Advertisements
Chapter 43 Reading A Lokacin Mu Ke by Zainab Idris Makawa Seenabu BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

A Lokacin Mu Ke by Zainab Idris Makawa Seenabu

Author :  Zainab Idris Makawa Seenabu Category :  Complete Novels

Chapter   43 / 92

126K to 129K   out of 275.8K words

dinta tafita sai dakin Umma.
Umma na zaune a kasa sai waya take bugawa ko anga Imiranah wa yan uwanta cikin
tashin hankali.
Ganin maji a dakin ta ya ta dan daure fuska a zaton ta tazo mata jajen munafuci
ne na kishiya.
Sai da maji ta zauna take cewa yaya ya mukaji da hakkurin wanan tashin hankalin
na yau.
Tace ai bai kare ba tunda ban san inda ya shiga ba har yanzu, don ina tsoron kada
mutane su ganshi su illanta min shi wallahi.
Maji tace bazasu ganbshi ba ma ai don yanzun ma shiya kawo ni gurin ki.
Ina son mu san yaya za,ayi mu fitar dashi daga gidan nan mu san ku ma maynene
abin yi yanzu?
Kina nufin yana gidan nan ko may Hauwa,u ?
Maji tace yana gurina yaya shiyasa ma nazo yanzu don ban son ko Alhaji yasan yana
nan.
Wani irin ajiyan zuciya Ummata sauke tace yanzun yana inane wai ?
Yana na dakina tunda rana nakaishi ciki lokacin da taron nan yai yawa mutanr basu
gane ba na bashi hijjab ya shiga ciki.
Umma da yaranta suka ce wai har sun danji sanyi wallahi .
Yanzu yaya za,ayi Sagir ?
Sagir yace wanan dai hijjab din zamu saka mai shine kawai za,a iya fita dashi daga
gidan nan ko shi a cikin dubara don wallahi naga matasa a zaune kofa group group
nasan ko shi suke jira ya dawo.
Nan dai aka hada plain yadda za,a fitar dashi daga gidan muna zaune sai ga Umma
da maji sun shigo dakin da yaya Sagir.
Can mukaji sun fito mani tace Amirah ke da Fatima ku sako hijjab kuzo ku fita da
yayan ku can gaba da layin nan Sagir zaizo ya dauke shi sai ku dawo.
Haka akayi muka futa tare da munafuki, yana bin mu solai solai har muka wuce
matasan nan sai hiran sukeyi suna cewa yau suna nan ba inda zasu sai yadawo don sun
san idan dare yayi ai zai dawo gidan ne.
Bamu dade tsaye ba saiga yaya Sagir da mashin yazo ya dauke shi yaciro muna
hijjab din maji muka dawo mata dashi.
Garin aka bari dashi zuwa wani kauye da yan uwan su suke can.
Muna shigowa still su Umma na dakin da mama da sauri suke tambayan mu sun tafi
mukace eh ya dauke shi sun tafi,
Tace cikin ajiyan zuciya wai Alhamdullahi yanzu dai sai asan abinyi don Alhaji ya
hau sosai wallahi.
Duk abinda ke nan abari da safe sai a san abida ya dace ayi.
Suka fita daga dakin tsomai tsomai dasu cikin tashin hankali nan akaje aka rufe
gida.
Haka yasa mutanen dake dakon shi suka fara watsewa daya bayan daya daga zaman
jiran shi da,sukeyi.
Washegari haka muka,wayi gari da yansanda sun dawo kara tambaya still sai da suka
kars search din gidan ko yana ciki.
Ganin bsina suka wuce suna fadin da zaran angashi a hanzarta kai shi ga hukuma
kafin su dauki mataki amma dole Alhaji ya tafi ya saka hannu a furin su.
Ranan kan anga tashin hankali don Baba ya ce sai Umma ta bar maigida ta nemo danta
in ba haka ba zai dauki mataki a kanta.
Umma kuka ranan yaranta kuka cikin tashin hankali duk gida ya rude da kuka.
Sun matukar ba mutane tausayi sosai ga irin yadda Baba yai mata kaca kaca a tsakar
gida.
Ganin haka yasa maji takira sadauki a waya yana dauka yake cewa maji yanzu nake
batun kiran ki ai.
Na kira Baba wayan shi bata shiga lafiya dai yake ko don hankalina ya tashi sosai.
Babana kabar duk abinda kakeyi kazo gida akwai matsala babba ya taso a gida jiya.
Maji may yafaru da Baba ?
Tace ba Alhaji bane yayanka Imirana ne kaddara ta hau kan shi yaiwa wata yarinya
karama fyade abin ba kyau wallahi.
Salati ya saka yace yanzu Imiranah yana ina maji?
Tace yana can anboye shi nan dai ta dan bashi bayani a takaice ta dora da fadin
nasan Alhaji zai dauki mataki mai zafine akan shi yadda ya hasala din nan.
Yace to gani nan zuwa maji zan taso yau insha Allahu.
Sadauki bai shigo ba sai guraren shidda na yamma ya iso garin shida Bashar suka
zo gida.
Ina daga ciki mukaji muryan shi ana gaidashi shine muma muka fito don gaidashi da
dawowa.
Hankalinshi a tashe yake sai fada yake akan abinda Imirah yaja masu a gari.
Bashar yace yanzu mataki guda ne mu ganshi muje dashi gurin yan sanda asan abinda
za,ai mai sai kuma muga iyayyen yarinyar mu basu hakkuri haka zai kawo dan sauki
abin.
Yaya abinci fa inji maryam ?
Yace maryam bari kawai mu fita mu san yadda za,ayi wanan al,amarin.
Gurin Umma ya shiga yace ina Sagir tace yafita yace Imirah din yana ina ne yanzu?
Tace yana bodinga gidan yaya hassan tun shekaran jiya da dare.
Daga haka suka fita duk ta ramay tafada kamar tai ciwon shekara daya.
Basu tsaya ba sai gatin BODIGA can gidan yayan Umma sun samay shi ya ramay ya
koma wani iri dashi.
Sunyi masu bayani kamar yadda suka tsara da farkon maganan duk da haushin dan
uwan da yake ji amma ya matukar bashi tausayi sosai daya gan shi.
Gidan mahaifin yarinyar da abin ya sama suka fara zuwa tare da dattijan da suka
dauko daga unguwan.
Nan dai aka,shawo kan mutumin sani Allah sani manzo har ya hakkura suka basu kudi
har dubu dari uku wai aiwa yarinyar magani dashi tare da biyan kudin maganin da
akai mata asibiti.
Nan kuma aka dunguma sai gurin yan sanda suma a kai rana dasu don sunce dole sai
sun kuleshi har hukumar dake da Alhakin wanan shatian suzo.
Haka yasa aka nemo masu alhakin irin wanan matsalan suka zo suma saida aka shafa
masu nasu rabon aka kashe case din sai dai anci kudi sosai wallahi.
Daga can suka kwaso zuwa gida gurin mahaifin su yana falon shi akace ana mashi
sallama.
Yana fitowa yaga su sadauki da wasu dattijan shiyan ya juta zai koma aka dinga
bashi hakkuri akan ya dauki al,amatin a matsayin kaddaran rayuwan yaron ne.
Yace aiba yaune yafara haka ba kungan shinan shedanin yaro ne don har wata yarinya
ya taba yiwa ciki yanzun haka dan zaman shi yakeyi.
Yaro yace ya zauna bai mayar da zina bakin komai ba.
Yace yabasu su uku nan da wata uku ko mutum bai shirya ba sai yai mashi aure da
kan shi.



ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,,,
.
YA ALLAH DUK WACE TA TURA MIN NOVEL GA,WANDA BAI BIYA BA ALLAH KAI MIN BAKAR ISA
AKAN MAISHI YA ALLAH DAMU DA WANDA DUK YA KARANTA A SANADIN TA,,,,


A yammacin da aka,sallamo sadauki baba ya tara duk ilahirin iyalin shi a falon shi
yana masu magana a cikin takaici da bakin ciki.
Ku san Nafisa ce ta karshen shigowa falon tana saye cikin wani dogon riga da yai
matukar matse mata jikin ta sosai.
Baba ya bita da kallo na tsana da yakaici yace cikin bacin rai ke ina hijjab dinki
zaki shigowa mutane kusan tsirara haka.
Tace cikin wani bakon murya mai baiyyana wani sabon al,amari a gareta,
Baba,,, nifa ba tsi, tsira rarra nake ba don a saye nake da, da da riga a jikina.
Ido ya kura mata cikin nazarin ta yace Nafisa kanki daya kuwa yau din nan?
Warassss nake Baba may ka gani kafin yai magana Umma take cewa daga barci take fa
take wanan ita shegen haka.
Yace maza jiki sako hijjab dinki na baki minti uku ki dawo nan mara mutunci kawai.
Ya juya gurin Umma yana fadin Atika ina son idan ina magana da yara na ki daina
saka bakin ki daga yau.
Ki bari idan na sako sunan ki a ciki ki saka bakin ki, idan kuma kinga kamar fadi
nayi kawai to kici gaba da hakan.
Yanzu saboda mugun halinki na yaro yayi laifi ki tsare ba ai mashi fada kinga
abinda wanan fasikin dan naki ya jawo muna a gida.
Wai dana mane yau tunda yai laifi ko?
Au to ba danki bane dan waye a gurin nan , saunawa kina fadin ke kikai daukan
cikin abinki don haka abar maki kayan ki.
Zaitai magana yace cikin daga hannu da daka tsawa ki min shiru don ban son jin
kazamin kalamin ki yau a gurin nan.
Yace Imirah kai kuma abinda kai min a idon duniya banda abinda zance maka sai dai
nace kaje duniya tana da fadi.
Don daga yau ina son ku sani na cire Imirah ga duk wani harkan kasuwancina.
Don ba a hada biyu a lokaci guda zina da neman arziki basu tafiya daidai.
Don haka tafi nima nema nayi Allah ya bani kaje ka nemi na kanka amma da kudi na
ni Abubakar ba za,a dinga zina dashi ba.
Wanan kalamin na Alhaji ya tayarwa Umma da yaran ta hankali sosai don sun wani
babban komawa baya ne ya samay su.
Yace daga yau duk wanda ya dauko min magana irin ta zubar da mutunci da kima a
idon duniya wallahi ku sani na tsamay ko wanene daga cikin zuria ta.
Ni ba mazinaci bane kowa ya sani a garin nan don kaucewa zina yasa na aje iyayyen
ku haka a gidan nan.
Duk wanda ya ganin a gurin mace to ka tabbatar aure ne yakaini ba yaudara ba.
Yanzu ina riba ga illanta wa mutane yarinya da kayi amma fa ka sani shi zina
bashi ne karike ka aje hakan a ranka.
Haba Alhaji kada kai mashi baki mana mama Asiya ta fadi haka da sauri ta tare
mashi numfashi.
Yace Asiya ki shiga hankalin ki duk kune barayin na,tsunta da baku iya kwabawa
diyan ku kun bar yara sun zama ni alkakan kafa a gida na.
Sai yai shiru can yanisa yace Maijidda ke kuma kada ki ga kamar ban san komai
ba da kikayi.
Nasani kuma nayi mamakin yadda kika boye, wanan mugu munafuki mazinaci akan
mumunan laifin da ya aikata haka.
Dukar da kai mama tayi tare da dan nisawa Baba yace ina kwana ki akanki yaso
sauke wanan iftila,in kan yar amanan da aka aje a gurin ki.
Idan da ita yaiwa hakan ashe boye shi zakiyi ke nan kici amanan iyayyen yarinyar
da aka danka maki.
Gaskiya kin bani mamaki kuma kin bani kunya matuaka dana ji hakan a kan ki.
Sannan ke mai da mai hali ko ?
Kika saka danki a gaba sai da yazo ya fitar da,wanan fasikin dana so ai mashi
daurin rai da rai ya karata can gidan yari inga yadda zai samu wata yar kuma ya
lalata.
Cikin karfi hali maji tace Alhaji ni ba na boye shi bane don kada a hukun tashi
kokuma wai ba mumunan laifi yayi ba.
Gani nayi a lokacin yadda mutane su kai dandazo suna neman shi zasu iya illanta
shi.
Yace da tsawa shi da ya illanta yar wasu fa ?
Tace idan sun kashe shi ko sunyi mashi wani mugun abin a lokacin Alhaji sai abin
yafi na farko muni.
Kai kuma ka hau sosai a lokacin ba shawara zaka ji ba don yadda ka hasala.
Wanan dalilin yasa nai hakan .
Amma da aka samu natsuwa ai an fahinci juna don kaddarace shima ai da yayi abin
ya koma mashi ciki.
Sannan ita wanan yarinyar mutane sun sheda ta da haka take watsatsa ce ita dama.
Yace ai shi ya fita watsewa,
Maji tace na kira sadauki ne don yazo ya san yadda zaiyi akan al,amari don duk
kan mu nan ai matsalar ta shafa don ba wanda bai shiga tashin hankali ba daga cikin
mu.
Ke da danki ya shiga wani hali a gidan nan wa hankalin shi ya tashi ina a tsakar
gida ake tsayawa ai maki gori dare da rana.
Wanan kuma ai ba komai bane don kowa ma uwace ai don dan sune suma.
Amma ni idan abinda nayi laifi ne don Allah ayi hakkuri a yafe min.
Sadauki ne yai magana yace Baba don, Allah ayi hakkuri tunda abin ya riga ya
faru.
Kai dakata don Allah ai kaima zanzo gareka ne watau kai yanzu ga mai kudi ko ?
Shine zakai amfani da wanan dama gurin tallafa ma alfasha idan haka ya kasance
daga daya daga cikin kannen ku yaya zakuji ne wai ?
Abinda nake son ku gane ke nan idan a cikin diyan mu akaiwa wanan keta haddi haka
aka gurbata rayuwan su ashe taimakawa mai fyaden zakuyi a sake shi ?
Shiru falon yayi ba,wanda yai magana kowa na tunanen zuci daga cikin su.
Sadauki ne still ya kara yin karfin halin yin magana yace Baba don Allah ayi
hakuri tun da iyayyen yarinyar sun hakkura.
Ido mahaifin shi ya watsa mashi cikin takaici yace eh maganan ta mutu ma na tunda
kai mai kudi ka basu kudi ba.
Amma ni a gurina wallahi case din nan bai mutu ba dayan biyu ne ko na kai shi
kotu ko kuma ya yarda cewa da zaran yarinyar nan ta kara dan tasawa zai aureta.
Da sauri kowa ya ke kallon baba cikin dago kawunan su.
Imiranah da,sauri ya dago yace haba Baba wanan yarinyar yar kauye yar talla ko
boko fa batayi ba.
Au baka san haka take ba ne har ka turata daki ka kwamashe ta har ka kai ga halaka
ta ?
Shiru kowa yayi ba wanda yace uffan Baba yace sannan kuma kaine zaka dinga dauka
duk wani nauyi nata daga yau har zuwa lokacin da za ta tare a gidan ka.
Kuma ku sani wallahi ko bayan raina duk wanda ya tayar da wanan magana ban yafe ma
maishi ba.
Daga haka ya mike zai shige ciki sadauki yace amma Baba don Allah ka barshi yaci
gaba da sana,an shi da yakeyi.
Baba yace wani ai nagama magana ta yaje ya nemi tashi shima, don nima nema nayi ba
gado nayi ba.
Ya shige abinshi yabar su nan a zaune kowa yai jigun jigun tsakanin su, hjy
Kubura ta mike tana fadi yau dai ga irin ta nan.
Yanzu kowa na da abin fadi ke nan a gidan nan tab da tsuliya bamu kadai bane masu
abin fadi ashe?
Ke tsohuwar kilakiya dama nasan a farin ciki kike don haka ya faru kuma nasan duk
kece mai wanan shirin.
Iyakar ki ke nan zagin wasu naji ni dadewa nayi banyi aure har mijin ki yazo
ya,aure ni gani kuma gidan zama daram ba inda zan tafi wallahi.
Ba kince lokacin da na,shigo kin bani wata uku ba dashi yau gani wata uku ya
shude har da riba gasu nan min.
Sai da ki shirya don kilakiya tana nan dakin ki zaune ko kinzaci bamu san komai
bane wai ?
Ni ba irin hajiya maijidda bace da kike wa yadda ranki yaso wai don takaici har da
taimaka maku.
Nan da Sadauki ke dan shaye shaye a baya may nene bakuyi mata ba a gidan nan.
Yau gashi ita da dan da kike mata gori kullun sun taimake ku ai da kun gane kuren
ku wallahi da ankamashi fasikin banza kawai.
Nan fada ya kici may masu hjy kubura tai masu tas ta fita maji dai tana ganin su
sarke tabar falon zuwa part din ta.
****** ********* ******
Ina zaune a falo ni kadai don ban tafi gurin kiran da Baba yai wa iyalin shi ba
don nasan magana ce da yashafi sirin iyalin shi.
Sadauki ne ya fara shigowa falon su maryam na bayan shi, nan ya samu kujera ya
zauna tare da furzo iska daga bakin shi.
Daga inda nake zaune cikin yar siririyar muryana nace sannu yaya.
Sai da ya nisa yace yauwa sannu Fatima ke ma.
Maryam tace Fatima dauko muna salad din mu, mu sha kinji.
Namike na nufi kitchen na dauko salad fruit din dana gyara mu a a cikin wani roba
mai fadi da cups din da zan zuba muna aciki.
Shina fara zubawa fruit din idon shi suna a lumshe na aje mai a gaban shi nace
yaya ga naka nan na juya zan wuce.
Kamar mai rada yace ki zo ki dauki kayanki inba zaki juri bani hannu da hannu ba
kuma ki tsaya nasha naji ko may nene?
Wani din nayi kamar na wuce sai kuma nai wani tunane tare da dukawa na dauko cup
din na mika mai,
Bai ce min kala ba ya karbi cup din daga hannu na, zan juya na wuce yace amma
kinji abinda nace maki ko?
Dan guntun tsuki naja wanda ban san zai fito fili ba yace, ai da ma na barki ki
tafi din yau kiga abinda zan ma shegen kunnen nan da baijin magana.
Babu shiri na dawo daga gefen shi na dan tsaya tsaye.
Yace ya haka kuma kamar wata soja can ko bodyguide, zama nayi daga kujeran gefen
shi ina cewa Anty maryam ki zuba naku kada yai sanyi har nazo.
Bai ce min kala ba ya fara kurban salad din da cibin dake cikin cup din a
hankali.
Ya kai cibi uku ya dago kadan yace me sunan wanan abin kuma ne wai ?
A hankali nace fruits salad ne.
Ya dan mayar da hankali ga sha can yace waya hada shi haka ?
Nace nice nayi shi dazun da safe.
Ya nuna cup din yace ina son kullun da safe da yamma idan ina gari ki dinga hada
min shi.
Zan so na sha shi kafin nasha komai da safe haka da yamma kafin na kwanta.
Kaina na gyada mashi kawai.
Yace baki ji may nace bane ?
Da sauri nace tau yaya.
Maryam tace Bintu zo dauki naki mana kafin yai sanyi ki sha.
Na yunkura zan mike sai naji tasa kafan shi ya take min kafa, wani mugun zafi
naji ban san lokacin da na sake wani dan kara ba

43 / 92