Author : Zainab Idris Makawa Seenabu Category : Complete Novels
kanta ai bataki abinda Allah ya, kawo mata,ba.
Maji aini wallahi yadda,naga,kunayi a,gidan nan bani ba,auren mai mata,kuma.
Tsuki uwar tayi tace tunda,kece Alkah basai ki zabawa kanki abinda kike so ba
mugani.
Nan dai mukai tahira,akan Kabir da iyalin shi dakuma inda yake aikin shi.
Washe gari tunda safe muka,tashi da,raba tsaraban mutanen kaduna ashe dankalin
Iris ya,sayo mai yawa inaga,buhu guda ne da,manjan miya,wa kowan su saida safe
mukaita kasawa,aka kaiwa kowa nata,kason suka,karba,suna,godiya cikin basarwa.
Maji tana da,wanan halin komai kankantan abu sai ta,rabashi tabawa kowa agidan
sai dai in abin ya tsaya,wamu, yaran tane kawai.
Bai shigo gida,ba,sai misalin sha,dayan rana,lokacin mun fita,zuwa gidan wata
kawar Amira da,matar yayanta ta haihu.
Maji kawai ya,samu a part din tana,zaune tana, gyara,tasbahan ta,daya,tsinke
ya,shigo.
Su gaisa take tambayan shi sai a lokacin ke nan yatashi ko yace Maji kin san na
kwaso gajiya shiyasa da,muka dawo sallah na,kara kwantawa.
Yace ina yaranan suka,tafi ne ina,son a danyi min aiki ne kadan wani magani wani
mutum ya bani na,hausa nake son su dafa min.
Sun fita,zuwa gidan kawar Amirah yanzun nan amma,aiba jimawa zasuyi ba a can din.
Shiru yayi sai zuwa can kuma yace amma maji wanan yarinyar sai naga kamar
fitsarta, ya,fara yawa fa?
Maji tace wake nan kuma ? duk da tagane wa yake nufi din.
Yace wanan bakuwar yarinyar taki mana,
Wa wai Fatima kakw nufi kowa dai?
Ita din ke nan don ban san sunan taba ni.
Fitsaran may tai maka,ko don ta,ceci rayuwanka da,halakan shan kwayoyin
data,kwashe a,dakin ka shine fitsaran da,kake gani tana dashi.
Kai haba Maji ni ba nufina,ke nan ba,wallahi amma ki duba,yadda,take
waya,da,namiji a gaban mutane babu kunya a,idon ta.
Au to idan batai waya da mai sonta,ba,dakai zatayi ke nan ko?
Koko anan zan tabbata,dasu basu aure su a,rayuwan su.
Kai ni Maji ba haka,nake nufi ba,fa kawai dai ina gudun kada ta bata,sauran yaran
nan ne kawai da irin fitsaran ta.
Ita Fatima ce zata bata yaran ko kai dakw abin kunya a gaban su suna,kallo
kuma,babu yadda zanyi dakai.
Akwai fitsaran daya,fi yau da,girmanka,ana ganin ka a cikin maye babba da,yaro
ana min dariya.
Dukar da,kan shi yayi kasa yana,dayasanin maganan dayayi a,lokacin daya sani
kawai ya dauke matakin daya kudurta a,rayuwan shi final.
Nan tace gaba da,fada mai maganganu masu tsuma zuciya na irin zabar mata da
mutuncin ta,da,yakeyi ga idon mutanen duniya.
Kanshi na,duke sai tafasa,zuciyar shi takeyi yarasa irin son da Maji takewa wanan
baren yarinyar haka wai.
Wani irin zafin rai yakeji a lokacin tankar aradu ce ta,sauka,mashi a kirjin shi
duk sanyin AC dake ratsa falon hakan bai hanashi zufa ba .
Muna,shigowa gidan da murnan mu yanayin da,muka,gan su a ciki sai da ya,tayar
muna da hankalin mu.
Suna gaida shi ya,dago idon shi da,suka kada,sukai mashi ja kamar garwashin wuta
ya amsa masu.
May yafaru kuma,yaya Amira take tambayan shi tare da,duban fuskan uwar su dake
zaune tana abinda takeyi.
Yace babu komai Amirah kaina,ke ciwo bari naje nasha,magani dakina.
Yana,fita Amira ta juya, gurin maji tana tambayanta da,cewa anyi wani abin ne
kuma,Maji ?
Shi dai ya,sani inji maji gaskiyane baiso k8n san da,anyi mai fada,sai ya,koma
kamar wani namijin zaki dashi.
Shiko yana fita gidan sashen shi ya nufa yafada kan katifan shi yai lamo dashi
kamar wanda,yake barci,sai dai ba barcin yake ba .
Damuwa ce ke damun shi na baisan abinda zaiyi ya,farautawa uwar shi rai yaji
dadin ta,ba.
A hankali wasu siraran hawaye ke zubo mashi yasan Maji tana,da,gaskiya don yau ba
mai son cikin dubu ace nashi ne ya lalace.
Ya juya,yana,cewa,wayyo ni wanan rayuwan may nayi rayuwana,ya,koma,haka,alokaci
guda.
Ba dadi ga,uwana,ba,dadi ga yan uwana,haka ma wasu al,umman garin danake tare
dasu ada can baya.
Shi dai yasan yayi iyawayin shi akan ya,daina wanan harkan amma,sai yayi kamar
ya,bari sai kuma,ya,tsunci kan shi dakara komawa gasha kuma.
Ya Allah ka kawo min agaji cikin wanan halin rayuwan da nake ciki.
Ai hakkuri da,wanan bayawa yau nagode da,bani lokacin ku da kukeyi kullun Allah
yasa,mu gama,da duniya lafiya yan uwa
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,,,
A LOKACIN MU KE,,,,,
Yanzu al,amarin Aliyu yakai har gidaje masu sayen ruwan pure water shi suke aiken
shi.
Ko kuma,su aike shi dakunan su na,gwauraye yakai masu abu ko ya dauko masu idan
ya dawo su dan yi mashi dan ihi sani na kudi ko wani dan abin kwadai.
Uwaye lokaci muke yanzu da,ba,yarinya mace ce kawai zaka,nisanta tata irin wa yan
nan abubuwan ba har da,namiji idan kina dashi dole idon ki yana a,kan shi tun dai
in ya fara shiga adolarcent year din shi na,balaga.
To yanzun ma yakai ko yaro baikai wanan shekarun ba,yawon yara,yai yawa don sun
san komai na,rayuwa,da birni da kauye.
Maria ba abinda ya damay ta binciken al,amarin dan ta sai alfahari take Allah ya
hore mata da mai hazaka ga kan talla gare shi yana da sa,an samun ciniki sosai.
Bata kula da cewa wani lokaci idan yadawo baya damuwa da cin abincin gida sai dai
yace mata ai ya koshi.
Daga cikin masu aiken shi a kwai wani matashi anace dashi sisko don irin wankan
da yakeyi na matasan zamani.
Amma shi ba ruwan shi da yan mata sai dai yawan son wasa da yara musan man maza.
Haka yasa sisko ya ke son Aliyu sosai a rayuwan shi don yana yawan ba yaron kudi
ya sayo mai abu idan ya dawo da canji ko nawa ne sai yace ya barshi kawai.
Haka yasa har Allah Allah Aliyu yake da,sisko yafito majalisar su hira idan bai
gan shi ba ya kafa tanbayan yau sisko bai fito bane wai.
Shiko idan ya fito ya,shiga wasa da yaron ke nan yana dan matsan shi cikin jikin
shi.
Har sai yagaji tace yaje ta sayo masu wani abu daga cikin kayan zaki ya dauki
rabi ya,ba yaron rabi tace ya,dauka duka.
Su kuma mutanen dake zama,gurin basu damu da saka masu ido ba,su dai kawai suna
ganin tasu ce tazo daya,kawai kamar yadda,jin mutane kan hadu.
Rana Sisko bai fito ba har kwana,biyu don haka Aliyu ya matsa,har saida,akai
mashi kwatancen gidan su Sisko din.
Yana zuwa,ya,samay shi a dakin da,yake haya,daga wajen wani gidan haya kasancewar
shi gwaro yake daga,dakin kofan gida.
Kwance yake dakin rubb da ciki yana kallon wani film a tv dakin shi,
Yaron ya dan tsaya daga,waje yai sallama ya gane muryan shi yake cewa,a,a Aliyu
mai pure water shigo mana.
Waya gwada ma gidana yaron yace tambaya nayi aka nuna min ance baka da lafiya
shine nazo dubaka.
Yace wa yaron ya zauna su nan zaune yana dan mashi wasa ne yake cewa ya ya karbi
kudi ya sayo masu cock su sha da maltina.
Yaron ya,sayo suna,sha,suna hira yake tambayan shi ruwan nawa ya,dauko yace mai
ta,dari uku ce yaciro dari uku ya,bashi yana cewa, idan baka,son talla tunda
kaga,dakina,sai ka,dinga,zuwa muna,kallo sai na,saye ma,ruwan ko.
Cikin jin dadi Aliyu ya,karbi kudin yafita yana godiya tun daga wanan ranan take
zuwa gurin Sisko don yasan lokacin da yake gida.
****** ********* ******
Raiha yanzu bata shayin kowa don ta riga ta bushe fitilar ta ko, a wani yammaci
sun shirya da Nura zasu wani bukin wata kawar Nura din a wani unguwa.
Acika an yi yawa gurin taron ida shahararun yan mata ke gwada kwalliyan su.
An fara program din ne Raiha da Nura suka,ratso ta gaban mutane suka,shigo inda
ake reception din.
Idon mutane caaa a kan su don kwalliyan su gaskiya,ba laifi ko a gidan wa zasu
iya zuwa a hakan.
A hankali suke duban gurin da babu mutane da yawa a saman kujerun zaman dake
gurin .
Can suka hango wata yarinya zaune ita kadai dan nesa da,bango take zaune.
Don haka can suka nufa suma,suka zauna sun so su basar da juna amma,sai take ce
masu sannun ku fa.
Su ma,suka amsa da,yauwa ya,garin dai ta ansa da lafiya kina tare da,wani ne ?
Nura dake gyara zaman ta take tambayan yarinyar da,suka,sama a gurin ita kadai.
No ni kadai ne ina jiran wani ne dama kuma,ba,a barshi ya shigo ba wai baida
pass.
Kallon junan,su sukayi sai kuma,suka,danyi murmushi kawai au shi wanan bukin har
da wani pass ake nunawa cikin sa.
Yarinyar tace wai haka sukace maza ba kowa za,a bari ya shigo ba,wai sai wanda
yake da pass din.
Ok ke kuma,sai kika kyaleshi kawai a,waje ya zauna yana dakonki kawai.
Sister maye naki a cikin, ne wai mu dai ba mun samu wajen zama ba kawai.
Abinda yaba yarinyar mamaki shine yadda haddadun gayu ke zuwa kawo wa su Raiha
gaisuwa har saman table din da suke.
Wasu sukanyi zaton tare da yarinyar suke sai su dan so kutsa kan su gare ta sai
Raiha ta dakatar dasu tana cewa kai wanan bakuwar hannu ce fa,bata san kaiba tukun.
Bayan su mata san masu ji da kan su sun tafi Nura ta juya gurin yarinyar tana cewa
waike ya sunan ki ne.
Ta dago daga dannan wayan da takeyi tana cewa, wani tace ke mana.
Yarinyar tace hmm sunana Nafisa Abubakar ok anan garin kike da zamane ta amsa da
cewa cikin dan dago kanta,
Eh nan ne gari mu muna zama a sama,road ne nida iyayyena.
Nan dai Nura take dan jan ta da fira da,zasu tafine sukai musayan waya.
Nafisa ta riga su fita don haka sai abin hawa yai mata,wuya a lokaci don matasa
na cikin hole din sosai ana ta shan shagali a ciki.
Sunzo wuce wa ne Raiha dake driving ta hango Nafisa tsaye sanan titi sai faman
kallon inda zata samu abin hawa takeyi.
Nurace tace don Allah tsaya mu ragewa wanan yarinyar hanya don yarinyar taimin
wallahi.
Ban gane tai maki ba,damay tai maki ne wai a,a kema kin sani don idan ta,waye ai
zata faso itama.
Nan dai Raiha tai ribas suka tsaya,suka taya mata shiga su sauketa a gida bata
musa ba kodon a ganta da,wa yan nan haddadun gayun abin bajintane ai.
Tashiga suna tafe Nura tana marming din wankan dake tashi a motar tare da dan
dakilar wayan ta da yazama rabin rayuwan mutanen yanzu.
Can ta dago ta juya kadan inda Nafisa take zaune komai na yan matan yana burge
ta wallahi don sun matukar wayewa.
May ma,sunan ki kace tace a hankali Nafisa nake , tace ok ban nombanki watara ai
za,ai zumunci ko Nafisa taji dadi dama tana so tana gudun ta zubar da kan tane
garesu.
Nan sukai musayan nomba a tsakanin su inda takirata da nombanta itama tace a
hankali wazan sa don ban san sunan ku ba .
Nura tace a baki bukaci hakan bane mukan ai mun tambayi naki don kin bamu gurin
zama.
Nuratace zaki iya kira na da Nuriya ko Nura ita kuma wanan driver din zaki iya ce
mara Raihanatu.
Wallahi sister zamuyi tsiya dake idan kina bata min suna ba Raihanatu ba yar
iskan banza sunana Raiha kiji baby.
A daidai kofan gidan su da tai masu kwatance suka tsaya da motan su a daidai
lokacin da Bintu ke fitowa daga cikin gidan ita da maryam.
Wani kallon banza suka,watsa masu suka,wuce su nan Nura ke tambaya wanan yaran
yan gidan nan ne naga sun wani hade rai da,suka gan mu mana.
Kyale su yan kishiyane bakin ciki suke kawai dashi kuma zasu mutu yan hassada
kawai.
Sukai sallama ta shiga gida suka,wuce sai sautin kida ke tashi daga motan su.
Bayan motan sadauki dake fitowa yagani tare da,bin Nafisa da harara ta make gefe
ya fice abinshi.
Tana,shiga ciki take cewa,uwarta ni ban san may naiwa wanan dan mayen ba,sai ya
wani kama hararana.
Da,sauri uwar ke cewa wa sadauki wallahi ahir din shi dake bari ma,na,samu uwar
shi tun yanzu.
Ta mike sai dakin maji sunyi daidai da ita a tsakar gida take cewa Hawau kiwa
danki fada wallahi ya,fita idon Nafisa don ban haifar mashi ita ba.
Shidake da abin fadi tab ga tsuliyane har zaicd zai sakawa wani ido akan may?
Da yake iskancin shi a gidan nan waya hanashi yin abinda yaga dama da zai wani
sa,wa yarinya ido.
Baima da kunya da bai kalli inda Nafisa take ba,sau nawa yake zubar da abin kunya
babu mai kwasa a gidan nan.
Kai bama gidan nan ba,duk gari kowa yasan irin tabargazan dayake mai abin kunya
kala kala har basu faduwa ma.
Tana juya sadauki yana tsaye sai su maryam da Bintu daga gefe Amira tana tsaye
daga kofan su cikin mamaki don ba dama ta tanka saboda mahaifiyar su ta hane su da
hakan.
Maji tace tau yaya in ma sadauki nada abin fadin da har bai faduwa ina dai uban
su daya da Nafisa ni ban san yadda zan raba tsajanin su ba.
Umma tace in baki sani ba,aini na sani don ba kare bin damo yabar ganin dan wanan
abinda yake torokon yana samu ko zai rudeni na kasa daukan wa diyata incin ta.
Wallahi duk randa yai gigin taba min yarinyar ranan ba kwaya, yaje sha ba ko dan
babule yake sha zai gane kuren shi.
Abin kunya ma hada alaka da irin ku ko barnan suna har yana wani kirarin wai yar
uwan shi ce ita.
Wai may akayi ne Maji ?
Sadauki dake karasowa yake tambayan mahaifiyar tashi cikin bacin rai.
Hannu kawai Maji ta daga mashi tace babu ruwanka bari ta fada min abindake ranta
dama,ba yau ba take dashi.
Kada ki min rashin kunya kan wanan tabararen dan naki mara mutunci wanda ya zama
abin nune ga mutane.
Ina fatan Allah ya,shirye shi dashi da,duk wani mai irin halin shi ma.
Daga,baya ke nan bayan an kasa,ba,yaro tarbiya,tun farko sai yanzune za,a roki
Allah kuma.
Ta,wuce a fusace tana fadin wallahi shege ka,fasa a gidan nan ni daku marasa
mutunci kawai masu abinfadi lodi lodi kawai.
Daki suka,shige gaba dayan su suna fadin wai may kuma yafaru yanzu yanzu ne
wai ?
Maimakon uwar tai magana,sai kawai ta,fashe da kuka mai tsuma zuciyan duk wanda
ke kusa a lokacin.
Sadauki yace wai maji don Allah may yajawo wanan cin mutuncin ne haka wai?
Kai ma ,
Wazai ja min in bakai ba mai abin fadi lodilodin da akace aiba karya aka fadi ba
ba a fadin ne ko yaushe.
May yakai ka ga yarta wata yar tata kuma ya tambaya da sauri don bai san kan
wanda ake zance ba.
Maji tace Nafisa mana,
May naiwa Nafisa kuma ya tambaya a cikin mamaki?
Ai duk abinda kai mata ka,sani tunda baka rabuwa da yarta bayan kasan gorin da
zai biyo min baya.
Wallahi azeemun ban cewa Nafisa kala ba kuma Allah ne shedun hakan wallahi.
Koma dai maye kaka sani kaita hi kana jamin gorin da banda baki akan shi.
Mamaki takaici, bakin ciki suka rufe mai zuciya sai muryan Bintu sukaji tana cewa
aiko kowa nada abin fadi don itama ai ta haifi yar iska.
Ranan ai ganin Nafisa nayi kwance saman jikin namiji a mota shiba iskanci bane.
Ke Fatima kada kiwa yar uwar ki sheri don ta bata min rai don sheri kare ne mai
shi yake bi, don haka ki bari.
Haka Allah yaso zamana acikin su don haka sai kowa yayi hakkuri.
Da,wanan bai fitar da kanshi daban acikin halin yan uwa ba da duk ban ga hakan
ba.
Ta mike zuwa ciki ranta a bace mata don zafin maganan da aka,fada mata bata
da,bakin mayarwa.
****** ********* ******
Wanan magana wasa wasa saida yakai maji kwace don tun lokacin da akayi shi Maji
bata,kara lafiya,ba a jikin ta haka ta koma,sukuku don zancen Umma yana,gasa mata
zuciyar ta sosai.
Bayan kamar sati da maganan zazzabin Maji ya tsananta ranan kwana mukayi ba muyi
barci ba ,
Gashi sadauki baya gari yai tafiya Baba ma bai nan ya tafi kasar Niger state
zancen noman shi.
Nace wa su Amira gaskiya ya kamata da,safe muje asibiti don bazamu zauna da ciwo
ba haka a gida.
Amma sai Amirah take ce min wai mu dai bari Baba ya,dawo tukun muji mai zaice.
Da,asuba nazo tayar da ita tai sallah naga irin yadda take numfashi yana fita
dai,dai.
Nace a raina kai wallahi nikan asibiti zamu da safe don in mun biye mata zata
halaka a daki kwance sai paracetamol muke dirka mata.
Muna idar da,sallah Na samu Amira a kwance, nake ce mata zan fita na nemo mota
idan gari yadan haska muje asibiti da mama.
Da wani mota zaku kin dai san babu mota yanzu a gida dashi akewa baba aikin gonan
shi.
Nace ai akwai na haya ko?.
Ta zaci zance kawai nakeyi nafita ina mamakin hali irin na su Amira halin ko
inkula da sukeyi uwar mutum ba lafiya amma su kamar ko a jikin su.
Gari na dan haske na,saka hijjab dina nafita daga gidan sai bakin titi nai sa,a
na samu mai adaidaita sahu irin masuyin sakko gurin neman kudi.
Muka,shirya dashi nace ya kaimu asibitin koyarwa ta gawon nama, watau teaching
hospital.
Na leka dakin su Amira suna,barcin su hankali a kwance na koma gurin Maji na samu
sai nishi take guda, guda.
Cikin matsanancin tsoro da,firgici nace mama tashi muje asibiti aduba,ki.
Batai min mussuba kamar yadda na,zata, don haka na,dauki hijjab na,saka mata tare
da son mu fita .
Cikin karfin hali take ce min, dauko jakata akwai kudi a ciki mu tafi dashi kada
muje mu wulakan ta.
Har muka fita daga gidan kamar babu mutane kowa na,dakin shi rufe na,sayawa su
Amirah kofa muka fita daga gidan.
Ban taba zuwa asibitin ba amma haka na daure muka shiga don ba wani nisa ne sosai
a tsakanin mu ba.
Munyi sa,a don sanmakon