Author : Zainab Idris Makawa Seenabu Category : Complete Novels
sai gobe ba dip
naji ya kashe wayan tashi.
Tun ranan bai kara kirana ba nima dai haka ban kara kiran nashi ba har lokacin.
Maryam ce ta ishe ni da korafi inda ta matsa min akan sai nakirashi a gaban ta
kokuma wallahi mu bata da ita.
Ba yadda na iya dole na dauko wayana daga cikin hand bag dina na kira wayan na
shi a lokacin kuma shi yana zaune tare da Linda.
Sai ganin kirana yashigo a wayan shi da sauri ya dago kanshi tare da cewa hello,
Nace wa,,alaikum sallam.
Ina wuni yaya ya amsa da lafiya a takaice sai nai shiru maryam dake gefe na ta
kafeni da ido don jin may zan kara fadi kuma.
Jin nai shiru yace min kuna lafiya dai ko?
Lafiya muke na bashi amsa a lokacin naji muryan mace tana tambaya cikin harshen
tiranci da wa yake waya ?
Naji yace mata sister din shi ce .
Lafiya dai ko naga kin kirani yau?
Nace ai kaji matsalar sai ba lafiya zan kiraka dama ni sai anjima kawai.
Dakata sai na tsaya ina sauraren shi yace nasan wani ni yasa ki kirani dole ko?
Nace eh.
Anty maryam ce gata a zaune tace sai nakiraka ko mu bata da ita shiyasa na
kiraka.
Ok
Maryam dake gefe na tace shit ta karbe wayan daga hannuna tace hello yaya ta
damay ni fa da zancen ka shine nace takiraka mana taji lafiyan ka.
Murmushi yayi yace maryam kin san fa yar kauye ce bata san darajan miji ba balle
ta san kiran shi taji lafiyan shi.
Daga inda nake a zaune nace, gara zama da kauyanci da hurda muranen banza ai
muryan mace naji tana magana dakai yanzu.
Dariya magana ta tabashi don ya fahinci nasan kishi ke nan nima don har na kasa
boyewa na fadi a fili.
Yace maryam fada mata Linda ce my wife to be nake tare da ita ba irinta yar kauye
da batasan komai sai kauyanci da rashin kunyan su na yaran kauye.
Haushi naji nace komai kauyanci mu dai mun san darajan kan mu da mutuncin iyayywn
mu dip maryam ta kashe wayan tana fadin.
Kinji halinki ko Bintu ke wanan bakin naki wai bai mutuwane nace cikin fada
wallahi muddin bai daina kirana yar kauye ba bazamu taba shiri dashi ba kinji na
fada maki.
Tace kai Bintu ada kema kice mashi kowa ma kauye ne asalin shi don mu kauyen mu
fa har yanzu babu ko titin mota ba wuta ba ruwa.
Nace nagode anty aiko zai rana kanshi don daya fada zance mai munfi mutane kauyen
tureta ai.
Ranan daga school maryam tace min mu tsaya salloon din dake kusa da school din mu
gyara kan mu baki ba don da wuri muka tashi.
Wanke min akai akayi tare da zuba min kayan kamshin da tazo dasu masu kyau sai
nace a dan gyara min kafana da yatsun hannu na haka akaimin gyara nafito wata yar
birni dani.
Sai da zamu rabu take ce ban sa zamu hadu ba sai zuwa next week amma ina son
ranan Friday don Allah kiyi girki mai dadi ki gyara gida da kanki sosai yadda yaya
zai gane cewa yanzun ke ba bakauya bace don ina sa ran Friday din nan zai shigo
garin suyi waya da yayana yace yana Abuja.
Muka rabu ina shigowa gida Amirah ta kasa boye haushin gyaran da nayi a zuciyar
ta tace sai dai kikare haka Bintu miji kan sai dai kamahi shi.
Murmushi nayi a raina nace kai kodan na kure anty Amira dole nabi shawaran
maryam.
Friday na yi kamar yadda tace sai bina da kallon mamaki Amirah keyi.
Kasa hakkuri tayi tace wa da ni yau wani kuma sheri kike son yi a gidan nan ne
haka ko bakin yan kauyen ku zasu zo ne wai?
Nace anty ashe kin gane bakin kauyan mune zasu zo yau gidan kuma anan zasu kwana
tare da mu.
Na gama komai na koma daki ganin biyar saura nan na bata lokacina gurin gyara
jikina zakace wani gasan gwajin kyau zan tafi a lokaci don har musa kanina saida na
bashi sabbin kayan da na,sayo mai ya saka yai aski irin ta matasa.
Falo muka dawo muka zauna ganin haka yasa Amira fitowa daga daki nasan ta hake
ne taiwa bakina wulakanci a lokacin.
Bamu dade da zama falon ba da kamshi ke tashi cikin shi mukaji ana nocking din
kofan shigowa don a rufe yake musa na tura ya bude kofan.
Yayin da Amirah ta sako idanuwan ta don ganin mai shigowa falon a lokacin don a
shirye take da cin mutunci a ran ta.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,,,
IDAN KUMA K8N BIYA KIKA TURAWA WANDA BAI BIYA NA BARKI GA ALLAH YAR UWA,,,,
A LOKAC8N MUKE,,,
Tun ranan da wanan abin ya shiga a tsakanin mu na kasa sakin jikina a gidan.
Ban yarda mu hadu da yaya sadauki ko da a falo ne ganin na dan samu sauki yau
natshi tunda safe ina son shiga school kasancewa monday ce yau din.
Tsaye nake a bakin zinc na kitchen ina dauraye kayan da akai amfani dashi daren
jiya.
Ga kuma girkin dana dora ina sauri ingamawa kada na makara ko ya futo yasamay ni
ban fita ba.
Jin kaman mutum tsaye a bayana yasani sauri juyowa ina kallon kofa shigowa
kitchen din, .
Gaba nane yai mugun faduwa da ganin shi yana tsaye ya saka hannayen shi biyu ya
raba kofan tsakiya jikin saye da kayan exercise din shi sunyi matukar yi mashi kyau
a jikin shi.
Dan daburcewa nayi daganin shi bansan lokacin da nakai kasa ba a tsorace ina cewa
ina kwana yaya.
Bai amsa ba,sai karasa shigowa daga cikin kitchen din da yayi gaba daya ina
durkushe.
Tsayawa yayi tare da jingina jikin shi da bayan inda nake tsaye da farko yace wa
kike boyewa kwana biyu a gidan nan.
Mikewa nayi don ganin bazai amsa min ga tambayan da ya jefo min kuma lokaci guda.
Fuskewa nayi nace may zan boyewa kuma ni don banda lafiya ne kawai.
Murmushi yayi yace may yasamay ki baki da lafiya kuma?
Turo baki nayi na karasa dauraye plate din dake a hannuna, na juya ji nayi ya
finciko ni tabaya na.
Tsoro ne ta kamani jikina ya dauki rawa a lokaci guda don balain tsoron shi nake
ji yanzu .
Idanuwa na a runtse tare da sauraren abin da zai biyo bayan rikon da yai min a
lokacin.
Hannuwan shi naji saukan su a saman kirjina tare da rankofo kan shi a daidai
wuyana a hankali.
Yana fadin abinda kike min rowan su ke nan gasu yau na kama su a hannuna.
Idona na ritse gam don jin abinda yaya ke min wanda ban taba ma kawo tunen hakan
ba a tsakanin mu.
Cikin wata yar murya nace da kyat don darajan Allah yaya kadai na wanan abin
please ?
Don Allah ka bari kada musa ya shigo ya samay mu a haka please.
Murmushi yayi yace idan yashigo and so what bada matata ya ganin ba.
Kara rintse idanuwa na nayi cikin rashin fahintar abinda yake min a lokaci zafi
ne ko haushi ko ko dadi.
Da karfi na zille daga jikin shi na koma gefe ina mai da numfashi kaina a duke.
Murmushin keta yai min yana cewa matsoraciya kawai yau ina bakin naki yashiga
kuma mai fadar bakat magana.
Idona da yakawo hawaye na dago kai nace don wanan cin zalin da ka dauko yi min a
gidan nan bashi zai sabakina ya mutu ba ai mugu kawai mai ruwa biyu.
Murmushi yayi ganin da nayi ya juyo kamar zai yo kaina na zille akasa tare da
kare fuskana da hanaye na sai naji yai dariya yace ashe bake bace ?
Har ya kao kofa ya juyo ya tsaya yace, kuma idan na kara shigo na samu kin boye
zakiga abinda zan maki gidan nan.
Yana fita na sauke ajiyan zuciya tare da mikewa na karasa abinda nakeyi ina yi
ina kwallon kofa kada ya dawo again.
Sauri sauri nagama komai tare da shiryawa zuwa school don lokacin har dining sai
dana hada komai na fito a cikin hijjab dina kamar kullun.
Naso nafita batare da na,sallamay shi ba sai naga rashin dacewan hakan gareni don
haka na nufi dakin nashi.
A hankali na tura kofan daki da yar sallama a bakina, yana kwance saman gadon shi
yai rigingine fuskan shi na kallon ruffing din dakin nashi.
Daga kofa na tsaya ina fadin zan tafi school, sai na dawo.
Da kyat ya iya dago kanshi idanuwan shi kamar yafara barci ne a hakan.
Kallo na yayi tun daga samana har kasa na sai ya mayar da kan shi yana fadin
akwai mai a motan, nan kuwa nace ranan da na fita last akwai mai a cikin sa sai dai
ban sanar ma yau din nan ba.
Mikewa naga yayi ba tare da yai min magana ba yafita a dakin nima bayan shi nabi
muka fita a tare dashi .
Motan ya bude ya shiga ya tayar da ita ya dan dade a cikin ta yana service din
motan ina tsaye daga gefe ina kallon shi.
Yafito daga cikin motan bayan ya gama warming dinta tare da ce min sai kin dawo
ya juya ya shige gida.
Mun hadu maryam a school duk yadda taso ta zolaye ni taji yadda muka kwasa da
yaya sam naki bada fuskan yin haka.
Dole ta gaji ta kyale ni muka canza hira kan hiran matar yaya Ahmad da akace
sunyi fada har da buge buge har gurin yan sanda sukaje.
Amma kuma sun dawo anshirya kamar basuyi ba nace ai dama irin su irin matan nan
yan duniya ne daidai dasu.
Tace ita kuma matar yaya Imirana ance kazama ce kumai tana dan kurba syrup akai
akai,
Sai dana gama saurare nace wai ubangiji Allah ya kyauta kawai zamuce ga al,amarin
don yanzu abubuwa daban daban lokacin nan da muke cikin ta.
Ba mu dawo gida ba sai yamma lis after six na shigo gidan agajiye dani daki na
shiga na cire hijjab dina na fito kitchen don dora girkin dare.
Misa ne yashigo yana ce min sannu da dawowa yace yanzun ko yaya ya bargidan nan
yana tambayan baki dawo ba.
Nace may zan mashi idan na dawo din sallon son yaiwa mutum muguntan shi dayasaba
kawai.
Kai haba anty yayane kuma mugu ni dai wallahi yana bani shawa wallahi don ba
ruwan shi rayuwan shi akwai sauki sosai.
Murmushi nayi a fili a zuciyata nace baka san komai ba yaro da baka fadi hakan
ba.
A gurguje na hada girki na koma dakin shi dake a hargitse na gyara mashi tare da
wanko bayi na feshe ko ina da kamshi nafito nazo na samu shikafan dana dora ya
tsane na tuka tare da kwashewa.
Kafin a gama kiran magariba na gama hada komai na shige dakina wanka nayi tare da
dauro alwala nafito.
Ban daga ba sai da nai sallah ishai na fito tare da kara feshe falon mu da kamshi
kafin ya shigo gidan.
Na koma na zauna tare gyara jikina wani riga da wando na saka daga cikin kayan
lefe suke English wear ne na gyara gashina da ribon jelae shi ya sako a baya.
Dan karamin gyale na yafa ga kaina na fito falo na samu musa ya shigo nace mai ya
dibi abinci yaci dare ya soma yi.
Ya dabe ya dawo inda muke zaune ya faracin abincin muna hiran mu ta zumunci
labarin rayuwan garin sokoto da ya gani yake bani ina dariya.
Haka yasa bamuji shigowan shi ba sai ganin shi mukayi har ya kawo tsakar falon.
Sannu da dawowa muka fara mashi ya amsa tare da zubewa saman kujera da alaman
daga gurin wasan su na ball ya fito a lokacin.
Sai ya kasance shigan da nayi na takura da zama falon dan wani kallon da naga yai
min ya wani lumshe idanuwan shi.
Can ya bude bakin shi da kyat yace musa ina gani gobe zaka wuce school don an
gama maka shirin komai ko.
Daga ni har musa dago kai mukayi muna kallon shi a cikin kasala yake maganan shi
yace.
Ban san ko akwai wani abinda zaka bukata ba kaje cikin buth din motana ka kwaso
abinda akasoyo ma ka gani idan akwai abinda zaku kara sai ku duba ku gani.
Mikewa musa yayi yafita yabar abincin don dauki sai lokacin na dago kai na kalle
shi ya rike goshin shi da hannun shi daya nace yaya mungode Allah ya saka da ,,,,,,
Hannu ya daga min yace is ok please nima ai kanina ne musa.
Kara cewa angode bai yi magana ba sai mikewan da yayi ya bar falon tunawa nayi
ban hada mai ruwan wanka ba a lokaci da sauri na mike nabi bayan shi.
Na samay shi a tsaye yana kokarin cire kayan jikin shi sallama nayi na shigo ya
bini da kallo kawai.
Bathroom na shige tare da joner mashi heater ruwan zafin da zai yi wanka dashi.
Nafito bayan na matsa mai su maclean da subulun da zai bukata na aje mai a gefe
nafito din.
Nazo zan wuce yana daure da towel iya kugun shi da sauri zan wuce naji ya
finciko ni zuwa jikin shi.
Yar kara nayi nace cikin wata irin murya wayyo yaya please kayi hakkuri don Allah
matse ni yayi gam yana kokarin hada bakin shi da nawa.
Sai kokarin zillewa nake don gaba daya balain tsoron shi yanzu ya cika min zuciya
na don bangane wannan son yawan hada jikin shi da yake son yi dani ba akoda yaushe.
Sosai ya tsayar dani sai tsotson bakina yake cikin wani irin sallo da shi yasan
irin shi.
Kafafuwa na ne naji basu dauka na a lokacin gashi ya cika min baki da harshen shi
ban iya maganan komai a lokacin jikina sai kyarma yake min.
Shi kan shi yaga dama ya sake ni tare da bina da shu,umin dariya yace zamu hadu
dake ai matsoraciya kawai.
Sai dana sai ta kaina a tsaye inda nake tare da bin bayan shi da zai shige
bathroom.
Lokacin ne na kara sheda girman jikin yaya sadauki sosai ashe karfafan mutum ne
haka ban sani ba.
Na samu musa a falon ya kwaso kaya gasu nan birjit a gaban shi.
Jakkuna na kaya guda biyu na hango sai na karasa gurin yace anty kinga abinda
yaya ya sayo min haka.
Nan muka shigo budewa daga kaya sawa takalma uniform sai kayan abinci na
gwagwani da na sha su madara da sauran abubuwan sha.
Kallon kayan nake cikin mamaki don ba karamin kudi ne aka kashe ba gurin sayayyan
wanan kayan masu yawa haka su bucket da kulan da zai ci abinci duk an sayo mashi
man shafi su maclean da sabulun wanki dana wanka da turare.
Musa yace kai yaya I love you wallahi ban ma san irin godiyan da zan mashi ba
idan yafito wallahi.
Murmushi nayi kawai naji dadi kwarai a raina don nuna kaunan da yayi wa dan
kanina haka.
Can yafito cikin wasu yan kananan kaya a jikin shi rigan mai dan karamin hannu
iya hammata sai wando three quater da yasa fari kal dashi sai kamshi ke tashi a
jikin shi.
Direct dining erea ya nufa hakan yasa na mike na nufi gurin tare da daukan flask
na fara zuba mai tuwon shikafa fara da miyan water leaf yaji agushi sosai da nama.
Dan kadan na tsakurawa kaina a plate a shiririce nake ci inda ya zauna ya kwashi
abincin shi sosai.
Sau biyu yake cin abinci a wuni da safe idan ya karya sai kuma da dare wani
lokaci kuma fruits salad kawai zai sha yakan ce wai ina son dirka mai abinci yaci
yai kiba kwana biyu ya kasa yin wasan shi.
Waya yake yi yana kallon yadda nake wasa da abincin dake gabana duk da rashin
yawan da baida shi.
Da ido yai min magana alaman maza na cinye shi na make kafada na alaman banyi,
sai dai ban daina cin da nakeyi ba a yangance.
Mikewa nayi tsam na fara kwasan kayan zuwa kitchen ban fito ba sai da na tsaya
na wanke kayan don na rage yawan aikina da safe.
Na dawo nasamay shi da musa yana gwada mai wasu takardu a hannun shi ashe
takardan addmition ne na makaran tan da zai tafi.
Zama nayi a gefe daya ina satan kallon su duk da hankalina yana gurin tv dake
aiki a lokacin.
Musa ya tatara kayan shi ya kwasa cikin jin dadi zuwa dakin shi tare da muna sai
da safe nasan zai tafi yyakara baje kayan ne yasake kallon su a tsanake.
Shiru falon yayi ba wanda ke magana a cikin mu sai tv dake aiki shi kadai ana ta
watsa turanci ganin ankirashi a wayan hankalin shi ya dauke yasa ni mikewa nabar
falon.
Bathroom na shiga da niyan nakewa sai naga kawai nai wanka na ji dadin kwanciya
kawai nafito na dan shafa mai laushi tare da saka yar rigar barci na dana feshe da
turare, light pink mai dagwari biyu sai dai iya cinya ya tsaya min rigar.
Ina zaune saman gado naji ya turo kofan daki sai dai ya sauya kayan jikin shi
saye yake da wani wando mai laushi iya gwaiwan shi kamar three quarter da rigan shi
mai kama da dinkin banga na maza.
Sau daya na daga kai na na kalle shi na dukar da kai kasa inda nake zaune a dan
stoll din mirror yazo ya zauna tare tare da kura min ido.
Muryan shi naji yana fadin tashi muje mu kwanta tunda ke baki san abinda ya dace
mace taiwa mijin ta ba sai an fada maki.