Advertisements
Chapter 22 Reading A Lokacin Mu Ke by Zainab Idris Makawa Seenabu BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

A Lokacin Mu Ke by Zainab Idris Makawa Seenabu

Author :  Zainab Idris Makawa Seenabu Category :  Complete Novels

Chapter   22 / 92

63K to 66K   out of 275.8K words

saka
mai ido akan al,amarin Bintu din da bata masan yasaka a saka mata ido ba.

****** ********** ******
Bayan haihuwan mama da sati biyu na shirya komawa gida garin mahaifina tunda
naga mama ta yi karfi yanzu,
Ba yadda batayi dani ba akan na tsaya na kara kwanaki amma naki, tsayawa.
Mama tace to idan Kabiru yadawo bai samay ki ba fa nace mama nifa ba,wai yana
gabana bane mutum da mata uku yaya zanyi dashi gani da tsoron tsiya.
Asalima ni saboda,shi zanbar garin nan idan ya tambaya kice mai na koma sokoto
gaba daya.
Tace kaiyya saikace ke ba diyar hausawa ba kuma musulmai zakice kina tsoron
kishiyoyi.
A,a mama ba zan iya ba naga yadda mamana na sokoto take fama da,nata don haka
abin tsoro yabani.
Gara na samu yaro bakauye dan uwana,a zarga min dashi yafi min ruwan idon sunan
muna Abuja.
Dariya naba mamana take cewa kai yaro dai yaro ne ai abin sa,a ne ni yanzu da
nake shan wahala a,nan kishiya gare ni?
Mama,naku daban ne nace ni dai zan tafi na kwashi komatsena sai yar karamar
tashar garin amma,sai na rasa mota .
Akan kada,na kara kwana a garin yasa na tare wani mai mashin mukayi ciniki dashi
la,asar sakaliya, sai gani garin mu har kofan dan gidan mu.
Tun daga kofa nafara jin harshen mama ta,bawa tana fada da,wata yar yan uwanta
da,ta dauko riko.
Na,shiga gidan da sallama na inda na samu kafin na,shiga mama ta kewaya ban daki
a lokacin.
Dakin da nake na nufa da kaya na nasamu dakin duk kashin awaki ya bata shi
kuma,wai akwai mai kwana acikin sa hakana.
Ina ciki na fara gyarawa naji muryan ta tafito daga ban dakin take zuciya ta ta
tsinke, don na san nadawo wa turke na mai cabo ke nan.
Na fito waje a tsorace nake da ita nafito ina cewa sannu da gida mama mun samay
ku lafiya.
A darara ta amsa min da yauwa anga dama andawo ni dai nasan ai ba gurin zuwa sai
gona.
Na juya zuwa cikin dakin naci gaba da gyarawa kamar yadda,na fara da farko kafin
wani lokaci dakin yai neat duk da dakin hakine da,daben kasa a,kasan shi.
Na idar da,sallah magariba naji shigowan mahaifina nan nafita zuwa yi mashi sannu
da,zuwa.
A bazata yaganeni yace a,a Bintu andawo ke nan yaya,su wajen maman naki nace duk
suna lafiya suna gaishe ku.
Na mike na koma dakin mu tare da kunna dan chager daki mai aiki da battery.
Daga cikin dakin namu ina jin mama tabawa tana,wa Baba na mita wai gashi na,dawo
wurin ta, na kasa zama da uwar nawa.
Naji Baba yai gyaran murya yana cewa tabawa ina son ki sani nan gidan uban Bintu
ne bata da gidan dayafi mata wanan don haka tana da incin duk lokacin da taga dama
ta shigo ta zauna iya adadin kwanakin da take son yi.
Jin firinan su zauyi nisa yasa na jawo wayana na kunna kira,a ta yadda ma,ba
zanjiyo hayaniyar su ba.
Ban fita ba daga dakin sai washe gari tun da safe nafito na fara gyaran tsakar
gidan mu dama har ta,wajen gidan.
Dama aikinane da nake gari da ban nan kuma ba mai yi kowa baida lokacin yin shi.
Na tara wanke wanke nafara saiga mama tafito tana wani yatsune fuska wai ita a
lokacin ta,tashi daga barci.
Muryan ta naji daga bayana tana fadin kada kuma mahaifinki da yan uwanku su gani
suce ina sakaki aikin bauta.
Bance komai ba,sai cewan danayi mama ina kwana.
Ta amsa,a,wulakance tana aikin girkin dumamay tana minti kan fadan su da Baba
akaina jiya da dare sai fadi take dadin abindai nima na haifa a gidan don haka na
wuce gori ga kowa balle ace min ni juya ce.
Ina kallo suka cinye dumay mayn su ita da,yaran ta ban damu ba na,shige daki sai
zuwa rana dana yunwa zai kashe ni nafito zuwa bakin wani shago na,dan sayo garin
kwaki yakai mudu biyu da,dan sugar na na,saka a hijjab dina na,shige dashi bata
gani ba.
Ina zaune ina sha idona yana kawo hawaye sai ga,wanan yarinyar da mama ke riko ta
dan zo gabana tanayi tana leken kofan mama tace don Allah ki san min nasha nima
basu bani dumamay ba wai ba yawa su Lawal taba suka cinye da ita sai cewa tayi na
kankare kanzo naci.
Kuma kanzon ba gishiri ba,komai wai haka zanci shi dan kadan ne bai isheni ba.
Gaba daya na tura mata kofin garin nace yi sauri ki shanye kafin ta fito tagan ki
tace zan koya maki munafunci.
Tas yarinyar ta,shaye garin gaba daya tafita da,sauri take tabani tausayi.
Tun ranan duk dan abinda naci tare muke ci da ita, komai rashin yawan shi kuwa
don a daki guda,muke kwana da ita.
A haka dai nai ta,zaman hakkuri a gidan mu da matar mahaifina watarana tabani
abinci watarana kuma tace bayawa ancinye.
A haka kwanaki suka shude min zuwa satittika har wata ina gidan mu zaune kamar
wata bare can.
Wata rana ina zaune na gama duk abinda nakeyi na gida kamar kullun sai ga wani
yaro ya shigo yana cewa wai ana sallama da Bintu.
Kafin in magana mama ta karbe da fadin wanene kuma wanan da yamman nan.
Yaron da aka aiko yace yace nace mata wai kabir ne kafin mama tai wani magana na
mike kawai na fada daki sai gani tayi na fito saye da hijjab dina har kasa cikin
wanda Maji ta dinka min lokacin ina gurin ta.
Nace mama zan fita na gan shi daga garin su mamana yazo, ban tsaya jin may zata
ce ba na,sakai na fita zuwa waje.
A jingine yake gabab motar shi kirar hilux irin ta,shiga kauye, ya,sanya wata
koriyar shadda da akaiwa dinkin Jamfa harda hular ta kalar kayan.
Tun daga fitowa na yake sakar min murmushi, sai dai wanan karon ya dan kara min
hasske da kiba kadan.
Barka da fitowa, kalman da ta tare ni dashi ke nan da na iso inda yake tsaye,
Tuni naji wani wani kunya ya lulubeni saboda tafiyan da nayi ban fada mai ba
kuma,nan garin mu da nazo ba,services ko dayaushe.
Na dan rusun na kadan na,gaishe shi, tare da,tambayan shi yaya hanya.
Cike da,fara,a yace hanya Alhamdullahi mai gaskiya,
Murmushi nayi nace gaakiyan may kuma nayi har ake kiran min ita cikin kunya
na,fadi hakan.
Sai murmushi naji yayi ya dan kalleni ya kada kan shi kawai,
Yace wallahi Fatima baki kyauta min ba haka,kawai ki kama hanya ki wuto baki
fada min ba ko a waya,
Sai kawai da naji shiru natura a,diba min ko lafiya ake ce min wai ai kin dawo
nan.
Gashi kuma ban samu zuwa ba,don an turani wani course a lagos sai last week na
dawo gaskiya banji dadin yadda kikai min ba.
Cikin yar muryata nace to kayi hakkuri nima,tafiyan tazo min bashiri ne.
Yace gaskiya banji dadi ba don sai ma na,fara zargin kodai ban samu karbuwa bane
a gurinki shi yasa.
Dan satan kallon shi nayi tukun, san nan nace a kunyace ,a,a ba hakana ne
gaskiya.
Sai naji ya sauke ajiyan zuciya yace tau Alhamdullahi,
Amma kuma kin shirya zaki iya auren mai mata har biyu ki zama ta uku?
Dammm naji gabana ya fadi don an tambayeni abinda nafi kowa tsoro yanzu watau
kishiya.
Na dan kwantar da murya cikin dakewa nace idan Allah yayi hakan ne ai ban isa
naja da ikon shi ba.
Sai ya dan zuba min ido can yace tau kin gama magana ke nan ai tunda kince Allah.
Ban nuna wani alama najin tsoron maganan shi ba amma sai nace ai Allah shike
komai dama.
Nan dai muka dan taba hira dashi yana min karin bayani a kan, shi.
Yace matar shi ta farko yar uwarshi ne garin su daya auren gida akai masu shida
ita duk da dai su suka hada kan su.
Azuciyata nace kaji matsalar ba yace sai tabiyun ita soyayyace ta hadani da ita
kaunar abokina ne dake sokoto lokacin ina,aiki a sokoto kafin na koma Abuja mukayi
aure da ita yanzun yaranta biyu dani.
Ya,kare da,cewa sai kuma yanzu da wata farar tantabara ta,sace min zuciyana a
lokaci guda duk da can baya banyi niyar karin aure ba ina ganin matana biyu sun
isheni rayuwa.
Sai gashi ganin farko da nai maki naji kin kwanta min a zuciyata fiye da tsanmani
na.
Dafatan zan kara samu karbuwa a gurin ki bayan mun dan taba hira yake ce min zai
koma don gobe yake son ya koma,sokoto ya dauki matar shi tare suka,shigo amma ya
barta sokoto taga gida.
Yace min ina zan samu yara su sauke min kaya a,bayan motan shi
Nace cikin yar murya lah, dama ka barshi zuwan da zakayi gurina shine harda
dawainiya.
Yace ai nasan baku rasa ba amma ni ban saba zuwa guri babu tsaraba ba.
Yaran makwabtan mu dake wasa a kofan gidan su na kira inda suka shiga da kayan
cikin gida.
Nayi sa,a mama tafita zuwa uguwa don bata zaci lokacin zai tafi ba nasan da bata
fitaba a lokacin.
Kafinta dawo nida Farida yarinyar da take riko muka tsince kayan tea da su
indomie muka,boye inda bata gani.
Sauran muka barsu kofan dakinta inda inta dawo zata gani.
Tana ko shigowa tai tozali da kayan sai cewa tayi cabdi jam wanan kayan alherin
kuma haka fa nake gani.
Farida tabata amsa dace wa Bintu aka kawowa su, mutumin da yazo kafintai wani
magana sai ga babana yadawo daga gona shima tambaya yake.
Tace yarka aka kawowa su sai ka tambaye ta ko waye nidai in kun kwaso rigiman
birni babu ruwana.
Allah ya,sauwaka babana yace sai ya samin kira nafito ina mashi sannu da zuwa.
Yakece sai na dawo na samu wanan uban kayan haka na tambaya akace waikece
aka,kawo wasu.
Nace eh Baba Kabir ne dan hakimin Rabah yakawo min su dazun dayazo.
A ina kika san shi Bintu, Baba ya tambaya cikin son jin inda na san Kabir, nace
Baba da naje gurin mamane shine muka hadu dashi a can.
Allah ya kyata yace inda ya isa gurin kayan buhun shinkafa dan gote sai jarkan
mangyda da doya mai yawa sai tumatur din leda katon guda da taliya leda biyu,
Dankari inji Baba duk wanan din muke dashi haka nace eh Baba mu yakawo wa tsaraba
yace,
Baba yace Bintu idan kin san bakya son shi kada muci kayan shi yazo yai
muna,tasau watarana nidai k8nga banda,shi.
Shiru nayi ban yi magana ba baba ya juta zai futa nace baba zan dauki doya da
taliya naba su Ama don su suka kwaso min kayan zuwa cikin gida.
Yace hakan na da kyau ki baau yadda ya dace azato mama tabawa bazata kalli kayan
ba amma dana dauki doya manya zai kaiwa su Ama sai ji nayi tace kai amma kedai baki
san ciwon kanki ba,
Wana abin duka zaki basu don kawai sun kwoso maki kaya maza rage su kinji nace to
mama.
Nan aka,shiga sha,ani da kayan mukan mun boye namu bata sani ba ni da farida mun
samu na karyawa safe da yamma mu faki idon ta,muyi amfani da abin mu.



ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU

IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,,,,,


A LOKACI MU KE,,,,,

Zancen neman da Kabir yake min ya kewaye kauyen mu,sai ga yan uwan shi har gidan mu
sunzo gaidani wai kuma suga ko wacece ni din.
Gami kuma da nuna goyon bayan su dari bisa dari akan neman da dan uwan su ke min.
Kamar yadda,dangin miji suke nuna goyon baya idan dan uwansu ya,tsiri aure, komai
mutuncin da akeyi da uwargida sai an samu masu hakan daga dangin shi.
Nima hakane ya kasance dani don yan uwan kabir maza,da mata haka suke shigowa
ganina,tunda ance masu nima ba a kauye nake zaune sokoto nake zama.
Basu san cewa ko a,sokoton labe nake zaune a gidan mutane kamar kuku.
A gaskiya da farko naso Muhammad Kabir kodon na samu inda na labe na,rufawa
rayuwa na,asiri na huta da guzuban mama tabawa da nake ciki.
Yakan zo kusan duk karshen wata gida cikin irin zuwan da yakeyi sai yazo har
garin mu da dan tsaraban shi na abin arzki yakawo muna.
Wata rana Kabir yazo wurina sai dai wanan zuwan bai dade ba kamar yadda ya saba
dadewa idan yazo inda nake.
Ya ce zai koma na ya bude mota ya miko min wasu kaya dinkakku yake ce min anko
yai min tare da,sauran matan shi.
Na karba nai godiya sai kuma ya kawo kudi masu yawa ya bani, amma sai nace ya,bar
kudin kayan ma,sunyi min.
Amma sai ya,aje min kudin saman hijjab dina ya,shiga motan shi sai horn din shi
naji na,dan daga kai ya sake min murmushi tare da jan motar shi yabar gurin.
A dakin mu saman tsohuwar katifan kadan da muke kwana akai amma na,gyara, shi
mutum bai sani tsohuwace ta yagalgale saboda bed shirt da na,sa na,rufe shi lif
ba,a ganin sirin ciki.
Dinkin kayane irin ta yan birni jakkuna da,takalma masu tsada sosai, sai kayan
makeup set mai kyau dasu turaren suma masu kamashi sosai.
Kayan abinci yadda ya,saba kawowa haka ya ke jibge su a,kofan gidan mu yanzu
tabawa shiru kake ji tsakani nada ita,sai lalashi.
Afili amma,a,kasan zuciyar ta,tankar ta soke ni takeji a rayuwan ta don kishi na
take balain ji duk kiyayyan da,takewa uwana ya koma a kaina yanzu. Sai dai tana dan
waye wane kawai don tasan wani lokacin nima nakan dan tsula mata tsiya yadda naso.
Don ban san ya,akayi tasan muna boye wasu kaya,ba,sai ranan ta zaci ko yanzu iri
dane da,zata kwace min abina tabawa diyan ta har yan agolan da tazo aure dasu gidan
mu sun fini dara a lokacin.
Sai ganin Tabawa mukayi a kofan dakin mu tayi tsaye kerere ta re da,daga labulen
dakin cikin tijaran ta na yan iskan matan kauye take cewa,
Ke Bintu kwaso sauran kayan nan da kika,boye wanda aka kawo muku wai ke
munafuka,shine kika boye kayan shayi wai don kada na,sha,
Ti jiya banyi barci ba ina jinku kuna sha ke da muna fukan can Farida, don haka
na leka naga may kuke don haka kifito dashi nan.
A zatonta zan mike na dauko mata kamar yadda da can nake mata cikin rawan jiki.
Amma,sai taji murya na yau ina cewa,
Eh ko kingani fa,
Sai may,
Ina dai ba,sata,nayi ba,nawane ni aka,kawo wa ko ?
Don haka sai yadda,naga dama da abina Farida ce idan kince na barbata abarta mana
yunwa ya kasheta.
Baki bamu abinci yadda ya dace sai dai kibawa diyan ki
Don Allah yai muna mafita shine kuma zaki nuna halin ki na hassada haka.
Eh lalai kuwa Bintu sai yau na,kara yarda kin shiga Birni tunda har ina fadi ki
fadi haka,
Nace mama kece kikaja hakan don yakamata ace yanzu na ci ragowa gareki ko dan dan
girman da na,kara.
Amma ke kullun sai kokari kike kiga kin mayar dani baya kin tausheni kin ha,ince
ni kin fifita diyan ki a kaina.
Don banda,uwa agidan ai ina dai gidan gidan ubanane dole ko abarni na zauna ciki.
Nan tafara rafa hannayen ta cikin mamaki da lalami tana fadin eh lalai zaman
bariki ya nuna kan shi yau kan.
Baba yana dawowa tafara fada mashi bata kai karshen zance ba yakwala min kira
nazo, nace gani ba.
Yace Fatima yanzu na dawo gida maman ku ta tare da,zancen da ban san halinki
bane.
Nan na koro mai duk kan maganan har karshen yadda mukayi da ita,da,safe.
Ya juya gurinta yana cewa Tabawa kiji tsoron haduwar ki da Allah horo da,yunwa ko
dabba,ba,ai ma,shi balle mutum dan adam mai tunane.
Yanzu ba gashi a,sana din ta alheri yana sauka muna duk karshen wata sai yaron ga
dan gidan hakkimi ya kawo muna abinci ba.
Nan dai har sun hau da Baba ko may ta gani sai gata ta sauko don kanta ta, dawo
tana cewa haba Bintu ke diya tace kada ki yarda mutane su zuga ki ki min rashin
mutunci suyi dariya.
Nace komai ya,wuce amma da safe indan Baba ya fita sai ta turo yaran ta da,kwano
wai na yan mata kayan shayi ta dan kada.
Da,nafita iyawa sai na,zuba mata dan kadan a cikin roban nace akai mata
hakana,baida yawa.
Shine samun saukina a gidan mahaifina da mama tabawa yanzu kadaran kadaham muke
da ita.

****** ********* ******
Shine yau da Kabir yazo ya,tafi da,wuri ashe tare da,matan shi yazo sun zo yin
bukin wata diyar yayan shi ne a,Rabah.
Shine yazo da iyalin shi gaba daya amaryan shi bata zama a,kauyen sai dai tazo
ta,wuni takoma gidan su.
A nan aka,samu wata,tsegumama ta tsegunta mata zancen neman auren da kabir keyi
yanzu.
Nan ta,tayar da,hankalinta sosai har ta tambaya,akai mata,kwatancen gidan mu sai
gata,ita,da,kannen zawarori biyu.
Ni dau ina daki kwance ina kallo a,wayana,da,aka,karbo min caji sai ji murya
mukayi ana,cewa,da karfi sallamu Alaikum ko nan ne Kabir Rabah ke neman aure a
fitsarance suka shigo muna gidan.
Eh nan ne inji Farida da,bata san da may suka shigo muna ba,
Eh lalai ashe dole a haukace a so mai mata,biyu an matsu a,tashi gidan haki akoma
alminium zalla.
A,a sannun ku da,zuwa sai wani kallon banza suke watsawa,mutane su ga yan birni a
dole.
Ina, ita gajar da kabir din ya,wullakanta kanshi yazo har nan gidan wai neman
aure.
Saye nake da,wani dogon riga baki cikin wanda yaya,sadauki ya,sayo muna,ghana, a
jikina don dashi naiwa Kabir kwalliya da,yazo don haka ban cire ba yana a jikina.
Nai rolling din kaina,da dan kwalin kayan tsaye nayi harde da,hannuwa,daga kofan
dakin mu ina kare masu kallo irin wanda,suke ma gidan mu da yan uwana .

22 / 92