Advertisements
Chapter 12 Reading A Lokacin Mu Ke by Zainab Idris Makawa Seenabu BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

A Lokacin Mu Ke by Zainab Idris Makawa Seenabu

Author :  Zainab Idris Makawa Seenabu Category :  Complete Novels

Chapter   12 / 92

33K to 36K   out of 275.8K words

shi aduk lokaci da yaso.
Ke kuma Amira na roke ki da kuyi hakkuri da kowa a gidan nan don rayuwan
mahaifiyar mu kin dai san ita ba mai son fitina bace a ranta.
Haka ke maryan wanan zuciyar taki matsayinki na mace ki rage shi don gidan wani
zaki tafi.
Inda Bintu take zaune ya kalla tare da,watsa mata harara yace ke kuma da sauri
Bintu ta dukar da kanta a kasa tare da mannewa jikin kujeran da Maji take zaune a
kai.
Yace kada ki yarda naji ance kinjawa uwar mu bacin rai a kanki a gidan nan zaki
hadu dani.
Sai lokacin Maji da takaici ya isa tai magana tace kai ku tsaya wasu,wasun ku
amma kada ka hada da yar mutane da bataji batagani ba da kowa a gidan nan iyakarta
imu a shiyan nan ba ruwan ta da kowa a gidan nan.
Inda na tsayar da ita anan take bata taba saka kanta ga harkan kowa ba cikin
gidan nan.
Don haka tafita a ido ka kada kasa min "ya a cikin zancen ku wallahi kaji na
fada maka gaskiya.
Mikewa yayi ya ce kun daiji abinda na fada maku kowa ta kiyayyeni akan hakan.
Barin dakin yayi kamar wanda aka tsakara baiko juya ba yafice abinshi har
lokacin yana jin hargowan Umma daga part din su.
Zancen bai kare ba don da maigidan yadawo an samay shi da zancen yana ji yace a
kira mashi su Amira da maryam tun kan hajiya Umma tafita daga gurin shi har Nafisa
din.
Bayan kowar su tashigo tare da uwarta harda mama Asiya da yaranta yan mata, yana
cin abincin shi hankali kwance ga hajiya kubura dake girki daga gefen shi suna zuba
soyayyan su a cikin style.
Alhaji kaifa kace a kiramu kuma kabar mu a zaune kana harkan gaban ka inji mama
Asiya da kishi ya kumay a lokacin na irin yadda yakeyi da mummy.
Mummy tace ke hjy Asiya ko so kike kuma yabar cin abincin ya tsaya shirmen
kishin ku na kullun da baku san angirma ba har yara sun fara irin shi.
Kada ki fara ki fada min maganan banza wallahi yanzu a jimu a gidan nan don ke
baki da kunya kowa so kike yabi ki kamar yadda kika mayar dashi a gurin ki.
Alhaji wanda yagama wanke hannun shi da hjy kubura ke zuba mashi ruwa yace ta
mayar dawa wai ni ko wa ?
Shiru tayi don tasan idan ta tanka yanzu zai iya watse ta a gaban kowa babu ruwan
shi da yara na gurin.
Gurin Amira ya juya yana cewa mamana yanzu Umman ku ke fada min wai kun taru
kunwa Nafisa duka yau a gidan.
Sai kuma ya juya gurin Maji yana fadin ina bakuwar yar ki ita bata zo bane don
nasan ba,a dukan Nafisa bata sa hannun ta ba.
Nafisa tai but tace wallahi danaci uban ta ko murmushi yayi tare da duban Umma
yace kin dai ji tarbiyan ki ko ?
Yace wa yar mama Asiya karama hauwa kira min yarinyar dake dakin maijidda tazo
da sauri yarinyar ta mike zuwa kiran Bintu.
Ta na shiga bako sallama Bintu da ke zaune hankali a tashe ta kurawa tv ido sai
dai hankalin ta ba,a kallon yake ba sai ji tayi ance ke yar kauye baba na kiran ki.
Tare da watsa mata harara tana yatsune fuska tare da bin dakin da kallon
wulakanci ta juya da sauri bintu ta jawo hijjab din ta dake gefe har kasa tasaka.
Tare da bin bayan yarinyar don bata masan falon baban ba duk zaman ta gidan da
tayi ba ruwan ta da sanin komai.
Saida tajawo kofan dakin Maji da zata fito tasaka key tabar dakin da key din a
hannun ta.
Inda taga hauwa ta shiga nan ta shiga itama tare da sallama dauke a bakin ta.
Maji da hjy kubura sai Alhajin ne suka karba mata sallaman ta da tayi tare da
samun guri ta tsugun na ta sunkuyar da kanta kasa tana fadin.
Ina wuni Baba, cikin lada bi tare da sunkuyar da kanta a kasa, yace tare da nuna
ta da hannu kun gani,
Sannan ya karba mata gaisuwan nata yace ku diba ke Asiya da kika samay ni kan
maijjidda ta dauko bakuwar yarinya takawo min gida.
Kinga abinda tabi ta jawo ta a jikin ta tarbiya natsuwa da sanin ya kamata ga yar
kauyen yar makwabtan da kika ce.
Hajiya kubura dake gefd tace kai Allah dai ya sawaka idan kuma anyi magana ace
wai wani ke hassada.
Ke kubura wai may kike so ma dashi ne ki fada min don kin san daidai nake da ke
wallahi.
Ai kaji maganan ke nan yanzu ku dakata da wanan bashi nakiraku yi ba anan ina
son nasan may yakai har ke Amira kuka taru kuka daki Nafisa yau a gidan nan.
Anyi magana kuma uwar ku ta daure maku harda ita ta shiga zancen, ana haka kuma
mahaukacin wanku shima ya shigo ya saya ya zama nashi.
Nafisa ta tare zancen dacewa baba bakin cikine fa kawai don sunga ana zuwa gurina
su ba,a zuwa kiran su kamar sauran yan mata.
Alhaji yace a gidan har ake haka banda labari Nafisat ?
Allah ya kyauta kawai yace tare da girgiza kan shi cikin takaici yana kada
kafan shi irin na magidantan da abu ya daurewa kai.
Yace ke tare da kallon inda Bintu take zaune yace mayye sunan ki ne ma ?
Tace a hankali Bintu Baba, yai yar murmushin manya yace Fatima bintu ke nan ko?
Eh Baba ta bashi amsa yace ki fada min abinda kika sani akan fadan da akayi a
gidan nan yau.
Shiru Bintu tayi na dan lokaci kamar ba zatai magana ba sai kuma can tace.
Baba muna daki bayan anty Amira ta shigo gida nan tafara bashi labarin abinda ta
sani da irin kalamin da kowa ya fadi har marin da Maryam taiwa Nafisat din.
Amma maryam wallahi kin kyauta min inji hjy Kubuta tare da kallon gurin da
maryam take zaune.
Eh zaki fadi haka mana tunda ba yarki akaiwa hakan ba a gidan.
Hjy Umma ce uwargidan su mahaifiyar Nafisa ta ke fadin haka din cikin bacin rai.
Batare da Alhaji ya kalli gurin da take ba yace kubura ban son na kara jin bakin
ki a zancen nan.
Daga haka yai shiru bai kara cewa komai ba kuma again, ya juya gurin Umma yace
to kinji ke maimuna zagin uwarsu tayi har dakin ta kuma tana zaune babu kunya don
kawai an bata mata rai akan saurayin ta da yazo kiranta ba,a fada mata ba.
Alhaji kada ka juya zancen nan fa dukan min ya akayi kuma shi nazo fada maka din
ka dauki mataki a kai.
Yace wani mataki zan dauka idan kece su Amira suka shiga gidan kike sukai maki
haka a gaban ki wani mataki yaran ki dake gurin zasu daukan masu ?.
Shiru Umma tayi yace ba amsa ke nan sunyi daidai dai din ke nan ko ?
Tace yanzu mai kake son nace tunda na fahinci ka daure masu gindi akan abinda
sukayi sunyi daidai.
Yace kin taba gani mai kai takaka yayi nasara gurin maida magana balle harda cin
mutuncin uwa a ciki.
Ai ko ke ne suka kawo wa takaka akai masu hakan iya matakin da,zan iya dauka ke
nan a kan su kinji na fada maki.
Ke kuma Nafisa wani yaro ne yake zuwa gurin ki gidan nan ban sani ba har kike iya
tsayawa kiwa yan uwanki cin muntunci akan shi don ya aiko kiranki ba,a fada maki ba
ranki ya baci kibi yarki har daki kina zagin ta don samun guri.
Shiru Amira tayi tare da dukar da kanta cikin tsawa ya daka mata tsawa yana fadin
badake nake ba nace dan gidan uban waye ke zuwa gurin ki gidan nan har kofan gida
na ?
Sai ga Nafisa tana hawaye don daga ita har uwarta basu zaci abin zai juye masu
haka ba a lokaci guda.
Yace tunda aure kike so ba karatu ba sai ki turo min yaron yazo ai maganan aure
dashi.
Ya juya gurin hajiya Umma yace maimuna yanzun saboda Allah kin san yarinyar nan
tana tara min samari a kofan gida haka shine baki fada min ba saboda Allah da
girmanki ?
Idan da da dan wani dakin ne yake haka dafa a gurin ki zan fara jin wanan
labarin.
Yanzun dai nafahinci ka juye maganan ya zama laifi akan mu, shike nan nida diyana
bamu da shakat kan yan mayen diyanka a gidan nan.
Duk abinda sukayi shine daidai mu bamuyi daidai ba indai duk wa yan nan marasa
mutincin yaran Hauwa ne ka daurewa gidin ai suje suyi tayi.
Ba sabon al,amari bane gasu nan daga dan maye sai yan iska data tara muna a gida.
Ta mike fuuu, ta fita daga dakin inda shima yabi ta da kallon takaici mama Asiya
ma mikewa tayi tana fita tana fadin babu dai adalci yanzu a gidan nan.
A dakin mutun kuma ace wai shine bai da gaskiya don samun guri da daurin gindi
kawai.
Ya juya inda yaran suke ya kara masu fada akan baya son ya kara jin fitina daga
gare su ko ya batawa mai shi rai suka mike suka mike suka bi bayan uwayen su rai a
bace su ma.
Suna ganin ba ai sharian gaskiya ba a gurin don sune da gaskiya amma mahaifin su
ya danne masu gaskiyan.
Bintu ma ganin yaran sun mike yasa ta mikewa tabi bayan su amma sai taji muryan
Baba yana cewa ke Fatima sai ta koma ta tsuguna don taji may zai ce mata din.
Yace ban son naji ance kin saka kanki a harkan cikin gidan nan kamar yadda ban
taba samun labarin banza ba a kanki fon haka ki kiyayye kin ji .
Ta amsa da to Baba nagode ta mike tabar dakin duk tsoro ya cika mata zuciyar ta
ta samu su Amira suna jiran ta takawo masu key din kofan su data rufe masu.
Hauwa kici gaba da hakkuri don ance dan kuka mai jawa uwarshi jifa yau duk
yaran ki bugu daya ake masu akan danki daya daya samu matsala,
Don haka saikin toshe kunnuwan ki don babba da yaro dashi zai zage ku duk wanda
ya tashi a magana gudu zai fake ya harbe ki dashi.
Sai kuma ya jijiga kan shi a cikin takaici da jin zafin sadauki a ran shi yace
Allah ya kauyata.
Sai lokacin hjy kubura tai magana tace rashin dai tunane ne ga mutane ai wanan
matsalar ta shafi kowa a gidan nan don ba nata bane ita kadai.
Amma hakkuri da addua bai bar komai ba Allah ya sauwaka ya kiyayye gaba kawai
za,ace.
Maji ta mike tare da cewa nagode Alhaji ranta babu dadi yabita da kallon tausayi
kawai.
Har takai kofa hjy kubura tace gobe dai ba aiki don Allah ki ara min yarki ta
tayani gyaran daki na.
Ta juyo tana cewa wai Fatima Alla ya kai gobe ai ita yaro ba kiuya ne bata jin
nauyin jikin ta ko kadan.
A daki ta samu su Amira suna dariya Bintu wai ta rufe kofa da zata, fita daga
dakin.
Tace ba dole ba don ni abin wallahi yanzu tsoro yake bani ma mutane haka ba
tsoron Allah.

****** ********* ******
Sadauki yana fita jin shi yake kamar yana taka kaya don bacin rai, duk wanda ya
yanzu ya tashi zagi akan shi akewa uwar shi gori.
Ya madai godewa Allah da jiya bai sha komai da da yai niyar sha yasan da yau
gorin da Maji zata sha akan shi Allah kadai yadan irin sa.
Gashi saida ya zuba kwayan a bakin shi sai yaji kamar ance ya furzo su waje duk
ya zube su a kasa suka narke yana kallon su.
Har ya usa filin kwallo zuciyar shi sai faman sake sake take mai kan abinda
zaiyi wanda zai sa Maji ta danji sanyi akan shi.
Amma ya rasa mafita akan haka, haka ya samu guri ya zauna ranan yana kallon masu
kwallo kawai ya kasa tsinanawa kan shi komai a lokacin.
Sai faman kulawa da warwarewa yake shi kadai a ran shi abin duniya duk ya damay
shi.



ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU

IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,,,,


Tun bayan dawowan Raiha daga tafiya gaba daya bata son fita zuwa ko ina ko yaushe
tana gida sai faman barci takeyi kamar wace tai wani aiki.
Gaba daya ta kashe wayan ta kuma ta hana kowa ganin ta tayi hakane don gujewa
Nasir kawai.
Kusan sati biyu yana sintiri a kofan gidan su gashi tun dawowanta wayanta a
kashe yake mata.
Ranan da ta bude wayan ta bayan kaman minti goma kiran unknown nomba ya shigo
mata layin ta.
Da farko kyale kiran tayi har ya gaji ya tsunke don kan shi amma,sai gashi mai
kiran bai hakkura ba ya kara kiranta again.
Cikin kasala ta dauki wayan sai taji murya cikin turanci a na cewa hey, baby,
It's me Michael, your friend from lagos, i hope you remember me now.
Cikin wata murya tace you mean, Michael Nasir friend ?
Yes it's me baby .
I called your nomber several time is switch up what happen with you baby?
Tsuki tayi tana fadin dan rainin wayo kawai har ma kana tambayana abinda ya
samay ni ne wai?
Sam batai tsanmanin ya taba iya hausa ba sai taji yace don Allah kiyi hakkuri
nasan bamuyi maki adalci ba shi yasa nakira layin ki na baki hakkuri don ban son
abinda zai dawo a gare ni wata rana.
Maimakon tayo magana sai ta kama kuka dama gashi mahaifiyarta bata nan gida ta
tafi makwabtan su .
Cikin rudewa michiel kece tayi hakkuri ta,saurare shi yana son magana da ita ne.
Da kyat ta dakatar da kukan ta yake cewa kina jina baby dama na dauki nomban ki
ne batare da sanin abokina ba.
Don kawai nakiraki saboda ya bani labarin irin abinda yake maki wanda banji dadin
shi ba kuma ranan ban san cewa two in one zamuyi maki ba don mun shirya dashi ne ni
kadai zanyi amfani dake.
Wani abinda baki sani ba yanzun hakama yana nan yana planning din yadda zai fita
dake waje, ne ya sayar dake ga turawa don ya tara kudi.
Bake ce ta farko da yai wa haka ba akwai yan mata biyu da ya kai waje daga garin
ku.
Batan lokkacin da tace what da karfi ba cikin wani irin murya mai karfi.
Yace cool down my friend, kin bani tausayi ne don naga ke yarinya ce karama.
Kuma d way yadda naga kina kuka yasa kika bani tausayi, ba zan yarda ya yaudare
ki ba shi yasa na kiraki na fada maki komai da fatan zaki rufeni bazaki bari yasan
na fada maki komai ba.
Godiya take mai tana fadin tagode tagode yace ba komai, sai dai idan kina da
account ki turo min zanturo maki da kudin ki.
Don shi ne ya hana na biya ki tun yana kuna nan yace free sex nayi dake ni kuma i
can't dole ne na baki hakkin ki.
No kabarshi kawai ba komai, nagode, sai kawai ta kashe wayan.
Kifewa tayi saman dan katifan dakin ta ta,shiga gurzan kuka wi,wi tana cewa Nasir
Allah ya isa tsakani na dakai wallahi.
Sai kuma tai shiru tafara tunane na, son, datakewa,Nasir ya haukatar da ita ta
kasa fahintar irin son da Nasir yake mata.
Sai yanzu tafara tunanen lalai maganar Michael yana da kamshin gaskiya sosai don
a wanan tafiyan ta fahinci wasu dabiun shi da bata sani ba.
Baida tausayi ko kadan son kan shi yai yawa bai damu da damurta ba ko kadan, shi
kan shi kawai ya sani.
Gashi in ba dan sayayyan da yai mata ba bai bata komai ba haka ya barta tadawo
gida sai dan dubu biyar dake a hannun ta.
Gashi kayan da,ta,sayo ta rasa yadda zata fitar tai amfani dashi a gani a gida,
a tambaye ta ina ta samo shi.
Don har yanzun tana da sauran burbushin tsoron iyayyenta a ran ta.
Maganan Michael yai matukar tsaya mata a rai sosai don duk da bata ga Nasir ba
amma matukar tsoron shi take ji a ranta.
Ko da Raiha tafara fita bata yarda ta hadu dashi ba sai guje mashi takeyi duk
inda tasan zasu hadu bata yarda su hade dashi.
Wata rana tana tsaye tana jiran taxi taga wata far mota ta tsaya a gaban ta.
Bata tsaya kallon kan motar ba, sai kokarin tare mota take yi hankalin ta yana
kan titi.
Ya fito daga cikin motar yana saye da shedda kalar kakin soja tai matukar yi
mashi kyau sosai da haka yake yaudaran yan matan gari.
Don Allah yai mashi matukar kyau don duk shigan da yayi zai mashi kyau sosai ya
karbe shi.
Baby ya karaso yana fadi kamar bata ji shi ba tayi ta kawar da kanta tana
kokarin shiga motan da ta tare.
Da sauri ya karaso gaban ta yana cewa haba baby wai may ke damun ki ne don Allah
na fa rasa gane kan ki.
Wani kallon tai mashi kamar bata san shi ba ta na kokarin zaunawa a motan da
zata shiga.
Hannun ta ya riko da karfi yana fadin sunan for d first time sabanin baby da
yake ce mata da, Ke Raiha wai may ke faruwa ne please ?
Sake min hannu tace cikin wani zafafan muryan tare da kokarin kwace

12 / 92