Author : Zainab Idris Makawa Seenabu Category : Complete Novels
Kada ki fada min magana Kubura don ke ba kunya ne dake ba yaya zan kyale shi yana
sashi magana bayan likita yaba da doka.
Hannu Alhaji ya daga masu yace don Allah ya isa hakana please,
Idan shi zakuyi min ku koma gida gaba dayan ku,
Sadauki dai yana duke ya kurawa mahaifin nashi ido dake cikin wani hali gwanin
ban tausayi.
Can ya mike ya juya gurin hajiya Kubura yana fadin wani likitane mai duba shi
mummy ?
Tace tau kasan likitocin yawa gare su amma dai doctor Ango shine yake shigowa
akai, akai gurin shi.
Man let's go yace wa Bashar dake tsaye daga can kofan shigowa dakin.
Ajima kadan sai gashi da likitan sun shigo dakin tare nan likita ya bukaci kowa ya
fita daga dakin a lokacin.
Umma kaman zatai magana sai tai shiru tamike ranta a bace suka bar dakin yaran ta
suka bi bayan ta.
Har an rufe kofan sai gashi an leko akace hjy kubura ta shigo.
Wanan abin yai matukar harzuka ran Umma sosai take ganin shi sadauki da hjy
kubura sun fitane ga Alhajin da za,ace ita ta fita daga dakin.
Mikewa tayi ta nufi kofan ta tura da sauri likitan dake duke kan Alhaji ya dago
kan shi hjy kubura tana kokari kamashi a daura mai abin gwaji.
Likita yace haba mama munce ku dan tsaya a waje har mu gama abinda zamuyi mashi
ko.
Wani haushi ya kumay ta ta buga kofan ta wucd fuuu tana cewa yaranta su zo su
tafi tunda basu da amfani a gurin.
Dan ta Sagir yace haba Umma yaya zamu wuce don kawai ana mashi gwaji ance mu
fito.
Sagir kai dama nasan baka da zuciya wallahi, baka san ciwon kanka ba ko kadan a
gidan nan.
Sagir yace ni dai ba zan tafi ba gaskiya tace zauna wanan mashayin ya gwada maku
iko anan.
Mama ma mikewa tayi tabi bayan Umma suka bar asibitin cikin fushi suna sake bakar
magana kai kishi ho.
Likita yace mai nan da kwana biyu idan ya kara jin sauki zasu iya fita dashi
din don dai yanzu yana jin jiki tukun na.
Sai dare sosai Sadauki ya bar asibitin don yazo gida yacewa Sagir da Mustapha
zai je ya gaida maji ya dawo idan basuyi barci ba.
Ya samu har mun rufe kofa don mama bata zuwa asibitin da dare don habaici da gori
ne idan taje suna nan.
Wanka yayi yajuya sai asibitin a can ya kwana gurin mahaifin shi a zaune tare da
kannen shi biyu.
Cikin dare Alhaji ya falka ya gan shi zaune saman kujera a gaban shi yana barci
yake cewa a ranshi Allah sarki .
Ya Allah ka kara shirya min wanan bawa naka Allah ka shirya min duk zuria ta baki
daya.
Jin kaman motsin Alhaji yasa shi saurin bude idon shi ya mike yana cewa Baba yaya
ne may ke damun ka ne?
Uban yai dan guntun murmushi yace Umar Faruk Allah yai maka albarka Allah ya kara
shirya min kai.
Jinkin sadauki yai sanyi zuciyan shi ta fara bugawa don hankalin shi yai matukar
tashi sosai a lokacin.
Nishi ya fara guda guda alaman yana jin jiki shi sosai a lokacin da sauri sadauki
ya ke kiran Sagir yana cewa.
Yi sauri kira min nurse a waje sagir ya mike da sauri ya fita shiko yana tsaye
sai sannu yake wa mahaifin cikin damuwa.
Nurse yashigo da sauri yana cewa bari akwai Alluran da dama za,ai mashi yanzu zai
samu sauki insha Allahu.
Bayan anyi alluran da yan mintoci ne, sai ya samu barci sukan yaran basu barci ba
suna tsaye a kan uban nasu har safe.
Jin kiran sallah yace su sagir su fara zuwa suyi sallah in sun dawo sai shi ya
tafi.
Sagir yace yaya ku tafi kawai idan kun dawo ni sai na tafi haka sukayi suna
dawowa sagir ya fita yai sallah.
Can Alhajin ya bude idon shi lokacin gari ya dan fara haske yace ba,ai sallah
bane sukace mashi anyi Baba.
Yace ku taimaka min kuyi min alwala sai nayi sallah da taimakon diyan nashi su
kai mai alwala yai sallah daga kwance inda yake.
Sai kuma ya koma barci suna gurin zazzaune ba wanda ya gusa daga cikin su har
lokacin.
A gida kuma tun da asuba muka tashi muka hada abin breakfast don mune da girkin
gidan.
Ni da anty maryam ne muka dauka zuwa asibiti don mukai wa wan yan da suka kwana
dashi abin karyawa.
Muna shiga dakin da,sallama yana tsaye yaba da baya jin sallaman mu yasa shi
juyowa.
Sai da gabana ya fadi danaga yadda ya sake min muka karasa muna masu ina kwana ya
amsa da kyat cikin yanayin damuwa.
Yaya yaushe ka dawo yace mata jiya da dare daga inda nake tsaye ina kallon yadda
Baba yake a kwance na dan dago kai nace mai,
Sannu da dawowa yaya sai lokacin ya dago kai ya dan kalle ni da sauri ya kawar da
kanshi tare da cewa yauwa.
Yace ya maji suna lafiya jiya na shiga na samu kun rufe kofa ai.
Maryam tace yaya shine baka buga ba mun kai sha biyu bamuyi barci ba ni da Bintu
ai.
Bai bata amsa ba yake cewa sagir su tashi su karya ga abin karyawa nan.
Sagir yace kaifa yaya naga alaman baka ci komai ba tunda kazo fa?
Yace No don't mind zan tafi gida yanzu na dawo sai karya a can idan na dawo sai
ku tafi kuma kuyi wanka ku dan huta.
Bashar ya kira yace yazo ya kaishi gida yanzu, ba a dauki lokaci ba nacewa
maryam mu tafi,
Tace zamu koma idan Baba ya tashi muna gaidashi don Allah.
Batare da ya juyo ba yake cewa, No ku tsaya Bashar yazo mu tafi tare ko kunzo da
mota ne ?
Dariya tayi tace kai haba yaya wani mota kuma ina muka gan shi sai dai mu tare
Napeo mu hau.
Dan dariya ciki ciki yai mata ba,adauki lokaci ba saiga bashar cikin jallabiya ya
shigo suka gaisa yana tambayan jikin mahaifin nasu yace Not bad gaskiya.
Mukai masu sallama muka fara fita daga dakin kafin su fito mu tafi.
Muna fita maryam tace tau dada ga dodon maza ya dawo yanzu za,a fara ke nan ko ?
Nace ni gida zan tafi sai ya tafi na dawo ban iya zama mugun nan yana gari
wallahi.
Ganin sun fito yasa nai shiru ba don na tashi ba yana cewa mutafin ku ko?
Nan muka bisu a baya suna gaba muna biye dasu magana suke akan jikin baba.
Baya muke Bashar na jan motar shi kuma yana gaba yana waya yadda naji wayan da
abokin shi yake wayan.
Har muka kai uguwar mu waya yake cikin wani yanayi nikan mota na tsayawa na bude
na fita abina ban tsaya ba.
Na shiga na samu mama tana zaune suna magana da Amira tana cewa ko sai yaushe zai
shigo garin yazo yaga mahaifin nashi .
Na zauna sunacewa mun dawo nace eh tare suke tambaya yaya jikin Baba nace da
sauki mun samu yana barci ne.
Tace Alhamdullahi ai barci alaman sauki ne ga mai jinya.
Maryam tashigo da ledan da ya bata a hannu n ta daganin ledojin na kasar waje ne
shi ya mayar da hankalin su mama a kan ta lokacin.
Tace Maji kina da bako fa ashe yaya ya dawo tun jiya wai yazo ya samu mun rufe
kofan mu.
Sai gashi ya shigo nan suka fara murna suna mashi sannu da zuwa, suka gaisa da
shi.
Nan suka zauna ana magana akan rashin lafiya Baba da halin da yake ciki.
Maji tace akwai abinda ke damun shi don tun ranan da ya dawo daga kasuwa rai a
bace washe gari yace ba zai iya fita ba shine har abin ya kai shi kwance haka.
Amirah tace wallahi yaya na zaci ko Baba ba zai tashi ba yadda aka kai shi
asibiti rai a hannun Allah wallahi.
Sadauki yace to may Baba yake tunane haka har ya ja mashi wanan matsala kai
tsaye.
Maji tace tau ana raba dan adam da damuwane ko al,amarin iyalin shi ai ya ishe shi
abinne dai bai faduwa kawai.
Maryam tace ni dai nasan akwai wani abu mama don ranan mun fita da Bintu zamu
tafi makaranta naga yan sanda da yan hisbah a kofan gidan nan.
Suna magana dashi kuma wallahi baba sai rantsuwa yakeyi bai zuwa ko ina shi.
Akwai dai gaskiya amma ko may ye ai muji idan yai wari.
Ka karya ne uwar take tambayan shi yace No sai nai wanka zan karya na koma
asibitin na duba Baba.
Bai jima ba ya fita daga falon yabar mu nan a zaune can yafito cikin shirin shi
yana fadin.
Abashi abin karyawan shi inda nake mama ta dan juyo tana fadin Fatima ba yayan
ku, abin karyawa kinji.
Har na fara tafiya na juya inda yake ina cewa na hado ma da indomei ne ?
Yace see you may zanyi da indomie ni kaman wani karamin yaro can?
Kayan tea nafara kawo mashi na juya na dauko mashi kwai da irish su yaci bai sha
tea din ba sai ga kira yazo likita ya shigo.
A hanya ya hadu su Umma suna jiran napep su tafi asibitin nan ya tsaya ya dauke
su a tare suka tafi dashi sai wani shan kamshi Umma take a bayan mota.
Sun zasu Alhaji a zaune likita yana dubashi suka gaidashi tare suka fita da
likitan yana fada mashi yadda suka kwana jiya dashi.
Maganin da aka rubuta da irin abincin da za,a bashi ya tafi ya sayo a nan ya samu
da hajiya kubura da maji sun dawo suna sauka da Napep mamaki ya faea wai ina motan
Baban sune ?
Zai iya cewa tun wancan karon ya fara ganin kaman arzikin mahaifin su ya fara ja
baya sosai.
An bashi maganin da abinci yacu sosai ya kwanta barci don maganin da yasha.
Sadauki ganin su gaba daya yasa shi cewa dama ina son nai magana da ku don ina
son nasan da,wa za,a tafi da Baba India ?
Umma tai farat tace kaman yaya dawa za,a tafi dani mana za,a ?
Hjy Kubura tace wanan ma ba magana bane wanan zance ne na jinya babu son kai a
cikin shi.
Mama Asiya tace to may kike nufi ke zaki tafi ke nan ko kuwa?
Dama aikin sani,
Wallahi baki isa ba don baki kai muna can ba ni din dai da baki son a tafi dani da
ni za,a tafi.
Fitayayi ya bar su dakin cikin dan hatsaniyan su da suka saba har suka falkan da
Alhaji daga barcin da yake yi.
Nan yake jin abindaya hadasu fadan yace dama kun bari don ni bazan tafi India ba
dan dama dama da saudiya ne ?
Sadauki ya shigo da abokan shi suka gaida Baba nan yake cewa kace za,a kaini
India ?.
Yace eh Baba,
Yace to ba zan yafi ba inda dai saudiya ne zan iya zuwa ko don na sauke farali a
can nai Umurah.
Yace tau Baba idan can kake son a tafi sai a tafi din ai yace dawa za,a tafi don
mu shirya passport din tafiyan.
Gaddama ya kara kaure tsakanin matan sai cacan baki sukeyi a tsakanin su.
Maji na zaune tun fara magana bace uffan ba a zance duk kuyi min shiru ban zuwa da
kowan ku, da Hawau zan tafi.
Tsit sukayi don jin furucin shi, yace tun da abin naku rashin hankali ne baku
damu da halin da nake ciki ba.
Dama haka zakace don ka gyara mata rai tunda dantane ya biya.
Sai dai dadin abin kowa ma dai ya hafa a gidan balle yanzu don ana ganin kaman
danta ya kawo karfi, za ai muna cin fuska.
Umma na fadin haka tamike tana daukan jakkan hannun ta zata fice daga dakin.
Sadauki yace ba matsala sai aiwa kowan ku passport a tafi ai umuran can sai a
dubi lafiyan ka.
Hjy Kubura tace Allah yai maka albarka sadauki wanan dawai niyan haka tace tau
sai a mayar da yuka a kube, don dan albarka ya yanke hukunci.
Wani kallon banza ta watso ma hjy kubura tace yanzu ke ake ji mara kunyan yarinya
kawai ni ba sa,an yinki bane,
Yaushe kuma muka zama daya tunda bori guda mukewa tsafi ni dake yanzu.
Maji dai mikewa tayi tana fadin ni zan koma Allah ya sauwa Alhaji hjy kubura tace
tsaya mu tafi tare anjima nadawo.
A waje suka samu sadauki shi ya dauke su zuwa gida, a hanya yace mummy bani son
wanan yawan fitinan da kukeyi da Umma ko don hallin da baba yake ciki yanzu.
Kai Sadauki wallahi yaya ta faye abin haushine ita kullun sai ta mulki mutane
tamayar damu da diyan mu abin banza.
Nikuma bazan yarda tayi zaune shirim tana zuba muna iko da mulki ba kaman ita ta
aje mutane.
Hajiya maijidda suka samu suke mata abinda suka ga dama a gidan gaskiya ni ban
daukan hakan.
Indai sheri ne ai ta matsa yanzu tunda kazo kaga Nafisa asibitin nan da sauri
maji ma tace yaya akayi.
Tace may nene ba,agiba yan hisba suna neman su sun hada party na iskanci a gari,
akai ta shedana da iya shege.
An kama yan uwanta su su gudu su masu party amma ce uwa tayi wai zata Abuja ne
gurin Atika kaunan ta.
To ko shine ya jawo wa Alhaji wanan abin hjy Kubura tace shine ma da dan banzan
ga na wurin Asiya Ahmad dayaje ya dauko rikici.
Dole Alhaji ya sayar da kayan shi har motar shi ya biya milayan biyar da wani
abu.
Sun dauka ba,a sani bane kawai don mutum baison ya fadi a ce ga bakin shi akaji.
Amma ni Nasir dina yake fada min tun dashi ya boye muna bai son a sani amma ai
sune suka jawo mashi hawan jinin ba wani ba.
Daga gaban mota sadauki yace to amma may yasa Baba bai fada min ba duk wanan
zancen.
Tace ina zai fadi kasan shi da zurfin ciki ai in sun kashe shi ai an huta ko ?
Har suka isa gida ba wanda yai magana a cikin su sai dai kowa da abinda zuciyan
shi ke saka mai.
Waahegari bai zauna ba sai shirin tafiya yakeyi na iyayyen shi, Imirana yace
aikin banza ne wanan shi yaushe yake da kudin da zai fitar da Baba waje har da
matan shi.
Sai ranan tafiya, ne suka tabbatar inda suka shirya sai kasa mai tsarki, ba tare
sukai tafiyan dashi ba zai samay su daga baya amma komai da za,ayi a can ya hada su
da abokin wasan shi dan kwallo dan kasan sadiya da yaya sagir suka tafi.
Tafiyan su da kwana biyu duk gidan babu dadi haka dai muke zaune amma sauran
yaran sai harkokin su sukeyi.
Na dawo daga sayo muna kayan miya zan shigo gida ban san da mutum tafe ba sai cin
kara nayi dashi.
Ina daga kai ya wani daga min gir irin na yan iska, har na zauda shi zan shige ya
rike min hannu yana fadin.
Yau shigeya kobaki so sai na kwashi gara gare ki, gidan nan sai da in munafukan
uwar ki ta dawo tayi abinda zatayi.
Dama na dade ina son in more wanan lafiyen jikin naki kafin wacan gara da zaki
aura ya more.
Sai naji ya jawoni gaba daya yana kokarin daukana zuwa dakin shi nasa hakora na
iya karfina na cije mai kunnen shi da sauri ya sake ni ya makure yakai min mari
gashi ba wanda yafito daga cikin gida balle ya taimake ni.
Na samu wuyan hannun shi na kara kaimai cizo iya karfina yaji zafi ya dinga kai
min nashi a bakina.
Naji zafi na sake sai nishi yake ban san lokacin da yanka wani irin ihu ba da
karfi.
Yakara cakumoni na samu sa,a na murde mai gaban shi iya karfi na ya yanka wani
irin ihu daidai lokacin, sadauki dake jin kamar ana danbe a waje daga dakin shi ya
leko,
Zan gudu yakara finciko ni nakara kai mai wani cizo tare da kamawa da karfin
Allah.
Daidai nan naji an kai mashi nashi a bakin shi sai da ya fadi ta baya zaune
dirsha.
Yace dabba kawai sauna mara hankali da,wayo kai dabban wani gari ne karasa wanda
zakaiwa haka sai Fatima da take zaman kaunan ka.
Tir da halinka halin dan akuya kawai kayi girman banza wallahi, ji ka raggo kawai
ji yadda ta mayar dakai jina jina amma baka ji kunya ba kace sai ka danne ta da
karfi.
Ya furzo miyan daga bakin shi duk jini ne kila ma hakkoran shi sun zube ne.
Ya juya inda nake tsaye ina kuka yace dauki kayan ki ki shiga gida ke kuma.
Na duka na dauki ledan da na sayo kayan miya duk sun watse a kasa da takalmana da
suke warwatse a gurin nai cikin gida da kuka na barsu nan suna fadawa juna magana.
Yana ce wallahi ba dan kwallo kake ba sai naga bayanka a garin nan yace
Bisimillah shege ka fasa in baka ga nawa ba ni zanga naka ai.
Sai lokacin naga yan gidan duk sun fito waje ashe suna tsaye cirko cirko cikin
tashin han kali.
Ina shiga gida na zube kasa gaban Anty Amirah ina wani irin kuka mai tsuma rai da
ban tausayi.
Tana kukatake tambayana bai maki komai ba dai ko na girgiza kai cikin kuka nake
fada mata ,a,a yaya sadauki ya ceceni gurin shi.
Maryam tafita ta dinga kantara mashi zagi da,ashar kamar ranta zai fita sai da
sadauki yazo yace ta shiga gida hakanan.
Wayan shi ya fitar ya kira Bashar yazo ya samay shi a cikin damuwa ya yasamu
abokin nashi.
Yana fito ya