Advertisements
Chapter 38 Reading A Lokacin Mu Ke by Zainab Idris Makawa Seenabu BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

A Lokacin Mu Ke by Zainab Idris Makawa Seenabu

Author :  Zainab Idris Makawa Seenabu Category :  Complete Novels

Chapter   38 / 92

111K to 114K   out of 275.8K words

bude take ce wa daganin na shigo da yaran
gidan lokacin suna kananan su.
Matar tace wai wai wai wake da wanan hamshakin yaron haka?
Wai akwai magana nan gaba a gurin nan yaro karami haka da,wanan baiwa irin haka.
Don Allah ku daina fita dashi don gudin idon makiya don wallahi wanan da kuke gani
ba karamin mutum bane gurin nan aje.
Umma tace na dauka fa da yaron nan take (Imirana) sai naga ta kama hannun Sadauki
kawai tana wani zuba mashi kirari har da dukawan ta.
Tace a lokacin na dauka ko shirmay su ne na yan bori ko neman kudi sai kuma
nakarajin shi a gurin maigadin ma,aikatan mu ranan shi ma ya kawo min sako gida sai
ga sadauki yafito naga yana kada kai yana fadi cabdi babban mutum Allah ya raya
muna kai watarana,akwai magana gidan nan.
Wallahi Asiya tun ranan nasan in bamuyi hankali ba diyan mu na zama shara a gidan
nan muna ji muna gani.
Hmmm ashe bani kadai nasan da haka ba tace ni wallahi a gurin baffa malami na
fara jin haka.
Ranan da,suka rakani na gayar dashi duk cikin su ba,wanda ya cewa yazo inda yake
zaune saman buzun shi wai sai sadauki.
Naji yana cewa manyan gobe Allah ya taya riko Asiya ki rike yaron nan don watarana
shine gatan ku ke da yaran nan.
Wallahi baki yadda wani mashe ya sokeni ba sai da na dawo gida abin ya tsaya min
arai sosai wallahi.
Nasan baffa kamar mai rafanne yake da,wuya yai magana ya zama karya wallahi.
Kinga wanan makiran nasan itama tasan komai shiyasa take wani wayayya,tana nuna
ita tana kaunan shi fiye da kowa.
Shekaran jiya Adamu ke ce min wai motar da yasayo yana shiga yanzu takai miliyan
goma.
Ke don Allah dai ki bari tace wallahi yace haka yaji ana fadi a gari wai ba kowa
kedashi ba yanzu a kasar nan.
Hmmm lalai Hawau takai makiran mace amma baki ganin wani alaman facakan kudi atare
da ita kuma kin dai san yana bata dai.
,A,a ba gashi yaron nan yana fada min ba,wai shi yayowa uban odan kayan da
aka,shigo masu dashi wanan wata yace kuma kayan sun samu shiga sosai.
Ai harda noman da Alhaji keyi yanzu shine mai bada kudi anayi don dai ranan naji
suna,waya dashi.
Dan banzan yaro maikama da dutsen tsakar ruwa , Asiya karkare mata da cewa, wai
bai san tudu ana rana ba.
Yanzu don Allah wazaice dan banza zai iya irin wanan dabara duk kwaya ta halaka
shege kullun gashi a bushe kaman kayan rani.
Sai suka sa dariyan keta har suna tafawa tace aiko yanzu in sun san wata ai
basu san wata ba ko?
Da yammaci, ranan laraba sadauki ya shirya yafita zuwa masana,antar shi don yaga
halin da,su Bashar ke ciki da sana,an tasu.
Ranan shirin musulunci yayi wanda da,wuya kagan shi saye da tufafi irin
na,al,adan hausawa.
Shadda ce gezenah mai ruwan kasa,sai maiko takeyi, sai dai dinkin gajeren hannu
ce,anyi ma,rigar aiki a gaba mai kyau da daukan ido.
Sai yar hular da ya dora akan shi mai tsada kalar kayan jikin shi,takalman shi
bakake sai shining sukeyi sunci polish.
Ga kanshi na tashi kamar duk kwalban ya juye a jikin shi a lokaci guda.
Gurin maji yafara shigo ya sanar da ita zai fita don har yanzu kudi bai hana shi
yiwa iyayyen shi biyayya ba.
Kuma baisa yace don yayi gina yabar gidan mahaifan shi ba yanan ciki tare dasu
saidai ya gyara gurin shi sosai harda na yan uwan shi.
Ina zaune antu maryam tana min kitso sai faman masifa take min ita gashina yai
yawa wahala kawai nake bata.
Azaune nake ba dama na gudu daga falon gashi fuskana yana facing din inda yake
tsaye yana dauko wayan shi dake ruri daga Aljihun shi.
Yace hello Bashar yaya akayine ?
Yanzu nake son fitowa tun dazu ina daki ina barci kasan wasan last week yabamu
jiki sosai.
Saidai duk da waya yake idonbshi yana kan kitson da Maryam take min kur dashi
gashi dole muna facing din juna dashi.
Yana kashe wayan ya mayar da shi cikin aljihun shi inda ya ciro ta da farko.
Yace maji fa?
Yanzun ta shiga ciki nasan zatafito tunda taji muryan ka ai inji maryam din.
Maryam tace yaya wanan wayan taka tayi wallahi ni dai taban sha,awa Bintu gashi
kaman wanda mukaga Kabir dinki dashi ranan.
Da sauri yace ke maryam ban son iskanci wallahi ki daina hadani da wanan tsohon
mai zarin tsiya.
Na muguda baki cikin tsiwa nace nikan banga tsoho ba wallahi.
Ban san ko tako nawa yayi ba,sai gashi gabana ya danko gashin kaina da karfi sai
da na,sake wani irin kara,da sauri mama tafito tana fani kai kai yayane kuma wai ?
May haka dan Allah kasheta zakayine ko may ?
Wallahi maji yarinyar nan ta raina ni wallahi kan wani tsohon mijin ta can take
son ta zage ni, ta zage ka tace maka may?
Maryam sai dariyan keta takw min idanuwana,sun kawo kwalla ko don har cikin raina
naji dankan da,yai min.
Kadai zama babban kwabo wallahi ka ishi yarinya da sherin mijin ta tsoho ne basai
ka,samo mata saurayi ba kowa ya huta.
Allah dai ya,sauwa wake son wanan bakauyan haka ko dressing ba ta iya ba balle
gyara irin na mata.
Kyalkyalkyal maryam ke min dariya Amira da,tafito daga kitchen don jin karana
take cewa, a,a yayana aiko wallahi yanzu ba may cewa Bintu bata iya dressing ba
gaskiya.
Kallonta yayi yaja tsoki ya juta gurin maji yana fadin maji zan dan shiga gurin
su bashar na,dawo yanzu.
Sai ka dawo tace mashi tare da samun guri ta zauna tana man fada na daina shiga
harkan shi kada ya halakani ga banza.
Nace cikin dan kuka ina,share hawaye da bayan hannu na mama,wallahi duk anty
maryam ce taja min.
Ban san may yakaita danganta,wayan shi dana Kabir ba,shine yake cewa wai za,a hada
shi da tsoho kazami.
Dariya abin yaba mama tace ni dai na rasa wanan kiyayyan na sadauki da Kabir
wallahi Allahbya sauwaka.
Amira tace jinin su ne bai hadu ba yace min wallahi haushin shi yake ji.
Wai babba dashi yazo zaiwa yarinya wayo itako sai shegen son maza duk ta mutu
akan tsoho.
Dariya suka sa nace tunda yana jin haushin shi ba,sai ya kashe shiba in ya isa.
Har lokacin ina jin zafin dankan da yai min don har kaina naji yana sarawa wani
iri.
Tafe yake cikin motan shi sai dai a hankali yake tukawa don akwai motoci da yawa
saman titin a lokacin.
Wani iri yaji kamar ina cikin motan na,sake wanan razananen kara da na sake
lokacin da yaja min kai.
Yace natural hair ne haka gare ta ashe nibna,dauka ko kari take ko yaushe ai.
Wawiya can zata karata dashi gurin dan tsohon ta babu ma gyara kila a karshe.
Yana faka motan daga inda ya tsaya yafito yasa remote ya kulle motar nan ya taka
a hankali zuwa gurin da office din Bashar yake don yasan yana nan yaga motar shi a
fake can ne sa.
Bashar na zaune yana cika wasu takardu sadauki ya shigo office din .
Bashar ya dago yana cewa kadai samu fitowa ke nan yanzu din na dauka sai ka tsaya
ka cinyewa tsohuwa dan tallenta ka fito ai.
Murmushi yayi yana kaiwa zaune yace don wa ake dafa tallen dama ba don mu ba.
Gaskiya ya kamata ace kayi aure haka wallahi man, don Maji ta huta da katon gwauro
haka kullun yana lashe mata talle.
Sadauki yai murmushi tare da daukan wani takardan dake gaban shi yace aiko nai
aure tallen maji ba zai huta dani ba.
Kana ma min zancen aure ga babban tazurai basuyi ba balle ni.
Da sauri cikin daga kai Bashar yace wa wai Imiranah kake nufi da Ahmad?
Yace su mana kai dan Allah rabu da wanan shashan yayan namu .
Cikin dare fuska sadauki yace ban son iskanci ba yayan nawa ne kuma sha sha.
Ce wallahi shi duk gari yanzu kowa yasan shi sai aukin bin yan yara masu tallah
yana latsawa a kasuwa.
Kaifa dan iskane wallahi wanan kuma ai sheri ne nasan dai yana da shegen son mata
amma ban san da wanan ba kan.
Yace aiku na gida baku sani kwanaki ma naji ana kudundumin yaiwa wata yarinya mai
kai shikafa layin su ciki ko yaya case din ya kare.
Bashar yau dai da sheri ka tare ni ke nan dai don nazo gurin ka dana sani na zauna
gida abina ko natafi stadium.
Wallahi ba sheri bane don ina ga Baba ma yasan da wanan case din ai .
Zai iya don kwanaki a gabana wallahi Fatima ta mare shi babu ko kunya wallahi.
Naso na lalatsata ai amma sai naga tana da gaskiya din taba tayi kasan bata da
kunya itako ta kwashe shi da mari kayau.
Wata Fatima ke nan kuma?
Ya dan bata fuska yace wanan dayan sister tawa dake gurin maji mana da zama.
Au kace min pretty mana gaskiya mutumina yar8nyar nan ta hadu sosai wallahi ni dai
tana min.
Dariya sadauki yayi mai kama da yake yace aiko dan tsohonta zaici ubanka wallahi.
Waye dan tsoho kuma babanta yace wanda zata aura dai wani guy ne mai mata biyu wai
itace ta uku .
Zokaga shegiya yadda take rawan kai nace kici uban ki indai kince rawan kaine.
Kai kai amma gaskiya an kwabsa wallahi gurin nan .
Wai ma kai kana may har ka bari haka ya kasance ga ka har kabari akaba wani kuma
can.
Wani kallon rainin hankali ya watso mashi gani sai ayi may kuma ?
Yace yar gida gida mai tuwona maina kawai musha buki mukan .
Kasan fa yarinyar wallahi matar manya ce sai ta samu gurima zakaga yadda zata baje
sosai wallahi.
Kai don Allah ni bashi yakawoni ba wai how far ne akan kayan can da suka shigo.
Bashar yace baka son zancen ke nan dai mubarta anan kawai ko?
Yace zancen may kuma may zanyi da wanan mai zubin yan arab da ita.
Bashar yai wani dariyan keta yace kaidai sai naba Maji shawara tafara maka hayaki
da rukiya wallahi.
Ya jawo wasu takardu daga drawer shi yana mikawa Sadauki yace duba nan ka gani
kafin mu koma topic din mu don gaskiya ni iam serious wallahi.
Ko tayi miji ai ana iya tayar da zance don gida bai koshiba ba a kaiwa dawa.
Karanta takardan yake bai bashi amsa ba sai can ya dago kai yace ikon Allah so
quick haka sun samu shiga da,wuri.
Yace yanzu haka ma munyi magana da SMG yace min kila zasu sa mukawo masu sabon
sanfarin su din suna son su rabawa sarakuna shi.
Amma ko gaskiya in haka ya kasance da muyi sa,a sosai wallahi ko.
Nan dai suka kara dan tattaunawa akan business din su inda suka fito don dama
suna da alkawrin zuwa wani guri da Bashar ya damu sadauki su tafi.
A hanya sadauki ya nisa yace amma gaskiya banji dadin labarin da ka bani ba na
Imirana .
Yace kai kana ga zancen ne har yanzu yace ai wallahi duk ya zubar da mutuncin shi
saikace ba Alhajin ku ya haisu ba.
Shifa Ahmad cewa akayi yana sanan kayan sata sai asato mota ko mashin ya saya .
Innalillahi da karfi sadauki ya furta tare da waigo inda Bashar yake zaune a
gefen shi yace wallahi man .
Wai kai kana nufin duk wanan zancen baka san dasu bane ko yaya?
Yace ina zan sani tunda ba shiga gati nake ba yawo iyakata idan ina gari ina
gida ko nan gurin ka,sai ko can site din da nake gina na kawai.
Lalai na yarda baka gari gama,wanan sister din naku kwanaki saida yan hizba suka
kamasu wai ance sun hada party suna abin banzan ga da mata keyi tsakanin su.
Da karfi ya taka burki yace Nafisa ko?
Yace ita wallahi naji kunyan wanan abin sosai wallahi ance ai shaye shaye takeyi
sosai yanzu kowa yasani ma agari.
Subbahanallahi ya,furta yace how comes abubuwa suke zo muna haka agidan mu kaman
mu kadaine a gari.
Kadai Allah ya,sauwaka kawai amma ai abin ba dadi wallahi.
Can suk shiga kasan gari gurin ginan shi irin na mutanen dana daganin gurin mutum
zai gane cewa tsohon gari ne gurin.
Da,kwatancen da Bashar ke mashi suka isa gidan da suke son zuwa,
Daganin gidan basai anfadawa mutum ba gidan wani masani ne na alkur,ani maigirma
don ga alluna nan na almajirai daga waje birjit dasu.
Nan suka,tura ai masu iso da,maigidan sai ga,yaron ya,dawo yace ance su shigo
daga cikin zauren gidan.
Wani tsohone ya tsufa sosai yana zaune saman shimfida irin ta mutanen da can baya
masu fada aji.
Bayan sun gaisa da tsohon ne Bashar ke cewa malam ka gan mu sai yau muka samu zuwa
ko yace tau harkokin ku na mutanen yanzu yawa gare shi.
Nan dai suka kara gaisawa Bashar yace malam kaman yadda na,fara maka bayani ne
akan al,amarin wanan abokin nawa dai.
Yau gashi nazo dashi malamin yai shiru can ya dan mike zaune tare da kallon su da
kyau yace.
Karbi wanan yana mai mika mashi tasbahan hannun shi dayake ja, yace ka zabi guda
ko wanine ma daga ciki.
Ya dauki wanda ke kusa da farko sai, tsohon yai dan murmushi yace ai abin yazo da
sauki tunda naga baka da zari.
Don da,wanine na tsaka zai dauka yana ganin yafi mai killla yawa.
Ya dinga karatu mus,mus mus dabaki can yace umm,umm Allahu akabar to Allah ya
sauwaka.
Su dai suna zaune suna kallon shi can yanisa yace Alhamdullahi Bashar don
al,amarin abikin ka ba acewa komai don yanzu ma kuka fara insha Allahu,
Sai dai gaskiya akwai dan matsa dana gani yanzu dai tunda bashi yakawo ku ba
harkankuce ta sana,a takawo ku bati muyi abindake nan.
Nan dai yai masu wasu bayanai yakuma basu yan abubuwa tun ana gaban shi yace su
sha.
Sadauki da cukin kyankyami yake ya matsu subar gurin don shi bai son irin harkokin
nan gaba daya a rayuwan shi.
Bashar ne ma ya matsa mashi kan lalai sai suzo don yanzu duniya ba,a shigan ta
haka kai tsaye don A LOKACI MU KE.
Sukai mai godiya tare da mikewa zasu fita bayan sun bashi, dan abincin goro don
yace bai karban komai nasu don abokin kakan Bashar din ne sosai.
Sadauki dake gaba ya dafa zauren na kasa zai fita sai tsohon yace ji mana idan
kaje gida kacewa mahaifiyar ka kada ta manta da zancen baya da tai alkawari kai ka
gurin da aka bukaci ta kai ka a baya.
Don idan bata maida hankali ba hannun agogo kullun zai dinga koma mata bayane.
Da mamaki sadauki ya kalli tsohon sai dan tsohon yai murmushi cikin kada kan shi
yace abinda nace zaka fada mata ni dai bata sanni ba ban san ta ba.
Yace cikin mamaki toshike nan malam zan fada mata insha Allahu kaman yadda kace
na fada mata yace Allah bada sa,a suka ce amin suka fita daga zauren.
Duk zukatan su fam yake da tunanen zancen tsohon saida suka fara hanyane Sadauki
yace kai guy man din nan fa ya bani mamaki.
A ina ya san maji kuma may yake nufi da sakon shine wai?
Bashar yace nima naji mamaki amma sanin halin malam babba yasa ban damuwa nasan
wani zance ne can ya hango akan ka kuma.
Baidai son ya fadine kawai kila tunda bashi yai aikin ba.

****** ********* ******
Maji ke da duty a gidan ranan duk da dai su girkin su bawai na duka gida bane gaba
daya.
Wace dai take da girki ranan itace zata girka abincin part din ta dana maigidan
kawai.
Ba ruwanta da sauran part din gidan kowa shi zai girka nashi da yaran shi.
Komai da ya dace a girka sungama da wuri kamar kulun sai ta wuce sashen maigidan
don ta gyara mashi daki kaman yadda sukeyi kullun kafin ya dawo gida daga kasuwa.
Amirah ta tafi kitso a wani shago cikin unguwa maryam kuma ta shiga makwabta don
ganin wata kawarta da tayi rashin lafiya.
Tare zamu tafi sai banda lafiya kaina da akaja min yana matukar damuna da ciwo
hakan yasa tatafi ita kadai.
Ina kwance saman doguwan kujeran dake falon na rufe fuskana da littafina da na
dauko don na karanta amma na kasa karantawa saboda kaina dake damuna da ciwo.
Sadauki ya shigo falon don ya ga mahaifiyar shi akan maganan da malam yai mashi.
Nan ya hangoni a kwance,kyakyawan suran jikina danabi kujera na kwanta rigingine
yafito a fili.
Farin kafa na da yake fari sol dashi ya dan baiyyana a fili sunyi fari sol gasu
lub lub dasu tankar wace bani taka kasa.
Sadauki yai saurin kawar da kan shi dan ganin irin yanayin da nake a kwance cikin
yar doguwar rigata mai dogon hannu da,sharp.
A hankali ya tako zuwa inda nake kwance din ya dan rage tsawon shi ta hanyan
dukowa ga kirjina ya dan ban karo gaba.
A hankali yasa hannun shi ya cire min littafin dana kare fuskana dashi,
Da sauri na bude idanuwana da suke min a lumshe don ganin waye ya cire min
littafi haka a fuskana don part din shiru yake a lokacin.
Daga cikin tsakiyar kaina da hancina naji kamshin turaren shi amma banzaci cewa
shine a gabana ba.
Nai saurin bude idanuwana da suke a lumshe alokacin shi nagani tsaye kerere a
kaina .
Haka yasa nai saurin yunkurin tashi zaune a lokacin tare da jifan shi da wani
fitinanen kallo na tsana.
Yace ke ina mutanen part din suka shigane wai ?
Wani guntu tsuki naja da ban yi niyar ja ba don cike nake dashi a lokacin saboda
ciwon kan daya haddasa min.
Ke ni kika ja,wa tsuki ashe baki da kunya haka ban

38 / 92