Advertisements
Chapter 82 Reading A Lokacin Mu Ke by Zainab Idris Makawa Seenabu BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

A Lokacin Mu Ke by Zainab Idris Makawa Seenabu

Author :  Zainab Idris Makawa Seenabu Category :  Complete Novels

Chapter   82 / 92

243K to 246K   out of 275.8K words

Nace kai haba mama yaya baba zai rage maki sakon ki kuma tace ai bashi ba wanan
munafukar matar tashi dai itace zata rage su.
Cikin natsuwa nace mama tabawa zata iyashi mama don bs imani ne da ita ba
wallahi.
Haka muka kwana muna hira harda Iyya da,ta kwanta waje da,farko har barci ya
dauke ta nasan tai hakane tabamu guri mu zanta ni da mamana.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU

IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,,,


IDAN KIN BIYA KIKA TURAWA WANDA BAI BIYA BA MUN BARKI GA ALLAH YABI MUNA HAKKIN MU
AKAN KI,


Yana isa zuwa yamma ya bar garin ya wuce zuwa lagos inda zai tafi ghana daga can
gurin business din shi.
Yana can ya bugo min washegari lokacin na tashi nai wanka ina shiryawa wayan shi
yashigo na dauka tare da gaidashi yake tambayana jikin yayi sauki ko nace na samu
lafiya sosai.
Dama ai idan na shiga mota ne kawai nai tafiya mai nisa nake jin haka.
Mundayi hira yana tambayana mutanen gida nace duk suna lafiya yace nagaida su nai
mai Allah ya tsare yaba da sa,an tafiya muka kashe waya.
Sai dana shirya ne mama tashigo dakin tana ce min karyawa fa nace mata da,dai
akwai dumamay tuwo ne shi nake son ci.
Tuwon aka dumamon an saka mai man shanu shi na danci kadan still ina jin tashin
zuciya har lokacin.
Nan mama take tambayana yaya za,ayi da kayan da mukazo dashi nace a fitar wa Baba
na da nasu sai su raba sauran amma sabulu da clean abawa makwabtan su.
Yadda nace haka mamana tai rabo na adalci don har na Baba na yafi yawa sai da
nazo nagani nace a,a daidai za,a raba ita dashi.
Mutanen da aka kai ma tsaraba sukai tashigo yi muna sannu da zuwa naji dadin
yadda mutane sukai ta nuna min karamci haka.
Ice dake gidan mama a karkashin shi muka mayar gurin zaman mu ni da iya sai dare
muke shiga daki don rana haka na wuni kwance rijib ba lafiya.
Iya ta matsa wai na fadawa maigida banda lafiya asan abin yi nace mata haka
nakeyi dama idan nai tafiya.
Sai mama ne da iya dake taya ta aiki suke ta faman kai kawo a tsakar gida kawuna
yazo amsa kiran mamana da ta aika tana neman shi.
Nan suka kebe tai mashi bayanin komai kuma ta kawo kudin aikin ta damka mashi don
shi a garin yake zaune dama gurin shi tazo har mijinta ya ganta ya aureta.
Sun gana da maigidan mama da kawu yace aiba matsala wanan taimako ne ai akai
mashi da yamma kuwa sai ga masu aiki sun shigo gidan suka fara awon yadda za,a
fitar da plan din ginan.
Dakuna guda biyu na mama ciki da falo dayan kuma single ne sai wasu biyu a gefe
daya su ma sai na samari washe gari yan aiki suka fara aiki akan idona akafara
komai ga katan aiki kawu har ya sawo an fara aiyuka ko.
Da dare daga ni sai mama na a daki Iyya na waje kwance wai zafi take ji.
Nace mama dama ina son mu samu lokaci in fada maki wani magani da aka anso muna
naba yaya yasha wanda ina gani shine sanadin barin shan abin maye da yakeyi.
Nan dai nai mata bayani da kuma garin don ba nisa tace tagane mutumin ai dan uwan
mahaifina ne tace insha Allahu zatayi kokari taje gurin shi.
Muna cikin hirane yaya sadauki ya kirani muka gaisa yana jin murya na yace Fatima
na amsa may ke damun ki nace may kagani ne yace you sound like baki da lafiya na
kakaro murmushi nace daga barci na tashi yanzu barci na somayi kata dani.
Ina ganin bai yarda ba sai naji yace humm kawai yace ina mama nace gata tare dani
barin bata ku gaisa dama tana son maka godiya.
Yace No No godiyan may kuma don nayi wa mamana alheri haba kada ma ki bata idan
hakane kice ina gaida ita nace to ya kashe wayan.
Koda ya kashe wayan hankalin shi bai kwanta ba yadda yaji muryana sai hankalin
shi yai matukar tashi.
Amma kuma baida yadda zaiyi tunda nace mai lafiya nake da ance sokoto nake da ya
zo gobe gobe taga yanayin da nake ciki.
Dole jiki ya matsa min ban samu tafiya ba ranan da muka ce zamu tafi sai da dare
ya samu time ya bugo min waya yana tambayana mun sauka lafiya da kyat nake magana
don da zazzabi na wuni.
Yake tambayana ko mun sauka lafiya yaya baba nace cikin karfin hali ban samu
wucewa ba yau yaya.
Ya rage fara,anshi yana tambayan saboda may nai mai shiru yace baki da lafiya ko
Fatima ?
Shine kika shige kauye kika zauna da ciwo yana cin ki ajiki haka.
Watau ke kin samu su mama kin manta da lafiyan ki ko ?
Na rasa abinda zance sai da ya kara tambayana may ke damun ki ne ma wai ?
Na rasa abinda zance mai sai can nace zazzabine amma naji sauki shine mama tace
na bari sai gobe mu tafi idan na kara jin sauki.
Yace a zaune zaki ji sauki bakiga likita ba ko may nace nasha magani ai na samu
sauki yace ina Iyya take ne wai nace tafita.
Yace gobe goben nan ki koma sokoto zan ma bashar magana yazo ya kaiki asibiti
idan kun isa kafin na iso.
Gabana yai matukar faduwa gashi banje gurin babana ba kuma yasan munzo.
Na marairaice nace don Allah yaya kayi hakkuri naje gurin baba nai kwana daya
jibi sai na karasa gida.
Bai jira may zance ba ya katse layin bayan dan tsokin da yaja.
Mama dake zaune gefe na takale ni a tsorace tace so yake ki koma gida baki isa
can ba ?
Na bata fuska tare da jan tsuki nace wai haka yake nufi ni kuma ba zan koma ba
banje gurin baba tunda ba bari yake nazo ba.
Tace a,a yar baba kirashi ki roke shi idan ya yarda sai ki karasa gurin su idan
kuma yace lalai sai ki koma gobe din sai ku shirya ku koma din.
Na dai daga wayan badon naso ba ga mama ta tsareni da ido na kirashi na zaci ba
zai daga wayan ba dana kira.
Amma sai naga ya dauka yace yaya akayi kuma ?
A hankali na ce mai kayi hakkuri yaya don Allah naje gurin baba gobe nai kwana
daya sai na dawo kada yace ko gudun shi na soma yi na rike uwata.
Yace as you wish ai jikin ki ne nace kadai yi hakkuri please gobe da safe zamu
karasa can mu kwana da safe sai mu taso.
Yace na fada maki da kun kwana daya ki dawo gida kije asibiti aduba lafiyan ki
nace insha Allahu jibi da safe zamu taso da yarda ubangiji.
Yace is ok Allah ya sauwaka nace nagode muka kashe wayan mama tace ai kinga haka
yafi da ran shi ya baci yakawo ki cikin dadin rai kuma akoma ana haka baiyi ba
gaskiya.
Nai mamaki irin tsaraban da mama ta hada muna mu tafi dashi wai kaji, man shanu
fura da nono kwakwamayti kuka daddawa da kuli kuli da kwanzabbi mai yawa.
Mijin mama ma yabani mamaki rago yasa akayanka aka,soya shi sai da ya cika bucket
din penti yace nashi tsaraban ke na da mazzakwaila mai yawa.
Tun da safe mukai masu sallama na wuto da kauna ta Sa,ade muka bar Asma,u tana
kuka nai mata alkawari itama zan dawo in dauke ta ai tai makaranta haka yasa tai
shiru.
Sai kauyen mu nan na samu baba bai gida da farko kamar mama tabawa bazata karbe
mu ba amma tana ganin an fara jido kaya ana shigowa dashi tafara washe bakin ta
tana cewa sai yau Hjy maryam tun fa shekaran jiya akace muna kina Rabah.
Nai dariya nace wallahi mama munje daniyar nai kwana biyu nazo nan nakarasa kwana
uku sai ga ciwo ya rike ni acan.
Tace assha subahanallahi inji da sauki dai ko nace naji sauki mama.
Nan muka basu tsaranan su na aika,wa kakanina da nasu sukai ta godiya.
Da baba yadawo shima na bashi nashi sakon yai ta saka albarka kwanan mu daya
tunda safe muka kama hanya sai sokoto.
Rijibb na iso garin na kwanta bamu jima dashigowa ba wayan yaya ya shigo yana
cewa yaya kun taso ko nace gani dakina kwance yace ki shirya bashar yazo yanzu kuje
asibiti.
Ba adade ba bashar yazo muka wuce asibiti ganin likita duk a lokacin na jigaye na
wahala sosai.

****** ********* ******
A gurin da zanga likita ma sai dana dan kwanta kafin shiga ya kawo kaina banda
kuzari sai yawan jin kasala dake damuna ko ruwa nasha sai na fitar dashi san nan
naji shakat a raina.
Nan yakira wayana nace gamu asibiti muna jiran layi yazo kan mu ne.
Yace wai may ke damun ki ne Fatima haka ?
Na lumshe idanuwa na nace ban sanni ba yaya komai naci dai sai na amaye shi kuma
banjin kuzari a jikina ina dai ganin maleria ne yai min yawa a jikina.
Yace bari a shiga gurin likita muji may ke damun ki haka kilama ruwan kauyen ku
ne bai karbe ki ba kike wanan wahala haka ?
Mun shiga gurin likita yai min yan tambayoyi irin nasu ina bashi amsa can dai
yajefo min tambaya yaushe rabona da period ne ?
Gabana ya fadi sai lokacin na tuna zancen wani period can nace gaskiya ina ganin
kamar yakai kusan three month yanzu sai dai koda nake gida ai nakan yi irin haka
din.
Test akai min cikine dani har wata uku da kwana takwas nan dai suka rubuta min
magani tare da,son na samu hutu don nayi weak da yawa.
Kunyane ya rufe ni da akewa yaya bashar din bayani tun nan yaya bashar yake min
congrats.
Muna fitowa wayan sadauki na shigo mashi yace wai may ake cikine kunga likitan.
Yace eh mungan shi gashi mun fito zan da tsaya na sai mata magani ne mu koma
gida.
Yace may sukace yake damun ta yace may ko zasuce banda cutar daka zubawa yar
mutane mugu kawai.
Gaban sadauki ya fadi shidai yasan baida wani cuta a tare dashi asalima shiba
mane min mata bane balle.
Yace for god sake may ya samu fatima din Bashar wani cuta ke gare ni da zan
zubawa Fatima shi ?
Yace kaiko keda cuta gatan kana kayan shi cikin wando kullun kana durawa yar
mutane wahala.
Nan yake ta tsokanar shi har yagane ciki yake nufi ke gare ni yace don Allah da
gaske kake yi ko shirmay ka bashar ?
Lokacin yake shigowa mota yake ce min karbi wayan maryam ki fada mai da kanki
tunda ni ya mayar dani makaryaci yanzu.
Kuma ka shirya tukwaici na wallahi don wanan ba karamin albishir bane nai maka.
Yamiko min wayan yace ga fitinanen mijinki kiyi mashi bayani da kanki ko zai
yarda murmushi kawai nayi mashi.
Na dauki wayan cikin sanyin murya nake cewa hello yaya.
Bai amsa ba sai cewa yayi wai wanan munafikin maganar gaskita yake fada min ko
wasa yakeyi nace uhumm kawai tare da murmushi na mikawa yaya bashar wayan shi.
Nan sukaci gaba do zolayan kan su har muka isa gida yaiwa iya bayani kan ance ana
son in samu hutu sosai don haka kada ta bari inyi aikin komai please.
Barci ne ya dauke ni mai nauyi ban falka ba sai misalin karfe takwas na dare
koshi amai din ne ya tayar dani a lokacin.
Sai dana natsu na jawo wayana kirane ciki barkatai na mutane nashi yafi yawa
amma.
Ban kirashi ba don yanzu ko hayani kwarai ban so sosai na shiga whastff nan naga
yayi posting din suraitai barkatai na farin ciki.
Ban dade ba nafita na kwanta sai ga Iyya tashigo dakin take min yaya jiki nace
mata naji sauki sosai.
Tai min tayin abinci nace tea nake so na ruwan liptop kawai ba madara ba sugar
tace ikon Allah shi ta hado min na zuba zuma ciki dan kadan nasha shine har naji
dan dadin bakina nai sallah na kara kwantawa.
Da safe kiran mama ne ya tayar dani daga barcin tace Fatima ashe kin dawo kuma ba
lafiya nai dan muushi nace wallahi mama.
To yaya jikin da sauki yanzu ko nace naji sauki sosai mama tace shima yace insha
Allahu yau zai dawo zuwa yamma don yana abuja babu jirgin safe yau.
Nace Allah yakawo shi lafita tace amin ki kula da kanki kinji Fatima Allah ya
inganta banyi magana ba don kunya.
Falo na fito na samu Iyya da Saade azaune suka gaishe ni tare da min Allah ya
sauwaka.
Can nace Iyya afito da tsaraban nan kiraba abawa mutane nasu tace to nace man
shanu da nama akai wasu mama shi idan kin dibi naki tunda munan akwai nama su zai
masu a.fani suna da yawa can nasa ta diban ma anty maryam nata da Inna mama bashar
kwai nace akaiwa mummy ta soyawa yaran ta.
Yadda nace haka iya tayi kayan miyane kawai tabar muna don muna da bukatan su
sosai.
Iyya ce da kanta takaiwa kowa nashi mama tai matukar jin dadin yadda nayi don
Iyya ta labarta mata komai kwai danace akawo wa yaran mummy da kwakwamayti ya
matukar burgeta har mummy din suka ce suma suna nan shigowa su gaidani.
Nan mama ta debarwa ko wani daki ta aika masu tana fadin ga tsaraban Fatima nan
da ta dawo dashi suka karba suna gyatsire fuska kuma suka shiga ci.

****** ********* ******
Bayan sallah azahar mama da mummy suka shigo tun a kofa mummy take fadin ina
yake tun bai fito ba na kwali kan na yana wahalar min da yarinyana haka ?
Kunya naji sosai na dan dukar da kaina,a kwance suka samay ni saman dogon kujera
na mike da kyat muka gaisa dasu nan mummy take fadin tun da dare sadauki yakirani
yake fada min ai ban san lokacin da nai ihu ba har Alhaji saida yafito.
Mama tace kai in ma ba abin kurciya ba yaya mutum zaiyi ciki har wata uku ba,a
sani ba tun fa tafiyan su ke nan ta dawo da cikin nan amma haukan shi bai bari ya
sani ba.
Taron dai kurciyane hajiya inbashi ba ai ko ita zata gane tana da ciki a jikin ta
ma kawai dai duk kan su kurciya yana cin su ne.
Mummy tace mazajen ki na gaishe ki sunce sunga tsaraba sun gode sunace suna
murna wai yayan su ya samu baby Banan da haukan ta wai nazo da ita ta dauki baby.
Murmushi nayi nace lah mummy shine baku zo min da ita ba tace ban iya kiriniyan
ta barta can suzo idan yayan su yadawo yakai su yawo ai yasaba da kwaram din su
shi.
Mama tace a,a Sa,adatu din ke nan ai ni dani kuka ba ita ta debe min kewan ku
wallahi gata kamar ku daya wallahi nace mama ai munfi kama ko da Asmau sosai idan
kingata kaman mu yayi yawa tana can mun barta tana kuka wai ita ma sai tazo mukai
mata wayo nace zanzo na dauke ta daga baya yanzun ba wuri.
Amma ko Fatima baki kyauta ba kikabar min Asmaun nawa kaunata ce ina ji da ita
duk cikin kanne na wallahi.
Bari ya dawo ai zan sashi ya tura azo min da ita tunda ku baku son zama da ita
nan.
Naji dadin jin haka kuma haka nake so don ina son yaran su fito suyi karatu itama
mama ta dan huta yawan iyali.
Idan kuma ta zauna gurin mama zata sha dadi sosai a gurin ta don mama uwace bata
fada ba.
Basu wani dade ba sukai muna sallama suka tafi akabarni da Iyya da Sa,ade a gida
musa ya fita abin shi.
Sai da dare ya shigo garin ina,falo kwance na dunkule yashigo gidan Sa,ade naji
tana mashi sannu da zuwa don tare muke zaune Iyya tana kitchen.
Yashigo idanuwan shi na akaina har ya karo inda nake kwance ina kokarin mikewa
zaune daga kwancen da nake.
Yace No don Alla kwanta abinki yazo ya zauna bakin kujeran da nake kwance haka
yasa Sa,ade mikewa ta nufi kitchen gurin iya tana fada mata dawowan shi.
Ya dan kai hannu shi a saman wuyana yana tabawa a hankali yaji ba zafi sosai yace
how the you feel now ?
Nace a hankali da sauki ya daga hannuwana ya rike a cikin nashi gama yace I dont
know what to say but nagode Fatima na gode kwarai da wanan babban kyauta da kikai
min.
Na lumshe idanuwa na a hankali tare da kwantar da kaina ga jikin shi nace yaya I
miss you.
Yai dan murmushi ya shafi fuskana yace kina hakan da fa fushi nake dake da kikaje
kika zauna da ciwo a kauye kamar wacce bata san zafin kanta ba.
Amma yanzu kin wanke kanki ko gare ni komai ya,wuce ko yake cewa yanzun may kike
ji kuma ne wai ?
Nace ba komai yaya bandai jin karfin jikina ne kawai sosai kamar farko yace ina
zakiji dadin jikin ki kina haka Allah dai ya rabaku lafiya kawai.
Wanka ya,shiga yafito ya dawo falo inda muke don ni na kasa tashi ma,a lokacin
sabada jiri dana ke ji.
Da dare ma dai haka muka kwana dole washe gari aka sa min ruwa don amai yai min
yawa sosai.
Wani irin ciki ne wanan kuma bai bani wahala ba da farko sai yanzu gashi yana son
kawo min cikas ga karatuna.
Haka nake daurewa na je lectures na dawo gida a,wahalce yau ciwo gobe lafiya.

****** ********* ******
Wasa wasa baba sani ya saka sadauki a gaba da zancen Rahama duk da mama tace
bata yarda ba ita.
Ido da ido sukayi

82 / 92