Advertisements
Chapter 28 Reading A Lokacin Mu Ke by Zainab Idris Makawa Seenabu BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

A Lokacin Mu Ke by Zainab Idris Makawa Seenabu

Author :  Zainab Idris Makawa Seenabu Category :  Complete Novels

Chapter   28 / 92

81K to 84K   out of 275.8K words

maijikin da kuma yadda ta
kara ji.
Baba yace, ai hjy masa yar ki zamanta a gurin mu yai amfani nan ya shiga yaba
kokarin da nake masu a gidan.
Gwago tace ai Bintu yatinyace maihankali saidai kuma gata abin tausayi don rashin
jin dadin rayuwan da ta tashi ciki.
Sadauki yashigo dakin rugumay da wasu kayan bukatun da yasayo amma gwago sai
faman ba su Alhaji labarin rayuwana da irin wahalan danasha a gurin uwar riko na
har yakai Baba na da kan shi yace azo dani birni wurinta ko zan samu sassauci a
rayuwana.
Mamakin gwagona dake ta zuba yake ta zage sai faman yabon wanan yar nata mara
kunya take haka a gaban mutane.
Nan dai yake tambayan maji ya jikin nata shine ya katse gwagona yake cewa ko
likitan ya shigo da rana dubani idan baizo ba sai ya shiga gurin su.
Mama tace ai shigowan shi biyu yau yana tambayan ka nace ka tafi gida.
Ya mike yana fadin bari na duba ko yana office din shi inda ya mike zuwa wurin
likitan.
Ya samu likita a office din shi bayan sun gaisa yake fada mashi yadda maji ta
samu sauki fiye da yadda suke tsanmani yace kuma gaskiya wanan yarinyar tana kokari
sosai wallahi.
Yace a ran shi kai may yasa wanan manyar yarinyar kowa dai yabonta yake ne haka
yar kauye kawai.
Ya daiji dadin yadda likita tabashi bayanin kan mahaifiyar shi. Don ko ba komai
yanzu hankalin shi ya dan kwanta ai.
Ya koma dakin har yanzu Baba yana ciki suna hira da gwagona sai Maji dakan dan
jefa masu baki jefi jefi.
Bai so haka,ba don hutu akace Maji ta samu ba yawan surutu ba gashi gwago tana
sata magana kuma.
Ga mamakin shi sai yaga Maji ma ta kara sakewa sosai akan baya don yinin da
sukayi da gwago suna da surutu batai yawan kwanciyar da takeyi ba ranan.
Da,ya,dawo da yamma gwago take cewa ita anan zata zauna da Maji sai dai ni na
koma gida.
Yasan idan na koma,akwai matsala don gwago jikinta ya yi nauyi bazata iya abinda
nakeyi ba kamar ni.
Yace ai ba matsala kubarta a,nan don koda ana son yin wani abu sai tai maku.
Haka muka zauna tun ranan da gwagona dake kawar wa maji da damuwanta.
Sarai Maji ta samu lafiya sosai yanzu har ita da kanta take bukatan sallama amma
sadauki ya hada,baki da likita a barta har zuwa lokacin da sukace sunan son su
sallamay ta.
Bayan na,wanke yan kayan da muke amfani dasu a,sibitin ne sai na fito waje na
zauna don nasha iska don zama ciki ya isheni.
A nan inda nake zaune ya samay ni yake tambayana barci sukeyi ne dana fito nace
mashi eh shiyasa nafito don kada na tayar da su.
Nai mamaki danaga yasa hankici daga gefena ya zauna wayan shi tai ruri ya dauka.
Magana sukeyi da wani akan zasu fita kasan waje wasa amma yace bazai samu zuwa ba
don yana jinyar mahaifiyar shi asibiti.
Mutumin yake ce mashi da ya daure su fita don akwai kudi da yawa a wanan wasan da
zasufita yi yace gaskiya sai mamana taji sauki zan iya fita wani wasa sai yakashe
wayan nashi baijira mai mutumin zai fadi ba.
Yana kashe wayan ya furzu da iska daga bakin shi tare da dukar da kanshi saman
cinyar kafar shi kamar wanda damuwa ta dama.
Tausayi ya bani a lokacin saidai shi ba abin tausayi ba ne don duk wanan halin da
mama take ciki shine sanadin hakan ai.
Ban san ya akayi ba sai ji nayi ina cewa yaya sadauki don Allah kayi hakkuri da
abinda zan fada maka bawai nakai na fadi bane amma dole tasa zan fada ma koda
bazakai amfani dashi ba.
Kan shi ya dago yana kallona cikin mamaki tare da kura min ido, nikuma banji
tsoron shi ba naci gaba da cewa.
Ba tare da fargaba,ba nace why baka tausayin kan ka dana mahaifiyar ka?
Nace yaya wanan ciwon ban fadawa kowa ba,kaine silar haka ga mama sanadin irin
rayuwan da kakeyi yasa mama cikin waban halin.
Idan dare yayi mama bata barci ko yaushe tana kai kukanta ga Allah akan
al,amarinka.
Amma kuma,,,
Sainai shiru na kasa,karasa abinda zan fadi yace amma kuma may fa.
Nace a hankali yaya sai naga kamar baka sani ba kai don kullun ba batun dainawa
kakeyi ba sai kara nausa,kanka kake a cikin wanan harkan ta,shaye shaye
kishiyoyinta suna fada maganan banza wanda ke saka,zurciyar ta,kara,fadawa cikin
halaka.
Shiru nayi kamar yadda shima,yai shiru nace yau abin bakin cikine ace duk yawan
gidan nan kaine kawai nata kuma kaine mai jawo masu magana.
Kowa fa yana da nashi illar amma sun boye nasu saikai dake yi afili ake ganin
naka.
Don Allah yaya idan ma,sha zakayi ka tafi can nesa da ita inda ba wanda ya sani
kayi abinka.
Amma da zaka bari gaba daya shine alheri gareka dama kowa naka don nan gaba ba
haka zaka zauna ba.
Kaima iyali zaka tara yau idan yaranka suka taso suka ganka cikin wanan halin
ashe baka ganin tarihi zai iya maimaita kan shi gaba.
Za ai masu gori za aiwa matarka gori za aiwa yan uwan ka gorin hakan.
Shi wanan abin an san jarabta ne daga Allah amma kuma sai bawa yayi kokarin
nisanta kan shi daga gareshi don gudun zama mujiya a cikin al,umma .
Baiwa arziki yaya duk Allah yai maka kamarya da kanka abin alfahari yadda ko wace
uwa zataji dadin yin alfahari da zurian ta.
Nace amma,,,,,
Yace ke dakata haka ya isheni na kuma gode da kika kalli idona kika fada min
gaskiyan abinda babu wani mahalukin da ya taba tarona ya fada min irin haka.
Nasan kinyi kokari yadda kika kalli idona yau kika fada min damuwarku akaina
wanda yan uwana dangina abokaina ba wanda zai iya fada min shi.
Koke nasan saida kika shirya fada min don naga saida babu kowa a tare damu kikai
min wanan magana ko haka na gode insha Allahu nima ina kokarin ganin na daina don
bayanin da likita yai min a officer din shi nasan zancen da Umma taiwa majine last
week ya hefata cikin wanan halin.
Da sauri nace ashe kaima ka sani yaya mikewa yayi yanackakabe wandon shi yace
tundani ba mutum bane yaya zan sani.
Ya sakai ya wuce ya barni zaune a gurin take naji kamar ancire min wani dutse a
zuciyana nace a raina koba komai dai na samu ya saurareni dole ne kuma daga cikin
zance na yai amfani da wani yai mashi tasiri aran shi.
Ina gurin a zaune yafito hakan yasani sanin har lokacin barci sukeyi basu tashi
ba.
Yana isowa inda nake yake cewa ni zan tafi idan sun farka ki fada masu cewa nazo
sai na dawo anjima.
Yatafi abin shi nabi bayan shi da kallo ga mutum har mutum amma kuma babu shedun
alheri tare dashi.



ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU

IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKK8N WASU PLEASE,,,,,,


A LOKACIN MU KE,,,,,,,,,,,


An sallamo mu daga asibiti bayan gwaje gwajen da akayi kan mama an tabbatar da ta
samu lafiya yanzu sosai,
Sai dai likita ya kara jaddada muna cewa a guje bata mata rayuwanta, wanan kalamin
na likita a gaban kowa akayi shi.
Duk yaran mama suna kusa haka yaya sadauki yakoso su zuwa gida motat tashi bata
daukan mu duka don haka ni da maryam muka hawo Nepep zuwa gida da sauran kayan mu.
A kofan gida muna sauka na hango yaya Imirana da wata yarinya yar makwabtar mu ya
rike mata hannu yana wasa da ita.
Kawar da kaina nayi tankatmr ban ganshi ba amma da yake baida zuciya muna kawowa
kusa sai cewa yayi adon gari kun dawo.
Yaya mune kuma adon gari yau inji maryam yai dariya yace inbada abinki maryam ai
yan mata adon gari ne ko?
Wanan yarinyar da Maji zata ban ita aida na more wallahi ta juya tana wa Bintu
yace ita fa.
Ai babban adon garice wanan tun dai in ta samu guri zakiga ta baje ne kwana biyi
lokacin caji ya fara daukan ta.
Nace ba adon gari ba adon dawa mara mutunci kawai, maryam tace ke Bintu yayan
nawa kike zagi a gabana yanzu zamuyi fada kuwa.
Ban tsaya basu amsa ba na kwashi kaya zuwa cikin gida, ban san yana tsaye ba
jikin motanshi sai da nazo shigewa na gan shi a tsaye ya sha bakin glass a idon
shi.
Ni dai na,shige yabini da harara kawai, tun kan nashigo nake jin hayaniyan yan
gidan ga kida na tashi dakin Umma.
Haka yasani sanin Nafisa tana gida a lokacin don idan tana na zakaji sauti yana
tashi a dakin su.
Na samu su mama da gwagona zaune a falo nan na zube kayan suna min kun iso nace
eh.
Nazauna ina cewa wai Allah mun gode ma, jiki dan tafiyan nan kikewa wai inji
Amirah.
Kafin nai magana cikin muryan mara lafiya mama tace tunda baki san kwana rayen da
takeyi akaina ba ai zaki fada mata hakan.
Amirah tace cikin make murya maji tare fa muke kwana da Bintu don dai na daina
kwana biyu kawai.
Kudai kuka sani ace uwar mutum na asibiti amma ku har kunji dadin kwana a gida.
Ashe badon Allah ya kawomin wanan yarinyar ba sai dai na karata can ni kadai.
Gwagona tace a,a haba hjy ai bazasuyi haka don dai sunga ita din tana masu kara
ne kada su raina mata shiyasa.
Mai masa bari yaran nan ban san irin su ba kodan sunga su kadaine min suke min
wanan halin ban sani ba.
Amirah ta tashi tashige daki tai fushi da maganan mama, nice ma na tashi nabi
bayan ta har zan shiga gwagona ke cewa dawo mana ki kwashe kayan zuwa ciki kada a
barsu nan watse.
Maji tace ai kinga abinda nake fadi din waya fara dawowa cikin su ba ita ba amma
batai azancin ta kwashe ba.
Suna ganin abinda sauran yaran gidan keyi sun zaci alheri ne basu san cewa suma
gidan wani zasuba.
Idan kaje gidan mutane kace kai baka iya motsa jikinka kai komai sai dai ai maka
aiko akwai aiki babba.
Da sannu za,a koya masu tunda basu saba da hakan ba tun farko amma ai zasuyi
insha Allahu .
Allah dai ya kyauta mai masa yaran nan halin su sai su wallahi basu san ciwon kan
su ba.
Koma irin yadda ake min a gidan su baya damun su dawasu ne ai basai an fada masu
abinda zasuyi ba wanda ya dace.
Kiyi hakkuri hajiya kowa da ir8n halin shi amma bari zasuyi idan ana lurar dasu.
Na samu Amira a daki tana, waya nashigo dakin , tabini da kallo tace yanzu duk
kokarin da nake wai maji bata gani.
Nace Anty uwa uwace duk abinda suka,fada muna gyara ne a garemu mu godewa Allah
da ya barmu dasu a raye.
Wanda baida uwa fa a duniya bai kuma damai kwabamashi fa.
For god sake may ye banyi a gidan nan ne wai amma kulun maji tace banyi daidai
ba.
Fadan iyayye fa takine gare mu anty tun da tace haka yanzu da ta dawo gida sai ki
matsa ki kula da ita yadda zata ji dadin ki.
Kallo na tayi kamar zatai magana sai kuma tai shiru kawai nikan na koma dakin mu
na,shiga wanka don duk warin asibiti nake jin ina yi a jikina.
Bayan nafito ne na tara duk kayan da mukai amfani dashi asibiti na wanke su tas
sannan nadawo falo na zauna sai naga Amirah tafito.
Taje gurin mama tace a kawo maki abinci ki dan ci ko da kadan ne maji don rana
yayi lokacin shan maganin ki ya kusa.
Uwar taji dadin haka sosai don ta kasa boye farincikin ta tace tau akawo min
Amirah.
Ta hado ta kawo mata har gaban ta tare da ruwa da maganin gaba daya.
Maji tace mata na gode Allah yai maku albarka da haka kuke min wa zaiji mu daku.
Gwagona tace tau gashi dai uwata ta gyara yanzu ai shiya fadan yake da dadi ga
yaro don ya gyara kuskuren shi.
Tajuya inda nake tana cewa ke kuma Bintu wallahi ki bar yi wa maji komai daga
yau kibarni ni zan mata.
Maryam tace wallahi saidai a raba amma ban yarda nima ai ina son albarkan .
Nan dai aka wasance zance ana dariya tajuyo tana daga min gira alaman godiya nima
hannu na daga mata alaman komai ya wuce.

****** ********* ******
Kabir yazo duban jikin maji da ya shigo kauyen su kamar yadda ya saba duk karshen
wata da yake zuwa.
Kabir ya iso gidan namu amma bai shiga ciki ba, ya tsaya daga kofan gida inda ya
zauna cikin motar shi.
Yana saye da kananan kaya amma dinkin shadda ce akai mashi karamin dinki dashi.
Sai kamshin turare yakeyi ajikin shi yai matukar kyau dashi sai annuri yake .
Waya ya buga min cewa gashi ya iso a kofan gidan da nai mashi kwatance.
Na fito acikin hijjab dina duk da nasha kwaliya daga ciki amma na rufe jikina da
hijjab.
Waya yake amma hankalin shi yana a kaina yana kallon yadda nake takona ina dan
waige don ban sheda motar shi ba da yazo da ita.
Saida yai min horn nagane cewa shine acan gefe daya zaune cikin motar shi.
Ina isowa inda yake ya kashe wayan shi yana min wani kallo can kasan idon shi.
Na dan duka kadan ina cewa barka da isowa ya hanya ya mutanen gida suke?
Yace duk suna lafiya suna gaida ke amma uwargida tace tana fushi dake wai baki
taba kiranta kun gaisa ba.
Nayi murmushi gami da cewa karufa min asiri don Allah, yaya ina ni ina kiran ta
tace banda kunya.
Yace aiko gara ki daina jin komai don Haulatu tace bata dauke ki kishiya ba a
matsayin yar uwa da kuka fito shiya daya ta dauke ki.
Nai murmushi kawai tare da cewa Allah sarki aiko na gode Allah ya bamu hakkurin
zama da junan mu.
Ya amsa cikin jin dadi da fadin amin my love, har kin sa naji wani sanyi a,raina
da na ga wanan gidan da kike har na fara fargaban kada wani ya kwace min ke anan.
Nace haba yayana ai kyau alkawari cikawa da bazanyi ba tun farko baxaka ga ma
fuskana ba ai har mukai haka dakai.
Yace nako gode da,wanan karamawan da akai mun yanzun hankalina ya kwanta sosai da
jin kala man ki.
Nan muka dan dauki lokacin muna hira dashi sai dariya yake bani na yadda zamu
zauna a gidan shi.
Tun daga nesa na hango motar shi tafe da karfi yazo ya park dan nesa kadan damu.
Tun karyo kwanan shi ya hango su mamaki yake irin yadda ya hangota tana dariya
abinda bai taba ganin tanayi ba a rayuwan ta.
Kallon wanda suke tare yake inda yaga maishi ai ba yaro bane ya ma girmi duk yan
gidan su balle shi.
Amma shine wanan yarinyar ta tsaya haka har take wasan baki a gaban shi koma may
wanan zai iya fadawa budurwa har taji dadi haka.
Ko dai dama da wanan tsohon take waya tana wani kashe murya a gaban mutane ba
kunya saboda wanan tsamuraren mutumin.
Wani ir8n haushi da takaicin yarinyar ne da baitaba jin irin shi ba ya kama shi.
Ya fito daga motan shi lokacin Kabir ke tambayana waye shi nace mashi yayanane na
nan gidan.
Don haka yafuto suka gaisa sama sama dashi kamar mai sauri ya shige abinshi tare
da gaura marfin motar shi.
Kabir ya juyo inda nake yace tau ikon Allah nace rabu dashi haka yake hutsune
dama shi baida mutunci.
Dakin shi yanufa yana jin wani gumin bacin rai yana fetso mashi ya bude dakin shi
ya shige hakana.
Mun dan kara dauka lokaci yai min sallama tare da mika sakon shi gurin mamana da
bata da lafiya.
Nan yake ce min shi abinda yakawo ma yaji kunya don wanan gidan abin yai kadan
wallahi.
Cikin mamaki nace haba aiba komai wake raina alheri sai mara godiyan Allah kawai.
Nan nasamo yara suka shiga dashi nace sukai dakin maman UF don sunfi gane ma
hakan.
Mukai sallama yatafi sai banji dadin hakan ba don ban so mu rabi dashi ba don jin
dadin dan kasancewar mu na dan lokaci a tare.
Har na shigo gida yana tsaye a kofan shi kamar may waya take yaji zuciyar shi na
azazzalar shi tankat ya shake a lokacin.
Can kuma yai tsuki yace ina ma ruwana da yar iska komay zatayi taje tayi mana may
ye hadina da itama dahar na damu kaina.
Sai zuwa dan wani lokaci ya shigo gidan inda ya samu kayan da Kabir ya kawo muna
a falon mama.
Ya shigo wani iri dashi idon shi akan kayan duk da kayan ba laifi amma sai yaga
ai duk komatsen banza ne kawai.
Ya samu guri ya zauna yana fadin wanan kayan kuma fa haka?
Amirah tace surukin kane yazo yaya mai neman Bintu shi yazo yakawo wa Maji na
dubiya da Allah sawaka.
Ance mai mu bamu iya saye ne sai ya kwaso muna wani tarkace haka ba kyau gani.
Ko an fada mai mu makwadaita,,,,,
Kai don Allah ya isa kai wani irin suruki ne kuma maimakon kasa albarka sai kuma
ka fara fadin maganan banza kawai don Allah kwashe min su zuwa ciki kinji maryam.
Maryam ta mike tana fadin ai yaya an fara kawo maku tarkace ke nan tun da maji ta
tara zuka zukan yan mata haka har uku a dakin ta.
Amirah tace wanan kan nima nawa yana tafe sai aka sa dariya kawai gaba daya maji
tace Allah kawo shi lafiya mugani ni dai naga ta ya ta saura naku din.
Wallahi Maji kina bata yaran nan haka fa na

28 / 92