Advertisements
Chapter 55 Reading A Lokacin Mu Ke by Zainab Idris Makawa Seenabu BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

A Lokacin Mu Ke by Zainab Idris Makawa Seenabu

Author :  Zainab Idris Makawa Seenabu Category :  Complete Novels

Chapter   55 / 92

162K to 165K   out of 275.8K words

dafa tace nasan baki son wanga hadin da naka shirin maku don shi ba son
kina yakai ba.
Amma na sani Fatima an, walleh sadauki sonki yakai so daina bai sani bashi, a
ruyuwa nai.
Kuma in kunyi aure duk bari shikai da yardan Allah ba zai wulakantaki ba Fatima
an kuma ni ban barin hakan ya hwaru tsakanin ku.
Jin tai shiru ni kuma ina duke na kwantar da kaina saman cinyan ta sai darzan
kuka nakeyi.
May zan bata amsa dashi nace ban son mashayin dan ta ko may, ?
Inace bata kyauta min ba don batai man adalci a rayuwana ba duk da nasan batai
min ba din ko may zan ce mata?
In ce, mama kin cuce ni da kika hadi da danki mara mutunci mara tarbiya lalattace
ko may?
Ince bata kyautawa rayuwana don da itace ta haife ni da cikin ta bazata taba min
wanan zaben da tai min ba ko may?
Haka yasa naja bakina nai shiru sai kuka nake yi wanda na rasa kukan mana wani
cikin tunane na nakeyi?
Shiru itama mama din tayi tana nata kukan tana sauraren nawa da nakeyi cikin
tashin hankali.
Fatima nasan zaki ce ban kyauta maki ba a yanzu don bazaki gane may nake nufi da
wanan hadin da nayi ba.
Amma nasan nan gaba idan ina raye insha Allahu zaki gane haka kuma zaki gode min
a rayuwan ki.
Fatima gida bai koshi ba ai ba akaiwa dawa muma nan mu na bukatan kki a cikin
mu, don haka mi zai sa in bari wanan baiwan taki ya tai gidan wani ina kallo bayan
muma nan muna da bukatan ki a cikin mu.
Ban iya cewa uffan ba har lokacin sai naji muryan mama tana fadin tai ki
kwantawan ki keji indai kega da takura ki hwada min sai a hwasa.
Da kyat na mike na fara tafiya kuka yaci karfi na don haka dashi na fita dakin
mama tabi bayana da kallo tace a fili.
Fatima am sai dai kiyi hakkuri don abinda ka hissheni na nakayi ke kadai ta ka
iya halin wanga baudaden yaron da Allah yya ban.
Kuka sosai nake a daki ni kadai gashi uwayen kallo suna can falo har wanan
lokacin suna kallo.
Maryam kamar an tsikare ta sai gata tashigo dakin dan wakan ta, sai ganina tayi a
kwance na kifa ciki ina darzan kuka ni kadai a dakin.
Mi nika gani haka shin?
Missa may ki Bintu?
Sai ma kara sautin kukan dana dan yi ban bata amsa ba, itakuma bata fasa
tambayana ba tare da zaunawa gap dani tana tabani.
Bintu baki hwada min ko missa may ki shi,?
Ko sai na tai na hwada ma maji ta taho ta tambaye ki da kan ta?
Ba amsa sai ta mike zuwa kiran mama don tazo ta tambaye ni da kan ta.
Riko hannun ta nayi nace cikin kuka anty don Allah ki dawo kada kitai wurin mama
don tasan ko may nakewa kukan.
Shi wai minana dan Allah missa may ki kika wanga bakin kuka, wane irin bakar
dabi,ata haka shin?
Cikin wanga dare ke zauna a daki ke kadai sai kuka kikai kaman wadda aka aikowa
mutuwa?
Shi ko wani na yya mutu anka bugo maki waya wai ?
Na fada jikin ta nace anty na shiga uku na lalace anty mika shirin hwaruwa dani
na wai ?
Shi wai mi an kayi na wai baki hwada min don Allah na sani ?
Gashi kece kan na kira maji ta taho tagane ki shin minana hallan?
Ina kwance a jikin ta nace anty na ga boni na lalace shi mi nai wa Allah da wanga
bakin rayuwa ka shirin fada min ?
Wane irin rayuwa na ka son hwada maki ?
Wai yaya sadauki mama ka son na aura Anty yaya sadauki mutumin da duk duniya
baida bakiyiya irina don dai ina hwada mai gaskiya.
Wani kallo ta watso min tace Bintu auren yaya sadauki na kika wa wanga kuka haka
shi ?
Dama ba soyayyana kukai dashi bana ?
Da sauri na girgiza mata kai nace ba wani zancen arziki da ya taba shiga
tsakanina dashi ni dai nasan kaman annabi da kafiri muke ni da shiya.
Maji na ta hwada maki haka ko wa?
Nace ita ta ttakirani dakin ta taka hwada min bukatan ta garan.
Yanzu kibar kuka Bintu muyi magana ta fahinta da keya don wanga kuka da kikai
nima kuka na kason yi.
A hankali na sasauta kukan da nakeyi don inji may zata fada min, ganin na rage
tace shin Bintu ke baki son yaya na ?
Nace walleh anty ban taba so nai ba a rayuwata mi zan yi da mutumin daya tsane ni
a rayuwa nai?
Tace ke yanzu zaki iya hwada ma maji baki so nai?
Ta kura min ido cikin kuka nace walleh ban iyawa anty amma da ma mama na tai min
wagga magana ba gaskiya hwada ma mai shi magana nakai.
Tace to ke gani.
Ni yanzu shawaran da nika baki shina hakkuri dai zakiyi kada maji ta fahinci haka
gare ki.
A yadda nasan halin nai shina kashirin balgace auren da kan shi ke ga dai ke komi
bai hito ta bangare ki ba.
Ko mi kki gani ga magana ta ?
Maganan ta dutse don shine mafita a gare ni nace cikin kuka anty na gode shawaran
ki na zanbi don shina kadai mahita agaran.
Tace to ke gani amma a,a kika zama cikin daki ke dai kina wanga irin darzan kuka
mi da baki kirani ba tundazun muyi shawara shin.
Tace ke ga yanzu in yya jiya nasan ba karamin rigima zaiyi a gidan nan ba, tun da
shi arniya mai dan buje yaka so.
Wanan magana shine ya kwantar min da hankalina nan muka raba dare muna magana
akan zancen har barci ya dauke mu zuwa asuba.

****** ********* ******
Tun ranan da akai zancen naji ban kara ganin shi bani haka nake ba walwala tare
dani ko kadan yanzun ma idan na dawo daga school ban zama a falo ina dakin mu.
Don ni idan da hali badon na gudu mama tace ban mata diyyauci ba da na gudu daga
gidan gaba daya.
Shima haka sadauki bai shigo ba gidan tun ranan da Baba yai mashi magana.
Haka ya gaji da fushin shi ga kiran da Amirah ke damun shi dashi tana tambayan
shi ko yai tafiyane bata ga ya shigo ba don ita batasan dawan garin ba.
Maryam bata fada mata ba don ta fahinci Amirah bata kaunan hadi tsakanina da
yayan ta don ita a ganin ta yayan ta yafi karfi wata Bintu can yar kauye can.
Don idan maryam na magana tana min sheri kan yaya Anty Amirah bata iya boye kin
da take wa hakan a zuciyar ta.
Tashiga fada ke nan da maryam tana cewa kefa baki da wayyo don Allah may ye kuma
na wanan magana ba dadi ina yaya zai kai wata Bintu can kuma haka.
Ina gani maryam din tagane zuciyar yar uwar ta ne yasa ta ki fada mata komai akan
halin da ake ciki.
Mun tafito zamu school muka ganshi tsaye a kofan gida shi da wani mutum da gani
dai mutumin ya girmay shi sosai.
Ina ganin shi na dukar da kaina kasa ban yarda na kalli inda suke ba inajin
maryam tana gaida shi ni kan ban tsaya ba na wuce abina.
Sai dai shi muna fitowa idon shi akan mu don yana facing din hanyar fitowa daga
cikin gida.
Ya ramay ya dan fada kadan sai dai ba kowane zai gane hakan ba sai wanda ya
sanshi sosai zai iya gane hakan.
Ina tsaye tazo da motan ta ta dauke ni muka fara hanya, sai da muka dan yi nisa
take cewa Bintu nace na,am anty.
Mayasa baki gaida yaya ba ?
Shiru nayi ba amsa tace indan kina haka maji bazata ji dadi ba gaskiya na fada
maki ki nuna bakomai a zuciyar ki haka zai sa tafitar da zargin komai a kan ki.
Nace anty ni wallahi ban son ganin shi ma yanzu bakiji yadda nake jiba a halin
yanzu dana gan shi a zuciyata.
Kada ki damu insha Allahu komai zai zama normal amma sai inkin bi shawara na fa.
Don haka dakikeyi kin san yafi wayo zai iya hada ki da maji laifin ya koma akanki
don haka ki gyara halinki tun wuri har inkina son kanki da lafiya.
Ban tanka mata ba shiru nayi tare da kwantar da kaina ga glass din motan ta
kawai.
Can tace dama ina son indan mun tashi daga makaranta na fara koya maki mota.
Da sauri na dago kai ina kallon ta nace, mota anty ni ina zan samu mota kuma?
Dariya ta kyalkyale dashi tace kin san abin Allah ne yar uwa da zakice haka?
Muna wucewa ya shiga gida bayan bakon shi ya wuce daga mamane sai Amirah zaune a
falo suna karyawa a lokacin.
Amirah tana ganin shi take cewa kai yayana har zan kai cigiya da sanarwa gidan
redio da talabijin a kan ka.
C U yace an fada maki ni raggone da zan bace ko ni bakauye ne da zanbace maku?
Ya juya gurin mama yace ina kwana maji cikin dukar da kan shi yake gaishe ta.
Ka gama fushin ne dakakeyi halan mara hankali kawai?
Fushi kuma maji akan may zanyi fushi da abinda kike so akaina ?
O nice ma mai so bakai ba ke nan ko mara tunane kawai, dariya yayi don zagin da
maji ke mai bai san dalilin shi abugi mutum kuma a hanashi kuka ke nan yace a ran
shi.
Zama yayi tare da cewa bani breakfast dina Amirah ya fadi Amirah dake masu kallon
mamaki bata fahinci komai ba a fadan tace.
Yayana may kuma kaiwa maji hakane wai?
Yace wallahi ban sani ba kaunata kawai dai maji na son min fada ne don taga ban
shigo ba kwana biyu ni kuma aikine yai min yawa.
Amirah tashige kitchen ta hado mashi abin karyawa tafito koda tafito ta samu maji
na fadin.
Kai akwai gatan da za,ai ma dayafi na daga kayi arziki ka samu yarinta gari yar
arziki zata rufa maka asiri daga shi har Amirah kallon maji sukeyi don jin abinda
ta fadi a lokacin tace eh ba rufa maka asiri zatayi ba may zatayi, kai may ya saura
a jikin ban da ragowan maye sai ball.
Yace maji nine yarinyar nan zata rufawa asiri ko zan rufa mata dai kece kike
ganina haka maji amma ai duniya ta san ba abin banza nake ba yanzu.
Wallahi maji inkina fadi haka a gaban ta dadi zataji ta raina ni don bata da
kunya Allah.
To ubana sai ka rufe min baki tunda kakawo karfi yanzu ka wuce fadana yace ni
bance maji cikin dariya duk yana kokari yaga ta sauko daga fushin ta.
Maji wai wata yarinya ta ki ka yiwa yayana sababi a kan tana haka?
Cikin bacin rai ta dago tace mata Fatima mana ko da me ya fita oho?
Itama Fatima in ba tauye tan danayi bata iya musa min ba mitakai dashi haka ba
makari.
Maji mi yayana zaiyi da Bintu kuma yar kauye da ita ba asali ga mata yan asali da
yawa a cikin gari.
Da may yahita da zakice haka, nice hwada min damay hita, ?
Shi har wani asali yakaso yabar kyau ne tun wurin wanka ai yanzu ya makara da
wanan ko?
Da mamaki furcin mahaifiyan shi ya dago kai yana kallon ta sai abinci yake cusawa
a cikin shi kaman dolle yake ci.
Amma gaskiya maji kaman mara galihu zakice wai da Bintu zaki hada shi Bintu may
can don Allah dai Amirah ta fadi haka cikin yanayin bacin rai.
Walle Amira kihita min ga ido tun banci kaniyaki ba gidan ke ko kwatan Fatima kin
kaine asali ne mi ake bukata ga asalin ba uwa da uba ba.
Hwada min wane ta rasa daga ciki?
Ko shi arzikin ga dakika gani Allah ya bashi kikawa katobara, haka.
Ita ke san inda Allah zai aje tane halan ?
Nikkara jin keyi wani magana mara dadi akan Fatima walle saina lahira yahiki jin
dadi a gidan nan marasa ta ido kawai.
Amirah tahau ta cika ranta ya baci ta kalli dan uwanta hadade guy ye haka son
kowa kin wanda ya rasa amma ace ga Bintu yar tallakawa zai kare.
Sai dai ba dama ta muda ko tak yadda uwarsu hau tasan yanzu nata na samun ta.
Bai jima zaune ba yamike yana fadin shi zai fita, maji bata tanka mashi ba don
haushi.
Mun dawo gida a gajiye don an kusa fara kiran magariba a lokacin saboda huturu
yayi.
Amirah ce a falo, zaune ina shigowa naga wani ir8n kallon banza da wulakancin da
tai min.
Take nasha jinin jikina da zargin akwai wani abu bani ba har Maryam sai da ta
tsargu .
Mun shiga saida mukai sallah muka fito maryam ta fara fitowa bata dade ba nafito
nima falon.
Zama nayi tare da cewa anty Amira an fara film din end of love ne?
Kamar batajini ba ta kyaleni maryam tace min yanzu za,a fara time yayi ai.
Can taja tsaki tace dama kwadai ya kawo mutum ai don kwadayin tsiya abi an
asarice muna uwa da tsafi sai yadda akayi muna da ita.
Komai tsafun mutum dai wallahi sai ya bar mu kuma sai ya bar gidan nan don yawan
kwadai ma har diyan mutum ba,a bari ba.
Ke dawa ye kuma Anty inji maryam, ke tambayan ta cikin kallin fuskan ta.
Ke dalla kyaleni da takaicin daka damuna yanzu don kwadai sai a asirce muna uwa
tasa dan ta ya tillatawa kan shi wata gaja can mara asali.
Kai amma anty Amirah na raina maki wallahi, wanga magana kuma ina ya fito maki
haka da girman ki.
Shi yaya din yace maki lakaka mashi ita akayi kan dole ko wa ya fada maki ?
Maryam kifita idona wallahi kafin na bata maki rai a gidan nan don naga ke kina
ganin kin girma wawiya kawai da batasan ciwon kan ta ba.
Kasa hakkuri nayi nace Anty Amirah kamar yadda kike gani an lakakawa yaya sadauki
ni haka nima aka lakaka min shi.
Don ni yaya sadauki baiko cikin irin namijin da so na aura a,rayuwa na, don kwata
kwata baya burgeni.
Shi kuma asali da kike nufin bandashi uwane banda ko uba, bski fini uwa ba baki
fini uba ba.
Tsafi kuma ni bamu san shi ba a gidan mu a gidan ku nazo naga a na tsafi.
Aiko tayo kaina wai zata mare ni maryam ta shiga tsakanin mu tace wallahi baki
bugun ta don amsan maganan ki tabaki.
Jin hayaniya yasa mama fitowa ta samay mu tana tambayan basin may yafaru kuma
mayye haka wai ?
Nan maryam ke dada mata abinda ya faru tsakanin mu da amsan da na bata.
Tace Fatima shiyasa nake son ki don baki shayin kowa gurin fadin gaskiya.
Wawiya kawai sakariya kinga har tabar ganin girma ki ta baki amsa ba yau ba nake
ganin take taken ki kan Fatima gidan nan.
Uba kika fita ko uwa ki fada min nace ?
Gurin ubanki ko uwarki tazo maula kin taba jin Fatima ta roki wani abu a gidan
nan duk zaman ta damu.
Ku arziki yake rudi har ya rufe maki ido kika manta da Allah, da tazo gidan nan
gurina may nake dashi.
Shiru Amirah tayi karshe bata tsaya falon ba ta tashi fuuuu ta shige ciki can ta
kira sadauki ta fada mai abinda ke faruwa a gidan yadda maji tai mata.

****** ********* ******
Ranan bamu zuwa school misalin sha biyu da rabi na rana maryam na baya tana wanki
mama tana dakin ta tana barci.
Sai ganin mutum nayi tsaye a kaina ban san shigowan shi falon ba sai da na gan
shi tsaye a kaina.
Ya nayi yana dan waige waige kamar mara gaskiya yace cikin daure fuskan shi ke
jinan.
Na dago na kalle shi saudaya na dukar da kaina yace wallahi duk kika sake kika
yarda har maganan maji ya zama gaskiya a kan mu sai na halakaki garin nan.
Mara mutunci kawai banza dake ina mai shawartan ki da kiyi maza maza ki sanarwa
maji baki son wanan hadin kema.
Jiki dan Allah ko na rasa mace a duniya may zanyi da kucakar mace mara fasali
irin ki.
Duk da zagin ya bata min rai sai nai murmushi a fili nace amma kaima kana da
bakin fada mata ko don naga kaman yan maye basu da ta ido kaga kaine daidai ka fada
mata idan kayo mayen ka.
Ni kasan lafiyata kalau don haka ina da kunya da daraja ba zan iya kallon idon
mama na fada mata ido da ido don ban da kuya ba wai ban son dan ta gudan jinin ta.
Amma kaika nasan zaka iya tunda bata idone dakai ba inkai haka ka taimaki
rayuwana da ga auren kaddara aure alkakai da zan tsinci kaina acikin shi gidan
mashay,,,,,
Kau ya kwashe ni da mari daidai maryam na shigowa falon daga waje, bata tsaya ba
tai ciki gurin maji.




ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU

IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,,,,,


IDAN KIN KARANTA KIKA TURAWA WANDA BAI BIYA BA ALLAH NE SHEDAN HAKA MUNA BINKI
BASHI,,,,


O lala ka kai mara mutunci sadauki ka gwada min baka da tarbiya yau, dana so nace
sai na bi ra,ayin Fatima akan wanan zance amma yanzu tunda haka ne abin bari kaji
indai har ni ce na haife ka ko bana raye sai ka auri Fatima.
Kuma idan ka sake ta

55 / 92