Advertisements
Chapter 23 Reading A Lokacin Mu Ke by Zainab Idris Makawa Seenabu BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

A Lokacin Mu Ke by Zainab Idris Makawa Seenabu

Author :  Zainab Idris Makawa Seenabu Category :  Complete Novels

Chapter   23 / 92

66K to 69K   out of 275.8K words

Sai da suka juyu ne mukai arba dasu, gaba dayan su ido suka tsura min,
A cikin min kallon kurrullah tun daga kafana gar zuwa kaina o lalai kice min farar
fata yabiyo mana kin sanshi maye farar mace ce ko manyace.
Nace ballw ba,farin ya,jawo shi ba,nan sai hali, don may yuyuwa yaga abinda
ya,rasa,a,gida ne yazo nan.
Ke kama kanki don ko ba,a,fada,ba,nasan kece yake nema don kece ki kadan yi
kama,da zubin yan birni kadan.
Ba shirmay ya,kawo mu ba ni matar Kabir ce ta biyu na,zo ne nai maki kashedi akan
mijina,wallahi,
Don ko ita bakauyar dake gida, ban dauke ta wata tsiya ba balle ke dake shirin
kawo kanki.
Nace hmmm mijin ki ko mijin mu yar uwa, ba,a kara aure aka,auro ki ke naga dani
dake din duk ba,matan gado bane,
Balle ki manta ki kirashi da su nan wai mijin ki aikin makara da,baki tsaya kin
auri wanan mai matan ba da,sai ki tsaya,ki auri wanda baida mata,a kiraki matar mai
shi.
Yanzu ko tunda mijin wata zamu aura da ni dake kinga kalman mijin mu ya,shigo ke
nan.
Ke wallahi, kama kanki dama ku yaran kauye haka kuke da iya magana tankar
tsofafin mata.
Nace mazan mu da matan mu kuwa din shi kika gani ga bakauyen mijin ki har ya,rude
ki kika,aure shi.
Sosai mukai musayan harshe da su su fadi in fadi wai tana min kashe di na rabu
mata da mijin ta,inva haka ba zaki shigo ki samu balai a gidan shi.
Nace kai dama baki zo ba da,ban san balai ke gidan Kabir ba
Don da ma kabir bai a,raina saboda bai min ba amma yanzu zuwan ki sai naji
ina,matukar sha,awan auren shi na zama koda ta hudu ne.
Gaskiya,zuwan ki yai min rana sosai din haka kikoma,ki fara shiri nima zan shigo
da shirina sai na zo.
Ina fadin haka na juya zuwa cikin daki dama gidan ya fara cika da,mutane don jin
hayaniyar da akeyi yayi yawa.
Mata ko suka,saka,su gaba da ihu da,tur da,Allah waddai da halinsu kishi wai
hauka,ne da zaku zo gari wa gari ku na kishin hauka wa mutane.
Sai bayan naji tayar da motan su na sauke ajiyan zuciya saboda karfin halin da
nayi don duk a,tsorace nake, kada suyi min dan banzan dukan tsiya tunda nice banda
gaskiya, nike bi masu mijin su.

Lokacin da,labarin cin mutuncin da matar shi tazo har gida tai min hankalin Kabir
yai matukar tashi sosai tunda safe sai gashi kofan gidan mu.
Da Baba na yafara ganawa, kafin daga baya asa a kira ni nafito ina daure da
fuskana tamau,
Tun fitowa na,Kabir ya kura,min ido yana kallon yanayin da,na,fito dashi don yana
son fahinta da sauki ko akwai magana.
A mutunce na durkusa na gaishe su sannan na koma gefe nace Baba gani,
Mutanen da Kabir yazo dasu suna zaune saman tabarman da aka,shimfida masu
idanuwan su a,kaina karrr,
Baba yace Bintu Kabir ne ya samu labarin abinda matar shi tazo hannan gida tai
maki shine yazo ya,bada hakkuri akan sabanin da aka samu da ita.
Kaina na sadda kasa nace cikin yar murya Baba gaskiya ayi hakkuri da wanan zancen
don tun ba,a shiga ba an fara irin hakan
Ina ga in an shiga gidan baki daya sai ai marus ke nan lokaci daya sukace ,a,a
wanan ma,ai baiyuyuwa sam.
Duk da sun fahinci kan zance na ina nufin nafasa ke nan sai suka shiga ba da baki
da gyaran zance .
Shiko kabir yana zaune yai shiru kawai abin duniya ya,kai mai ko ina abinda matar
shi tazo tayi ta bashi kunya.
Baba dai da yaji irin yadda suke bada hakkuri ni kuma na kafe akan sai dai
a,rabu.
Sai baba yace Bintu tashi jeki ciki kawai ma,karasa,maganan dasu.
Namike nashige ina jin yadda Kabir yake sauke ajiyan zuciya daga inda nazo
wucewa ta gaban shi.
Ban kara jin zancen ya tashi ba sai bayan kwana hudu sai gashi yazo har lokacin
bai sake jikin shi ba dani.
Na fito saye da zani da rigar atamfa mai ruwan jan kalla, dinkin shi yai matukar
karban jikina da kyau.
Son in mashi kwalelenka, ranan gyale na yafa ajikina sabanin hijjab din da ko
yaushe nake rufe jikina dashi.
Na durkusa na gaida shi a cikin ladabi da biyayya tare da,tambayan shi gajiyan
buki.
A,sanyayw yace Fatima kinga yadda kika,wahal dani da,kalman ki dakike fadin wai
kin fasa aurena.
Don Allah Fatima koda nine nai, maki laifi, kada kice kin fasa aurena, don baki
san irin wahalar da na,sha ba na ganin za,a raba ni da wanan kyakyawan halittan mai
suran larabawa a hannu na.
Don Allah Fatima koma may ye kada ki kara cewa zaki rabu dani akan wata, wacce
dama ita bukatan ta ke nan nayin haka.
Wallahi ranan da,muka,bar nan nayi tunane dubu a raina don sai na kasa banbance
so na yasa kika ce hakan ko kina.
Nan yadan zubo min ido yanaxmai kare min kallon kurullah , akunyace na dan rufe
fuskana da hannayena .
Yai ajiyan zuciya yace nagode Fatima don ko hakan ma,sheda ce ta kin sauko zaki
yarda dani.
Mun jima muna hira dashi yana bani labarin irin fitin matar tashi saratu yadda
sukw kwasan masifa da uwargidan shi a kan lalai ita ala,dole abar mata miji ita
kadai
ko da ya zo tafiya sai yace kin hana ni shakat wallahi Fatima gashi haka nazo ban
riko maki komai ba.
A hankali nace mai babu,komai, ko haka,na gode ai,
Ya ce sure ?
Nace, mashi insha Allahu.
Haka yatafi ba don ya,so ba yana ta,faman bani hakkuri ya,wuce abinshi.
Anyi wanqn rikicin da Sati biyu ina gidan mu gaban iyayyena hankali a kwance
abina na fitar da komai a raina,
Ina zaune ina gyaran ganyen da mama,tabawa tasayo lanbu zamuyi miyan dare dashi.
Ina cikin gyaran ganyen ne sai naji karan diran mota ta tsaya a kofan gidan mu.
Dan dakatawa nayi da aikin nawa ina sauraren ko anyi bakine gidan daga bisani
dai naci gaba da aiki na.
Gwago na ce ta shigo gidan da sallaman ta saura kiris na zubar da ganyen da nake
gyarawa don murnan ganin ta danayi.
Fuskanta dauke da yalwatacen fara,a take ce min dana karaso gurin ta cikin
daukin ganin ta.
Bintu baki da kirki banzaci zaki zo ki share ki zaman ki haka a kauye kin bar
uwar dakin ki sai damuna take tunda na koma.
Ledan dake hannun ta na karba daidai lokacin da mama tabawa takw dawowa da
makwabtan su.
Mama tabawa tace a,a yau gwagon yara ce a garin kwana biyu kin shige birni
abinki.
Nan dai suka dan taba wasa tsakanin su sai kuma gwago take tambaya yayanta yana
gona ke nan ko bai dawo ba har yanzu kuma tana son ganin shi.
Ba ,a jima,ba Baba na ya dawo daga daji, sun jima suna hira da babana wanda
akasarin hiran akan yar uwar suce da gwago tai jinya takare.
Can tun ina jin hiran su sai na bar jin tashin muryan su, ma,ana dai za ai magana
ta,siri a tsakanin su ke nan.
Zuwa can Baba na ya daga murya ya kira ni nazo, na,samu guri dan nesa dasu kadan
na,tsugun na.
Baba na yace Bintu gwagon ki tazo tafiya dake ne akan umurnin mijin uwar dakin
ki, na can.
Don haka,sai ki harama ki shirya ku kama hanya don kinga mota,sukutun ya bayar
azo a tafi dake don ba,ayi zaki zo ki zauna haka,ba harki dade.
A take na bata rai na,tare da,dukar da kaina a kasa, baba na yace ko baki ji may
nace bane Bintu.
Cikin yar karamar murya nace naji Baba yace tau yau din nan ki hada kayan ki ku
tafi tunda sunyi mutunci haka nima idan na samu lokaci wuri yasha iska zan shigo
naga inda kuke.
Na dago kai din nai magana gwago ta watsa min harara dole na noke kai bance uffan
ba.
Namike jiki ba karfi idanuwa na,sun ciko da,hawaye amma,ba,wanda ya kula da
damuwa na nafara ashirya kayana.
Kafin sallah magariba haka gwago tace sai muyi hara man tafiya kada muyi dare
sosai a hanya.
Nan na,dauko yan abubuwa nabawa Farida yarinyar da zantafi na bari cikin uku ban
mama tabawa,
Komai da muke boyewa,nabar mata,ban dauka,ba, sai kudin dana,bata ta boye ta tafi
garin su dashi idan taga wuya,zai kashe ta a gidan.
A sanyaye na gama hada kayana raina a bace don kwata kwata ban son komawa gidan
su maji don bani bukatan zama cikin wanan babban gida mai cike da tarin rikici a
cikin shi.
Saboda wancan karon ma banji dadi ba don a tauye nake cikin su sai dai na kulla a
raina wanan karon kan zasuga canji sosai a gare ni don su barni na,dawo kauyen mu.
Munyi sallama da kowa mun kama hanya sai dai kallo daya ya ishi mutun sanya
alaman tambaya a kaina din yadda nai kicin kicin da raina.
Sai ranan naga mama tabawa ta,tausaya,mun tana fadin haba baban binta in bata son
zuwa abarta mana.
Daga Baba har gwago na ba wanda yabita kanta sai kyaleta sukayi kawai.
Mun hau titi da kyau mun saki hanyar dajin mu gwago ta kalle tana cewa Bintu kin
bani mamaki sai kace wace za,a kai mugun guri.
Acikin wata raunaniyar murya da take gap da,narushe da kuka nace gwago bawai
mugun wuri bane.
Amma zama gidan da,baka,da,alaka da kowa,sai zaman girma,da,arziki kawai, shine
nake jiyewa.
Tace da kika zauna wancan karon anyi wani abin ne sai da na nisa kadan nafara
fada,mata,duk yadda aka,kwashe da,bata,garin.
Tace ni na sani ai ba yau ba Hajiya kubura munafukace ta,karshe wallahi ko.
Tsayin lokaci muna,tafiya muna hira har muka fara hango cikin garin sokoto.
Unguwan sama road muka dosa inda muka tsaya a kofan gidan Alhaji habu.
Lokacin dare yayi ko don har anyi sallah isha,i don haka cikin gidan muka shiga
kai tsaye.
Na zaci gidan mu zamu shiga amma,sai naga sabanin hakan kawai mun shiga gidan
masu hali.
A dan tafiyan da,nayi na,samu canji na sauyin launin gidan sosai an canza abubuwa
da dama a gidan.
A kofan da aka,sake wanda ban zaci na,maji bane muka tsaya tana sallama daga
kofan shiga.
Muryan maryam ce naji tana a,a mai masa,oyoyo harkin dawo ashe?
Sai tafara leken bayan gwago tagani ko ita kadaice tazohangini tayi ina,saye da
lace din da Kabir ya dinka min da matan shi cotton lace ne mai laushi sosai da
duwatsu caaa a jikin shi.
A razane tace maji yau kan ga yarki ta dawo gare ki gwago ta cika alkawari kowa
ya huta dada.
Da sauri ta karaso gareni ta rugumay ni cikin jin dadin ganina a lokacin.
Jin abinda ta,fadi yasa Amira fitowa daga dakin ta cikin sauri tana min sannu da
zuwa cikin murna da jin dadi itama.
Maji tafito a hankali daga daki ganin yanayinta yasani saurin fahintar bata
da,lafiya a jikin ta.
Inda,take na nufa da,sauri na,fada jikin ta sai ta rungumayni cikin jin dadi.
Ta,dago kai ta kalli gwagona tace mai masa nagode da,wanan karamcin da kikai min
dawo min da Fatima,a kusa dani.
Kai amma dai Bintu badai a kauye kike ba dai ko gaba daya kin canza kin koma wata
big girl dake haka.
Nan aka faea hiran yaushe rabo bayan nadan huta anmin tayin abinci nace na koshi.
Sai Maji tace naje na gaida Baba kafin ya,shige da sauran mutanen gidan gaba
daya.
Ido na,runtse gami da,cewa ya Arhamanin Rahimin, ahankali na mike nafita,duk kallo
suka,bini dashi.
Ina fita maryam tace maji gaba,daya, fa diyar ki ta,sake ta canza kyaunta
ya,dada,fitowa a fili, jita kamar wata wace take zaune a abuja ba kauye ba.
A falon Baba na samu hjy kubura na shiga da sallama na itace tafara cewa wa nake
gani haka kamar Bintun hajiya maijidda.
Na karasa inda suke gefe kadan na tsugunna ina gaishe su Baba ya nuna j8n dadin
gani sosai tare da min ba,a naje gida na lake na manta da karatu a gabana.
Na dan kai lokaci a gurin Baba yana dan min tambayoyi a kan noman mutanen kauyen
mu nai masu sallama nafita daga dakin.
Dakin Umma da nake jin haya niyar su na fara shiga duk sunyi mamakin gani na a
wanan lokacin da kuma yanayin da suka ganni ba,wani fita hayacin da nayi banda kara
kyau.
Nan dai duk na zagaya nagaida su na,dawo dakin mu nan aka zauna a ta hira inda
maji da gwago suna can gefe suna,maganan su ta mayan wanda bamu san akan may
sukeyin shi ba.
Sai dai yanayin Maji ya nuna min cewa tana a cikin damuwa sosai ko ba,a fadi ba.
Ban dade dasu ba na mike ina fadin zanyi sallah dake kaina.
Nan dai bayan na idar na mika,kukana ga Allah akan ya,kareni daga duk wani rintsi
ko matsalar da zan fuskanta agidan mutane.
Ban fito ba na koma na kwanta amma kuma na kasa barci sai sunayen Allah maigirma
nake kira ina neman agaji a gurin shi.
Tun dawowana kula,da lafiyan maji ya koma kaina ko yaushe ina daki tare da ita.
Banga Sadauki ba kuma,ban tambaya ko ina yake ba nasan dai kila baya garin ne.
A hankali natsuwa yazo min da zamana dasu don suna nuna min kulawa sam mutum bai
gane cewa ba Maji ce ra haifeni ba a gidan.
Satina biyu a,sokoto nagane yanzu yanayin gidan ya kara canzawa sosai ba ruwan
wani da wani a gidan har yanzu.
Amma,akwai ci gaban rayuwa,sosai da,suka,samu don yanzu budi ya kara sanuw masu
sosai.
Hankalina yafara kwanciya sai dai kullun ina kewan iyayyena da yan uwana adan
zaman da mukayi da,mamatabawa da sauko da,akidar nuna min tsana,a fili datakeyi.
Kuma wani abinda ya,tsaya min a,rai shine tunanen Kabir yadda zaiji idan yazo
ya,samu banan nan nabar gari bada sanin shu ba.
A haka takardan makarantana ya fito wanda ban san baba yai min process ba saida
yazo a hannuna.
Ranan nai murna da farinciki garda kuna don murna,saboda ban taba zaton zan samu
ci gaba da karatuna ba.
Na fara zuwa makaranta tare da Anty maryam muke tafiya don makarantar daya da ita
state university muke.

Wata rana mun taso daga makaranta ga hadari ta gauraye garin da kyat muka samu
Napep din da zai kawo mu gida.
Ganin iska da kura ya,taso a lokaci guda nace wa mai Napep malam don Allah
ka,samu dan guri ka Parker har iskan nan ya dan rage yawa don tafiyan mu a haka
hatsari ne.
Guri ya samu kamar tadda nace ya dan tsaya a gefen titi kamar ance na daga kai na
hango Nafisa a cikin motan wani matashi.
Yanayin dana ganau yasa gabana faduwa da,sauri na juta gurin da Maryann take
zaune sai naga hankalinta a,waya yake ita, don haka naja bakina nai shiru ban fada
mata ba.
Can naji mai Napep na cewa bari mu lalaba don ga alamar ruwa nan tafe da sauri
yake tuki sai gamu a unguwar mu har kofan gida yakaimu daidai ruwa yana fadowa da
karfin Allah.
Take ruwa ya zubu ga iska sai kamshi yanayin garin ya canza launi alaman sabon
damana yazo ke nan.
Haka muka sauka shiga gida ruwa,na kada mu yana daga muna mayafin jikin mu.
Yaya Imirana na hango can tsaye daga kofan part din shi tawani kura muna ido
kamar tsohon maye.
Da,sauri muka nufi hanya shiga cikin gida duk habar kafan mu iska na dagawa yana
fita a fili.
Daga inda yake naji muryan shi yana fadin kai ashe cikan nan tadawo ne
tubarkallah dai kan komai tsab wallahi akwai kayan dadi a gurin nan.
Banzaci maryam taji shi ba saiji nayi tace dan iska a haka dai zaka kare gindin
mata.
Mukan da,sauri muka karasa ciki muna kankamay kayan mu daya jike sharkaf da,ruwan
da,akeyi.
Da karfi maryam ta rura kofan falon maji muka fada ciki a guje saukar da ajiyan
zuciya nayi yain da naji ruwan bai dukan mu.
Ashe maji na,falon cikin damuwan rashin ganin mundawo kafin ruwa ya fado din sai
ce muna take sannuku ku shiga ku cire wa yan nan kayan kafin sanyi yakara hawan ku.
Sam ban lura da mutum a zaune ba a lokacin sai ji da nayi Anty maryam ta,saji
kara da karfi.
Da sauri na juya zan kona,waje da gudu sai naji tana fadin oyoyo yaya sadauki.
Najuya da sauri inda naga ta nufa yana zaune fuskan shi dauke da murmushi.
Yace jeki cire kayan sanyin nan kafin yai maki illa,
Cikin shagwaba tace yaya ni har na manta dasu ina murnan ganin ka ai.
Nikan ban tsaya ta kan su ba na,shige daki nafara rage kayan jikina tare da zuwa
faban mirror dakinmu nayi wata futu, futu dani don jikewan danayi.
Na fada ban daki nawatsa ruwa tare da,dauro alwala nazo nai sallah.
Saida na,gama komai nafito falon ina,saye da,wata doguwar riga dark blue doguwa
ce rigar har kasa hannun ta shara shara nazo na zauna falon har lokacin yana zaune
suna hira da kannen shi.
Zamana yai daidai da kiran wayana da akayi na dauka ina mamakin wanda ya kirani a
wanan lokacin haka.
Sai na,dan basar ban dauki wayan ba don ban san mai kiranaba alokacin.
Sai kuma ga,kiran ya kara shigowa again na dauka da,sallama ban damu da cewa wai
na daga daga falon ba.
Don nasan daga inda suke babu wanda zai iya jin abinda nake fadi don tsabar
kwantar da muryana da keyi.
Bayan na gaisa da may shi na nuna bangane mai magana ba.
Yace haba Fatima na zaci ko a mafarki kikaji muryana zaki sheda ai tau Kabir
dinki ne wanda aka gudo akabari a kauye.
Maganan shi ce ta dab sani dariya sai duk suka juyo gareni hardashi suna min
kallon mamaki.
Nan na,fara bashi hakkuri ina,fada mashi yadda tafiyan yazo min a bazata nadawo
sokoto.
Amma yayi hakkuri dan banda nomba shine yasa ban

23 / 92