Author : Zainab Idris Makawa Seenabu Category : Complete Novels
sani ba?
Nace cikin turo baki da kokarin tashi tsaye ni halan nai maka tsikine ?
Yakai hannun shi ga dan bakina iya karfin ya murde shi da karfin tsiya, ban san
lokacin da nasa kuka ba da karfi ina cewa.
Ya sadauki nimay ne maka katsane ni haka kaja min ciwon kai yanzu kuma kazo ka
murde min baki.
Na karashe fadi cikin wani irin kuka nace in gidan kune baka son ganina sai in
bari nima fa diyace kamar kowa.
Na juya zuwa cikin dakin da kuka na sai muka hafe da Maji dake shigowa falon,
hannun ta dauke da kayan su jik dinta, da hapic na wanke bathroom.
Tsaya tayi cikin mamaki takaleshi ta kalleni cin son jin may yafaru bayan futan
ta .
Sai kukana take ji a cikin dakin daga inda take tsaye, tana mai wani irin kallon
tuhuma.
Tace may kai mata sadauki?
Cikin ko in kula ya nufi saman kujera ya zaune, yace shagwaba take ji kawai dai.
Kai may kaimata nace?
Tambaya kawai nayi ina kuke sai tai min rashin kunya nikuma na murde mata baki.
Kana ko da hankali sadauki?
Shin yarinyar nan tobashiyar kace ko kuwa wai?
To bari kaji wanan kukan da ka sata ko ka bata hakkuri koo na rama mata abinda
kai mata.
Wa zan ba hakkuri Maji?
Tace Fatiman.
Yace cikin mikewa kai haba maji don Allah ki bari kada ta kara raina ni mana.
Kai har wani raini kake gudu bayan wanda kajawa kan ka?
Ya mike kawai yabar dakin don shima kukan da yake ji yafara shiga zuciyar shi a
lokacin.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,,,,,,
IDAN KIN TURAWA WANDA BAI BIYA BA, BA MU YAFE MAKI BA ALLAH YA ISAN MUNA,,,,,
Bayan dawowan su maji daga saudiya da yan kwanaki jin ba wanda ya tayar da zancen
abinda akai min agidan,
Maji ta kawar da kaiwaici a idon ta inda ta samu Imirah ya dawo daga kasuwa ke
nan zai shigo gida take ce mai,
Imirana ji mana sai ya dan waigo yai tsaye kerere yana kallon ta cikin rashin
mutunci.
Yace ina jin ki,
Ganin babu mutunci yanzu a tare dashi yasa maji cewa ,yanzu Imirah baka ji kunyan
abinda kayiwa yarinyar nan ba da bamu nan?
Amatsayinka na babba a gida anbar maka amanan yaran nan shi ne kuma kaida kanka
kai kokarin keta mata haddinta?
Fuska a daure yace dama don wanan maganan kika tsayar dani ?
Saurayi nake ita kuma nudurwace zan iya shigar da kai na akanta ko hakan kuma
illa ne.
Murmushin takaici maji tayi tace amma tir da halinka na dan akuya, halin
maha,inta.
Idan zina abin yine jeka ka nemi yar uwar yin zinanka can kuyi tayi amma ba yar
mutane da aka bani amana ba.
Murmushi yayi yace Maji kada kiga laifina yar taki ce da shegen kyau wanan aiba
komai bane,
Allah ya shirye ka,Allah kuma ya tsare amma ni dai Hauwa,u ina maka kashedi akan
diyan mutane a gidan na wallahi muddin ka kara yi mata wani abin tashin hankali
again zan ba mutun mamaki don shiru ,shiru ba tsoro bane kuma in mutum bai jiba ya
gwada ya gani.
Sai muryan Umma daga bayan su akaji tace tau isassarsa masu gida wallahi duk
sherin ki baki na kakan ki ba.
A hir din ki akan diyana ina fada maki Hauwa,u ki sakan min maran diya don bani
nasa danki yayi tambada ba abaya.
Haka,kawai don yar kauyen diyarki zaku saka min yaro gaba dasheri don kawai a
bata mai suna.
To wallahi ta Allah ba taku ba kuma karya kukeyi nagaba yayi gaba nabaya sai
labari.
Kuma kijawa karuwan diyar ki kunne da take kokarin cusa kanta gare shi tayi
kwantai a kauye ankawo ta gari ana neman mashinshini a cafke.
Murmushin takaici maji tayi tace kaice yaya a matsayin ki na uwa kuma diya mace
kin san zafi da munin irin abinda Imirana ya tashi aikatawa yarinyar nan amma idon
ya rufe da kin gaskiya.
Babu komai ai Allah ba azzalumin kowa bane yana sama yana gani duk bayin shi.
Ta juya inda Imiran ya fara tafiya tace wallahi kaji na fada maka duk ka sake
kokarin ketawa yarinyar na hadin ta sai kayi mamakina a gidan nan.
Tashige cikin part din mu duk muna jin yadda suka kwashe da Umma da dan ta maji
tace kai Allah dai yasa kin kusa aure ma kowa ya huta, ki bar wanan gidan namu mai
tarin fitina cikin shi.
Muryan Baba ne daga waje yake fada kamar haka amma dai ke kan anyi uwar banza
wallahi.
Yanzu ashe abinda yaron nan yaiwa yarinyar nan ke nan bansani ba shine har kike
fada don kunya bai ishi idon ki ba ke,
Ida da yarkice wani katon gardi haka yai niyar illantawa haka zaki fadi an mashi
kazafi ne ba gaskiya bane hakan
Dama ai nasan hakace zai kasance muddin kaji ba ka tsaya kai bincike irin yadda
ya dace,
Tunda da matar so dinka ake fitina to ku sani ni diyana basu da gadon iskanci
masuyi dai kowa yasan su don haka sherin mutum yabishi can cikin kayan shi .
Haka Umma ta tare ta hana Alhaji ya,tsaya yai fada akan wanan zancen don idan ya
matsa zagine da tonon asiri zai dawo akan sadauki da,uwar shi .
Wanda yanzu daga uwar har dan tausayi sukw bashi sosai don duk abinda zasu gujewa
gudun magana agidan suna kokarin yin shi don kimar su ta riga ta zube ,
Su Umma da mama an samu gurin zagi da gori da habaici koda akan da tsinke ne.
Shiyasa yakan kawo ido yasa,wa Umma inda ita ko tana ganin kamar tafi karfin
kowane a gida sai yadda tayi da kowa agidan baki daya.
Hjy kubura ce kawai bata samu ta mallake yadda ranta ke so ba amma ko ita din ba
laifi don bata iya kifar mata da,gwaunati a gurin mijin su ba.
Amma wanan munafukan Hauwa,u zamani amarcin ta Alkah daine yanufi takai wanan
lokacin a gidan Alhaji don gaba daya hankalin shi ya koma ga majine kamar ita
kadaice mace.
A ganin su Umma ke nan a lokaci amma kuma a gurin Alhaji tausayin Maji yake jin
don ya dakatar da ita ga karautun ta yadauko ta ya hada cikin matan da ke aikin
gwaunati suna da abin kansu.
****** ********* ******
Yanzu abinda ya,rage bukina baifi wata bakwai ba don an dagar da zancen bukin da
babana yai ciwo ne shi ya roka abari har guri ya sha iska sai ayi.
Haka kawai kwatsan ranan muna zaune sai ga sadauki ya shigo ya fito daga cikkin
garine fun safe safe ya fita sai da yamman nan ya shigo gida.
Suna hira ne da maji yayin da mu muke harkan gaban mu can ya sa murya ya kira
sunan Amirah ta amsa da sauri tana fadin na,am yayana.
Yace zaku iya yin aiki hajji bana kuwa don tare nike son in tafi daga club din mu
na samu kyautan kujera har har biyar.
Kinga dani dake da maryan nake son mu tafi sai tsagal Maryan tace da Bintu ko?
Tsit falon yayi don sun san maryam tayi tsaga da fadi gaskiya.
Yace wanan bakauyan taje mijin ta ya kaita mana nidai ni dake da Amirah nace kina
min gayyan wasu takarce can daban.
Kai ban son rashin kunya Fatima ce takarce kuma yace ba tana da miji ba taje ya
kaita.
Ai dai kasan zai iya kaita tunda yana da halin shi shima maji ta fada mai hakana.
Don Allah dai yaya ka hada,harda Bintu mu tafi ita ma ta sauke don Allah tana
fadin cikin dan marairaicewa kamar karamar yarinya.
Yace maryam ashe ke karamar yarinyar ce yaya zai kai ta saudiya bayan tana da
miji idan yai karana fa na kai mai mata saudiya bada sanin shi ba.
Don haka ki bar wanan zance don Allah nikan da naji ta matsa zance ina duke kaina
akan littafi.
Nace Anty maryam bar zancen nan nima ban faye saka kaina inda Allah baikaini ba.
Nafi kowa murna yau dajin yan uwana zasu gabas su sauke farali at early age din
su.
Muryan maji ne tace ai yadda Allah ya bashi ikon , biya wa yan uwanki ko ke haka
zai bashi ikon ya biya maki atafi dakw kafin kiyi aure.
Maji na fada maki wanan kujeran kayautan su na,samu nima daga wa ni kungiyan mu
dake can kasan Dubai.
Jin nan babana ban son tsaya wani kace nace kawai ka bari yaran nan su tafi da
yar uwar su .
Kai kanka kasan da cewa, bamu taba tsan manin irin haka ba a rayuwan mu.
Shiru yayi har maji ta gama fadan ta baice uffan ba nidai takaicin irin wanan
halin da yakw min sun kai min ko ina amma indai har nai aure na bar gidan su na
huta da komai ma.
Can ya dan furzo iska yace yauwa Maji na dade ina son in tambaye ki naji sai
abubuwa sukai min yawa ban samu lokacin tsayawa tambaya ba.
Fadi ina jikin muma dai shiru mukayi muna saurarwn shi sai da dan garani ina
kokarin yin abindake a gabana ne alokacin.
Yace Maji wai akwai wa ni tsoho da naje gurin shi kwanaki bashar ne yakaini gurin
mutumin
To da zan dawo sai yake cewa idan nazo gida na fadawa mahaifiya na kada ta manta
da alkawarin da tayi na cewa zata kaini da kanta gurin da aka bukaci ta kaini.
Ni din nan inji maji ta fadi cikin dan murmushi da mamaki a fuskan ta a lokaci
guda.
Tace kai mutane akwai yaudara wallahi ko sai mutum yai karya ne zai samu abu daga
gurin mutane ?
Shiru nayi idona akan littafi amma kuma zuciya ta tana nazarin wani zance can a
baya tun farko.
Amma maji wanan mutumin wallahi tsoho ne sosai kuma ban tsan mani yaudara bane
yadda yai min maganan
Don zanfita cikin murmushi yace nacewa mahaifiya na tayi niya ta tafi inda tai
alkawarin zata kaini da kanta in ba haka ba gaskiya akwai matsala,babba nan gaba.
Don tana tunka ana walwale mata ne za,a mayar da hannun agogo baya sosai .
Mai makon naji maji ta tuna alkawarin da tayi a baya sai naji sun buge da zagen
tsohon mutane kawai.
Suna kiran macuci ne ma yaudari don taci kudinw yake fadin haka Allah yasa dai ni
ba mai zuwa gurin malamai bane da yan tsubbu neman taimakon su na dogara ga Allah.
Amirah tace ba dai maman ba kan yaje can ya yaudari wasu gaba amma ba nan ba kan.
Batare da na kalle su ba don shima mai maganan kanshi na duke ne kawai alaman
surutun su yai mashi yawa.
Sai muryana kowa yaji a falon ban juyo ba ban dago kai ba nace mama kece ba karya
mutumini keyi ba.
Da sauri sadauki ya dago kai yana kallona itama uwar hakane ixo ta tsura min don
ban taba mata haka,ba duk zamana da ita.
Tace Fatima kikace nine nace zan kai sadauki wani guri ban kai shi ba nace eh
mama ,
Kai Bintu yau kuma maji zaki kullawa sheri haka maryam ke nan ke fadin haka cikin
dariya.
Na girgiza kai na nace bazan taba yiwa mama sheri ko wani nataba har abada.
Dan tabe baki yayi daga inda yake zaune yana wani game da,wayan shi na,wasan
driving.
Don yakan dan taba wasan mota a America tare da,samari yan uwan shi don nishadi
kawai haka har kudi suke sakawa ko kyautan wani abu ga wanda yaci.
Mama tace dada,Fatima kikace nine nai alkawari na kara cewa eh mama sai dai
bazan tuna maki ba sai wani lokaci in kuma kin tuna shike nan.
Amira tace a to dama dai ba,a shiga tsakanin Bintu da maji don sun fi kusa, kila
tare da ita akai zancen.
Nace ai harda ke anty don gaba dayan mu musan da zancen sai dai mantuwa kawai .
Dan dariya yayi yace wanna yarinyar Allah munafukace Maji baki dai son ana fadi
ne kawai amma ji daurewa wai kowan ku yana gurin.
Dakata Babana tunda Fatima ta kuke da haka akwai magana ke nan ya mike tsaye yana
fadin ni kan na fita don bsn iya sauraren shirmayn yarinyar nan gaskiya.
Yana ba da baya na,shake murya nace mama kin manta maigani yace kikai mashi
sadauki inda gwago mai masa ta tafi.
A,a,a anyi haka Fatima shiku jin ina kus,kus da maji yasa shi juyowa ta ce tabbas
anyi haka Amirama,tace wallahi na manta muna zaune kuwa aikai maganan.
Cikin wani fargaba Maji tace babana dawo ka,zauna don Allah da mamaki yake kallon
mahaifiyar nashi don bai san may shu,umar yarinyar na tafada mata ba a lokaci guda
yaga ta birkice.
Tace don girman Allah ka fada min yadda aka fada maka ka fada min a take ya kara
nanata mata, sakon da tsohon ya fada mai.
Tace inko ba wani ikon Allah ba yaya akayi wani yasan wanan zancen don dai ba,a
nan akayi shi ba.
Mamakin yadda maji ta rude a lokaci guda haka ya bashi mamaki matuka yace Maji
injin dai lafiya ko yace cikin kallon fuskan ta ido cikin ido.
Take ya fahinci da akwai matsala ke nan yace please Maji may ke faruwa ne wai?
Ko zancen mutumin gaskiyane dai yake fada don ni ban dauki zancen da wani
muhinmanci ba kada haka ya tayar maki da hankali.
Maji a sanyaye ta,ke ce mai gaskiya Babana akwai matsala saboda akwai wani mutum
da haduwa kawai nayi dashi ranan ina asibiti ya shigo gaida mu yake cewa kana da
matsala don Allah nayi kokari nazo dakai gurinshi ya ganka.
Nai alkawarin zan kaika amma kuma kaga na manta shaf wallahi inba yanzu da Fatima
ta tuna min ba.
Ban san lokacin da na sauke ajiyan zuciya ba jin yadda Maji ta canza maganan a
lokaci guda.
Don dama ina gudun ace daga gwagona zancen yafito yace zata koya wa uwarsu bin
bokaye nima yana iya sakani gaba da zagi don nasan halin shi.
Yace amma Maji kin dauki zancen serious ke nan ko?.
Tace idan ba serious matter bane yaya za,ayi zancen ya fito daga gurin wanan
tsohon.
Kaga ke nan maganan mutumin gaskiyane tunda ga zancen yafito a gurin ka.
Jikin maji yai sanyi sosai a lokacin don sai ta shiga tunane watau ke nan masu
sherin basu daina ba ake nufi ke nan.
Tai mamaki da taji yace yanzun za,a tafi gurin mutumin ke nan tace ya kamata
gaskiya .
Zan samu lokaci sai mu tafi kafin na koma ke nan don na kusa tafiya ba kuma zan
dawo ba sai nazo daukan yaran nan mutafi don ta inter national zamuyi tafiyan.
Maji tace amma na fada maka da diyata za,a atafi baice komai ba har ya mike zuwa
kofa sai lokacin ya ke cewa Maji sai ki shirya mu tafi dake kenan don bazan kwashi
wa yan nan ba duka su zama min wahala a can.
Don nima ina son nayi inganttacen ibada banda lokacin taulali dasu gaskiya don
kin san yar ki bakauya ce matar bakauye kuma.
Yana fadin haka Fita yayi daga dakin nima sai yau banji haushin shi ba don ya gama
min komai a duniya.
Mutumin da adalilin shi zai shiga kasa mai tsarki ai yagama min komai wallahi ko a
duniya dole nayi hakkuri dashi don iyanzu na fahinci halin shine haka gwatsale
mutum a take don bai son raini.
Nikuma yar kauye ce baruwan mu da banbants babba da karami gurin fadin magana.
****** ********* ******
Maji ta tsara Baba hat ya yarda cewa zadu duba jikin Baba na ne akauye don haka
muka fara shirin zuwa gurin da akai magana.
Don ta kira gwago ga waya sunyi magana akan tafiyan mu kuma gwago taiwa dan uwan
nata magana yasan da zuwan mu gurin shi.
Sadauki ne dai bai san cewa da mu za ai tafiyan ba sai lokacin da za,a tafi yaga
duk mun shirya tafiya yake cewa
Wa yan nan fa kuma Maji ?
Tace dasu zamu tafi don suma ina son na kaisu gurin mutumin ya gan su.
Kaman zai yi magana sai kuma yai shiru yana tsaye tsakar falon ya harde hannayen
shi guri guda.
Can yace sai dai da Bashar zamu tafi ban tsan mani motar zata dauke mu ba fa.
Tace ai zamu iya matsawa mu hudu a bayan dukkan yace da yake ita wanan yar fillon
ba jiki gareta ba ko?
Yadda maji tace hakane mu hudu muka matse a bayan motan muka kama hanys sai
garin.
Tun shigan mu mota banyi magana ba don idan na shiga mota amai nakeyi ko yanzu
shi ke damuna.
A hankali na bude ledan da na riko na shige cikin hijjab dina naita kwarara amai
tun ina yi a boye har Maji ta gane da sauri tace subbahanallahi.
Fatima amai kikeyine ?
Da sauri ya juyo yana fafin oh shit,
Don Allah Bashar parke motan da sauri kada ta damay mu da wari a mota.
Fada yake yana fadin kin san baki da lafiya don gulma shine sai kin biyo mutane
kuma?
Yaja tsaki aka fito da sauri na samu guri nai ta shara amai mama tana a kaina sai
sannu take min.
Da ya tsaya min muka shiga mukaci gaba da tafiya, an fara tafiya cikin jan tsuki
yace i hate naga ana amai wallahi.
Bashar tace kasan wasu mutane idan sun shiga mota sai su dinga amai don warin
petror.
Da kyat naga,mun kawo garin kaina yana,duke sai ciwon kai dake damuna a lokacin
sosai.
Gida ne irin ginan kauye na haki da itattuwan dake basu innuwa manya manya a
kofan gidan.
Suka tambaya kamar yadda aka fada masu wani