Author : Zainab Idris Makawa Seenabu Category : Complete Novels
ya mayar da dan da yafito daga tsatso na haka a,rayuwa ba.
Ai bazata bari a,fadi ba don kaga har roban ta,sayo ta mayar ma Asiya da abinta
wai don ta nuna ita ta haife ta.
Maji tace yaya Asiya ya kike son nayi kin face yau idan ba,a biya ki roban ki
ba,akwai tsiya a gidan nan don babu mai rabaki da shrgiyar uwar shi sai Allah.
Alhaji ya juya yana cewa ke ko Asiya haka kika ce mata don maganan maji yadan sa
jikin shi yin sanyi.
Ba dole ince haka ba tunda yana takamar shi dan iska ne har iskancin yakawo ga
kayana tun yana dukan min yara yau kuma ya koma ga kaya na.
Idan ko haka kikace gaskiya baki kyauta ba don dai kinga maijidda ba itace ke
tura shi wanan aika aikan ba.
Wai haka ma zakace Alhaji akan may zan zauna yaro kamar sadauki yana min cin
fuska kala kala tsoron shi nake ji ko may da,zan kyale shi.
Yanzun dai idan har ya kara takalar wata a gidan nan don Allah na rokeku da kuyi
hakkuri har lokacin da na dawo sai na dauki mataki da kaina.
Ke kuma Maijidda nasan kiyi hakane don kawar da fitinan don a zauna lafiya amma
ba daidai bane ki biya Asiya roban ta don Sadauki ya fasa mata roba.
To ayi hakkuri in har ban kyauta ba amma ni bada wani manufa na biya roban ba.
Ai dan tane shi don haka ba zancen biya a tsakanin ku don dan wani yai wa,wani
barna.
Mama Asiya tace wa ni sadauki ne dana Allah dai yai min katangar tsari wallahi da
wanan bakar haihuwa a,rayuwana.
Ikon Allah Asiya a gabana kike wanan zancen haka ?
Ai gaskiya na fadi don bani fatan haihuwan dan majiciji a rayuwana na haife shi
ya kasheni.
Allah ya kyauta inji Baba yafadi ciki kunar rai tare da mikewa yai shigewan shi
daki kawai su ma mikewa sukayi suka watse daga dakin mama Asiya tana ta bakar
magana.
Maji tadawo daki zuciyar ta na mata kuna ta samu su Amira suna ta hiran su Bintu
tana gefe zaune a makure bata tanka masu a hiran nasu.
Suna ganin ta sun fahinci ranta a bace yake anyi ba dadi ke nan a can falon baba.
Amira tai tsuki tana fadin wallahi yaya sadauki dai yana jawo muna matsala a
gidan nan.
Bintu tace sai ko mu bishi da addu,a don adfua makamin mumine ne tunda ba haka
Allah ya halicce shi ba ai.
Dago kai Maji tayi ta dan tsura wa Bintu ido sai kuma ta kawar duk yadda taso ta
danne hawayen ta kada su zubo saida suka zubo mata.
Hankalin yaran gaba daya ya tashi sai cewa Amira take halan mi sukace maki maji.
Bintu tace haba Anty Amira maganan manyane fa sai su kawai dai mama tayi hakkuri
tabarwa Allah al,amarin shi, ian Allah mai karban adduan bayin shine idan Allah ya
tashi canza shi sai kowa yai mamaki a gidan nan.
Hmmm Bintu ke nan baki san ko waye yaya sadauki ba ko a gidan nan ki barshi kawai
kuyi yar nisa danisa dashi shine sauki wallahi.
A,a anty Amira insha Allahu wata rana sai kunyi mamakin shi Allah dai yasa wanan
halin na iya kurciyane kawai.
Ikon Allah ke kin iya magana kamar tasbin kaka kamar wata babba van wallahi.
To Antu ai ba abinda yafi karfin ubangiji nagani don shine maitin komai a lokacin
kuma da yaso wanan fa jerabawa ne akan su mama da baba sai dai muce Allah ya basu
ikon cinyewa kawai.
Shiru dakin yayi suna nazarin zancen Bintu yarinya karama da babban magana kamar
wata babba can.
Jin sunyi shiru Bintu tace da zamu dage ko mu iya dakin ga mu dinga aiwatar da
ibada akan shi kawai ba,wai mu tsaya muna magana kamar sauran mutane ba muna kuma
yin sadaka akai insha Allahu ba,dadewa zamuga saukin al,amarin da yardan Allah.
Don ni wallahi na yarda da addua takobin mumine sosai don da na roki Allah saiki
ga an karba min.
Dariya,suka saka mata kai Bintu wanan cika baki haka kamar wata,shirihiya can.
Hmmm anty ke nan nifa tun ina karama Baba na ya kowaya min yin addua kin san ban
tashi a gaban mahaifiyata ba.
Da sauri maji wacce sai yanzuta sa masu baki a zancen su tun shigowan ta tana
hawaye tace.
Fatima ina mahaifiyar ki take Bintu tace tana can wani kauye tana aure sun rabu
da Baba ance tun ana goyo na da ya auri kishiyar mamana.
Shine da aka yayeni iyayyen ta suka dawo dani gurin mahaifina wai bazasuyi
wahalan banza ba .
Tayar dake shine suke gani wahalan banza Bintu tace cikin yar murya haka suke
gani sai kawai ga kwallah ya zubo mata,
Bata daina magana ba don kwallan sai cewa tayi, mama nasha wuya a gurin mama
hausi sosai don har tsakar gida na kwana ni kadai tun ina yarinya na.
Da kuma na girma abin ba,a cewa komai don ba irin wahalan da bata gwada min.
Amma sai gashi duk yaran ta ba wanda ya kaini don mazan su da matan su duk sun
lalace mata sai nice ma nadawo tana dan jin sanyi a gurina.
Ina ganin ganin da Baba yayi aikin wahala zai kashe shine suka hada baki
da,gwagona wai nazo nai mata hutun sati biyu na koma.
Sai daga baya gwago take fada min cewa wai Baba na yace na zauna gurin ta kada na
koma garin mu.
Takarasa maganan cikin kuka tace ina kewan gida da yan uwana sosai da farko amma
yanzu don rikon da gwago take min yasa na manta da komai gashi yanzu zama daku
yakara sa hankali na ya kwanta sosai bisa ga zamana a can kauye don abubuwan da ban
sani ba,a,rayuwa yanzu na,san su sosai.
Tun ina shekara sha hudu na haddace alkur,ani maigirma yanzu tulawa nake sai dai
akwai banbancin karatun mu na can da naku na,nan birni sosai.
Kinga ashe na,dan san wani abu nima ga,addini ke nan don malamin mu yana gwada
mu abubuwa siri sosai.
Allah sarki ashe mahaifiyar ki bata tare da mahaifinki gaskiya wasu mata akwai
ha,inci a tare dasu sosai wallahi.
Shi yasa nake ta hakkuri tun farko da cin fuskan da ake min a gidan nan don
yaran nan dake gabana don idan na fita na barsu cikin gidan nan wa kuke ganin zai
rike min ku amma na cikin su, ina ciki ma yaya muka kare dasu balle na fita na
barku.
Duk shiru sukayi suna nazarin maganan Maji don sun san gaskiya ta fadi ba mai iya
rike su amma kamar yadda suke rike yaran su.
Kowan su tasan gaskiya Maji tafadi don ba mai iya rikon su amana suji dadi kamar
yadda tace don haka sukaji tausayin uwar tasu ya kara shigan su sosai a gidan.
****** ********* ******
Salamu Alaikum wai ana sallama da Raiha sai mama dake duke a kitchen ta dago tana
cewa kai waye da yamman nan ka ce bata nan.
Kai tsaya Raiha dake fitowa daga bandaki tace wa yaron je kace gani tafe kaji.
Raiha yanzu don baki da kunya zance zaki fita da rana haka kowa yana ganin ki
kikau a kofan gida tsaye da namiji duk wanda ya wuce yai miki tir da halinki ko?
To mama kin san ko waye da,zaki kore min mai shi mama bari naje naga ko waye
nadawo, kawai sai ta shiga daki ta shiga gyara fuskan ta tsab ta saka hijjab din ta
sai waje.
Mama dake waje ta rike habar ta cikin mamaki sai cewa tayi ikon Allah yaran yanzu
Allah ya kyauta kawai.
Raiha tana fita taga gidan su tunfitowan ta ya kura mata ido yana kare mata
kallo nan yasan yarinyar tayi mashi ga komai kuma,zai more mata sosai idan yai sa,a
ta yarda da bukatan shi gare ta.
Dan waige waige taks don bata ga mai neman taba a lokacin sai wani bakar mota
mai tsada da ta hango, daga wajen gidan su, dan nesa kadan da gidan.
Hon din da mutumin dake cikin motar yayi yasa tagane shine mai neman ta a
lokacin.
Raiha ta nufi gurin a cikin mamaki don ita duk iya sanin ta,bata da saurayin da
keda koda karamar mota balle wanan dirkekiyar motan dake gaban ta.
Mutimin da tagani a motar bata taba ganin shi ba,a,rayuwan ta don haka sai tai
tsanmanin ba gurin ta yazo ba.
Sai taji yace malama,Raiha ko ?
Eh nice
Bisimillah shigo daga ciki mana ko kina tsoro ne kuma.
Tai wani irin har da idanuwan ta ce tsoron may zanji kawai dai ban gane ka bane
dai.
Bazaki gane ni ba,asalima baki sanni ba ni ne dai na,san ki ta hanyar gane gane
na nahagonki kawai.
Shine na biyo ki har nagane gidan ku ne nan sai yau na yanke shawaran nazo gurin
ki dafatan zaki fahince ni ai.
Wani kallo tai mai kamar bata yarda da,zancen shi ba sai tace mai a ina ka
ganni ne ?
Sai da yai murmushi sannan yace a gurin birthday din Salim murmushi tayi don
tasan anyi hakan .
To amma duk tsararun yan matan;dake gurin bai gansu bane sai ita zaizo gurin ta,
sai kuma,wata zuciya tabata amsa dacewa kece kikai masa kawai a gurin.
IkonnAllah tace a fili tare da,fadin shine kabiyo ni har gida kuma ?
Yace eh mana ko nayi laifi ne tace bance ba yace to sunana Abdul amma ana kirana
duwel ne don haka abokaina ke kirana dashi.
Hmm tau nagode da,har ka zabi kazo guri na,dafatan lafiya kazo har gidan mu
a,kaina.
Murmushi guy din yadan yi tare da,cewa ai tunda kika ganni a gurin ki ke ma kin
san alheri ne yakawoni gareni da,fatan zaki fahinci manufata a,gare ki batare da
kin fassara min zance na ba.
Murmushi Raiha tamayar mashi tana cewa da fatan zan samay ka mai cika alkawari
nima.
Nan suka tsaya suna dan kara fahintar da junan su kan shi tare da dan hira yana
fada mata ko shi waye da inda yake aiki.
Ganin yamma tayi sosai tasan mahaifinta zai iya dawowa a lokacin yasa ta yi
mashi sallama ta,shiga gida da fara,anta.
Tana shiga takasa boye farin cikin ta take cewa mama yau saura kiris ki kore min
sa,a ta kin kuwa ga mutumin da yazo gurina ne.
Uwar ta mayar da hankalinta akan yar ta tana sauraren bayan nin da takd mata
akan bakon ta.
Har saida mahaifinta ya shigo gidan suka bar zancen don gudun kada yaji zancen
su.
Tun daga wanan ranan suka hada alaka a tsakanin su ita da Abdul din guy din da
ya tafi mata da imanin ta gurin son ta.
Ba uwarta ba har mahaifin ta saida ya,san da zaman Abdul din don masifan son da
Raiha take mashi.
Wasa wasa Abdul ya fara dan test din Raiha da,wasu yan abubuwan da yake son sani
ko tasan da su a sabon sallon so da matasan yanzu ke ciki yanzu.
Bai samu matsala ba don ya samay ta yarinya ce yar rock sosai ba wasa don haka
harkoki suka fara tafiya a tsakanin su ba bata lokaci.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
IDAN BAKI BIYABA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,,,,
A LOKACIN MU KE,,,
Murna sosai takeyi don ganin ta dauko sabon fridge dinta da ta dade tana gurin taga
ta saye a rayuwan ta, don bunkasa sana,arta.
Ta bude fridge din yafi a kirga tana duba ciki da wajen shi don tabbatar da
lafiyan shi.
Ba laifi don ta samu yadda take bukata saboda sanyi da kankara yake daga sama
har kasan shi tsab.
Wanan abin yasa ta yini tana farin ciki da wanan karuwan da ta samu na ci gaban
ta.
Ranan sai da ta aikawa makwabta da kankara tana fada masu idan suna son saye ta
sai fridge mai kankara da ruwan sanyi, don haka su sa mata albarka a ciki.
Wasu sun yaba, wasu kuma sun kushe don haka duniya take dama wani baka hada
komai dashi ba amma yana bakin ciki da karuwan ka a duniya.
Shima maigidan ta bawan Allah da ya dawo yai mata fatan alheri akan fridge din,
tare da yar guntuwar nasiha akan sai tayi hakkuri da jama,a don mai saye da sayarwa
sai hakkuri dama.
Sai dai kassh matsalan hauwa shine bata da hakkuri don ta sawa ranta masifan son
kudi sosai.
Ta manta cewa zafin nema baya kawo samu sai in Allah yaso bawan shi da arziki
yake arziki.
Ba dama mutum yazo sayen kankara ya mayar mata koda yace bai kankareba sai ta
hau masifa da fada taki canzawa mutum abinda yake so.
Gashi duk samun da takeyi yanzu baisa mijin nata yakai idon shi ba ga kudin ta,
don ko ba dadi sai yakawo masu dan abinda zasu dafa agidan suci.
Yana da matukar kokari gurin ganin ya kare hakkin iyalin shi sosai a rayuwan shi.
Amma daidai da rana daya idan dan wani abu ya kasa ga cefanen shi sai Hauwa tai
mirsisi taki yi masu girki wai sai ya ciko ta girka masu.
Don ita bazata yarda da akidar cikawa namiji kudun cefane ba saboda itama tana da
nata bukatan ai da kudin ta don yanzu ta sa rai wai fili take son saye ta yarda
kaddaran itama.
Baida fushi hakan bai damun shi, dole sai ya samo ya cika mata sai ta girka masu
inba haka ba su kwana da yunwa har yaranta.
Wanan kuma ba komai bane sai zugin uwarta da kullun take mata hudubar shedan
akanta.
Na karta yarda da namiji don tana ganin ta ita kadai bai hana wata rana sai
tagama kashe maijiki ya ce zai jajibo mata kishiya.
Halin Rashi hakuri irin na hauwa yasa mutane suka dan rage shigowa sayen kayanta
yanzu sosai sun kwammace suje wani guri su saye.
Haka yasa ake barinta da kimin kankara a fridge har su narke tayi hasaran kudin
ta.
****** ******* ******
Cikin mota suke a kofan gidan su Raiha yana yadda ranshi yaso da ita, a cikin
rashin damuwa Raiha ta barshi yana juyata yadda yake so.
Don son shi da kalaman shi ko yaushe suna kara tasiri ne a zuciyar ta don ta
yarda dashi 100%.
Daga nesa matasan dake zaune suna hira hankalin su yana gare su tun shigar Raiha
motar, daya daga cikin matasan yake cewa kai yanzu dai mutane basu da tsoron Allah
wallahi.
Kadiba fa yarinyar can ina lura da ita tun dazun suke zaune a motar nan har takai
motar tana motsi don kanta.
Ashe bani daya nake lura da hakan ba inji dayan matashin yaba dayan amsa.
Sai dayan da sai yanzu yai magana yake cewa ai wanan yarinyar batayi ba wallahi.
Gaba daya haliyar ta baida kyau bata dauki kanta diyan tallakawa ba ko kadan
takai kanta inda Allah baikaita ba ko.
Ni yanzu Raiha tafita raina tunda abokina yake fada min cewa yagan ta uguwar su
gurin sayen kayan maye.
Kaifa Nasir ?
Yace wallahi ranan daya ganta a uguwar nan yake ce min a uguwar nan take ne nace
mashi eh.
Shine yake cewa babba yar hannu ce sosai tana zuwa uguwar su gurin wani deler ta
sayo kayan aiki masu karfi a can.
Sai wanda yafara magana yake cewa kai amma ko udan gaskiya ne wallahi dole mu
saka mata ido don kada ta kawo muna matsala ga sauran yan matan shiyan nan.
Yanzu kai ya kake ganin zamuyi yace kokari zamuyi mu kamata a hannu sai mu dauki
mataki daga iyayyen ta mana ko yaya kuka gani.
Hakane sauran suka bashi amsa da,sauri suna cewa wallahi in har ba,a,dauki
mataki ba zata iya gurbata wasu ba,a sani ba.
To yanzu ita ina ta koyo wanan bakar akidar naga dai a uguwar nan ta tashi a
gaban mu ai.
Kai yanzu sai wani ya koya wa mutum hakane abin fa masifa ne kawai sa warai ne
ai.
Ni wallahi mamaki take bani yadda idon ta ya bude baki daya a lokaci guda haka.
Kaidai bari ai yanzu haka kila a makaranta ko kuma wasu sabbin kawaye ne suka
koya mata wanan harkan.
Tana shiga gidan mu gurin kanne na zan shiga nai masu fada wallahi su rabu da ita
tun bata lalata min kanne ba.
Kaidai kawai Allah ya,sauwaka ita kuma Allah ya shirye ta don kaga ai mahaifinta
mutumin kirki ne.
Uwarta kuma bata ko magana shiru shiru mutumiyar kirki ce sosai don bakajin ance
ga abinda tayi a uguwar nan na assha.
Sai wani lokaci Raiha ta bude kofar mitar ta sako kafan ta guda daga waje, daga
inda matasan suke zaune suna iya hango ta daga cikin motar tana gyara rigar ta da
kuma saka hijjab din ta.
Allah ya kyauta amma dole mu dauki mataki akan wanan fitsaran da ake muna da rana
tsaka a uguwa.
****** ********* ******
Abin duniya ya ishi zuciyar Umar faruq ya rasa yadda zai shawo kan Maji ta yarda
ta mara mai baya akan zancen tafiyan shi zuwa ghana kwallo kamar yadda yan club din
su suke son yaje ya buga masu ball.
Haka yasa yafara dirkawa cikinshi kwaya kala kala har takai