nace zan cika uku a gida na zan
iya wake da hasara ba ita ba.
Dariya bashar yayi yace wallahi da watan kunyan ka ya kama a garin nan don kafin
ma ka gama zagaye dakin su ka dawo gareta gari yasan ko kaiwaye ko ?
Jeka auro mata uku yau kagani waye a matsa in ba kai ba zata kwabe mawa.
Kana zaune kalau da matar ka kai mata abinda bata so ta dauki mataki maimakon ka
bata hakkuri ka lalashi abinka tunda kaine baka da gaskiya amma wao kai shine har
kake neman hanyan kuntata mata Allah ya baka sa an auro mata ka tara a gida tinda
kana da kudin hakan .
Wallahi batin fada maka mata da kake gani suna da nasu ranan idan kace bazaka
bari ba itama rana da hanyan rama cutar ta akan ka sai ka shiga hankalin ka.
Fatima dai ce ba yadda zakayi da ita don tai maka zara a zuciya kuma muddin
bakane me shiri ba har mama taji naka ya samay ka kuma ji zarayi tunda inta gidana
ta samu labarin halin da kuke ciki.
Dariya yayi yace ashe kaima kasan maryan magulmaciya ce ke na kyashan ta manne da
sarki.
Yace to dakata don kawai tana gyara shine zakai mata mugun lakanin suna kawai
wallahi yanzu zamu saba dakai akan maryam.
Kallon bashar yake yana dariya yace kai dai ka fadi da bakin ka bashar yace ai
mantawa nayi a gaban makiyin mu nake.
Yace wallahi kaje kasan yadda zaka rarashi fatima ku fahinci juna idan ma kana
fasa wanan shan yafi maka alheri don ko wata mace bazata ji dadin ace mijin ta ko
dan ta yana sha ba ga mata da gorin tsiya wallahi.
Sun dauki lokaci suna musayan magana kan zancen karshe bashar yai mashi sallama
akan zai tafi gidan Inna ya gaida ita bai samu zuwa da safe ba.

****** ********* ******
Yashigo gida fuskan shi a sake ya samay ta zaune a falo ta kunna tv sai kida da
rawa na yan iska ake a wani tasha na kasar ghana.
Zama yayi a gaji saman kujera ta watso mashi harara tace kasamo kudin ne da ka
dawo min gida haka?
Kallon mamaki yai mata yace cikin karfin hali wai Jamila may yasa baki son a
zauna lafiya ne ke ?
Tace lafiya kudi kaima kasan idan ba kudi ni ba zaman lafiya gare ni don dasu
nasaba.
Kasan wallahi inda ba kudi kai Ahmed baka isa ka aure ni ba don kasan da wa yanda
nake hurda a baya.
Murmushi yayi yace Jamila ke dai in ba kudi sam babu zaman lafiya dake ni yanzu
fa ban son abinda ya taba min rayuwan yar matata don ashirye nake akan duk
bukatanki ko ina zan shiga na samo maki don kiji dadi kawai.
Hararan shi tayi tace in kana son kaji dadi na mike min su kawai inji dumus sai
kaji dadin nawa.
Hannu ya tura a cikin aljihun shi yana fadin angama inda za a bar ni yau na shafi
wanan body da ake min kwalelen ka dashi kwana biyu.
Kudi ya mika mata da sauri ta fisgi kudin tare da sake wani murmushi tace dama
nasan kana dasu ai boyewa kawai kayi don kaji may zanyi.
Ajiyan zuciya ya sauke a ranshi yace don baki san zubar da kaina danayi na samo
su bane don kwadayin ki da masifan ki kawai.
Yana matukar son jamila a ranshi do ba laifi yarinyar ta iya gado sosai gurin ma
irin hakane suka hadu da ita har yaji ya kamata ya aure ta kawai yanuna mata karya
ya auro ta din duk da mama asiya taso kawo cikas ga maganan amma yai sa,a ba ya
yarda akayi abin.
Ranan kan yasan ya kawo kudi don tun wurin suka fara harkan ma,aurata a tsakanin
su duk bashin da ke kan su na kewan junan su sai da suka biyawa kansu.
Don jamila irin matan da basu iya kwana biyu ba tare da namiji bane ya kusance ta.
Tun a gaban shi bayan sun huta tafara kashe kudin gurin sayen banza da wofi yana
kallo ba yadda zai yi don son da yake mata.
Ranan da dare ma tare suka fita yawo da ita ya kara kashe mata dan canjin dake
hannun shi kuma.

****** ********* ******
Ina zaune a dakina kayana da aka wanke nake kokarin nikewa a lokacin don najera
su a wardrobe dina.
Dakin ya shigo saye yake cikin kayan barcin shi sau daya na daga kaina na
kalleshi na kawar da kaina tare da ci gaba da abinda nakeyi a lokacin
Karaso yayi bakin gadon da nake zaune yai tsaye akaina tare da kura min idon shi
na wani dan lokaci.
Can naji muryan shi yana cewa kina ganin kamar wanan abin da kika zaba zai fishe
mune Fatima.
Banyi magana ba illa mikewan

73 / 92